Bitar Sashe na 3
Ka tattauna tambayoyi na gaba da malaminka:
- Ku karanta Karin Magana 27:11. - Me ya sa kake so ka kasance da aminci ga Jehobah? - (Ka duba Darasi na 34.) 
 
- Ta yaya za ka tsai da shawarwari masu kyau a batun da babu takamaiman doka a Littafi Mai Tsarki? - (Ka duba Darasi na 35.) 
- Ta yaya za ka zama mai faɗin gaskiya a dukan abubuwa? - (Ka duba Darasi na 36.) 
- Ku karanta Matiyu 6:33. - Ta yaya za mu ci gaba da sa bautar Allah a kan gaba fiye da aiki da kuɗi? - (Ka duba Darasi na 37.) 
 
- A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna kana daraja rai yadda Jehobah yake yi? - (Ka duba Darasi na 38.) 
- Ku karanta Ayyukan Manzanni 15:29. - Ta yaya za ka bi dokar Jehobah game da jini? 
- Kana ganin dokokin da ya ba mu game da hakan sun dace? - (Ka duba Darasi na 39.) 
 
- Ku karanta 2 Korintiyawa 7:1. - Mene ne kasancewa da tsabta a zahiri da zuciya yake nufi? - (Ka duba Darasi na 40.) 
 
- Ku karanta 1 Korintiyawa 6:9, 10. - Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da jima’i? Ka amince da hakan kuwa? 
- Wane umurni ne Littafi Mai Tsarki ya ba da game da shan giya? - (Ka duba Darasi na 41 da 43.) 
 
- Ku karanta Matiyu 19:4-6, 9. - Waɗanne ƙa’idodi ne Allah ya bayar game da aure? 
- Me ya sa wajibi ne a yi aure ko kuma a kashe aure bisa doka? - (Ka duba Darasi na 42.) 
 
- Waɗanne bukukuwa ne suke ɓata wa Jehobah rai, kuma me ya sa? - (Ka duba Darasi na 44.) 
- Ku karanta Yohanna 17:16 da Ayyukan Manzanni 5:29. - Ta yaya za ka guji saka hannu a harkokin duniya? 
- Idan dokar ’yan Adam ta saɓa wa dokar Allah, me za ka yi? - (Ka duba Darasi na 45.) 
 
- Ku karanta Markus 12:30. - Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar Jehobah? - (Ka duba Darasi na 46 da 47.)