Ka Kasance Da Bangaskiya Cikin Kalmomin Annabci Na Allah!
“Muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatarda ita.”—2 BITRUS 1:19.
1, 2. Wane annabci ne aka rubuta da farko, kuma wannene ɗaya cikin tambayoyi da suka taso?
JEHOVAH ne Tushen annabci na farko da aka rubuta. Bayan Adamu da Hawa’u suka yi zunubi, Allah ya gaya wa macijin: ‘Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da ɗanta kuma. Shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.’ (Farawa 3:1-7, 14, 15) Ƙarnuka da yawa sun shige kafin aka gane waɗannan kalmomin annabci sosai.
2 Annabci na farkon yana ɗauke da bege na gaske ga mutane masu zunubi. Daga baya Nassosi sun nuna cewa Shaiɗan Iblis shi ne “tsohon macijin.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Amma wanene zai zama Ɗa na alkawarin Allah?
Neman Ɗan
3. Yaya ne Habila ya nuna bangaskiya cikin annabci na farko?
3 Ba kamar ubansa ba, Habila mai ibada ya nuna bangaskiya cikin annabci na farko. Lallai Habila ya gane cewa za a bukaci zubar da jini don a rufe zunubi. Saboda haka bangaskiya ta motsa shi ya ba da hadayar dabban rago da Allah ya amince da shi. (Farawa 4:2-4) Duk da haka, sanin Ɗa na alkawarin ya zama asiri.
4. Wane alkawari ne Allah ya ba Ibrahim, kuma menene hakan ya nuna game da Ɗa na alkawarin?
4 Shekara 2,000 bayan kwanakin Habila, Jehovah ya ba uban iyali, Ibrahim, wannan alkawari na annabci: “A kan albarka zan albarkace ka; wajen daɗuwa, zan riɓanɓanya tsatsonka kamar taurarin sama . . . cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Farawa 22:17, 18) Waɗannan kalmomin suna da alaƙa da Ibrahim game da cika annabci na farkon. Sun nuna Ɗa wanda ta wurinsa za a gama da ayyukan Shaiɗan zai bayyana ne ta ’ya’yan Ibrahim. (1 Yohanna 3:8) “Garin kafa ido bisa alkawarin Allah, [Ibrahim] ba ya raurawa ta wurin rashin bangaskiya ba,” haka ma shaidun Jehovah kafin Kiristoci waɗanda “ba su amshi alkawarin ba.” (Romawa 4:20, 21; Ibraniyawa 11:39) Maimakon haka sun riƙe bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah.
5. A kan waye alkawarin Allah na Ɗa ya cika, kuma me ya sa ka amsa haka?
5 Manzo Bulus ya yi maganar Ɗa na alkawarin Allah yayin da ya rubuta haka: “Waɗannan alkawura fa ga Ibrahim aka faɗi, da zuriyarsa. Ba ya ce, Zuriyoyi, watau dayawa ne; amma, Ga zuriyarka, watau ɗaya ne, Kristi ke nan.” (Galatiyawa 3:16) Ba duka ’ya’yan Ibrahim ne ke ƙunshe cikin Zuriyar da al’ummai da za su albarkaci kansu ta wurinsa ba. Ba a albarkaci mutane ta ’ya’yan ɗansa Isma’ilu da ’ya’yansa ta wurin Ketura ba. Zuriyar albarka ta fito ne daga ɗansa Ishaƙu da jikansa Yakubu. (Farawa 21:12; 25:23, 31-34; 27:18-29, 37; 28:14) Yakubu ya nuna cewa “al’ummai” za su yi biyayya ga Shiloh na ƙabilar Yahuda, amma daga baya an yarda ma Ɗan ya zo ta ’ya’yan Dauda ne kawai. (Farawa 49:10; 2 Samuila 7:12-16) Yahudawa na ƙarni na farko sun tsammanci mutum guda ya zo wanda shi ne Almasihu, ko kuma Kristi. (Yohanna 7:41, 42) Kuma annabcin Allah na Ɗa ya cika a kan Ɗansa, Yesu Kristi.
Almasihu Ya Bayyana!
6. (a) Yaya ya kamata mu gane annabci na makonni 70? (b) Yaushe, kuma ta yaya Yesu ya ‘ƙare zunubi’?
6 Annabi Daniel ya rubuta wani muhimmin annabci na Almasihu. A shekara ta farko na Darius Ba’medi, ya gano cewa halakar Urushalima ta shekara 70 ta kusa ƙarshensa. (Irmiya 29:10; Daniel 9:1-4) Yayin da Daniel yake addu’a, mala’ika Jibrailu ya zo ya bayana cewa an ‘ayana makonni saba’in na ƙare zunubi.’ Za a yanke Almasihu a tsakiyar mako na 70. ‘Makonni bakwai na shekaru’ ya soma a shekara ta 455 K.Z., lokacin da Sarkin Pashiya Artaxerxes na I ya ‘ba da umurni a sake gina Urushalima.’ (Daniel 9:20-27; na Moffatt; Nehemiah 2:1-8) Almasihun zai zo bayan makonni 7 da kuma makonni 62. Waɗannan shekaru 483 sun soma ne daga shekara ta 455 K.Z. zuwa shekara ta 29 A.Z., yayin da aka yi wa Yesu baftisma kuma Allah ya shafe shi ya zama Almasihu, ko kuma Kristi. (Luka 3:21, 22) Yesu ya ‘ƙare zunubi’ ta ba da ransa ya zama fansa a 33 A.Z. (Markus 10:45) Dalilai ne masu kyau na kasance da bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah!a
7. Ka yi amfani da Littafi Mai-Tsarki ka nuna yadda Yesu ya cika annabci na Almasihu.
7 Ta wurin bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah ya yiwu mu san Almasihu. Cikin annabce-annabce game da Almasihu da ke cikin Nassosin Ibrananci, da yawansu marubutan Nassosin Hellenanci na Kirista sun yi amfani da shi wa Yesu. Ga misali: Budurwa ce ta haifi Yesu a Bai’talahmi. (Ishaya 7:14; Mikah 5:2; Matta 1:18-23; Luka 2:4-11) An kira shi daga cikin Masar, kuma an kashe jarirai bayan haihuwarsa. (Irmiya 31:15; Hosea 11:1; Matta 2:13-18) Yesu ya ɗauki rashin lafiyarmu. (Ishaya 53:4; Matta 8:16, 17) Kamar yadda aka annabta, ya shigo Urushalima a kan ɗan jaka. (Zechariah 9:9; Yohanna 12:12-15) Kalmomin mai zabura sun cika bayan an rataye Yesu, lokacin da sojoji suka raba tufafinsa tsakaninsu kuma suka jefa kuri’a a kan taguwarsa. (Zabura 22:18; Yohanna 19:23, 24) Lazun cewa ba a karya kasussuwan Yesu ba kuma sukarsa da aka yi ma ya cika annabci. (Zabura 34:20; Zechariah 12:10; Yohanna 19:33-37) Waɗannan kaɗan ne kawai cikin misalai na annabce-annabce na Almasihu da marubutan Littafi Mai-Tsarki huraru daga Allah suka yi amfani da su wa Yesu.b
Ka Yabi Sarki Almasihu!
8. Wanene Mai-Zamanin Dā, kuma ta yaya annabcin da ke a Daniel 7:9-14 ya cika?
8 A shekara ta farko na Sarkin Babila, Belshazzar, Jehovah ya ba annabi Daniel mafarki da kuma ru’uya masu girma. Da farko annabin ya ga manyan bisashe huɗu. Mala’ikan Allah ya ce su “sarakuna huɗu” ne, yana nuna suna alamar masu ikon duniya da suka bi bayan juna. (Daniel 7:1-8, 17) Sai kuma Daniel ya ga Jehovah, “mai-zamanin dā,” yana zaune da daraja a kan kursiyi. Ya hukunci bisashen da tsanani, ya kwace sarauta daga hannunsu kuma ya halaka bisa na huɗun. A lokacin aka ba da sarauta mai daɗewa a hannun “mai-kama da ɗan mutum” a kan “dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna.” (Daniel 7:9-14) Dubi wannan annabcin mai girma da ke game da naɗa “Ɗan mutum,” Yesu Kristi, a sama a shekara ta 1914!—Matta 16:13.
9, 10. (a) Sashe dabam dabam na mafarkin yana nuni ga menene? (b) Yaya za ka fassara cikar Daniel 2:44?
9 Daniel ya sani cewa Allah ya kan “tuɓe sarakuna, ya kan sarautadda sarakuna.” (Daniel 2:21) Tare da bangaskiya cikin Jehovah, wanda “ya kan tone asirai” ne annabin ya fassara mafarkin babbar siffa na Sarkin Babila, Nebuchadnezzar. Sashensa dabam dabam yana nuna tashiwa da fāɗiwar masu ikon duniya su Babila, Mediya da Persiya, Hellas, da kuma Roma. Allah ya kuma yi amfani da Daniel ya jera aukuwan duniya har zuwa lokacinmu da kuma gaba da haka.—Daniel 2:24-30.
10 Annabcin ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” (Daniel 2:44) Lokacin da “zamanan Al’ummai” sun ƙare a 1914, Allah ya kafa Mulkinsa na samaniya ƙarƙashin Kristi. (Luka 21:24; Ru’ya ta Yohanna 12:1-5) Ta ikon Allah “dutse” na Mulkin Almasihu ya fito daga cikin “babban dutse” na sararin samaniya na Allah. A Armageddon dutsen zai mangare siffar kuma ya niƙa ta ta zama gari. Babban dutse na gwamnati wadda ta shafe “dukan duniya,” Mulki na Almasihu za ta tsaya har abada.—Daniel 2:35, 45; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.c
11. Menene sake kamani na Yesu ya nuna, kuma me wannan ru’uyar ta yi a kan Bitrus?
11 Da yake tunawa da sarautar Mulkinsa, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Akwai waɗansu a cikin na tsaye a wurin nan, da ba za su ɗanɗana mutuwa ba daɗai, har sun ga Ɗan mutum yana zuwa cikin mulkinsa.” (Matta 16:28) Bayan kwanaki shida, Yesu ya kai Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna cikin wani dutse mai girma inda kamaninsa ya canja a gabansu. Yayin da gajimare ya rufe manzannin, Allah ya sanar: “Wannan Ɗana ne ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai; ku ji shi.” (Matta 17:1-9; Markus 9:1-9) Ɗan kaɗan cikin darajar Mulkin Kristi ke nan! Abin da ya sa ke nan Bitrus ya yi nuni ga wannan ru’uyar mai ban sha’awa kuma ta ce: “Muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatarda ita.”—2 Bitrus 1:16-19.d
12. Me ya sa wannan shi ne lokaci na musamman da za mu nuna bangaskiyarmu cikin kalmomin annabci na Allah?
12 Lallai “maganar annabci” ba kawai annabce-annabce na Almasihu na Nassosin Ibrananci ya ƙunsa ba, amma furcin Yesu cewa zai zo “da iko da ɗaukaka mai-girma.” (Matta 24:30) Sake kamanin ya tabbatar da kalmomin annabci game da zuwan Kristi cikin ikon darajar Mulki. Ba da daɗewa ba, bayanuwarsa cikin daraja zai nufa halaka ga marasa bangaskiya, albarka kuma ga waɗanda suka nuna bangaskiya. (2 Tassalunikawa 1:6-10) Cikar annabcin Littafi Mai-Tsarki ya tabbatar da cewa waɗannan “kwanaki na ƙarshe” ne. (2 Timothawus 3:1-5, 16, 17; Matta 24:3-14) Mika’ilu, wanda shi ne Yesu Kristi, Babban Mai Hukunci na Jehovah, yana shirye ya kawo ƙarshen wannan mugun shirin abubuwa a lokacin “ƙunci mai-girma.” (Matta 24:21; Daniel 12:1) Wannan shi ne lokaci da za mu nuna muna da bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah.
Ka Adana Bangaskiya Cikin Kalmomin Annabci na Allah
13. Me zai iya taimaka mana mu adana ƙaunarmu ga Allah kuma mu kasance a farke cikin bangaskiyarmu ga kalmarsa?
13 Babu shakka mun yi marmari sosai a farko da muka koyi game da cikar kalmomin annabci na Allah. Amma tun lokacin bangaskiyarmu ta ragu ne, ƙaunarmu kuma ta yi sanyi ne? Kar dai mu zama kamar Kiristoci cikin Afisus da suka ‘bar ƙaunarsu ta farko.’ (Ru’ya ta Yohanna 2:1-4) Ko da yaya muka daɗe muna bauta wa Jehovah, za mu iya yin hasara irin wannan, lallai sai mun ‘biɗi mulkin Allah da farko da kuma adalcinsa’ ne za mu yi ajiyar dukiya a sama. (Matta 6:19-21, 31-33) Nazarin Littafi Mai-Tsarki da ƙwazo, yin rabo cikin taron Kirista na kullum, da kuma aikin wa’azin Mulkin da himma zai taimake mu mu adana ƙaunarmu ga Jehovah, ga Ɗansa, da kuma ga Nassosi. (Zabura 119:105; Markus 13:10; Ibraniyawa 10:24, 25) Da haka, wannan zai taimake mu mu kasance a farke cikin bangaskiyarmu ga kalmar Allah.—Zabura 106:12.
14. Ta yaya aka ba shafaffun Kiristoci lada don bangaskiyarsu cikin kalmomin annabci na Jehovah?
14 Kamar yadda kalmomin annabci na Allah ya cika a dā, za mu iya kasancewa da bangaskiya cikin abin da ya faɗa game da nan gaba. Alal misali, bayanuwar Kristi yanzu cikin darajar Mulki ya zama gaskiya, kuma shafaffun Kiristoci masu aminci har mutuwa sun ga cikar annabci na wannan alkawarin: ‘Wanda ya yi nasara, a gareshi zan bayar da ci daga cikin itace na rai, wanda ke cikin aljanna ta Allah.’ (Ru’ya ta Yohanna 2:7, 10; 1 Tassalunikawa 4:14-17) Yesu ya ba waɗannan da suka ci nasara gatar “ci daga cikin itace na rai” a cikin ‘aljannar Allah’ na sama. A tashinsu kuma ta wurin Yesu Kristi, suna zama marasa mutuwa kuma marasa ɓatanci yadda Jehovah ya ba da izini, wanda shi “Sarki na zamanu, mara mutuwa, mara ganuwa, Allah makaɗaici.” (1 Timothawus 1:17; 1 Korinthiyawa 15:50-54; 2 Timothawus 1:10) Lada mai girma kuwa ne ƙaunarsu ga Allah da bai yi sanyi ba da kuma bangaskiyarsu cikin kalmomin annabcinsa!
15. An kafa tushe na “sabuwar duniya” a kan su wanene, kuma su wanene abokan tarayyarsu?
15 Jim kaɗan bayan an tashe shafaffu da suka mutu zuwa ‘aljana ta Allah’ a samaniya, an ’yantar da ringin shafaffu na Isra’ila a duniya daga “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 14:8; Galatiyawa 6:16) A cikinsu aka kafa tushen “sabuwar duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 21:1) Ta haka, aka haife wata “ƙasa,” kuma an gina ta cikin aljanna ta ruhaniya da ta ci gaba a duniya duka a yau. (Ishaya 66:8) A cikinta abokan tarayya masu kama da tumaki da yawa suna rugawa ciki a yanzu, “a cikin kwanaki na ƙarshe.”—Ishaya 2:2-4; Zechariah 8:23; Yohanna 10:16; Ru’ya ta Yohanna 7:9.
An Annabta Abin da Zai Faru nan Gaba ga Mutane a Cikin Kalmomin Annabci na Allah
16. Menene masu ba wa shafaffu goyon baya da aminci suke zato?
16 Menene masu ba wa shafaffu goyon baya da aminci suke zato? Su ma suna da bangaskiya cikin kalmomin annabci na Allah, kuma begensu na shiga sabuwar Aljanna ce. (Luka 23:39-43) A ciki za su sha daga “kogin ruwa na rai” mai ƙosad da rayuwa za su sami warkarwa daga “ganyayen itacen” da suke a bakinsa. (Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2) Idan kana cikin babban begen nan, bari ka ci gaba da nuna ƙauna mai zurfi ga Jehovah da bangaskiya cikin kalmomin annabcinsa. Bari ka zama cikin waɗanda suke more farin ciki mai yawa na rai na har abada a cikin duniya ta Aljanna.
17. Waɗanne albarkatai suke ƙunshe cikin rayuwa cikin Aljanna ta duniya?
17 Mutane ajizai ba za su iya kwatanta rai cikin Aljanna mai zuwa ta duniya ba, amma kalmomin annabci na Allah ya ba mu fahimi game da albarkatai da ke a ajiye wa mutane masu biyayya. Lokacin da Mulkin Allah zai yi sarauta ba tare da hamayya ba kuma a yi nufinsa a duniya yadda ake yi a sama, babu wani mutum mai kama da bisa—ko kaɗan, har dabbobi ma—ba za su “yi ciwutarwa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina” ba. (Ishaya 11:9; Matta 6:9, 10) Masu tawali’u za su gaji ƙasan, kuma “za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” (Zabura 37:11) Ba za a ga masu yunwa kuma ba, domin “za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.” (Zabura 72:16) Ba za a ƙara yin hawaye na azaba ba. Rashin lafiya zai wuce, har mutuwa ma ba za ta ƙara kasancewa ba. (Ishaya 33:24; Ru’ya ta Yohanna 21:4) Kana iya tsammanin—babu likitoci, babu magunguna, babu asibitoci ko kuma ƙungiyoyin warkar da mahaukata, babu jana’iza. Lallai wannan tsammani ne mai kyau sosai!
18. (a) Game da me aka tabbata wa Daniel? (b) Menene zai zama ‘rabon’ Daniel?
18 Har kabarbaru ma za su zama babu kome cikinsu yayin da tashin matattu zai ɗauki matsayin mace-mace. Ayuba mai adalci yana da irin wannan begen. (Ayuba 14:14, 15) Haka ma annabi Daniel ya yi, domin mala’ikan Jehovah ya ba shi tabbaci mai ta’azantarwa: “Yi tafiyarka, har ƙarshen kwanaki ya yi; gama za ka huta, ka tsaya a cikin rabonka, a ƙarshen kwanaki.” (Daniel 12:13) Daniel ya bauta wa Allah da aminci har ƙarshen ransa. Yanzu yana hutawa a mutuwa, amma zai “tashi” a “tashin masu adalci” a lokacin Sarautar Kristi na Alif. (Luka 14:14) Menene zai zama ‘rabon’ Daniel? To, a cikarsa ta Aljanna, annabcin Ezekiel ya nuna cewa mutanen Jehovah suna da wuri, har ma aka ba su ƙasa babu wariya kuma bisa ƙa’ida. (Ezekiel 47:13–48:35) Saboda haka, Daniel zai sami wuri a cikin Aljanna, amma rabonsa a wurin zai wuce samun ƙasa kawai. Zai haɗa da wurin da zai samu cikin nufin Jehovah.
19. Menene ake bukata don rayuwa cikin duniya ta Aljanna?
19 Kai da rabonka kuma fa? Idan kana da bangaskiya cikin Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki, lallai kana da muradin samun rai cikin duniya ta Aljanna. Kana iya ƙaga kana ciki, kana more albarka masu yawa, kana kula da duniya, kuma ka yi ma matattu maraba. Ballantana ma, Aljanna ita ce wuri da aka ba mutane. Allah ya halicci mutane biyu na farko su zauna cikin irin wurin nan ne. (Farawa 2:7-9) Kuma yana son mutane masu biyayya su zauna har abada cikin Aljanna. Za ka bi daidai da Nassosi don ka iya zama cikin biliyoyi da za su zauna cikin Aljanna ta duniya? Kana iya kasance ciki idan kana da ƙauna ta gaskiya ga Ubanmu na samaniya, Jehovah, da kuma bangaskiya mai daɗewa cikin kalmomin annabci na Allah.
[Hasiya]
a Duba sura ta 11 na Pay Attention to Daniel’s Prophecy! da ‘Makonni Bakwai’ a cikin Insight on the Scriptures, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga.
b Duba “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial,” shafofi 343-344, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga.
c Duba surori 4 da 9 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!
d Duba talifin nan “Ka Saurara ga Kalmomin Annabci na Allah,” da ke cikin Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Afrilu, 2000.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene annabci na farko, kuma wanene Ɗa na alkawarin?
• Waɗanne annabce-annabce game da Almasihu ne ya cika a kan Yesu?
• Ta yaya Daniel 2:44, 45 zai cika?
• Ga waɗanne abubuwa na nan gaba kalmomin annabci na Allah ya yi nuni?
[Hoto a shafi na 16]
Kana begen samun rai cikin duniya ta Aljanna?