Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 27 p. 68-p. 69 par. 2
  • Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Sandan Haruna Ya Yi Fure
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Jehobah Ya San Ka Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Girman Kai Yana Kaiwa Ga Kunya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 27 p. 68-p. 69 par. 2
Korah da kuma magoya bayansa sun tsaya a gaban Musa da Haruna

DARASI NA 27

Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya

A lokacin da Isra’ilawa suke yawo a jeji, sai Korah da Dathan da Abiram da kuma wasu mutane 250 suka yi wa Musa taurin kai. Suka ce masa: ‘Ya ishe ka! Me ya sa za ka zama shugabanmu sa’an nan Haruna ya zama babban firist? Jehobah yana tare da dukanmu, ba kai da Haruna kaɗai ba.’ Jehobah bai ji daɗin wannan maganar ba sam domin hakan raini ne a gare shi!

Sai Musa ya gaya wa Korah da mutanen da suka goyi bayansa cewa: ‘Ku zo mazauni gobe kuma ku kawo kaskon turare cike da turare. Jehobah zai nuna mana wanda ya zaɓa.’

Washegari, sai Korah da mutane 250 da suke goyon bayansa suka je suka sami Musa a mazaunin. Suka ƙona turare kamar yadda firistoci suke yi. Sai Jehobah ya gaya wa Musa da Haruna cewa: ‘Ku janye kanku daga Korah da masu goyon bayansa.’

Ko da yake Korah ya je wurin Musa a mazaunin amma Dathan da Abiram da kuma iyalansu sun ƙi zuwa. Sai Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su matsa daga tantin Korah da Dathan da kuma Abiram. Da sauri sai Isra’ilawa suka matsa daga wurin. Amma Dathan da Abiram da kuma iyalansu sun tsaya a wajen tantinsu. Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye su duka! Wuta kuma ta fito daga sama ta ƙone Korah da maza 250 da suka goyi bayansa.

Korah da kuma magoya bayansa sun tsaya a gaban Musa da Haruna

Bayan haka, Jehobah ya gaya wa Musa cewa: ‘Ka karɓi sandar kowane shugaban ƙabilun kuma ka rubuta sunayensu a kan sandunan. Amma a kan sandar ƙabilar Lawi, ka rubuta sunan Haruna a kai. Ka ajiye sandunan a mazauni kuma sandar mutumin da ta fitar da fulawa shi ne wanda na zaɓa.’

Washegari, sai Musa ya kawo sandunan kuma ya nuna wa shugabannin. Sandar Haruna ta fito da fulawa da ’ya’yan itacen almond nunannu. Ta haka ne Jehobah ya nuna musu cewa Haruna ne ya zaɓa ya zama babban firist.

“Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umurnansu.”​—Ibraniyawa 13:​17, Littafi Mai Tsarki

Tambayoyi: Me ya sa Korah da waɗanda suka goyi bayansa suka yi rashin biyayya? Ta yaya muka san cewa Jehobah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist?

Littafin Lissafi 16:1–17:13; 26:​9-11; Zabura 106:​16-18

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba