Me Ya Sa Za Ka Keɓe Kanka Ga Jehobah?
“A cikin wannan dare mala’ikan Allah wanda ni nasa ne . . . ya tsaya daura da ni.”—A. M. 27:23.
1. Waɗanne matakai ne waɗanda suka miƙa kansu don baftisma sun riga sun ɗauka, kuma waɗanne tambayoyi ne hakan ya ta da?
“BISA ga hadayar Yesu Kristi, kun tuba daga zunubanku kuma kun keɓe kanku ga Jehobah domin ku yi nufinsa?” Wannan tana ɗaya daga cikin tambayoyi biyu da waɗanda suke son su yi baftisma suke amsawa a ƙarshen jawabin baftisma. Me ya sa Kiristoci suke bukatan su keɓe kansu ga Jehobah? Ta yaya keɓe kai ga Allah zai amfane mu? Me ya sa mutum ba zai bauta wa Allah yadda ya dace ba idan bai keɓe kansa a gare shi ba? Don mu fahimci amsoshin, muna bukatan mu fara bincika ko menene keɓe kai.
2. Menene keɓe kai ga Jehobah yake nufi?
2 Menene keɓe kai ga Allah yake nufi? Ka lura da yadda manzo Bulus ya kwatanta dangantakarsa da Allah. A gaban mutane da yawa da suke cikin jirgin ruwan da ya saka su cikin haɗari, ya kira Jehobah “Allah wanda ni nasa ne.” (Karanta A. M. 27:22-24.) Dukan Kiristoci na gaskiya na Jehobah ne. Akasin haka, duniya gabaki ɗaya “tana kwance cikin Shaitan.” (1 Yoh. 5:19) Kiristoci sun zama na Jehobah sa’ad da suka keɓe kansu a gare shi cikin addu’a. Irin wannan keɓe kai alkawari ne da mutum ya yi. Bayan hakan sai a yi baftisma cikin ruwa.
3. Baftismar Yesu alamar mecece, kuma yaya mabiyansa za su iya yin koyi da misalinsa?
3 Yesu ya kafa mana misali mai kyau sa’ad da ya zaɓi ya yi nufin Allah. Domin an haife shi cikin keɓaɓɓiyar al’ummar Isra’ila, an riga an keɓe shi ga Allah. Duk da haka, a lokacin baftismarsa ya yi wani abu fiye da wanda ake bukata a ƙarƙashin Doka. Kalmar Allah ta nuna cewa ya ce: “Ga ni, na zo . . . garin in aika nufinka, Ya Allah.” (Ibran. 10:7; Luk 3:21) Saboda haka, baftismar Yesu ta nuna cewa ya ba da kansa ga Allah don yin nufin Ubansa. Mabiyansa suna yin koyi da misalinsa sa’ad da suka miƙa kansu don baftisma. Amma, baftismar da suka yi a cikin ruwa ta nuna a fili cewa sun keɓe kansu cikin addu’a ga Allah.
Yadda Muke Amfana ta Wurin Keɓe Kanmu
4. Mecece abuta tsakanin Dauda da Jonathan ta koya mana game da wa’adi?
4 Keɓe kai na Kirista batu ne mai muhimmanci sosai. Wannan ba yin wa’adi kawai ba ne. To, ta yaya keɓe kai yake da amfani a gare mu? Ta wurin yin kwatanci, bari mu yi la’akari da yadda yin wa’adi a dangantaka na ’yan Adam yake kawo amfani. Misali guda shi ne yin abota. Don ka more gatan samun aboki, dole ne ka karɓi hakkin zama aboki. Hakan ya ƙunshi wa’adi, wato, son cika hakkin kula da abokinka. Ɗaya cikin fitattun abokantaka da aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki ita ce ta Dauda da Jonathan. Sun ma ɗauki alkawari yin abota da juna. (Karanta 1 Sama’ila 17:57; 18:1, 3.) Ko da yake yana da wuya a samu abuta da irin wannan wa’adi, yawancin abokantaka na yin nasara sa’ad da mutanen suka ji suna da hakki ga juna.—Mis. 17:17; 18:24.
5. Ta yaya bawa zai amfana ta wurin zama har abada da shugabansa mai kirki?
5 Dokar da Allah ya ba Isra’ila ta kwatanta wata dangantaka da mutane suka amfana ta wurin yin wa’adi. Idan bawa yana son ya ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kāriyar shugaba mai kirki, yana iya yin wa’adi na dindindin da shi. Dokar ta ce: “Idan bawan ya faɗi a sarari, Ina ƙaunar ubangijina, da matata, da ’ya’yana; ba ni fita: sa’annan ubangijinsa zai kai shi wurin Allah, ya kawo shi wurin ƙyaure kuma, ko dogarin ƙofa: ubangijinsa kuwa za ya huda kunnensa da basilla; zai yi masa bauta har abada.”—Fit. 21:5, 6.
6, 7. (a) Ta yaya wa’adi yake amfanar mutane? (b) Menene hakan yake nunawa game da dangantakarmu da Jehobah?
6 Aure dangantaka ce da ke bukatan yin wa’adi sosai. Wa’adi ne ga mutum, ba yarjejeniyar da aka cika a takarda ba kawai. Mutane biyu da suke zama tare kawai ba tare da yin aure ba ba za su taɓa more kāriya ta ainihi ba, yaransu ma haka. Amma waɗanda suka yi aure mai daraja suna da dalili na Nassi da zai sa su ƙoƙarta su magance matsalolinsu cikin ƙauna sa’ad da suka taso.—Mat. 19:5, 6; 1 Kor. 13:7, 8; Ibran. 13:4.
7 A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, mutane sun amfana ta wajen yin yarjejeniyar kasuwanci da kuma aiki. (Mat. 20:1, 2, 8) Hakan gaskiya ne a yau. Alal misali, muna amfana ta wajen rubuta yarjejeniya na kwangila kafin mu soma kasuwanci ko kuma kafin mu soma yin aiki a wani kamfani. Saboda haka, idan wa’adi yana ƙarfafa dangantaka kamar abota, aure, da kuma aiki, to, keɓe kanka gabaki ɗaya zai amfane ka a dangantakarka da Jehobah! Bari yanzu mu bincika yadda mutane a dā suka amfana ta wajen keɓe kansu ga Jehobah Allah da kuma yadda hakan ya fi yin wa’adi kawai.
Yadda Isra’ila Ta Amfana Daga Keɓe Kai ga Allah
8. Menene keɓe kai ga Allah yake nufi ga Isra’ila?
8 Al’ummar Isra’ila gabaki ɗaya sun keɓe kansu ga Jehobah sa’ad da suka ɗauki alkawari ga Allah. Jehobah ya sa sun taru a kusa da Dutsen Sinai, kuma ya gaya musu: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya.” Mutanen suka amsa da murya guda: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” (Fit. 19:4-8) Keɓe kai yana nufin cewa Isra’ila za ta yi abin da ya fi wa’adin yin wani abu. Yana nufin cewa su na Jehobah ne, kuma Jehobah ya bi da su a matsayin “keɓaɓiyar taska.”
9. Ta yaya Isra’ila ta amfana ta wajen keɓe kanta ga Allah?
9 Isra’ilawa sun amfana daga zama na Jehobah. Ya kasance da aminci kuma ya kula da su yadda uba mai ƙauna yake kula da ɗansa. Allah ya gaya wa Isra’ila: “Ya yiwu mace ta manta da ɗanta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin ɗan cikinta ba? i, ya yiwu waɗannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” (Isha. 49:15) Jehobah ya ba su Doka don ta yi musu ja-gora, ƙarfafawa daga annabawa, da kuma kāriya daga mala’iku. Wani mai zabura ya rubuta: “Yana nuna maganatasa ga Yaƙub, farillansa da hukuntansa ga Isra’ila. Ba ya yi haka nan da wata al’umma ba.” (Zab. 147:19, 20; karanta Zabura 34:7, 19; 48:14.) Yadda Jehobah ya kula da al’ummarsa a dā, zai kula da waɗanda suka keɓe kansu a gare shi a yau.
Dalilin da Ya sa Za Mu Keɓe Kanmu ga Allah
10, 11. An haife mu ne cikin iyalin Allah na samaniya da na duniya? Ka bayyana.
10 Yayin da suke tunanin keɓe kai na Kirista da baftisma, wasu suna iya yin mamaki, ‘Me ya sa ba zan iya bauta wa Allah ba tare da keɓe kaina a gare shi ba?’ Dalilin ya fita sarai sa’ad da muka bincika ainihin matsayinmu yanzu a gaban Allah. Ka tuna cewa domin zunubin Adamu, ba a haife dukanmu ba a cikin iyalin Allah. (Rom. 3:23; 5:12) Keɓe kanmu ga Allah bukata ne mai muhimmanci don a karɓe mu a cikin iyalinsa na samaniya da kuma duniya. Bari mu ga abin da ya sa.
11 Babu wani a cikinmu da yake da uban da zai ba shi rai irin wadda Allah ya nufa, wato, kamiltaccen rai. (1 Tim. 6:19) Ba a haife mu ba a matsayin ’ya’yan Allah domin sa’ad da mutane biyu na farko suka yi zunubi, an ware ’yan Adam daga Ubansu mai ƙauna kuma Mahalicci. (Gwada K. Sha 32:5.) Tun daga lokacin, dukan ’yan Adam ba sa cikin iyalin Jehobah na samaniya da na duniya, sun zama bare daga Allah.
12. (a) Ta yaya ’yan Adam ajizai za su kasance cikin iyalin Allah? (b) Waɗanne matakai ne dole mu ɗauka kafin baftisma?
12 Duk da haka, a matsayin mutane ɗaɗɗaya muna iya roƙon Allah ya karɓe mu cikin iyalinsa na bayin da ya amince da su.a Ta yaya hakan zai yiwu ga masu zunubi kamar mu? Manzo Bulus ya rubuta: “Tun muna maƙiya muka sulhuntu da Allah ta wurin mutuwar Ɗansa.” (Rom. 5:10) Sa’ad da muka yi baftisma mun roƙi Allah ya ba mu lamiri mai kyau don ya amince da mu. (1 Bit. 3:21) Amma, kafin mu yi baftisma, da akwai matakai da za mu ɗauka. Dole ne mu san Allah, mu dogara da shi, mu tuba, kuma mu canja tafarkinmu. (Yoh. 17:3; A. M. 3:19; Ibran. 11:6) Za mu yi wani abu kuma kafin a karɓe mu cikin iyalin Allah. Menene wannan?
13. Me ya sa ya dace mutum ya yi alkawari na keɓe kansa ga Allah domin ya kasance cikin iyalinsa na masu bauta da aka amince da su?
13 Kafin wani da yake bare daga Allah zai iya zama cikin iyalin Allah na bayi da aka amince da su, yana bukatan ya fara yin alkawari ga Jehobah. Don mu fahimci dalilin da ya sa, ka yi tunanin uba wanda yake son wani matashi da ba shi da iyaye kuma yana son ya kasance cikin iyalinsa. An san cewa uban mutumin kirki ne. Duk da haka, kafin ya karɓi matashin a matsayin ɗansa, mutumin yana son yaron ya ɗauki alkawari. Saboda haka mutumin ya ce, “Kafin na karɓe ka a matsayin ɗa, ina son ka gaya mini cewa za ka ƙaunace ni kuma ka ba ni daraja a matsayin babanka.” Sai idan matashin yana shirye ya ɗauki alkawarin ne mutumin zai karɓe shi cikin iyalinsa. Hakan ba daidai ba ne? Hakazalika, Jehobah yana karɓan waɗanda suke shirye ne kawai su yi alkawari na keɓe kansu a gare shi zuwa cikin iyalinsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku miƙa kanku a gare shi: hadaya mai-rai, keɓaɓɓe wadda ta cancanci karɓansa.”—Rom. 12:1, The New English Bible.
Nuna Ƙauna Ce da Kuma Bangaskiya
14. A wace hanya ce keɓe kai yake nuna ƙauna?
14 Yin alkawarin keɓe kai ga Allah yana nuna ƙaunar da muke yi wa Jehobah da dukan zuciyarmu. A wasu hanyoyi, hakan ya yi kamar yin alkawarin aure. Ango Kirista yana furta ƙaunarsa ta wajen yin alkawarin kasancewa da aminci ga amaryarsa ko da menene ya faru. Hakan rantsuwa ce ga mutumin maimakon alkawari kawai na yin wani abu. Ango Kirista ya san cewa ba zai samu gatan zama da amaryarsa ba idan ba zai yi alkawarin aure ba. Hakazalika, ba za mu more amfanin zama waɗanda suke cikin iyalin Jehobah ba, ba tare da yin alkawarin keɓe kai ba. Saboda haka, muna keɓe kanmu ga Allah domin, duk da ajizancinmu, muna son mu zama nasa kuma mun ƙuduri aniya mu kasance da aminci a gare shi, ko da menene zai faru.—Mat. 22:37.
15. Ta yaya keɓe kai nuna bangaskiya ce?
15 Sa’ad da muka keɓe kanmu ga Allah, muna nuna bangaskiya. Me ya sa? Bangaskiyarmu ga Jehobah ta sa mu kasance da tabbaci cewa kusantar Allah yana da kyau a gare mu. (Zab. 73:28) Mun san cewa ba zai kasance da sauƙi mu bi Allah a koyaushe ba yayin da muke zama cikin “tsakiyar karkataciyar tsara mai-sherare,” amma muna da tabbaci a alkawarin Allah cewa zai tallafa mana a ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu. (Filib. 2:15; 4:13) Mun san cewa mu ajizai ne, amma muna da tabbaci cewa Jehobah zai bi da mu cikin jin ƙai har sa’ad da muka yi kuskure. (Karanta Zabura 103:13, 14; Romawa 7:21-25.) Muna da bangaskiya cewa Jehobah zai albarkaci shawarar da muka tsai da na riƙe amincinmu.—Ayu. 27:5.
Keɓe Kai ga Allah na Kawo Farin Ciki
16, 17. Me ya sa keɓe kai ga Jehobah yake kawo farin ciki?
16 Keɓe kai ga Jehobah na kawo farin ciki domin hakan ya ƙunshi ba da kanmu. Yesu ya faɗi gaskiya sa’ad da ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (A. M. 20:35) Yesu ya shaida farin cikin da ake samu na bayarwa a lokacin hidimarsa a duniya. Idan da bukata, ba ya hutawa, ba ya cin abinci, ko kuma ya wala domin ya taimaki mutane su samu hanyar rai. (Yoh. 4:34) Yesu yana jin daɗin faranta zuciyar Ubansa. Yesu ya ce: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.”—Yoh. 8:29; Mis. 27:11.
17 Ta hakan, Yesu ya nuna wa mabiyansa hanyar rai mai gamsarwa sa’ad da ya ce: “Idan kowane mutum yana da nufi shi bi bayana, sai shi yi musun kansa.” (Mat. 16:24) Yin hakan, yana sa mu kusaci Jehobah. Babu wanda zai iya kula da mu cikin ƙauna kamar Yesu, ko ba haka?
18. Me ya sa yin rayuwar da ta jitu da keɓe kanmu ga Jehobah take kawo ƙarin farin ciki fiye da keɓe kai ga wani abu ko kuma wani mutum?
18 Keɓe kanmu ga Jehobah kuma bayan haka mu yi rayuwar da ta jitu da keɓe kanmu ta wajen yin nufinsa zai sa mu farin ciki fiye da keɓe kanmu ga wani abu ko kuma wani mutum. Alal misali, mutane da yawa suna ba da ransu ga biɗar dukiya ba tare da samun farin ciki na gaske ba da kuma samun tabbatacciyar gamsuwa. Amma, waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah suna samun farin ciki na dindindin. (Mat. 6:24) Ɗaukaka na zama “abokan aiki na Allah” yana sa su farin ciki, duk da haka ba su keɓe kansu ga aiki ba amma ga Allahnmu mai nuna godiya. (1 Kor. 3:9) Babu wanda zai nuna godiya ga ba da kansu fiye da shi. Zai mai da amintattunsa zuwa ƙuruciyarsu don su amfana daga kulawarsa har abada.—Ayu. 33:25; karanta Ibraniyawa 6:10.
19. Wane gata ne waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah suke morewa?
19 Keɓe kanka ga Jehobah yana sa ka kasance da dangantaka na kud da kud da shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙ. 4:8; Zab. 25:14) A talifi na gaba, za mu bincika abin da ya sa za mu kasance da tabbaci game da yin zaɓin zama na Jehobah.
[Hasiya]
a “Waɗansu tumaki” na Yesu ba za su zama ’ya’yan Allah ba sai ƙarshen shekara dubu. Amma, tun da yake sun keɓe kansu ga Allah, suna iya kiran Allah “Uba” kuma za a iya ɗaukansu a matsayin waɗanda suke cikin iyalin masu bauta na Jehobah.—Yoh. 10:16; Isha. 64:8; Mat. 6:9; R. Yoh. 20:5.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene keɓe kai ga Allah yake nufi?
• Yaya keɓe kai ga Allah yake amfanar mu?
• Me ya sa Kiristoci suke bukatan su keɓe kansu ga Jehobah?
[Hoton da ke shafi na 6]
Yin rayuwar da ta jitu da keɓe kanmu tana kai ga farin ciki na dindindin