‘Ka Ceci Kanka Da Waɗanda Suke Sauraronka’
“Ka maida hankali da kanka, da kuma koyawarka. . . . gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.”—1 TIMOTHAWUS 4:16.
1, 2. Menene yake motsa Kiristoci na gaskiya su ci gaba a cikin aikinsu na cetan rai?
AWANI wararren ƙauye a arewacin Thailand, mata da miji waɗanda Shaidun Jehovah ne sun yi amfani da sabon yare da suka koya wa wani ƙabila da suke da zama a kan dutse. Domin su yi bisharar Mulkin Allah ga waɗannan ƙauyawan, mata da mijin ba da daɗewa ba suka koyi yaren Lahu.
2 Maigidan ya yi bayani cewa: “Yana da wuya a kwatanta murnarmu da kuma gamsuwa da muka samu, a yin wa’azi tsakanin waɗannan mutane masu ban sha’awa. Babu shakka, mun ji muna cikin waɗanda suke cika Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7, shelar bishara ga ‘kowane al’umma da ƙabila da harshe.’ Da akwai sababbin wurare kaɗan da suka rage, waɗanda bishara ba ta isa ba tukuna, kuma wannan babu shakka tana ɗaya daga cikinsu. Muna da ɗaliban Littafi Mai-Tsarki kusan fiye da yadda za mu iya nazari da su.” Hakika, wannan mata da miji suna da begen cetan ba kansu kawai ba amma waɗanda suka saurare su. Mu Kiristoci, ba dukanmu muke da begen yin haka ba?
“Ka Maida Hankali da Kanka”
3. Domin mu ceci wasu, menene dole mu yi da farko?
3 Gargaɗin manzo Bulus ga Timothawus, “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyawarka” ya shafi dukan Kiristoci. (1 Timothawus 4:16) Lallai kuwa don mu taimaki wasu su sami ceto, dole ne da farko mu mai da hankali ga kanmu. Ta yaya za mu yi wannan? Abu ɗaya shi ne, dole ne mu zauna a farke ga lokatai da muke cikinsu. Yesu ya ba da alama haɗaɗɗe saboda mabiyansa su san lokacin “cikar zamani” ya zo. Duk da haka, Yesu ya ce kuma ba za mu san ainihin lokacin da ƙarshen zai zo ba. (Matta 24:3, 36) Me ya kamata mu yi ga wannan gaskiyar?
4. (a) Wane hali ya kamata mu ɗauka game da lokaci da ya rage wa wannan tsarin? (b) Wane hali ya kamata mu guje wa?
4 Kowannenmu na iya yin tambaya, ‘Ina amfani da wannan lokaci da ya rage wa wannan tsarin abubuwa domin in ceci kaina da kuma waɗanda suke sauraro na kuwa? Ko dai ina tunani cewa, “Tun da ba mu san ainihin lokacin da ƙarshen zai zo ba, ba zan dami kaina da shi ba”?’ Tunani na biyun yana da haɗari. Yana karo da gargaɗin Yesu: “Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’an da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.” (Matta 24:44) Babu shakka wannan ba lokaci ba ne da za mu kasala a hidimarmu ga Jehovah ko kuma mu juya ga duniya don kwanciyar rai da gamsar da rai.—Luka 21:34-36.
5. Wane misali Shaidun Jehovah kafin lokacin Kiristoci suka kafa?
5 Wata hanyar da za mu nuna muna mai da hankali ga kanmu ita ce ta jurewa cikin aminci yadda muke Kiristoci. Bayin Allah a dā sun ci gaba da jurewa, ko suna tsammanin ceto na take ko babu. Bayan ya ba da misalin shaidun nan kafin Kiristoci kamar su Habila, Anuhu, Nuhu, Ibrahim, da kuma Saratu, Bulus ya lura: “Ba su rigaya sun amshi alkawura ba, amma daga nesa suka tsinkaye su, suka yi masu maraba, suka shaida hakanan su baƙi ne, bare ne cikin duniya.” Ba su ba da kansu ga neman rayuwa mai sukuni ba, ba kuma sun faɗa ga matsi na lalata da ya kewaye su ba, amma sun jira su “amshi alkawura” da ƙwazo.—Ibraniyawa 11:13; 12:1.
6. Ta yaya yadda Kiristoci na farko suka ɗauki ceto ya shafi yayin rayuwarsu?
6 Kiristoci na ƙarni na farko ma sun ga kansu “baƙi” ne a cikin wannan duniyar. (1 Bitrus 2:11) Har ma bayan da an cece su daga halaka ta Urushalima a shekara ta 70 A.Z., Kiristoci na gaskiya ba su daina yin wa’azi ko kuma sun koma yin rayuwa irin ta duniya ba. Sun sani cewa ceto mai girma yana jiran waɗanda suka jure da amincinsu. Hakika, a shekara ta 98 A.Z., manzo Yohanna ya rubuta: “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:17, 28.
7. Ta yaya Shaidun Jehovah suka nuna jimiri a lokatan zamani?
7 A lokatan zamani ma Shaidun Jehovah sun jimre a aikinsu na Kirista, ko da yake sun fuskanci tsanantawa mai tsanani. Jimiri da suka yi banza ne? A’a, domin Yesu ya ba mu tabbaci: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira,” ko wannan ya kasance ƙarshen wannan tsohon tsarin ko kuma ƙarshen rayuwarmu ta yanzu. A lokacin tashin matattu, Jehovah zai tuna kuma zai ba wa dukan bayinsa da suka mutu lada.—Matta 24:13; Ibraniyawa 6:10.
8. Ta yaya za mu nuna cewa mun yi godiya ga jimiri na Kiristoci na dā?
8 Bugu da ƙari, muna murnar cewa amintattun Kiristoci na farko ba su damu da cetan kansu kawai ba. Babu shakka mu da muka koyi game da Mulkin Allah ta wurin ƙoƙarinsu muna godiya cewa sun jimre wajen bin umurnin Yesu: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . koya masu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Yayin da muna da zarafi, za mu iya nuna godiyarmu ta wurin yi wa wasu wa’azi waɗanda har yanzu ba su ji bisharar ba. Ko da yake wa’azi mataki na farko ne a wajen almajirantarwa.
‘Ka Mai da Hankali ga Koyarwanka’
9. Ta yaya hali mai kyau zai taimake mu mu fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da mutane?
9 Aikinmu ya ƙunshi ba wa’azi kawai ba amma har da koyarwa. Yesu ya umurce mu mu koyar da mutane su kiyaye dukan abubuwa da ya umurta. Hakika, a wasu wurare, kaɗan ne kawai suke nuna suna son su koyi game da Jehovah. Amma ganin yankin da baƙin ido zai gurgunta ƙoƙarinmu na fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da mutane. Yvette, majagaba a wani yanki da wasu suka taɓa kira busashe, ta lura cewa baƙi da suke wurin waɗanda ba su da irin wannan halin, sukan fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da mutane. Bayan ita ma ta canja yadda take ɗaukansu, Yvette kanta ta sami mutane da suke so su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki.
10. Menene ainihin aikinmu mu masu koyar da Littafi Mai-Tsarki?
10 Wasu Kiristoci suna jinkirin su gaya wa waɗanda suke da marmari za su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da su, domin suna jin cewa ba za su iya tafiyar da nazarin Littafi Mai-Tsarki da su ba. Hakika, iyawarmu ta bambanta. Amma ba sai muna da basira sosai kafin mu yi nasara ba, mu masu koyar da Kalmar Allah. Saƙo mai tsarki na Littafi Mai-Tsarki yana da ƙarfi, kuma Yesu ya ce masu kama da tumaki sun san muryar Makiyayi na gaskiya in sun ji ta. Aikinmu shi ne, mu gabatar da saƙon Makiyayi Mai Kyau, Yesu, ya fita sarai daidai yadda za mu iya.—Yohanna 10:4, 14.
11. Ta yaya za ka iya ka taimake ɗalibin Littafi Mai-Tsarki da kyau?
11 Ta yaya za ka gabatar da saƙon Yesu da kyau? Na farko, ka sanar da kanka abin da Littafi Mai-Tsarki ya ce game da jigo da ake bincikawa. Dole ne ka fahimci abu kai kanka kafin ka koya wa wasu. Ƙari ga haka, lokacin nazari ka yi ƙoƙari ka zamana a cikin yanayi mai kyau kuma na wartsakewa. Ɗalibai manya da ƙanana, sukan koyi abu da kyau idan suna sake kuma idan malamin ya daraja kuma yana kyautata masu.—Misalai 16:21.
12. Ta yaya za ka tabbata da cewa ɗalibi ya fahimci abin da ka ke koya masa?
12 Yadda ka ke malami, ba ka son kawai ka bayyana gaskiya kuma ɗalibin ya yi kwaikwayonka. Ka taimake shi ya fahimci abin da yake koyo. Ilimi, da abin da ɗalibin ya gani a rayuwa, da kuma sanin da yake da shi na Littafi Mai-Tsarki zai shafi fahimtar abin da ka ke gaya masa. Saboda haka, za ka iya tambayar kanka, ‘Shin ya gane muhimmancin nassi da aka nuna a wannan littafin nazari kuwa?’ Za ka iya bugun cikinsa da tambayoyi da ba za a iya amsa su da i ko a’a ba amma waɗanda suke bukatar bayani. (Luka 9:18-20) A wani gefen kuma, wasu ɗalibai suna jinkiri su yi wa malami tambaya. Saboda haka, za su ci gaba kawai ba tare da cikakkiyar fahimtar abin da ake koya masu ba. Ka ƙarfafa ɗalibin ya yi tambaya kuma ya gaya maka lokacin da bai fahimci wasu abubuwa ba.—Markus 4:10; 9:32, 33.
13. Ta yaya za ka taimake ɗalibi ya zama malami?
13 Muhimmancin nazarin Littafi Mai-Tsarki shi ne ka taimaki ɗalibin ya zama malami. (Galatiyawa 6:6) Domin a cim ma wannan, lokacin maimaita darussa, za ka iya tambayarsa ya bayyana wani abu a hanya mai sauƙi, kamar yana bayani ne ga wani wanda bai taɓa jin wannan abu ba. Daga baya, lokacin da ya ƙware ya fita hidima, za ka iya gayyatarsa ya bi ka zuwa fage. Wataƙila zai fi sakewa wajen yin aiki da kai, kuma abin da ya gani zai taimake shi ya sami gaba gaɗi har sai lokacin da ya kai ya je hidima da kansa.
Ka Taimake Ɗalibin Ya Zama Abokin Jehovah
14. Menene ainihin burinka na malami, kuma menene zai taimaka ka ci nasara?
14 Ainihin burin kowane malami Kirista shi ne ya taimake ɗalibi ya zama abokin Jehovah. Za ka cim ma wannan ba da baki kawai ba amma kuma da naka misali. Koyarwa da misali yana da ƙarfi wajen taɓa zukatan ɗalibai. Gani ya kori ji, musamman ma idan ya zo zancen koyar da ɗabi’a da kuma shuka ƙwazo cikin ɗalibin. Idan ya gani cewa kalmominka da kuma ayyukanka suna fitowa ne saboda dangantakar da Jehovah, zai motsa shi ya gina irin wannan dangantakar shi kansa.
15. (a) Me ya sa yake da muhimmanci ɗalibin ya gina nufi mai kyau na bauta wa Jehovah? (b) Ta yaya za mu taimake ɗalibi ya ci gaba da cin gaba a ruhaniya?
15 Kana son ɗalibin ya bauta wa Jehovah don ƙauna da yake masa, ba don kawai ba ya so ya halaka a Armageddon ba, amma don ƙauna da yake masa. Ta wurin taimakonsa ya gina irin wannan tsarkakken nufi, za kana yin gini da kayayyaki da ba sa cin wuta waɗanda zai jimre gwajin bangaskiyarsa. (1 Korinthiyawa 3:10-15) Mummunan nufi, kamar su muradi mai yawa na son ya yi koyi da kai ko kuma wani bil Adam, ba zai ba shi ƙarfi ya tsayayya wa rinjaya da ba na Kirista ba ko kuma ya ƙarfafa shi ya yi abin da yake da kyau ba. Ka tuna, ba za ka zama malaminsa har abada ba. Da ka ke da zarafi, za ka iya ƙarfafa shi ya matso kusa da Jehovah ta wurin karatun Kalmar Allah kowace rana kuma ya yi tunani a kansa. Ta wannan hanyar zai ci gaba da tsotsan “sahihan kalmomi” daga Littafi Mai-Tsarki da kuma littattafai na Littafi Mai-Tsarki bayan ka gama nazari da shi.—2 Timothawus 1:13.
16. Ta yaya za ka koya wa ɗalibin ya yi addu’a daga zuciya?
16 Za ka iya taimakon ɗalibin ya matso kusa da Jehovah ta wurin koya masa ya yi addu’a daga zuciyarsa. Ta yaya za ka yi wannan? Wataƙila ka nuna masa addu’ar misali na Yesu, da kuma wasu addu’o’i masu yawa daga zuci da aka rubuta cikin Littafi Mai-Tsarki, kamar waɗanda suke cikin Zabura. (Zabura 17, 86, 143; Matta 6:9, 10) Ƙari ga haka, idan ɗalibinka ya ga kana addu’a tukun ka fara kuma ka rufe nazarin, zai fahimci yadda ka ke ji game da Jehovah. Saboda haka, addu’arka ya kamata ta zama ta gaskiya ce kuma ba wata ɓoye-ɓoye, kuma ta nuna ta ruhaniya ce da kuma jiye-jiye daidai wa daida.
Yin Aiki don Ka Ceci ’Ya’yanka
17. Ta yaya iyaye za su taimake ’ya’yansu su tsaya a kan hanyar ceto?
17 Babu shakka waɗanda muke so mu cece su, sun ƙunshi iyalinmu. Da yawa cikin ’ya’yan da iyayensu Kiristoci ne, suna da gaskiya kuma ‘tabbatattu ne cikin bangaskiya.’ Ko da yake, wasu gaskiya ba ta yin jijiya mai zurfi a zukatansu ba. (1 Bitrus 5:9; Afisawa 3:17; Kolossiyawa 2:7) Da yawa cikin waɗannan matasa suna barin hanyar Kiristanci lokacin da suka kusa ko kuma suka balaga. Idan kana da ’ya’ya, me za ka yi domin irin wannan kada ya faru? Na farko, za ka yi aiki don ka sami yanayin iyali mai kyau. Rayuwar iyali mai kyau takan kafa hali mai kyau na bin doka, daraja ɗabi’u da suke daidai, da kuma farin ciki wajen dangantaka da wasu. (Ibraniyawa 12:9) Domin wannan, zumunci na kurkusa a iyali zai iya zama tushe da abota na yaro da Jehovah zai ƙarfafa. (Zabura 22:10) Iyalai masu ƙarfi suna yin abu tare—ko idan iyayen dole su sadakar da lokaci da za su yi amfani da shi wajen neman abin kansu. Ta wannan hanyar, kana koyar da ’ya’yanka ta misali su tsai da shawara mai dacewa a rayuwarsu. Iyaye, abin da ’ya’yanku suke bukata a gareku, shi ne ku kanku—lokacinku, kuzarinku, da kuma ƙaunarku ba abin duniya ba. Kana ba wa ’ya’yanka waɗannan abubuwan?
18. Waɗanne irin tambayoyi ne dole iyaye su taimake ’ya’yansu warwarewa?
18 Kada iyaye Kiristoci su yi zaton cewa ’ya’yansu ma za su tashi take su zama Kirista. Daniel, wani dattijo kuma mai ’ya’ya biyar, ya lura: “Dole iyaye su ɗauki lokaci su fitar da tantama da ’ya’yansu lallai za su ɗauko a makaranta da kuma wasu wurare. Dole su taimake ’ya’yansu cikin haƙuri su sami amsoshi ga tambayoyi kamar su: ‘Da gaske ne muna rayuwa a cikin lokacin ƙarshe? Da gaske ne addini na gaskiya ɗaya ne kawai? Me ya sa wasu ’yan makaranta waɗanda kamar suna da halin kirki bai kamata a yi cuɗanya da su ba? Da gaske ne ba shi da kyau a yi jima’i kafin aure?’ ” Iyaye, za ku iya dogara ga Jehovah wajen sa wa ƙoƙarinku albarka, domin shi ma yana damuwa da lafiyar ’ya’yanku.
19. Me ya sa ya fi muhimmanci iyaye su yi nazari da ’ya’yansu?
19 Wasu iyaye suna jin ba su cancanta ba idan ya zo yin nazari da ’ya’yansu ma. Duk da haka, bai kamata ka ji haka ba, domin babu wanda ya cancanta ya koyar da ’ya’yanka fiye da kai. (Afisawa 6:4) Yin nazari da ’ya’yanka zai sa ka san abin da yake zukatansu da kuma tunaninsu. Furcinsu daga zuci ne ko kuma dai daga baki ne kawai? Sun gaskata abin da suke koya kuwa da gaske? Jehovah ya tabbata kuwa a garesu? Za ka sami amsoshin waɗannan da kuma wasu tambayoyi masu muhimmanci idan ka yi nazari da ’ya’yanka.—2 Timothawus 1:5.
20. Ta yaya iyaye za su sa nazari na iyali ya zama mai daɗi kuma mai amfani?
20 Ta yaya za ka ci gaba da tsarin nazari na iyalinka sa’anda ka fara? Joseph, wani dattijo kuma uban ɗa da ’ya, ya ce: “Kamar dukan nazarin Littafi Mai-Tsarki, nazari na iyali ya kamata ya zama da daɗi, abin da kuwa kowa yake sauraro. Don mu cim ma wannan a cikin iyalinmu, bai kamata a kasance da yawan tauri ga zancen lokaci. Nazarinmu zai iya ɗaukan sa’a guda, amma idan a wasu lokutta muna da minti goma ne kawai, za mu yi nazarin. Wani abin da yake sa nazarinmu ya zama mai muhimmanci a mako ga yara shi ne wasan kwaikwaiyo da muke yi daga Litafi Na na Labarun Bible.a Tunani da kuma fahimi da za a samu sun fi muhimmanci da izifi da yawa da za a karanta.”
21. Yaushe ya kamata iyaye su koyar da ’ya’yansu?
21 Hakika, koyar da ’ya’yanka bai ƙare kawai da lokacin nazari da aka kafa ba. (Kubawar Shari’a 6:5-7) Shaidan a Thailand wanda aka ambata da farko ya ce: “Na tuna sarai yadda Baba yake ɗauka na zuwa aikin wa’azi a kan kekenmu, zuwa ɓangarori masu nisa na yankin ikklisiyarmu. Babu shakka, misali mai kyau na iyayenmu da kuma koyar da mu a cikin kowane yanayi ne ya taimake mu muka tsai da shawarar shiga hidimar cikakken lokaci. Kuma darussan sun ci gaba da amfani. Har yanzu ina aiki a cikin ɓangarori masu nisa na fagen!”
22. Menene zai zama sakamakon “maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka”?
22 Wata rana ba da jimawa ba, a lokaci da ya dace, Yesu zai zo ya yanka hukuncin Allah a kan wannan tsarin. Wannan babban aukuwa zai shiga tarihin halittu, amma amintattun bayin Jehovah za su ci gaba da bauta masa da tunanin samun ceto na har abada. Kana sa rai za ka kasance tsakaninsu, tare da ’ya’yanka da ɗalibanka na Littafi Mai-Tsarki? To ka tuna: “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka. Ka lizima cikin waɗannan; gama garin yin wannan za ka ceci kanka duk da masu-jinka.”—1 Timothawus 4:16.
[Hasiya]
a Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Yaya halinmu ya kamata ya zama, tun da ba mu san daidai lokacin hukunci na Allah ba?
• Ta waɗanne hanyoyi ne za mu ‘mai da hankali ga koyarwanmu’?
• Yaya za ka taimaki ɗalibi ya zama abokin Jehovah?
• Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su ɗauki lokaci don su koyar da ’ya’yansu?
[Hoto a shafi na 25]
Koyarwa a yanayi na daraja da kuma abokantaka yana inganta koyo
[Hoto a shafi na 28]
Kwaikwayon labarun Littafi Mai-Tsarki, kamar su Sulemanu yana yanke wa karuwai biyu hukunci, yakan sa nazari na iyali ya zama da daɗi