Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 2/1 pp. 28-29
  • “Aiki ne da ba Shi da Lahani”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Aiki ne da ba Shi da Lahani”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sabuwar Hanyar Shelar Bisharar
  • Abin da ke a Bayansa
  • Kayan Aiki Mai Ƙarfi don Shela
  • Hanyoyin Yin Wa’azi​—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam Wajen Yin Wa’azi
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Yesu Ya Yi Shekara 100 Yana Sarauta
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Ƙaruwarsu da Bunƙasarsu ta Zamani
    Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 2/1 pp. 28-29

Ka Tsaya Cikakke Kana Haƙƙaƙewa

“Aiki ne da ba Shi da Lahani”

A FARKON kwanakin tarihinsu na zamani, Shaidun Jehovah sun damu ƙwarai da annabci guda na Yesu Kristi: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Matiyu 24:14) Da 1914—farkon “zamanin ƙarshe”—ta gabato, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na gaskiya suka fara kamfen da babu irinsa a dukan duniya, na ilimantarwa bisa Nassosi Masu Tsarki da haƙƙaƙewa.—2 Timoti 3:1.

Domin su cim ma niyyarsu ta shelar bishara a dukan duniya, waɗannan bayin Jehovah suka yi amfani da sabuwar hanya, na gaba gaɗi, bayyananniya. Domin mu samu ƙarin bayani, bari mu koma lokacin dā.

Sabuwar Hanyar Shelar Bisharar

Janairu ne na shekara ta 1914. Ka yi tunanin kana zaune tsakanin mutane 5,000 a babban filin wasa mai duhu a New York City. A gaban ka ga labulen majigi babba. Wani mutum mai furfura ya bayyana da dogon kwat a majigin. Ka taɓa ganin majigi da ba ya magana, amma wannan mutumin yana magana, kuma kana jin kalmominsa. Kana ganin abu ne sabon ƙira, kuma saƙonsa babu irinsa. Mai maganar Charles Taze Russell ne, shugaban Watch Tower Society na farko, kuma abin da aka ƙirƙiron shi ne “Photo-Drama of Creation.”

C. T. Russell ya fahimci amfanin majigi mai motsi wajen isa taron mutane. A shekara ta 1912, ya fara shirya “Photo-Drama of Creation.” A ƙarshe ya kasance majigi ne mai magana da mara magana mai tsawon awa takwas, a ciki da launuka da kuma sauti.

An shirya shi a nuna kashi huɗu, “Photo-Drama” ɗin ya nuna wa masu kallo daga lokacin halitta har zuwa tarihin ’yan Adam zuwa ƙarshen nufin Allah domin duniya da kuma mutane a ƙarshen Sarautar Alif na Kristi. Shekaru da yawa za su shige tukuna a fara amfani da irin wannan fasahar wajen kasuwanci. Hakika, miliyoyi sun kalli “Photo-Drama of Creation” kyauta!

Waƙoƙi masu daɗi da kuma jawabai wajen 96 daga garmaho aka shirya domin “Photo-Drama” ɗin. Aka shirya majigi masu motsi masu zane mai kyau waɗanda ke kwatanta tarihin duniya. Kuma ya kasance tilas a yi sababbin zane-zane da kuma ƙira. Wasu majigan marasa maganar da masu maganar, masu launuka an mai da hankali sosai wajen zana su. Kuma an yi hakan a kai a kai, a wani lokaci, ana shirya 20 mai kashi huɗu. Wannan ya sa ya yiwu a nuna “Photo-Drama” a birane dabam dabam har 80 a kowacce rana!

Abin da ke a Bayansa

Menene ke faruwa a baya a lokacin nuna “Photo-Drama” ɗin? “Majigin ya fara da nuna hoton Ɗan’uwa Russell,” in ji Ɗalibar Littafi Mai Tsarki Alice Hoffman. “Da ya bayyana a labulen majigin, leɓunansa sai su fara motsi, sai a kunna garmaho . . . mu kuma muna jin daɗin sauraron muryarsa.”

Da take magana game da majigin mai sauri, Zola Hoffman ta tuna: “Na zauna a wajen baki buɗe domin mamaki da muke kallon kwatancin zamanin halitta. Da akwai furannin bi-rana suka fara tahowa a hankali a idanunmu.”

Masoyin kaɗe-kaɗe Karl F. Klein na Hukumar Mulki ta Shaidun Jehovah ya daɗa cewa: “A wannan lokacin da ake nuna waɗannan hotunan, ana kuma yin kaɗe-kaɗe mai daɗi, wannan kiɗa mai daɗi ƙwarai kamar Narcissus da kuma Humoreske.”

Har ila da akwai kuma abin tunawa. “Wani lokaci abin ban dariya na rashin sa’a sai ya faru,” in ji Clayton J. Woodworth, Ƙarami. “Akwai lokacin da garmahon yake magana ‘Ku Gudu Kamar Tsuntsaye Zuwa Dutsensu,’ sai majigin ya nuna hoton wata babbar dabba, wadda ta wanzu kafin lokacin Ambaliya”!

Ban da “Photo-Drama of Creation,” ba da daɗewa ba aka sami “Eureka Drama.” (Dubi akwati.) Ɗaya yana ɗauke da laccoci da aka ɗauka a kan faifai, da kuma kaɗe-kaɗe. Wani kuma yana ɗauke da laccocin da kuma majigi. Ko da yake “Eureka Drama” ba ta da hotuna masu motsi, ta yi nasara ƙwarai idan ka nuna a inda babu taron mutane da yawa.

Kayan Aiki Mai Ƙarfi don Shela

A ƙarshen shekara ta 1914, an nuna “Photo-Drama” ga mutane da suka kai fiye da 9,000,000 a Amurka ta Arewa, Turai, da kuma Australiya. Ko da yake ba su da yawa, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna da tabbaci mai ƙarfi na shelar bishara ta wannan sabuwar hanyar. Da farin ciki sun ba da kyauta da ake bukata don hayar wajeje masu kyau domin nuna wannan. Saboda haka, “Photo-Drama of Creation” ya yi aiki mai girma wajen sanar da mutane Kalmar Allah da kuma nufe-nufensa.

A wata wasiƙa zuwa ga C. T. Russell da wani ya rubuta: “Wannan ziyara ta farko zuwa Drama naka ta canja mini rayuwa; ko kuma dai in ce, canji a sani na na Littafi Mai Tsarki.” Wata kuma ta ce: “An rinjaye ni cikin tarko na haɗari na ruhaniya kuma ina jin ‘Photo-Drama of Creation’ wanda aka nuna a nan bara ne ya cece ni. . . . A yanzu ina da salama wanda duniya ba za ta iya bayarwa ba, wadda ba zan rabu da ita ba da dukan arzikinta.”

Demetrius Papageorge, ma’aikaci a hedkwata na Society na dogon lokaci, ya yi kalami: “ ‘Photo-Drama’ aiki ne da ba shi da lahani, idan muka duba adadi kaɗan na Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin da kuma kuɗi kaɗan da ke akwai. Babu shakka ruhun Jehovah ya tallafa!”

[Box/Hotuna a shafuffuka na 28, 29]

“Eureka Drama”

Wata takwas bayan nuna “Photo-Drama,” na farko Society ya ga da bukatar yin tanadin wani irinsa da aka kira “Eureka Drama.” Yayin da aka ci gaba da nuna dukan “Photo-Drama” a manyan birane, “Eureka” kuma tana idar da saƙon a ƙauyuka da kuma karkara. Wani ɓangaren “Eureka Drama” an kwatanta ta da ba wa “ ’yan’uwa mata damar” yin wa’azi. Me ya sa? Domin nauyin kwalin garmahonta awo 30 ne kawai. Amma fa, domin nunawa dole ne a ɗauki garmaho.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba