Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 9/15 pp. 25-29
  • Jehobah Ya San Ka Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya San Ka Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Uba ga Waɗanda Suke da Bangaskiya
  • Yin Imani ga Jehobah Alamar Bangaskiya Ce
  • Bambanci Tsakanin Tawali’u da Fahariya
  • Muna Bukatar Kasancewa da Tawali’u don Yin Biyayya ga Jehobah
  • Jehobah Ya San Waɗanda Suke Nasa
  • Ka Miƙa Kai Da Aminci Ga Ikon Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Sun Yi wa Jehobah Rashin Biyayya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Girman Kai Yana Kaiwa Ga Kunya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 9/15 pp. 25-29

Jehobah Ya San Ka Kuwa?

“Ubangiji ya san waɗanda ke nasa.”—2 TIM. 2:19.

1, 2. (a) Mene ne ya fi muhimmanci ga Yesu? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi tunani a kansu?

WATA rana wani Bafarisi ya tambayi Yesu: “Wace ce babbar doka a cikin Attaurat?” Yesu ya ce masa: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Mat. 22:35-37) Yesu yana ƙaunar Ubansa na samaniya sosai kuma yana nuna hakan ta ayyukansa. Yesu ya kuma mai da hankali ga dangantakarsa da Jehobah, kuma ya nuna hakan ta amincin da ya yi. Saboda haka, gab da mutuwarsa, ya faɗi da tabbaci cewa Allah ya san cewa yana biyayya ga dokokinsa cikin aminci. Da hakan, Yesu ya kasance cikin ƙaunar Jehobah.—Yoh. 15:10.

2 Mutane da yawa a yau suna da’awa cewa suna ƙaunar Allah. Babu shakka, mu ma muna faɗin hakan. Amma akwai wasu muhimman tambayoyi da ya kamata mu yi wa kanmu: ‘Yaya Jehobah yake ɗauka na? Zan iya faɗi cewa Jehobah ya san ni kuma ya amince da ni kuwa? Shin Jehobah ya san ni a matsayin nasa ne?’ (2 Tim. 2:19) Gata ne sosai sanin cewa za mu iya kasancewa da irin wannan dangantaka na kud da kud da Mamallaki duka!

3. Me ya sa wasu suke shakka ko su na Jehobah ne, kuma mene ne zai iya taimaka musu su kawar da irin wannan tunanin?

3 Duk da haka, yana yi wa wasu da suke ƙaunar Jehobah wuya su yi tunani cewa za su iya zama abokan Allah. Wasu suna tunani cewa ba su isa kome a gaban Allah ba. Saboda haka, suna tunanin cewa ba za su iya zama na Jehobah ba. Amma yana da kyau mu san cewa Jehobah ba ya ganin mu hakan! (1 Sam. 16:7) Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci: “Idan kowane mutum yana ƙaunar Allah, wannan mutum sananne ne gare shi.” (1 Kor. 8:3) Ƙaunarka ga Allah dalili ne mai kyau da zai sa ka sanu ga Allah. Ka yi la’akari da wannan: Me ya sa kake karanta wannan mujallar? Me ya sa kake ƙoƙari ka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka da dukan tunaninka da kuma dukan ƙarfinka? Idan ka keɓe kanka ga Allah kuma ka yi baftisma, mene ne ya motsa ka ka yi hakan? Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Jehobah da ke bincika zuciya ne ke jawo mutane wurinsa. (Karanta Haggai 2:7; Yohanna 6:44.) Saboda haka, za ka iya kammala cewa kana bauta wa Jehobah domin ya jawo ka wurinsa. Ba zai taɓa yin watsi da waɗanda ya jawo ba idan sun kasance da aminci a gare shi. Allah yana ɗaukansu da tamani kuma yana ƙaunarsu sosai.—Zab. 94:14.

4. Me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin tunani a kan dangantakarmu da Allah?

4 Da zarar Jehobah ya jawo mu wurinsa, ya kamata mu yi ƙoƙarin kasancewa cikin ƙaunarsa. (Karanta Yahuda 20, 21.) Ka tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa zai yiwu mu bijire ko kuma nisanta kanmu daga Allah. (Ibran. 2:1; 3:12, 13) Alal misali, gab da kalaman da ke 2 Timotawus 2:19, manzo Bulus ya ambata Himinayas da Filitas. Babu shakka waɗannan mutane biyu bayin Jehobah ne a dā, amma daga baya sun bar bin gaskiya. (2 Tim. 2:16-18) Ka kuma tuna cewa a cikin ikilisiyar Galatiya, wasu da suka sanu ga Allah ba su kasance cikin imanin da suke morewa a dā ba. (Gal. 4:9) Ya kamata mu ci gaba da ɗaukan dangantakarmu da Allah da tamani.

5. (a) Mene ne wasu halaye da Allah yake daraja? (b) Waɗanne misalai ne za mu tattauna?

5 Da akwai wasu halaye da Jehobah yake daraja sosai. (Zab. 15:1-5; 1 Bit. 3:4) Biyu cikinsu su ne bangaskiya da kuma tawali’u. Bari mu tattauna misalan mutane biyu da ya nuna yadda waɗannan halayen suka jawo su kusa ga Jehobah. Za mu kuma tattauna game da wani mutum da ya yi tunani cewa ya sanu ga Allah amma ya yi fahariya kuma Jehobah ya ƙi shi. Za mu iya koyon darussa masu kyau daga waɗannan misalan.

Uba ga Waɗanda Suke da Bangaskiya

6. (a) Mene ne Ibrahim ya yi don nuna cewa yana da bangaskiya ga Jehobah? (b) A wacce hanya ce Jehobah ya san Ibrahim sosai?

6 Ibrahim mutum ne da ya “bada gaskiya ga Ubangiji.” Kuma ana kiransa “uban masu-bada gaskiya duka.” (Far. 15:6; Rom. 4:11) Cikin bangaskiya, Ibrahim ya bar gidansa da abokansa da dukan dukiyoyinsa kuma ya tafi wata ƙasa mai nisa. (Far. 12:1-4; Ibran. 11:8-10) Kuma Ibrahim ya ci gaba da kasancewa da bangaskiya sosai shekaru da yawa bayan wannan lokacin. Hakan ya kasance gaskiya sa’ad da yake “cikin miƙa Ishaƙu” ɗansa don yin biyayya ga umurnin Jehobah. (Ibran. 11:17-19) Ibrahim ya nuna bangaskiya ga alkawuran Jehobah, saboda haka, Allah ya ɗauke shi a matsayin mutum mai muhimmanci, domin ya san Ibrahim sosai. (Karanta Farawa 18:19.) Jehobah bai dai san kawai cewa Ibrahim ya wanzu ba, amma ya daraja shi a matsayin aboki.—Yaƙ. 2:22, 23.

7. Mene ne za a lura da shi game da cikar alkawuran Jehobah, kuma yaya hakan ya shafi Ibrahim?

7 Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa ’ya’yansa za su “gaji ƙofar” magabtansa kuma za su zama “kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku.” (Far. 22:17, 18) Ko da yake waɗannan alkawuran ba su cika ba sa’ad da Ibrahim yake da rai, amma ya ci gaba da kasance da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehobah. Ya san cewa alkawuran Allah suna cika a koyaushe kuma ya nuna cewa yana da imani ga wannan a hanyar da ya yi rayuwa. (Karanta Ibraniyawa 11:13.) Shin Jehobah ya san mu a matsayin masu bangaskiya kamar na Ibrahim?

Yin Imani ga Jehobah Alamar Bangaskiya Ce

8. Waɗanne abubuwa ne yawancin mutane suke so sosai?

8 Babu shakka muna da muradin da muke son su cika, kamar yin aure da samun yara da kuma koshin lafiya. Ba laifi ba ne idan muna da irin wannan muradin. Amma ba dukan mu ba ne za mu samu dukan abubuwan da muke so ba. Idan akwai abin da muke son mu samu sosai amma hakan bai yiwu ba yanzu, mene ne za mu yi? Yadda muka aikata a wannan yanayin zai nuna ƙarfin bangaskiyarmu.

9, 10. (a) Mene ne wasu suka yi don su samu abubuwan da suke so? (b) Mene ne kake tunani game da cikar alkawuran Jehobah?

9 Ba zai kasance abin hikima ba idan mun karya dokar Allah don biyan bukatunmu. Hakan zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Alal misali, wasu sun yi jinyar da ta saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Wasu kuma suna yin aikin da ke cinye dukan lokacin da ya kamata su kasance tare da iyalinsu da kuma halartar tarurruka. Wasu kuma suna fita zance da wanda ko wadda ba ta bauta wa Jehobah. Idan Kirista ya yi hakan, shin yana son ya sanu ga Jehobah? A ce Ibrahim ya ƙi jiran Jehobah ya cika alkawuran da ya yi masa. Yaya Jehobah zai ji? Da a ce Ibrahim ya yanki shawara kuma ya sayi gida yana neman suna kuma fa? (Gwada Farawa 11:4.) Shin da Jehobah ya ci gaba da ɗaukansa a matsayin aboki?

10 Waɗanne abubuwa ne kake bukata sosai? Shin kana da bangaskiya sosai har ka jira sai Jehobah ya ba ka waɗannan abubuwan? Ya yi alkawari cewa zai “biya wa kowane mai-rai muradinsa.” (Zab. 145:16) Wataƙila wasu alkawuran Jehobah ba za su cika nan da nan kamar yadda muke zato ba. Amma idan mun ci gaba da yin rayuwa a hanyar da ta nuna cewa muna da bangaskiya kamar Ibrahim, Jehobah ba zai manta da mu ba. Zai yi mana albarka.—Ibran. 11:6.

Bambanci Tsakanin Tawali’u da Fahariya

11. Waɗanne gata ne wataƙila Kora ya more, kuma mene ne hakan ya nuna game da ra’ayinsa ga Allah?

11 Za mu yi magana game da mazaje biyu da rayuwarsu ba iri ɗaya ba ce, wato, Musa da Kora. Abin da suka yi ya taimaka mana mu fahimci cewa yadda muke kiyaye dokokin Jehobah da kuma yadda muke aikatawa zai shafi yadda Jehobah yake ɗaukanmu. Kora Balawi ne na ƙabilar Kohatawa kuma yana da gata da yawa, kuma sun haɗa da ganin sa’ad da al’ummar ta ketare Jar Teku da kuma goyon bayan Jehobah wajen hukunta waɗanda suka yi rashin bayayya a Dutsen Sinai da kuma taimakawa wajen ɗaukan sanduki. (Fit. 32:26-29; Lit. Lis. 3:30, 31) Babu shakka, ya yi biyayya ga Jehobah cikin shekaru da yawa kuma saboda haka Isra’ilawa da yawa sun daraja shi.

12. Kamar yadda aka nuna a shafi na 28, ta yaya fahariya ta shafi dangatakar Kora da Allah?

12 Amma duk da haka, sa’ad da Isra’ilawa suke hanyar zuwa Ƙasar Alkawari, Kora ya ji cewa yadda Jehobah yake ja-gorarsu bai dace ba. Yana son ya yi gyara. Don hakan mazaje 250 daga ƙasar suka goyi bayan Kora. Sun tabbata cewa Jehobah ya amince da abin da suke yi. Suka gaya wa Musa: “Kun cika alfarma, da shi ke dukan jama’a masu-tsarki ne, kowane ɗayansu, Ubangiji kuma yana tare da su.” (Lit. Lis. 16:1-3) Wannan fahariya ne sosai! Musa ya gaya musu: “Ubangiji za ya nuna waɗanda su ke nasa.” (Karanta Littafin Lissafi 16:5.) Washegari, Kora da dukan waɗanda suka yi tawaye da shi suka mutu.—Lit. Lis. 16:31-35.

13, 14. A waɗanne hanyoyi ne Musa ya nuna cewa shi mai tawali’u ne?

13 Akasin Kora, Musa “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Lit. Lis. 12:3) Ya nuna cewa yana da tawali’u ƙwarai ta ƙuduri aniyar yin biyayya ga Jehobah. (Fit. 7:6; 40:16) Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba cewa Musa yana yin musu da Jehobah ko kuma yana fushi domin Jehobah ya ba da doka. Alal misali, Jehobah ya ba da umurni dalla-dalla a kan yadda za a gina mazaunin, kuma wannan ya haɗa da launin zaren da kuma adadin hantuna da za su yi labulen da shi. (Fit. 26:1-6) Idan wani shugaba na ’yan Adam a ƙungiyar Allah ya ba ka umurnin da wataƙila yake da wuya, za ka iya yin sanyin gwiwa a wasu lokatai. Amma Jehobah shugaba ne kamili, wanda ke ba mu hakkoki cikin ƙauna kuma ya amince da bayinsa. Sa’ad da ya ba mu umurni, yana yin hakan da dalili mai kyau. Ka lura cewa, Musa bai yi fushi don umurnin da Jehobah ya ba shi ba, kamar dai Jehobah yana ƙasƙantar da shi ko kuma ya hana shi ’yancinsa. Maimakon haka, Musa ya umurci masu aikin su yi daidai abin da Jehobah ya ce a yi. (Fit. 39:32) Wannan halin tawali’u ne sosai! Musa ya fahimci cewa aikin Jehobah ne kuma Jehobah yana son ya yi amfani da shi don cim ma hakan.

14 Musa ya kuma nuna cewa shi mai tawali’u ne sa’ad da yake da dalilai masu yawa da ya kamata su sa shi sanyin gwiwa. Alal misali, sa’ad da mutanen suka yi gunaguni cewa ba su da ruwa, Musa ya yi fushi da su sosai kuma bai ɗaukaka Jehobah ba. A sakamako, Jehobah ya gaya wa Musa cewa ba zai ƙyale shi ya ja-goranci mutanen zuwa Ƙasar Alkawari ba. (Lit. Lis. 20:2-12) Musa da ɗan’uwansa Haruna sun yi haƙuri da gunagunin Isra’ilawa cikin shekaru da yawa. Amma saboda wannan kuskure guda, Musa ba zai more abin da yake ɗokin cikin shekaru da yawa ba! Mene ne Musa ya yi? Ya yi baƙin ciki sosai, amma duk da hakan ya yi biyayya ga shawarar da Jehobah ya tsai da. Ya san cewa Jehobah Allah mai adalci ne wanda ba ya son kai. (K. Sha 3:25-27; 32:4) Idan ka yi tunani game da Musa, shin ba ka ɗaukarsa a matsayin mutum da ya sanu ga Jehobah?—Karanta Fitowa 33:12, 13.

Muna Bukatar Kasancewa da Tawali’u don Yin Biyayya ga Jehobah

15. Mene ne za mu iya koya daga fahariyar da Kora ya yi?

15 Za mu samu amincewar Jehobah idan mun yi na’am da gyare-gyaren da ake yi a ƙungiyar kuma mu nuna ladabi ga waɗanda Jehobah yake amfani da su wajen yin ja-gora a cikin ikilisiya. Kora da masu goyon bayansa sun dogara ga kansu, sun kuma yi fahariya da rashin imani kuma hakan ya sa ba su zama abokan Allah kuma ba. Kora ya yi zato cewa Musa tsoho ne da kawai yake yin abin da ya ga dama, amma ya manta cewa Jehobah ne ainihi yake wa al’ummar ja-gora. A sakamako, bai yi biyayya ga waɗanda Jehobah yake amfani da su wajen yin ja-gora ba. Da zai fi kyau Kora ya jira Jehobah ya ba da ƙarin bayani ko kuma ya yi gyara idan da bukata. Amma a ƙarshe, fahariyar da Kora ya yi ta ɓata dangantakarsa da Jehobah!

16. Ta yaya misalin tawali’u na Musa zai iya taimaka mana?

16 Wannan labarin ya ba da kashedi ga dattawa da kuma ’yan’uwa a cikin ikilisiya a yau. Ana bukatar tawali’u don jiran Jehobah da kuma bin umurnin waɗanda aka naɗa su yi ja-gora. Muna nunawa cewa muna da tawali’u da kuma jinkirin fushi kamar Musa kuwa? Mun fahimci kuma mun amince cewa Jehobah yana amfani da waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya? Muna bin umurninsu kuwa? Muna kame fushinmu kuwa sa’ad da ranmu ya ɓace? Idan muka yi hakan za mu samu amincewar Jehobah. Tawali’u da kuma ba da kai da muka yi za su sa mu kusace shi.

Jehobah Ya San Waɗanda Suke Nasa

17, 18. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da zama abokan Jehobah?

17 Yana da kyau mu yi tunani a kan misalan waɗanda Jehobah ya ƙaunace su kuma ya sa suka zama abokansa. Ibrahim da Musa ajizai ne kuma sun yi kurakurai kamar mu. Duk da haka, sun sanu ga Jehobah a matsayin waɗanda nasa ne. Misalin Kora ya nuna mana cewa zai yiwu mu nisance Jehobah kuma mu yi hasarar abokantakarmu da shi. Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Yaya Jehobah yake ɗauka na? Mene ne zan iya koya daga waɗannan misalan Littafi Mai Tsarki?’

18 Za mu iya samun ta’aziyya sosai don sanin cewa Jehobah yana ɗaukan amintattun bayinsa a matsayin waɗanda nasa ne. Ku ci gaba da kasancewa da bangaskiya da tawali’u da wasu halaye da za su sa ku kusaci Allah. Babu shakka, zama abokan Jehobah gata ne mai tamani da yake kawo farin ciki a rayuwa a yanzu, kuma albarka masu yawa a nan gaba.—Zab. 37:18.

Ka Tuna?

• Wace dangantaka mai tamani ce za ka iya more da Jehobah?

• Ta yaya za ka iya yin koyi da bangaskiyar Ibrahim?

• Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Kora da Musa?

[Hoto a shafi na 26]

Muna da bangaskiya irin ta Ibrahim cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa kuwa?

[Hoto a shafi na 28]

Kora bai da tawali’u kuma ya ƙi bin ja-gora

[Hoto a shafi na 29]

Jehobah ya san ka a matsayin wanda yake ba da kai da tawali’u ga umurni kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba