Girman Kai Yana Kaiwa Ga Kunya
“Lokacinda girman kai ya zo, kunya tana nan tafe: Amma wurin masu-tawali’u akwai hikima.—MISALAI 11:2.
1, 2. Menene girman kai, kuma a waɗanne hanyoyi ne ya kai ga bala’i?
WANI Ba’lawi mai hassada ya ja-goranci taron ’yan banza su yi adawa da waɗanda Jehovah ya sanya wa iko. Wani ɗan sarki ya ƙulla ya hambare ubansa. Wani sarki mara haƙuri ya raina umarnin annabin Allah. Waɗannan Isra’ilawa uku suna da hali iri ɗaya: girman kai.
2 Girman kai yanayin zuciya ne da ke jawo mummunar jaraba ga duka. (Zabura 19:13) Mai girman kai yana yin abu ba tare da an ba shi izinin yin haka ba. Sau da yawa, wannan yana kaiwa ga bala’i. Hakika, girman kai ya halaka sarakuna kuma ya ɓingira dauloli. (Irmiya 50:29, 31, 32; Daniel 5:20) Har ya kai wasu bayin Jehovah kuma ga halaka.
3. Ta yaya za mu iya koyo game da haɗarin girman kai?
3 Da kyakkyawar dalili Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Lokacinda girman kai ya zo, kunya tana nan tafe: Amma wurin masu-tawali’u akwai hikima.” (Misalai 11:2) Littafi Mai-Tsarki ya yi mana tanadin misalai da ke tabbatar da gaskiyar wannan karin magana. Bincika wasu cikin waɗannan zai taimake mu mu ga haɗarin wuce gona da iri. Saboda haka, bari mu duba yadda hassada, dogon buri, da rashin haƙuri suka sa mutane uku da aka ambata a farko suka yi girman kai da ya kai su ga kunya.
Kora—Ɗan Tawaye Mai Hassada
4. (a) Wanene Kora, kuma wane abu ne da ya faru lallai ya kasance a ciki? (b) A cikin shekarunsa na gaba, wane muguwar hali ne Kora ya zuga?
4 Kora Ba’lawi ne na iyalin Kohat, ɗan babar Musa da Haruna. Babu shakka, shi amincacce ne wurin Jehovah na shekaru da yawa. Kora ya sami gatar kasancewa tsakanin waɗanda aka cece su ta Jan Teku, ƙila yana cikin waɗanda suka zartar da hukuncin Jehovah a kan Isra’ilawa da suka bauta wa ɗan maraƙi a Dutsen Sinai. (Fitowa 32:26) Amma kuma, daga baya Kora ya zama shugaba a ta da zaune tsaye wajen adawa da Musa da Haruna, ya haɗa kai da ’ya’yan Ra’ubainu Datan, Abiram, da On, tare da wasu hakiman Isra’ilawa 250.a Suka ce wa Musa da Haruna: ‘Kun cika fahariya, da shi ke dukan jama’a masu tsarki ne, kowanne ɗayansu, Jehovah kuma yana tare da su; don menene fa ku ke ɗaukaka kanku gaba da taron jama’ar Jehovah?’—Litafin Lissafi 16:1-3.
5, 6. (a) Me ya sa Kora ya yi wa Musa da Haruna tawaye? (b) Me ya sa za a iya cewa Kora bai daraja matsayinsa ba cikin tsarin Allah?
5 Bayan shekaru da yawa na aminci, me ya sa Kora ya yi tawaye? Hakika shugabancin Musa a kan Isra’ila ba na zalunci ba ne, domin shi mutum “mai-tawali’u ne ƙwarai gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Litafin Lissafi 12:3) Duk da haka, kamar dai Kora ya yi kishin Musa da Haruna kuma ya yi fushi da ganin sun shahara, wannan ya sa ya faɗā cikin—kuskure—cewa sun ɗaga kansu fiye da jama’a.—Zabura 106:16.
6 Damuwar Kora wataƙila, ita ce butulci, bai yi godiya ga gatarsa cikin tsarin Allah ba. Hakika, Lawiyawa da suke ’ya’yan Kohat ba firistoci ba ne, amma masu koyar da Dokar Allah ne. Su suke kwasan kujeru da kwanoni na mazauni lokacin da ake bukatar a ƙaurar da su. Wannan ba ƙaramin aiki ba ne, domin kwanoni masu tsarki mutane da suke da tsabta na addini da kuma na ɗabi’a ne kaɗai za su taɓa. Shi ya sa, lokacin da Musa ya fuskanci Kora, kamar dai yana tambayarsa ne, Kana ganin aikinka ba shi da muhimmanci ne har sai ka nemi ka zama firist? (Litafin Lissafi 16:9, 10) Kora bai gane cewa ɗaukaka mafi girma, ita ce bauta wa Jehovah cikin aminci bisa tsarinsa—ba sai ka sami wani matsayi na musamman ko kuma aiki ba.—Zabura 84:10.
7. (a) Ta yaya ne Musa ya bi da Kora da mutanensa? (b) Ta yaya tawayen Kora ya ƙare cikin bala’i?
7 Musa ya gayyace Kora da mutanensa, su taru washegari a rumfar taro ɗauke da kaskon wuta da turare. Kora da mutanensa ba su da izinin su ƙona turare, da yake su ba firistoci ba ne. Idan suka zo da kaskon wuta da turare, wannan zai nuna a fili cewa waɗannan mutane har ila suna ganin ya kamata su zama firistoci—har bayan an ba su isashen lokaci su yi tunani a kan wannan duk cikin dare. Washegari da suka bayana a wajen, Jehovah ya nuna fushinsa. Su Ra’ubainu, “ƙasa kuwa ta buɗe bakinta, ta haɗiye su.” Wuta daga Allah ta ƙone sauran, haɗe da Kora. (Kubawar Shari’a 11:6; Litafin Lissafi 16:16-35; 26:10) Girman kai na Kora ya kai shi ga kunya ƙwarai—rashin gamsuwan Allah!
Ka Tsayayya wa “Marmari Zuwa Kishi”
8. Ta yaya “marmari zuwa kishi” zai iya bayyana kansa tsakanin Kiristoci?
8 Labarin Kora gargaɗi ne a garemu. Tun da yake “marmari zuwa kishi” yana cikin ’yan Adam ajizai, yana iya bayyana a cikin ikklisiyar Kirista. (Yaƙub 4:5) Alal misali, muna iya zama masu son matsayi. Kamar Kora, muna iya kishin wasu domin gatarsu da muke so. Ko kuma muna iya zama kamar Kirista na ƙarni na farko mai suna Diyoturifis. Ya cika zargin ikon manzanni, babu shakka domin yana so ya zama shi ne mai kula da kome. Yohanna ya rubuta cewa Diyoturifis wanda “ya ke so ya sami shugabanci.”—3 Yohanna 9.
9. (a) Wane hali ne game da nawayoyi na ikklisiya muke bukatar guje masa? (b) Wane ra’ayi ne ke daidai na matsayinmu cikin tsarin Allah?
9 Hakika, ba laifi ba ne namiji Kirista ya kai ga samun nawayoyi na ikklisiya. Bulus ya ma ƙarfafa irin halin nan. (1 Timothawus 3:1) Amma, kada mu ɗauki gatar hidima kamar wata alama ce ta lada, kamar hawa tsani ne na ci gaba. Ka tuna, Yesu ya ce: “Dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, baranku za ya zama; kuma dukan wanda ya ke so shi zama nafari a cikinku, bawanku za ya zama.” (Matta 20:26, 27) A bayyane yake, ba daidai ba ne a yi kishin waɗanda suke da manyan nawaya, kamar a ce darajar mu wajen Allah ta dangana ne bisa “matsayin” da muke da shi a cikin ƙungiyarsa. Yesu ya ce: “Ku duka kuwa ’yan’uwa ne.” (Matta 23:8) Hakika, ko mai shela ne ko majagaba, wanda ya yi baftisma ba da daɗewa ba ko wanda ya daɗe yana riƙe aminci—dukan waɗanda suke bauta wa Jehovah da dukan zuciyarsu suna da matsayi mai daraja cikin tsarinsa. (Luka 10:27; 12:6, 7; Galatiyawa 3:28; Ibraniyawa 6:10) Albarka ce sosai mu yi aiki tare da miliyoyi da suke fama su yi amfani da gargaɗin Littafi Mai-Tsarki: “Ku ɗaura wa gindinku tawali’u, da za ku bauta ma juna.”—1 Bitrus 5:5.
Absalom—Mai Dogon Buri don Zarafi da Ya Samu
10. Wanene Absalom, kuma yaya ya yi ƙoƙarin ya samo tagomashi daga waɗanda suke zuwa wajen sarki don shari’a?
10 Yayin rayuwar ɗan Sarki Dauda na uku Absalom ya tanadar mana da darasi game da dogon buri. Wannan ɗan ƙulli, ya yi ƙoƙarin ya gamsar da waɗanda suke zuwa wajen sarki don shari’a. Da farko ya yi da’awar cewa Dauda ba ya damuwa da bukatunsu. Sa’an nan ya bar yin dabara, ya nuna nufinsa kai tsaye. ‘Kai, in da a ce ni alƙali ne a ƙasar nan,’ Absalom yana ta faɗā cewa, “da kowane mutum wanda ya ke da ƙara ko maganar shi ta zo wurina, ni ma da na yi masa shari’ar gaskiya!” Ƙullin Absalom cikin dabara bai kasance da iyaka ba. “Sa’anda kowane mutum ya guso garin yi masa sujada,” in ji Littafi Mai-Tsarki, “sai ya miƙa hannunsa, ya kama shi, ya yi masa sumba. Hakanan Absalom ya yi ga Isra’ila, kowane mai-zuwa wurin sarki garin neman shari’a.” Menene sakamakon haka? “Absalom ya sace zukatan maza na Isra’ila.”—2 Samuila 15:1-6.
11. Ta yaya Absalom ya yi ƙoƙari ya hamɓare sarautar Dauda?
11 Absalom ya ƙudura aniyar ya hamɓare sarautar ubansa. Shekara biyar daga baya, ya sa aka kashe Amnon, ɗan Dauda magaji don ya rama fyaɗe da ya yi wa ’yar’uwarsa Tama. (2 Samuila 13:28, 29) Amma, har ila idanun Absalom yana kan kursiyin, ya ɗauki mutuwar Amnon hanya ce da ya kawar da abokin gabansa.b Ko da yaya dai, yayin da lokaci ya kai, Absalom ya ɗauki matakinsa. Ya sa aka yi shelar sarautarsa a cikin dukan ƙasar.—2 Samuila 15:10.
12. Ka ba da bayanin yadda girman kan Absalom ya kai shi ga kunya.
12 Absalom ya yi nasara na ɗan lokaci, domin “tayarwan kuwa ta yi ƙarfi; gama kullum masu-zuwa wurin Absalom suna ƙaruwa.” A kwana a tashi, Sarki Dauda ya ga tilas ne ya tsere domin ransa. (2 Samuila 15:12-17) Amma, bai daɗe ba sai burin Absalom ya yanke, lokacin da Jowab ya kashe shi, aka jefa shi cikin rami aka rufe da duwatsu. Ka ji fa—wannan mai burin da yake neman ya zama sarki ba a yi masa jana’iza ba ma!c Hakika, girman kai ya kai Absalom ga kunya.—2 Samuila 18:9-17.
Ka Guje wa Dogon Buri
13. Ta yaya hali na buri zai iya shiga zuciyar Kirista?
13 Samun iko da kuma faɗuwar Absalom darasi ne a garemu. A cikin duniyar yau ta zalunci, yana da sauƙi mutane su yi daɗin baki wa manyansu, domin su samo wa kansu yabo ko wataƙila su samu wata gata ko kuma girma. Har ila su kuma su yi wa waɗanda suke kasa da su fahariya, a neman samun gamsuwarsu da kuma goyon baya. Idan ba mu mai da hankali ba, irin halin nan na buri zai iya shiga zuciyarmu. Hakika, wannan ya faru tsakanin wasu cikin ƙarni na farko, da ya sa manzannin suka ba da gargaɗi masu ƙarfi game da waɗannan.—Galatiyawa 4:17; 3 Yohanna 9, 10.
14. Me ya sa ya kamata mu guje wa dogon buri, na girman kai?
14 Jehovah ba shi da wuri cikin ƙungiyarsa domin masu ƙulli da suke ƙoƙari su “biɗa ma kansu daraja.” (Misalai 25:27) Hakika Littafi Mai-Tsarki ya yi kashedi: “Ubangiji za shi kawaitadda dukan leɓuna na bambaɗanci, da harshe kuma mai-fankama.” (Zabura 12:3) Absalom yana da leɓuna na bambaɗanci. Yana gaya wa waɗanda yake neman gamsuwarsu abubuwa masu girma—dukan wannan don ya ƙwace matsayin iko. Akasarin haka, mu masu albarka ne da muke tsakanin ’yan’uwanci da ke bin gargaɗin Bulus: “Kada a yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya maida wani ya fi kansa.”—Filibbiyawa 2:3.
Saul—Sarki Mara Haƙuri
15. Yaya Saul a wani lokaci ya nuna kansa mai filako?
15 A wani lokaci Saul, wanda daga baya ya zama sarkin Isra’ila mai filako ne. Yi la’akari da abin da ya faru lokacin da yake ƙarami. Lokacin da annabin Allah Sama’ila ya yi magana mai kyau game da shi, cikin tawali’u Saul ya amsa: “Ni ba Ba’banyamin ba ne, daga mafi ƙanƙanta cikin ƙabilar Isra’ila? Gidana kuma mafi ƙanƙanta cikin gidajen ƙabilar Banyamin? Don menene fa ka ke yi mini wannan irin zance?”—1 Samuila 9:21.
16. A wace hanya ce Saul ya nuna rashin haƙuri?
16 Amma daga baya filakon Saul ya ɓace. A lokacin yaƙi da Filistiyawa, ya janye zuwa Gilgal, inda yake bukatar ya jira Sama’ila ya zo ya roƙi Allah ta wurin hadayu. Da Sama’ila bai zo a kan lokaci ba, Saul cikin girman kai ya ba da hadayar ƙonawa da kansa. Da ya gama, sai ga Sama’ila. Sama’ila ya yi tambaya: “Me ka yi?” Saul ya amsa: “Domin na ga jama’a sun watse, sun rabu da ni, kai kuwa ba ka zo a cikin kwanakin da aka sanya ba, . . . sai na tilasa ma raina, na miƙa hadaya ta ƙonawa.”—1 Samuila 13:8-12.
17. (a) Da farko, me ya sa za a ga kamar abin da Saul ya yi ba laifi? (b) Me ya sa Jehovah ya tsauta wa Saul domin halinsa na rashin haƙuri?
17 Da farko, za a iya gani kamar abin da Saul ya yi ba laifi. Ko da yaya, mutanen Allah “sun matsu,” “sun damu,” kuma suna rawar jiki domin yanayinsu na ban razana. (1 Samuila 13:6, 7) Hakika, ba laifi ba ne a ɗauki mataki idan yanayin ya wajabci hakan.d Amma, ka tuna cewa Jehovah ya san zukata kuma yana gane tunaninmu na ciki. (1 Samuila 16:7) Saboda haka, lallai ya ga wasu abubuwa game da Saul da ba a faɗe su ba sarai cikin labarin Littafi Mai-Tsarki. Alal misali, ƙila Jehovah ya ga cewa rashin haƙurin Saul saboda fahariya ce. Wataƙila Saul ya yi fushi cewa shi—sarkin dukan Isra’ila—zai jira wani da yake ganin tsoho ne, annabi mai jinkiri! Ko da yaya dai, Saul ya ga cewa makarar Sama’ila ce ta ba shi zarafin ya yi nasa abu kuma ya yi banza da umurni da aka ba shi. Sakamakon fa? Sama’ila bai yabi matakin da Saul ya ɗauka ba. Akasarinsa, ya tsauta wa Saul, ya ce: “Mulkinka ba za ya dawwama ba . . . da shi ke ba ka kiyaye abin da Ubangiji ya umurce ka ba.” (1 Samuila 13:13, 14) A nan kuma, girman kai ya kai ga kunya.
Guje wa Rashin Haƙuri
18, 19. (a) Ka kwatanta yadda rashin haƙuri zai iya sa bawan Allah a zamanin yau ya aika da girman kai. (b) Me za mu tuna game da yadda ikklisiyar Kirista take ci gaba?
18 An rubuta labarin girman kai na Saul cikin Kalmar Allah don amfaninmu. (1 Korinthiyawa 10:11) Yana da sauƙi mu yi fushi domin ajizancin ’yan’uwanmu. Kamar Saul, za mu iya yin rashin haƙuri, da jin cewa idan abubuwa za su tafi daidai, tilas ne mu sa hannu. Alal misali, a ce ɗan’uwa ya gwanance a yin shirye-shirye. Yana zuwa a kan lokaci, ya san tsarin ikklisiya daidai, kuma ya gwanance wajen magana da koyarwa. Hakanan kuma ya fahimci cewa wasu ba su kai shi bin mizanai ba, ba sa yin abubuwa yadda zai so su yi. Zai zama daidai ne ya nuna rashin haƙuri? Zai dace ne ya zargi ’yan’uwansa, ƙila ya nuna cewa idan ba da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa ba, da ba abin da za a yi ya yi daidai cikin ikklisiyar? Wannan girman kai ne!
19 To, menene yake riƙe ikklisiyar Kirista tare? Fasahar tsari? iyawa? ilimi mai yawa? Hakika, waɗannan abubuwa ne suke taimakawa ga ci gaban ikklisiya. (1 Korinthiyawa 14:40; Filibbiyawa 3:16; 2 Bitrus 3:18) Amma, Yesu ya ce za a san mabiyansa musamman ta wurin ƙaunarsu ne. (Yohanna 13:35) Shi ya sa dattiɓai masu kula, sun fahimci cewa ikklisiya ba wani kasuwanci da ke bukatar nace bin tsarin ba; maimako, ya ƙunshi garken da ke bukatar kula mai kyau ne. (Ishaya 32:1, 2; 40:11) Yin banza da irin ƙa’idodin nan sau da yawa yakan jawo jayayya. Akasarin haka, ƙa’ida ta ibada tana kawo salama.—1 Korinthiyawa 14:33; Galatiyawa 6:16.
20. Menene za a bincika cikin talifi na biye?
20 Labaran Littafi Mai-Tsarki game da Kora, Absalom, da Saul sun nuna a fili cewa girman kai yana kaiwa ga kunya, yadda aka ambata a Misalai 11:2. Amma, ayar Littafi Mai-Tsarki ɗin ya daɗa: ‘Wurin masu-filako hikima take.’ Menene filako? Waɗanne misalai ne na Littafi Mai-Tsarki za su taimaka wajen ƙara bayani a kan wannan hali, kuma ta yaya za mu iya nuna filako a yau? Za a bincika waɗannan tambayoyi a cikin talifi na biye.
[Hasiya]
a Tun da yake Ra’uba ne ɗan farin Yakubu, waɗanda suke cikin zuriyar da Kora ya ruɗe su su yi tawaye lallai suna fushi da Musa—wanda daga ƙabilar Lawi ne—da yake da iko a kansu.
b Chilead, ɗan Dauda na biyu ba a ambaci sunansa ba bayan haihuwarsa. Mai-yiwuwa ne ya mutu kafin tawayen Absalom.
c A lokatan Littafi Mai-Tsarki jana’iza da ake yi wa mamaci, nuna darajar mutumin ake yi. Shi ya sa, idan ba a yi wa mutum jana’iza ba bala’i ne, sau da yawa kuma yana nuna rashin gamsuwar Allah ne.—Irmiya 25:32, 33.
d Alal misali, Phinehas ya ɗauki mataki da sauri ya dakatar da annoba da ya kashe dubban Isra’ilawa, kuma Dauda ya ƙarfafa mutanensa da suke jin yunwa su ci daga gurasa ta “gidan Allah.” Babu wani cikin waɗannan da Allah ya kira girman kai.—Matta 12:2-4; Litafin Lissafi 25:7-9; 1 Samuila 21:1-6.
Ka Tuna?
• Menene girman kai?
• Ta yaya kishi ya sa Kora ya yi girman kai?
• Menene muka koya daga labarin Absalom mai dogon buri?
• Ta yaya za mu guje wa rashin haƙuri da Saul ya yi?
[Hoto a shafi na 20]
Saul ya yi rashin haƙuri ya kuma aika da girman kai