Ta’azyya a Lokatan Tarzoma
LABARAN yanzu ba sa ƙarfafawa. Wani mutum ya rubuta: “Aukuwa na yanzu na kawo baƙin ciki da ba za mu iya tsai da shawara ko za mu iya sauraran labarai da ake bayar wa da yamma ba.” Duniya ta cika da yaƙe-yaƙe, ayyukan ta’adanci, wahala, yin laifi, da cututtuka—mugunta da ba da daɗewa ba za ta shafe mu kai tsaye, idan ba su shafe mu ba ma ke nan.
Littafi Mai Tsarki ya annabta daidai yanayin na yau. Da yake kwatanta lokacinmu, Yesu ya ce za a yi yaƙe-yaƙe, annoba, yunwa, da girgizan ƙasa. (Luka 21:10, 11) Hakanan ma, manzo Bulus ya rubuta game da “miyagun zamanu,” sa’ad da mutane za su zama masu zafin hali, masu son kuɗi, da marasa son nagarta. Ya kira lokacin “kwanaki na ƙarshe.”—2 Timothawus 3:1-5.
Saboda haka, a kwatanta yanayin duniya, labarai a wasu hanyoyi sun yi kama da abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta. Amma a nan kamanin ya ƙare. Littafi Mai Tsarki ya ba mu ra’ayi da labaran ba su ba mu ba. Ta wurin hurarriyar Kalmar Allah, za mu fahimci abin da ya sa mugunta ta yi yawa da kuma abin da zai faru a nan gaba.
Yadda Allah Yake Ɗaukan Mugunta
Littafi Mai Tsarki ya yi bayanin yadda Allah yake ɗaukan yanayi mai wuya na zamaninmu. Ko da ya riga ya hangi wahala na yanzu, bai amince da su ba kuma bai da nufin ya ƙyale su dindindin. Manzo Yohanna ya rubuta, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Jehovah yana kula da mutane sosai kuma yana ƙyamar dukan mugunta. Ya dace mu juya ga Allah don ta’aziyya, tun da shi nagari ne kuma mai juyayi kuma yana da ikon da zai kawar da mugunta daga duniya. Mai Zabura ya rubuta: “[Sarki da Allah ya naɗa a sama] za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.”—Zabura 72:12-14.
Kana jin tausayin waɗanda suke wahala? Wataƙila kana ji. Jin tausayi hali ne da Jehovah ya saka cikinmu, domin an halicce mu cikin surarsa. (Farawa 1:26, 27) Saboda haka, za mu kasance da tabbaci cewa Jehovah yana damuwa da wahalar ’yan Adam. Yesu da ya san Jehovah sosai fiye da kowa, ya koyar da cewa Jehovah yana damuwa da mu kuma yana cike da juyayi.—Matta 10:29, 31.
Halitta kanta ta tabbatar da cewa Allah yana kula da mutane. Yesu ya ce Allah “ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Matta 5:45) Zuwa ga mutanen birnin Listra, manzo Bulus ya ce: “[Allah] ba ya bar kansa babu shaida ba, da shi ke yana yin alheri, yana ba ku ruwaye daga sama da kwanukan ƙoshi, yana cika zukatanku da abinci da farinciki.”—Ayukan Manzanni 14:17.
Waye Yake da Alhakin Mugunta?
Abin lura ne cewa Bulus ya ce wa mutanen Listra: “A cikin zamanun da suka wuce [Allah] ya bar dukan al’ummai su yi tafiya cikin nasu tafarku.” Da haka, al’ummai—ko mutanen kansu—suna da alhakin yawancin yanayin da suka iske kansu ciki. Ba za a ɗora wa Allah laifi ba.—Ayukan Manzanni 14:16.
Me ya sa Jehovah ya ƙyale mugunta? Zai yi wani abu game da ita? Za a samu amsar waɗannan tambayoyi a cikin Kalmar Allah ce kawai. Domin amsar ta ƙunshi wata halittar ruhu da kuma mahawarar da ya tayar a duniya marar ganuwa.
[Hotuna a shafi na 4]
Mutane suna da tausayi. Allah bai damu ba ne da wahalar ’yan Adam?
[Wuraren da Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 2]
BANGO: Tanka: UN PHOTO 158181/J. Isaac; girgizar ƙasa: Hoton Kamfani na San Hong
[Wuraren da Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]
Sama a ta hagu: Croatia: UN PHOTO 159208/S. Whitehouse; yaro mayunwaci: UN PHOTO 146150 BY O. MONSEN