Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 2/1 pp. 18-23
  • Kana Rayuwa Daidai Da Keɓe Kai Da Ka Yi Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Rayuwa Daidai Da Keɓe Kai Da Ka Yi Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ba Su Musunci Keɓe Kansu Ba
  • Misalan Zamani na Keɓe Kai
  • Ɗaukan Keɓe Kanmu Yadda Ya Kamata
  • Mayar da Kowace Rana ta Zama da Muhimmanci
  • Ka Sa Idonka a Buɗe
  • Mecece Aniyyarka?
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Wa Jehovah Da Zuciya Da Ta Kahu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Za Ka Keɓe Kanka Ga Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • ‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 2/1 pp. 18-23

Kana Rayuwa Daidai Da Keɓe Kai Da Ka Yi Kuwa?

“Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba.”—KOLOSIYAWA 3:23.

1. A duniya, me ake nufi da furcin nan “keɓe kai”?

TA YAYA ’yan wasan guje-guje suke kai wa ƙarshen iyawarsu? A wasan tanis, ƙwallon ƙafa, guje-guje, ƙwallon galf ko kuma kowane irin wasa, mafi iyawa yake kai wa matsayi na ɗaya idan ya ba da kansa. Abubuwa mafi amfani sune lafiyar jiki da kuma na hankali. Wannan ya dace da wata ma’anar furcin nan “keɓe kai” wadda take nufi “ba da kai a hanyar wani tunani ko kuma aiki.”

2. Menene “keɓewa” take nufi a cikin Littafi Mai Tsarki? Ka ba da kwatanci.

2 Amma, me “keɓe kai” yake nufi a Littafi Mai Tsarki? “Keɓe” ya fassara wani izifi na Ibrananci da ke da ma’anar “kasancewa a ware; ka ware; janye.”a A Isra’ila ta dā, Babban Firist Haruna ya naɗa rawaninsa ‘kambi mai tsarki, alamar keɓewa,’ wanda allo ne na ɗamara na zinariya tsantsa wanda aka haƙa rubutun Ibrananci a kai ‘Tsarki ya tabbata ga Jehovah.’ Wannan ya kasance abin tuni ga babban firist ɗin cewa dole ne ya guji yin wani abu da zai ɓata alfarwa ta sujjada ‘domin alamar keɓewa ce, da kuma man shafewa na Allah, suna kansa.’—Fitowa 29:6; 39:30; Littafin Firistoci 21:12.

3. Ta yaya ya kamata keɓe kai ya shafi ɗabi’armu?

3 Za mu ga cewa a wannan hanyar keɓe kai babbar magana ce ƙwarai. Tana nufin ba da kai a sani kai bawan Allah ne, kuma tana bukatar ɗabi’a mai tsabta. Saboda haka, za mu yi farin cikin dalilin da ya sa Bitrus ya ɗauko abin da Jehovah ya ce: “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.” (1 Bitrus 1:15, 16) Yadda muke Kiristoci muna da hakki mai girma na rayuwa daidai da keɓe kai da muka yi, mu kasance amintattu har zuwa ƙarshe. Amma menene keɓe kai na Kiristoci ya ƙunsa?—Littafin Firistoci 19:2; Matiyu 24:13.

4. Ta yaya muka kai matsayin keɓe kai, kuma da me za a kwatanta shi?

4 Bayan mun sami cikakken sani na Jehovah Allah da kuma nufe-nufensa da kuma na Yesu Kristi da kuma aikinsa cikin waɗannan nufe-nufen, mu muka tsai da shawarar za mu bauta wa Allah da dukan zukatanmu, hankalinmu, ranmu, da kuma ƙarfinmu. (Markus 8:34; 12:30; Yahaya 17:3) Za a iya ɗaukar wannan rantsuwa ce da mutum ya yi, keɓe kai ga Allah babu ragi. Keɓe kanmu ba abu ba ne da muka yi domin zuciya ta kwashe mu. Abu ne da muka auna a hankali da addu’a, ta wajen amfani da hujja. Saboda haka, ba shawara ba ce ta ɗan lokaci. Ba za mu taɓa zama kamar wani wanda ya fara huɗa a gona sai ya yasar a hanya domin aikin yana da wuya ba, ko kuma domin girbi yana can gaba da nisa, ko ma dai domin babu tabbas. Ka ga misalan wasu da suka ɗaura hannunsu a ‘keken noma’ na hakki na tsarin Allah cikin dukan wahala.—Luka 9:62; Romawa 12:1, 2.

Ba Su Musunci Keɓe Kansu Ba

5. Ta yaya Irmiya ya ba da misali da ya fice na bawan Allah da ya keɓe kai?

5 Hidimar annabci na Irmiya a Urushalima ya kai shekara fiye da 40 (647-607 K.Z.), kuma ba aiki ba ne mai sauƙi. Ya san inda ya kasa ƙwarai. (Irmiya 1:2-6) Yana bukatar ƙarfafa da kuma jimiri don ya fuskanci mutane masu taurin zuciya na Yahuda kullum. (Irmiya 18:18; 38:4-6) Amma dai, Irmiya ya dogara ga Jehovah Allah, wanda ya ƙarfafa shi har da ya zama bawan Allah wanda ya keɓe kansa da gaske.—Irmiya 1:18, 19.

6. Wane misali ne manzo Yahaya ya kafa mana?

6 To, yaya game da bangaskiyar manzo Yahaya, wanda ya yi hijira da tsufarsa zuwa mugun tsibirin nan da ake kira Batamusa domin “maganar Allah da kuma shaidar Yesu”? (Wahayin Yahaya 1:9) Ya jimre kuma ya rayu daidai da keɓe kai da ya yi na Kirista na kusan shekara 60. Ya rayu har bayan halaka Urushalima da sojojin Roma suka yi. Ya sami gatar rubuta Lingila, wasiƙu uku hurarru, da kuma littafin Wahayin Yahaya, a ciki ya ga yaƙin Armageddon. Ya bari ne da ya ga cewa Armageddon ba zai zo ba a lokacin da yake raye? Ya faɗa cikin rashin damuwa ne? A’a, Yahaya ya kasance amincacce har mutuwarsa, da sanin cewa ko da yake ‘lokaci ya gabato,’ cikar wahayinsa a can gaba ce.—Wahayin Yahaya 1:3; Daniyel 12:4.

Misalan Zamani na Keɓe Kai

7. Ta yaya wani ɗan’uwa ya ba da misalin keɓe kai mai kyau na Kirista?

7 A zamanin yau, dubban amintattun Kiristoci sun manne wa keɓe kansu da ƙwazo duk da cewa ba su rayu su ga Armageddon ba. Ɗaya cikin irin waɗannan shi ne Ernest E. Beavor na Ingila. Ya zama Mashaidi a shekara ta 1939 a farkon Yaƙin Duniya na II, ya bar harkokinsa na kuɗi na buga hotuna, domin ya fara aikin hidima na cikakken lokaci. Domin yana riƙe tsakatsakinsa na Kirista, aka tura shi gidan sarƙa na shekara biyu. Iyalinsa suka tallafa masa, kuma a shekara ta 1950 ’ya’yansa uku suka halarci Makarantar Watchtower ta Littafi Mai Tsarki ta Gilead domin koyar da masu wa’azi a ƙasashen waje, a New York. Ɗan’uwa Beavor yana da ƙwazo ƙwarai a ayyukan wa’azi har abokanansa suna kiransa Armageddon Ernie. Ya rayu daidai da keɓe kansa cikin aminci, har zuwa mutuwarsa a shekara ta 1986, yana shelar kusancin yaƙin Allah na Armageddon. Bai ɗauki keɓe kansa kamar kwangila na gajeran lokaci ba tsakaninsa da Allah!b—1 Korantiyawa 15:58.

8, 9. (a) Wane misali ne matasa da yawa suka kafa a Spain a lokacin mulkin Franco? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka dace?

8 Wani misali na ƙwazo da bai sanyaya ba an samo shi daga Spain. A zamanin mulkin Franco (1939-1975), Shaidu matasa da suka keɓe kansu sun dage a kan tsakatsakinsu na Kirista. Da yawa cikinsu sun yi shekara goma ko ma fiye da haka a fursunar sojoji. Wani Mashaidi, Jesús Martín, da aka tara shekaru da ya kashe a fursuna sun kai 22. Ya sha bugu ƙwarai da yake fursuna a Arewacin Afirka. Babu cikin waɗannan da yake da sauƙi amma ya ƙi ya ba da kai.

9 Sau da yawa, waɗannan samari ba su san ma lokacin da za a sallame su ba, idan ma za a yi ke nan, domin an yi musu ɗaurin talala. Duk da haka, sun riƙe amincinsu da ƙwazonsu a hidima a cikin wannan yanayin. Da yanayi ya fara gyaruwa a shekara ta 1973, da yawa cikin waɗannan Shaidun, a shekarunsu na 30, aka sallame su daga fursuna suka fara hidimar cikakken lokaci babu ɓata lokaci, wasu suka zama majagaba na musamman da kuma masu kula masu ziyara. Sun rayu daidai da keɓe kansu a fursuna, kuma yawanci suna ci gaba da yin haka tun da aka sallame su.c Mu a yau fa? Muna da aminci a keɓe kanmu kamar waɗannan amintattu?—Ibraniyawa 10:32-34; 13:3.

Ɗaukan Keɓe Kanmu Yadda Ya Kamata

10. (a) Yaya ya kamata mu ɗauki keɓe kanmu? (b) Yaya Jehovah yake ganin hidimarmu dominsa?

10 Yaya muke ɗaukan keɓe kanmu ga Allah don mu yi nufinsa? Shi ne abu na farko a rayuwarmu? Ko yaya yanayinmu, ko yara ne ko tsofaffi, masu aure ko marasa aure, masu lafiya ko majiyyata, ya kamata mu yi ƙoƙari mu rayu daidai da keɓe kanmu, daidai da yanayinmu. Yanayin wani zai ƙyale shi ya yi hidima ta cikakken lokaci na majagaba, wanda ya ba da kansa a ofishin reshe na Watch Tower Society, mai wa’azi a ƙasashen waje, ko kuma a hidimar ziyara. Wasu iyaye kuma, hannunsu zai cika da ɗawainiya ta zahiri da kuma ta ruhaniya a kan bukatun iyalin. Sa’o’i kaɗan da suke bayarwa a hidima kowane wata yana kaɗan ne a idanun Jehovah fiye da sa’o’i da yawa da masu hidima ta cikakken lokaci suke bayarwa? A’a. Allah bai taɓa bukatar abin da ba mu da shi daga wurinmu ba. Manzo Bulus ya faɗi wannan mizanin: “In mutum na da niyyar bayarwa, bayarwa tasa za ta zama abar karɓa ce bisa ga yawan abin da ya ke da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.”—2 Korantiyawa 8:12.

11. A kan me cetonmu ya dangana?

11 Ko yaya dai, cetonmu bai dangana a kan wani abin da za mu yi ba, amma bisa ga alherin Jehovah ta wajen Kristi Yesu, Ubangijinmu. Bulus ya ba da bayani sarai: “ ’Yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah. Amma ta alherin da Allah ya yi musu kyauta sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.” Amma dai, ayyukanmu tabbaci ne na bangaskiyarmu ga alkawuran Allah.—Romawa 3:23, 24; Yakubu 2:17, 18, 24.

12. Me ya sa bai kamata mu yi gwaji ba?

12 Babu wani amfani mu yi gwaji da wasu game da lokacinmu a hidimar Allah, ko kuma littattafai da muka bayar, kuma adadin nazarin Littafi Mai Tsarki da muke gudanarwa. (Galatiyawa 6:3, 4) Ko da me muka cim ma a hidimar Kirista, dukanmu muna bukatar mu tuna kalmomin tawali’u na Yesu: “Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da ke wajibinmu kurum.’ ” (Luka 17:10) Sau nawa za mu iya cewa mun yi “duk abin da aka umarce” mu? Saboda haka, tambayar ita ce, Yaya ingancin bautarmu ga Allah ya kamata ya zama?—2 Korantiyawa 10:17, 18.

Mayar da Kowace Rana ta Zama da Muhimmanci

13. Wane hali muke bukata yayin da muke rayuwa ta keɓe kai?

13 Bayan ya yi wa matan aure, magidanta, yara, iyaye, da kuma bayi gargaɗi, Bulus ya rubuta: “Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba, da ya ke kun sani [Jehovah] zai ba ku gādo sakamakonku. Ubangiji Almasihu kuke bauta wa fa!” (Kolosiyawa 3:23, 24) Ba ma bauta domin mu burge mutane ta abin da muka cim ma a hidimar Jehovah. Muna ƙoƙarin mu bauta wa Allah ta wajen bin misalin Yesu Kristi. Ya yi hidimarsa wadda take na ɗan lokaci cikin gaggawa.—1 Bitrus 2:21.

14. Wane gargaɗi Bitrus ya bayar game da kwanaki na ƙarshe?

14 Manzo Bitrus ma ya nuna gaggawa. A cikin wasiƙarsa ta biyu, ya yi gargaɗi cewa a kwanaki na ƙarshe za a yi masu ba’a—’yan ridda da masu shakka—waɗanda domin nasu ra’ayi, sun yi tambaya game da bayyanar Kristi. Duk da haka, Bitrus ya ce: “Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma’anar jinkiri, amma mai haƙuri ne gare ku, ba ya so kowa ya halaka, sai dai kowa ya kai ga tuba. Duk da haka ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo.” Hakika, ranar Jehovah babu shakka za ta zo. Saboda haka, ya kamata mu damu kowace rana game da yadda muke da tabbaci da kuma bangaskiyarmu take da ƙarfi game da alkawarin Allah.—2 Bitrus 3:3, 4, 9, 10.

15. Yaya za mu ɗauki kowacce rana ta rayuwarmu?

15 Mu rayu daidai da keɓe kanmu a hanyar da ta dace, ya kamata mu yi amfani da kowacce rana ga yabon Jehovah. A ƙarshen kowacce rana, za mu iya dubawa mu ga yadda muka daɗa ga tsarkake sunan Allah da kuma shelar bisharar Mulkinsa? Wataƙila ta wajen ɗabi’a mai tsabta, taɗi mai kyau, ko kuma ta wajen nuna ƙauna da damuwa ga iyali da kuma abokane. Muna amfani da zarafi da muka samu wajen gaya wa wasu begenmu na Kirista? Ka taimake wani ya yi tunani a kan muhimmancin alkawuran Allah? Ya kamata mu yi abu mai kyau a hanya ta ruhaniya kowacce rana, kamar yadda take, mu tara ajiya mai kyau ta ruhaniya.—Matiyu 6:20; 1 Bitrus 2:12; 3:15; Yakubu 3:13.

Ka Sa Idonka a Buɗe

16. A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan yake ƙoƙari ya raunana keɓe kanmu ga Allah?

16 Muna rayuwa cikin lokatai da suke zama da wuya ƙwarai ga Kiristoci. Shaiɗan da barorinsa suna ƙoƙarin ruɗar da bambanci tsakanin nagarta da mugunta, tsabta da ƙazanta, ɗabi’a da rashin ta, abu mai kyau da marar kyau. (Romawa 1:24-28; 16:17-19) Ya sauƙaƙa mana yadda za mu ɓata zukatanmu ta wajen telibijin da kuma kwamfuta. Idanunmu na ruhaniya za su iya zama da hazo hazo, ko kuma su rinjayu, saboda mun kasa fahimtar kissoshinsa. Ƙudurinmu na za mu ci gaba da rayuwar keɓe kai zai raunana kuma hannunmu a kan “keken noma” zai iya zama sako sako idan muka ƙi abubuwa masu muhimmanci na ruhaniya.—Luka 9:62; Filibiyawa 4:8.

17. Ta yaya gargaɗin Bulus zai taimake mu mu adana dangantakarmu da Allah?

17 Kalmomin Bulus ga ikilisiya ta Tasalonika sun zo a kan kari: “Wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci, kowannenku kuma ya san yadda zai [bi da jikinsa] da tsarki da mutunci, ba ta muguwar sha’awa ba, yadda al’ummai ke yi, waɗanda ba su san Allah ba.” (1 Tasalonikawa 4:3-5) Lalata ta kai ga yanke wa wasu zumunci a ikilisiyar Kirista waɗanda suka yi wasa da keɓewar kansu ga Allah. Sun ƙyale dangantakarsu da Allah ta raunana, saboda haka bai kasance da wani muhimmanci ba a rayuwarsu. Duk da haka, Bulus ya ce: “Ba ga zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne. Saboda haka kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, Allah ya ƙi, shi da ke ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.”—1 Tasalonikawa 4:7, 8.

Mecece Aniyyarka?

18. Mecece ta kamata ta zama aniyyarmu?

18 Idan mun fahimci muhimmancin keɓe kanmu ga Jehovah Allah, me ya kamata mu ƙudiri aniyyar yi? Aniyyarmu ita ce mu riƙe lamiri mai kyau game da ɗabi’armu da kuma hidimarmu. Bulus ya yi kashedi: “Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.” (1 Bitrus 3:16) Wataƙila mu wahala kuma mu sha zagi domin ɗabi’armu ta Kirista, amma haka ya kasance ga Almasihu domin bangaskiyarsa da kuma amincinsa ga Allah. Bitrus ya ce: “Tun da ya ke Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra’ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan.”—1 Bitrus 4:1.

19. Me za mu so a ce game da mu?

19 Hakika, aniyyarmu ta rayuwa daidai da keɓe kanmu za ta kāre mu daga tarkon duniyar Shaiɗan da take jiyya a ruhaniya, a ɗabi’a, da kuma a zahiri. Amma fiye da haka ma, za mu samu tabbacin cewa muna da tagomashin Allah, wanda ya fi ko menene da Shaiɗan da barorinsa za su ba mu. Saboda haka, kada mu yarda a ce muna ƙyale ƙaunar da muke da ita lokacin da muka san gaskiya da farko. Maimakon haka, ya kamata a ce da mu kamar yadda aka ce da ikilisiyar Tiyatira ta ƙarni na farko: “Na san ayyukanka, da ƙaunarka, da bangaskiyarka, da ibadarka, da jimirinka, ayyukanka kuma na yanzu sun fi na farkon.” (Wahayin Yahaya 2:4, 18, 19) To, kada mu kasance a tsaka-tsaki game da keɓe kanmu, amma mu “himmantu a ruhu” da ƙwazo har ƙarshe—domin ƙarshen ya yi kusa.—Romawa 12:11; Wahayin Yahaya 3:15, 16.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro, 15 ga Afrilu, 1987 (Turanci), shafi na 31.

b Duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 1980 (Turanci), shafuffuka 8-11, domin cikakken labarin rayuwar Ernest Beavor.

c Duba 1978 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka 156-158, 201-218, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.

Ka Tuna?

• Menene keɓe kai ya ƙunsa?

• Waɗanne bayin Jehovah ne da suka keɓe kai na dā da na zamani suka cancanci mu yi koyi da su?

• Yaya ya kamata mu ɗauki bautarmu ga Allah?

• Menene ya kamata ya kasance aniyyarmu game da keɓe kanmu ga Allah?

[Hoto a shafi na 19]

Irmiya ya kasance da aminci duk da wulakanci da aka yi masa

[Hoto a shafi na 20]

Ernest Beavor ya kafa misali na Kirista mai ƙwazo ga yaransa

[Hoto a shafi na 21]

Ɗarurruwan matasa Shaidu a fursunar Spain sun riƙe amincinsu

[Hotuna a shafi na 22]

Bari kowacce rana mu kasance da abu mai kyau na ruhaniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba