Ka Biɗi Allah da Zuciya Da Kuma Azancinka
Kiristanci na gaskiya yana ƙarfafa yin amfani da zuciya da kuma azanci a kasancewa da imani da ke faranta wa Allah rai.
HAKIKA, wanda ya kafa Kiristanci, Yesu Kristi, ya koyar da cewa dole ne mu ƙaunaci Allah da ‘dukan azancinmu,’ ko kuma basira, ba da ‘dukan zuciyarmu’ da ‘dukan ranmu’ kawai ba. (Matta 22:37) Hakika, dole ne ƙofofin hankalinmu su kasance a babban matsayi a batun bautarmu.
Da yake gayyatar masu sauraronsa su yi tunani a kan koyarwarsa, sau da yawa Yesu yakan ce: “Me ku ke tsammani?” (Matta 17:25; 18:12; 21:28; 22:42) Hakanan ma, manzo Bitrus ya rubuta wa ’yan’uwa masu bi domin ya ‘ta da sahihin hankalinsu.’ (2 Bitrus 3:1) Ɗan wa’azi na ƙasar waje, da ya yi tafiye-tafiye da yawa, manzo Bulus, ya ƙarfafa Kiristoci su yi amfani da ‘hankalinsu’ kuma su “gwada [wa kansu] ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (Romawa 12:1, 2) Sai ta wurin irin wannan bincike na ƙwarai, a hankali game da imaninsu ne Kiristoci za su iya kasancewa da bangaskiya da ke faranta wa Allah rai kuma wadda za ta sa su tsaya wa gwaji a rayuwa.—Ibraniyawa 11:1, 6.
Don su taimaki wasu su kasance da irin bangaskiyar nan, Kiristoci na farko masu bishara suna ‘mahawara da su daga cikin littattafai, suna yi musu bayani, suna tabbatar’ da abin da suka koyar. (Ayukan Manzanni 17:1-3) Irin wannan mataki mai kyau ya kawo martani mai kyau daga masu zuciyar kirki. Alal misali, mutane da yawa a birnin Makidoniya na Biriya suka “karɓi magana [ta Allah] da yardar rai sarai, suna bin cikin littattafai kowace rana, su gani ko waɗannan al’amura [da Bulus da abokansa suka yi bayanin] haka su ke.” (Ayukan Manzanni 17:11) Akwai abubuwa biyu da za a lura da su a nan. Na ɗaya, mutanen Biriya suna ɗokin su saurari Maganar Allah; na biyu, ba kawai sun yi na’am da cewa abin da suka ji daidai ne amma sun koma su bincika cikin Nassosi. Kirista ɗan wa’azi na ƙasan waje, Luka ya yaba wa mutanen Biriya domin wannan, yana ce da su masu “darajar hali.” Kana nuna irin darajar halin nan a yadda ka ke ɗaukan al’amura ta ruhaniya?
Azanci da Zuciya Suna Jituwa
Yadda aka ambata a farko, bauta ta gaskiya ta ƙunshi azanci da zuciya. (Markus 12:30) Ka tuna da misalin nan cikin talifi na farko game da mai shafa fenti da ya yi amfani da fenti da launinsa bai dace ba wajen yin fentin gidan. Da ya saurari maigidan, da zai sa zuciyarsa da ransa a aikinsa kuma ya tabbata cewa aikinsa zai gamshi maigidan. Haka yake game da bautarmu.
“Masu-yin sujjada da gaskiya,” Yesu ya ce, “za su yi ma Uba sujjada a cikin Ruhu da cikin gaskiya.” (Yohanna 4:23) Shi ya sa manzo Bulus ya rubuta: “Saboda wannan mu kuma, . . . ba mu fasa yin addu’a da roƙo dominku ba, ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima mai-ruhaniya da fahimi kuma, da za ku yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, kuna gamshe shi sarai.” (Kolossiyawa 1:9, 10) Irin ‘cikakken sanin’ nan yana sa sahihan mutane su sa zuciyarsu da ransu cikin bautarsu da cikakken tabbaci domin suna “yin sujjada ga abin da [suka] sani.”—Yohanna 4:22.
Domin waɗannan dalilai, Shaidun Jehovah ba sa yi wa jarirai baftisma ko sababbin mutane da suke son gaskiya da ba su yi nazarin Nassosi ba sosai. Yesu ya umurci mabiyansa: “Ku almajirtadda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Sai bayan sun samu cikakken sanin nufin Allah ne sahihan ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su iya tsai da shawara mai kyau a batun bauta. Kana ƙoƙari ka samu irin wannan cikakken sanin?
Fahimtar Addu’a ta Ubangiji
Domin mu ga bambanci tsakanin samun cikakken sanin Littafi Mai Tsarki da kuma sani na sama sama kawai na abin da yake faɗa, bari mu bincika abin da aka saba kira Ubanmu, ko kuma Addu’ar Ubangiji, da ke a Matta 6:9-13.
Miliyoyi a coci suna maimaita addu’ar misali na Yesu a kai a kai. Amma mutane nawa ne aka koya musu ma’anarta, musamman sashe na farko na addu’ar da take magana a kan sunan Allah da kuma Mulkinsa? Waɗannan al’amura suna da muhimmanci ƙwarai shi ya sa Yesu ya sa su farko cikin addu’ar.
Ta soma: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka,” yana nufin a ɗaukaka, ko kuma a sa ya zama da tsarki. Ka lura cewa Yesu ya ce a yi addu’a domin a tsarkake sunan Allah. Ga mutane da yawa aƙalla wannan zai ta da tambayoyi biyu, Na farko, menene sunan Allah? Na biyu, me ya sa ake bukatar tsarkake sunan?
Ana iya samun amsar tambaya ta farko a wurare sama da 7,000 cikin Littafi Mai Tsarki a harsunansa na asali. Ɗaya cikin wuraren Zabura 83:18 ta ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Game da sunan Allah, Jehovah, Fitowa 3:15 ta ce: “Wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.”a Amma me ya sa ake bukatar tsarkake sunan Allah, wanda shi ne asalin tsabta da tsarki? Domin an zarge shi kuma an lalata shi daga farkon tarihin mutane.
A Adnin, Allah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u cewa za su mutu idan suka ci daga ’ya’yan itace da ya haramta. (Farawa 2:17) Shaiɗan ya furta raininsa na saɓa wa Allah, yana cewa: “Ba lallai za ku mutu ba.” Da haka ne Shaiɗan ya tuhumi Allah da yin ƙarya. Har ila, bai tsaya a nan ba. Ya tula zargi a kan sunan Allah, ya gaya wa Hauwa’u cewa domin ha’inci ne Allah ya hana ta sanin wani abu. “Gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki [itacen sanin nagarta da mugunta], ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” Mugun tsegumi!—Farawa 3:4, 5.
Ta wurin ci daga ’ya’yan itace da aka haramta, Adamu da Hauwa’u suka tsaya a gefen Shaiɗan. Tun lokacin, yawancin mutane, da saninsu ko babu, sun daɗa ga wannan zargi na asali ta ƙin mizanan adalci na Allah. (1 Yohanna 5:19) Har yanzu mutane suna zargin Allah ta ganin laifinsa domin wahalarsu—ko ma wataƙila saboda mugun hanyoyinsu ne. “Wautar ɗan Adam ta kan ɓata rayuwarsa, sai ya yi gunaguni wa Ubangiji,” in ji Misalai 19:3. (The New English Bible) Ka ga dalilin da ya sa Yesu, wanda yake ƙaunar Ubansa da gaske, ya yi addu’a a tsarkake Sunansa?
“Mulkinka Shi Zo”
Bayan da ya yi addu’a a tsarkake sunan Allah, Yesu ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Game da matanin nan, za mu iya tambaya: ‘Menene Mulkin Allah? Kuma me ya shafi zuwansa da yin nufin Allah a duniya?’
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “mulki” asali tana nufin “sarauta ta sarki.” Daidai kuwa, Mulkin Allah zai yi nuni ga sarauta, ko kuma gwamnati ta Allah, da take da sarki wanda ya zaɓa. Wannan Sarkin, Yesu Kristi ne da aka tayar daga matattu—“Sarkin sarakuna, da Ubangijin iyayengiji.” (Ru’ya ta Yohanna 19:16; Daniel 7:13, 14) Game da Mulkin Allah na Almasihu a hannun Yesu Kristi, annabi Daniel ya rubuta: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [gwamnatin ’yan Adam da suke sarauta yanzu] kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”—Daniel 2:44.
Hakika, Mulkin Allah zai mallake dukan duniya, ya kawar da dukan miyagu kuma ya yi sarauta “har abada.” A wannan hanyar, Mulkin ne Jehovah zai yi amfani da shi ya tsarkake sunansa, ya kawar da dukan zargin ƙarya na Shaiɗan da kuma na mutane.—Ezekiel 36:23.
Kamar dukan gwamnatoci, Mulkin Allah yana da waɗanda za ya sarauce su. Su wanene? Littafi Mai Tsarki ya amsa: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” (Zabura 37:11) Haka kuma, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” Babu shakka, waɗannan suna da cikakken sani na Allah, wanda farilla ce don rai.—Matta 5:5; Yohanna 17:3.
Za ka iya tsammanin yadda dukan duniya za ta cika da masu tawali’u, mutane da suke ƙaunar Allah da gaske kuma suna ƙaunar juna? (1 Yohanna 4:7, 8) Abin da ya sa Yesu ya yi addu’arsa ke nan yayin da ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” Ka fahimci dalilin da ya sa Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a a wannan hanyar? Mafi muhimmanci, ka fahimci yadda cikar addu’ar za ta shafe ka kai kanka?
Miliyoyi Yanzu Suna Mahawara Cikin Nassosi
Yesu ya annabta kamfen na dukan duniya don ilimi na ruhaniya da zai sanar da Mulki mai zuwa na Allah. Ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa [ta wannan zamani, ko kuma tsari] za ta zo.”—Matta 24:14.
A dukan duniya Shaidun Jehovah wajen miliyan shida suna raba wa maƙwabtansu bishara. Suna gayyatarka ka ƙara koyo game da Allah da kuma Mulkinsa ta wurin “bin cikin littattafai,” kana amfani da hankalinka. Yin haka zai ƙarfafa imaninka kuma ya sa ka sami bege na rai na har abada a aljanna a duniya, wadda za ta “cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe da teku.”—Ishaya 11:6-9.
[Hasiya]
a Wasu ɗalibai sun fi yin amfani da “Yahweh” maimakon “Jehovah.” Amma, yawancin masu fassarar Littafi Mai Tsarki na zamani sun share sunan Allah daga fassararsu a duk inda yake, suna sake shi da laƙabi “Ubangiji” ko kuma “Allah.” Domin bayani mai zurfi a kan sunan Allah, sai ka duba mujallar nan The Divine Name That Will Endure Forever, wadda Shaidun Jehovah suka buga da (Turanci).
[Box/Hoto a shafi na 8]
KA YI KOYI DA BABBAN MALAMI
Sau da yawa Yesu yana koyarwa ta wajen yin amfani da wasu muhimman darussa na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, bayan tashinsa daga matattu, ya bayyana matsayinsa cikin nufin Allah ga almajiransa biyu da suka damu game da mutuwarsa. Luka 24:27 ta ce: “Ya soma kuwa tun daga Musa da dukan annabawa, cikin dukan littattafai yana fasalta musu al’amura na bisa kansa.”
Ka lura Yesu ya zaɓi jigo—“shi kansa,” Almasihu—kuma ya ɗauko zance daga “dukan littattafai” cikin mahawararsa. Watau, Yesu ya haɗa wasu matani na Littafi Mai Tsarki ga misalai, da ya taimaki almajiransa su fahimci tafarki na gaskiya ta ruhaniya. (2 Timothawus 1:13) Sakamakonsa shi ne, ba kawai sun sami wayewa ba amma sun motsa ƙwarai. Labarin ya gaya mana: “Suka ce ma junansu, Zuciyarmu ba ta ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yana yi mamu zance a kan hanya, yana bayyana mamu littattafai?”—Luka 24:32.
Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su yi koyi da tafarkin Yesu cikin hidimarsu. Muhimman littattafan da suke nazari daga ciki su ne mujallar nan Mi Allah ke Bukata Daga Garemu? da kuma littafin nan Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Waɗannan suna koyar da darussa masu daɗi na Littafi Mai Tsarki, kamar su: “Wanene Allah?,” “Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?,” “Waɗannan ne Kwanaki na Ƙarshe!,” da kuma “Gina Iyali da ke Daraja Allah.” Kowanne darasi na da nassosi ciki da yawa.
Ana ƙarfafa ka ka sadu da Shaidun Jehovah a yankinka ko kuma ka rubuta zuwa adireshi da ke shafi na 2 na wannan jaridar don nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta a kan waɗannan darussa.
[Picture]
Ka motsa zuciyar ɗalibinka a kan muhimman jigo na Littafi Mai Tsarki
[Hotuna a shafi na 7]
Ka fahimci ma’anar addu’ar misali na Yesu?
“Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka . . . ”
“Mulkinka shi zo . . . ”
“Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”