Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 6/1 pp. 3-4
  • Menene Ra’ayinka Game da Mutuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Menene Ra’ayinka Game da Mutuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mamakin Mutuwa?
  • Warewa don Mutuwa?
  • Batun da Za a Yi Tunani a Kai
  • Bincika Wasu Ƙage-Ƙage Game da Mutuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ta Yaya Za A Kawo Karshen Mutuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 6/1 pp. 3-4

Menene Ra’ayinka Game da Mutuwa?

MUTUWA tana bin mu yayin da muke ayyukan rayuwa na yau da kullum, ko muna da ƙoshin lafiyarmu da kuma arziki. Tana iya zuwa a lokacin da muke ƙetare titi ko muna kwance a kan gado. Bala’in irin farmaki na ’yan ta’ada na ranar 11 ga Satumba 2001, a New York City da Washington, D.C., ya sa mu fahimci hakikancin “maƙiyi na ƙarshe,” mutuwa, tana kwasan rayuka daga ko’ina kuma a dukan tsararraki, wani lokaci tana kwasan rayuka dubbai cikin mintoci kaɗan.—1 Korinthiyawa 15:26.

Duk da haka, mutuwa tana ba mutane mamaki. Ba abin da zai sa a sayar da jaridu ko kuma ya sa mutane su matsa kusa da telibijin fiye da rahoton mutuwa, musamman mutuwar mutane da yawa a yanayi mai ban tsoro. Kamar ba ya isan mutane, ko mutuwa ce a yaƙi, a tsarar bala’i, a aikata laifi, ko don ciwo. Wannan shagala cikin batun mutuwa ana nunawa a hanya da ta fi ban mamaki, juyayi da mutane suke yi lokacin mutuwar manyan mutane da kuma fitattun mutane.

Duka wannan gaskiya ne. Mutane suna cin gaba da mamakin mutuwa—mutuwar wasu. Amma, in ya zo zancen tasu mutuwar, suna tsoron tunaninta. Namu mutuwar ne batun da yawancinmu ba ma son mu yi tunaninta.

Mamakin Mutuwa?

Tunanin tamu mutuwar ba ta da daɗi, kuma hakan zai kasance. Me ya sa hakan? Domin Allah ya saka a cikinmu muradin rayuwa na har abada. “Ya kuma sa dawwama a zuciyarsu,” in ji Mai-Wa’azi 3:11, bisa Anchor Bible. Saboda haka, tabbacin mutuwa ya sa damuwa ta ciki ga mutane, azanci na rashin jituwa da ke ci gaba. Don a sulhunta wannan yaƙin ciki kuma a gamsar da muradin ci gaba da rayuwa, mutane sun ƙaga irin-irin imani, daga koyarwa na rashin mutuwar kurwa zuwa imanin sake zuwa duniya.

Ko yaya dai, mutuwa na kawo damuwa, kuma ana tsoron mutuwa a ko’ina. Saboda haka, bai kamata mu yi mamaki ba da galibin mutane suna ganin mutuwa ƙalubala ce. Abu ɗaya, mutuwa tana bayyana rashin amfanin rayuwa da aka ba da ita ga biɗan arziki da iko.

Warewa don Mutuwa?

A lokacin dā, mai ciwon ajali ko kuwa wanda aka yi masa raunin ajali ana barinsa ya mutu a mahallin gidansa abin ƙaunarsa. Haka yake a lokatan Littafi Mai Tsarki, kuma har ila hakan yake a wasu al’adu. (Farawa 49:1, 2, 33) A irin wannan yanayi, iyali na taruwa, kuma ana haɗa yara a wannan zancen. Wannan na sa kowanne cikin iyali ya ji cewa ba shi ko ita kaɗai ba take baƙin ciki kuma wannan na ƙarfafa su cewa dukansu ne ke da hakkin.

Wannan ya saɓa ƙwarai da abin da yake faruwa a wurin da an haramta yin zancen mutuwa, da an ɗauka ba shi da kyau, ba a haɗawa da yara domin cewa “za su damu sosai.” Mutuwa ta baya bayan nan dabam take a hanyoyi da yawa, kuma sau da yawa ana kaɗaita. Ko da yake yawanci za su so su mutu a gida, cikin salama kuma cikin hannun iyalinsu, ga mutane da yawa gaskiya mai wuya ita ce suna mutuwa a asibiti, sau da yawa a ware kuma cikin azaba, an jojjona musu na’urori. A wani ɓangare, miliyoyi suna mutuwa babu labari—waɗanda suka mutu a yaƙin ƙare-dangi, wasu kuma don yunwa, wasu don ƙanjamau, wasu a yaƙin basasa, ko kuma don tsananin talauci.

Batun da Za a Yi Tunani a Kai

Littafi Mai Tsarki bai ce kada a yi tunanin mutuwa ba. Hakika, Mai-Wa’azi 7:2 ta ce: “Gwamma a tafi gidan kuka, da a tafi gidan da a ke biki; gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane.” Yayin da muka fuskanci gaskiyar mutuwa, za mu iya juyowa daga damuwarmu ta kullum ko kuma ayyuka mu mai da hankali kan gajertar rayuwa. Wannan zai taimake mu mu yi rayuwarmu a hanya mai ma’ana maimakon yin rayuwa kawai marar ma’ana.

Menene ra’ayinka game da mutuwa? Ka bincika motsin ranka, imaninka, begenka, da tsoronka game da ƙarshen rayuwarka?

Rayuwa da mutuwa sun wuce iyawar mutum ya bayyana ko ya fahimta. Wanda zai iya magana game da batun da cikakken iko Mahaliccinmu ne. Wurinsa “maɓulɓular rai take,” wurinsa kuma “makuɓutan mutuwa.” (Zabura 36:9; 68:20) Ko da zai kasance abin mamaki, bincika wasu imani game da mutuwa ta bincika Kalmar Allah zai kasance da ƙarfafawa da kuma wartsakewa. Zai bayyana cewa mutuwa ba ita ce ƙarshe ba.

[Bayanin da ke shafi na 4]

Kasancewar mutuwa za ta sa mu yi rayuwa a hanya mai ma’ana

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba