Ka Bi Misalin Yesu Kuma Ka Nuna Damuwa Ga Matalauta
TALAUCI da zalunci sun kasance na kusan tsawon tarihin ’yan adam. Ko da Dokar Allah ga Isra’ila ta so ta kāre matalauta kuma ta sauƙaƙa wahalarsu, sau da yawa ba a bin wannan Dokar. (Amos 2:6) Annabi Ezekiel ya yi Allah-wadai da yadda ake bi da matalauta. Ya ce: “Mutanen ƙasa suna yi aikin zilama, sun yi ƙwace; i, sun wahalda talakawa da masu-mayata, sun yi ma baƙo zilama ba kan shari’a ba.”—Ezekiel 22:29.
Haka yanayin yake sa’ad da Yesu yake duniya. Shugabanan addinai ba su damu ba sam da matalauta da fakirai. An kwatanta shugabanan addinai da “masu-son kuɗi” waɗanda suke “cin gidajen gwauraye” kuma waɗanda suka fi damuwa da bin nasu al’adu fiye da kula da tsofaffi da mabukata. (Luka 16:14; 20:47; Matta 15:5, 6) A almarar Yesu na nagarin Basamariye, firist da Balawin da suka ga wani mutumin da aka ji wa rauni, suka bi ta wani gefe maimakon su taimake shi.—Luka 10:30-37.
Yesu ya Kula da Matalauta
Labaran Linjila game da rayuwar Yesu ya nuna cewa ya fahimci wahalar matalauta sosai kuma ya mai da hankali ga bukatunsu. Ko da Yesu ya zauna a sama, ya ƙasƙantar da kansa ya zama ɗan adam, kuma ‘sabili da mu ya zama da talauci.’ (2 Korinthiyawa 8:9) Da Yesu ya ga taro masu yawa “ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Labarin gwauruwa mabukaciya ya nuna cewa Yesu ya yi farin ciki don ƙaramin kuɗi da gwauruwa matalauciya ta bayar ba don kyauta mai yawa da mawadata suke bayarwa “daga cikin falalarsu” ba. Abin da ta yi ya motsa zuciyarsa domin “ta zuba dukan iyakar abin zaman gari da ta ke da shi.”—Luka 21:4.
Yesu bai yi juyayin matalauta kawai ba, amma ya kula da bukatunsu. Da shi da manzanninsa suna da asusu da suka tanada don taimaka wa Isra’ilawa mabukata. (Matta 26:6-9; Yohanna 12:5-8; 13:29) Yesu ya ƙarfafa waɗanda suke son su zama mabiyansa su fahimci hakkinsu na taimaka wa mabukata. Ya gaya wa wani basarauce mawadaci: “Ka sayarda abin da ka ke da shi duka, ka rarraba ma fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo, ka biyo ni.” Da yake mutumin ba ya son ya rabu da dukiyarsa, ya nuna cewa ya fi ƙaunar arziki maimakon Allah da kuma ’yan’uwansa. Wannan ya nuna cewa ba shi da halayen da ake bukata na zama almajirin Yesu.—Luka 18:22, 23.
Mabiyan Kristi Sun Kula da Matalauta
Bayan mutuwar Yesu, manzanni da wasu mabiyan Kristi sun ci gaba da kula da matalauta da ke tsakaninsu. A misalin shekara ta 49 A.Z., manzo Bulus ya haɗu da Yakubu, Bitrus da Yohanna kuma suka tattauna game da aikin yin wa’azin bishara da Ubangiji Yesu Kristi ya gaya masa ya yi. Sun yarda cewa ya kamata Bulus da Barnaba su tafi wajen “al’ummai” su mai da hankali ga yi wa ’yan Al’ummai wa’azi. Amma, Yakubu da abokansa sun aririci Bulus da Barnaba su “tuna da gajiyayyu.” Kuma Bulus ya yi hakan da ‘himma ƙwarai.’—Galatiyawa 2:7-10.
A lokacin babban sarki Kuludiyus, an yi babbar yunwa a ɓangare dabam dabam na Daular Roma. Kiristoci da suke Antakiya “kowane mutum gwargwadon abin da ya iya, suka kudurta su aike gudunmuwa ga ’yan’uwa da ke zaune cikin Yahudiya, har kuwa suka yi, suna aike wurin dattiɓai ta hannun Barnaba da Shawulu.”—Ayukan Manzanni 11:28-30.
Kiristoci na gaskiya a yau sun fahimci cewa dole ne mabiyan Yesu su damu da matalauta da mabukata, musamman tsakanin ’yan’uwa masu bi. (Galatiyawa 6:10) Shi ya sa suke damuwa sosai da bukatun rayuwa na mabukata. Alal misali, a shekara ta 1998, fari mai tsanani ya ragargaje yawancin wurare a arewa maso gabashin Brazil. Farin ya halaka gonakin shinkafa, wake, da na masara, wannan ya kawo yunwa a ko’ina, wanda ya fi muni a cikin shekara 15. A wasu wurare ma da ƙyar ake samun ruwan sha. Nan da nan, Shaidun Jehobah da suke wasu ɓangare a ƙasar suka kafa kwamitin kayan agaji, kuma ba da daɗewa ba, suka tara abinci mai yawa kuma suka biya kuɗin motar kai waɗannan kayayyaki.
Shaidu da suka ba da wannan kayan agaji sun rubuta: “Mun yi farin ciki sosai da muka iya taimaka wa ’yan’uwanmu, musamman domin mun tabbata cewa mun faranta wa Jehobah rai. Ba mu taɓa manta da kalmomin Yaƙub 2:15, 16 ba.” Waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki sun ce: “Idan wani ɗan’uwa ko kuwa wata ’yar’uwa suna tsiraici, kuma sun rasa abincin yini, ɗaya kuwa daga cikinku ya ce musu, ku tafi lafiya, ku ji ɗumi, ku ƙoshi; ba ku ko ba su bukatar jiki ba; me ya amfana?”
A wata ikilisiya na Shaidun Jehobah a birnin Sāo Paulo, wata Mashaidiya mai tawali’u mai himma kuma matalauciya ce sau da yawa ba ta da na biyan bukatunta na rayuwa. Ta ce: “Ko da yake ni matalauciya ce, saƙon Littafi Mai Tsarki ya sa na san ma’anar rayuwata. Ban san abin da zai faru da ni ba da a ce ba na samun taimako daga Shaidu ’yan’uwana.” Akwai lokacin da, ake bukatar a yi wa wannan ’yar’uwa mai himma tiyata, amma ba ta iya biyan kuɗin asibitin ba. A wannan yanayin, ’yan’uwa Kirista a cikin ikilisiya suka biya kuɗin fiɗar. Kiristoci a dukan duniya suna ba da taimako ga ’yan’uwa masu bi.
Ko da irin waɗannan labarai suna daɗaɗa rai, a bayane yake cewa irin waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce ba za su kawar da talauci ba. Ko da gwamnatoci masu iko da kuma taimako na wasu ƙasashe suna ɗan yin nasara, ba su iya kawar da matsalar talauci na tun lokacin dā ba. Amma tambayar ita ce, Menene zai kawar da talauci da wasu matsaloli da ke damun ’yan adam?
Koyarwar Littafi Mai Tsarki na Ba da Taimako na Dindindin
Labaran Linjila ya ce Yesu Kristi na yin nagarin ayyuka a kai a kai don matalauta ko waɗanda suke da wasu bukatu. (Matta 14:14-21) Amma, wane aiki ya fi masa muhimmanci? Wani lokaci, bayan ya ba da lokaci wajen taimakon mabukata, Yesu ya gaya wa almajiransa: ‘Bari mu tafi wani wuri zuwa garuruwa na kusa, domin in yi wa’azi a can kuma.’ Me ya sa Yesu ya daina aikinsa domin masu ciwo da mabukata don ya soma aikin wa’azi? Ya ba da bayani cewa: “Dalilin fitowata ke nan [wato, yin wa’azi].” (Markus 1:38, 39; Luka 4:43) Ko da yin nagarin ayyuka ga mabukata suna da muhimmanci ga Yesu, yin wa’azi game da Mulkin Allah ne aikinsa na musamman.—Markus 1:14.
Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya aririci Kiristoci su “bi sawun” Yesu, Kiristoci a yau suna da ja-gora sarai game da kafa abubuwa da suka fi muhimmanci wajen taimakon wasu. (1 Bitrus 2:21) Kamar Yesu, suna taimakon waɗanda suke da bukata. Amma kuma kamar Yesu suna sa aikin koyar da saƙon Littafi Mai Tsarki game da bisharar Mulkin Allah a kan gaba da kome. (Matta 5:14-16; 24:14; 28:19, 20) To, me ya sa wa’azin saƙon da ke cikin Kalmar Allah ya fi muhimmanci da wasu irin taimakon mutane?
Labaran rayuwar mutane daga wasu wurare na duniya ya nuna cewa sa’ad da mutane suka fahimci kuma suka bi gargaɗin Littafi Mai Tsarki sun fi kasancewa a shirye su bi da matsalolin rayuwa na yau da gobe, har da talauci. Ƙari ga haka, saƙon Littafi Mai Tsarki na Mulkin Allah da Shaidun Jehobah ke wa’azinsa a yau na ba mutane bege don nan gaba, begen da ke sa rayuwa ta kasance da ma’ana, ko a yanayi mafi wuya ma. (1 Timothawus 4:8) Wane irin bege ne wannan?
Kalmar Allah ta ba mu tabbaci game da nan gaba: “Bisa ga alkawarinsa [Allah], muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13) Idan Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “duniya” wani lokaci yana magana ne game da mutane da ke zama a duniya. (Farawa 11:1) Saboda haka, “sabuwar duniya” na adalci da aka yi alkawarin za ta zo, mutane ne da suke da amincewar Allah. Kalmar Allah ta ƙara yin alkawari cewa a sarautar Kristi, waɗanda Allah ya amince da su za su sami kyautar rai madawwami kuma su yi rayuwa mai gamsarwa a cikin aljanna a duniya. (Markus 10:30) Dukan mutane za su iya kasancewa a wannan lokaci mai ban al’ajabi, har da matalauta. A wannan “sabuwar duniya” za a kawar da matsalar talauci har abada.
[Box/Hoto a shafi na 6]
TA YAYA YESU “ZA YA CECI FAKIRI”?—Zabura 72:12
SHARI’A: ‘Za ya shar’anta matalauta na cikin mutane, za ya ceci ’ya’yan masu-mayata ya ragargaza azalumin.’ (Zabura 72:4) Sa’ad da Kristi zai yi sarauta bisa duniya, za a yi adalci ga kowa. Ɓatanci ba zai kasance ba, matsalar da ke sa ƙasashe da ya kamata su yi arziki su talauta.
SALAMA: ‘A cikin kwanakinsa mai-adalci za shi yalwata; da salama mai-yawa, har batun wata ya ƙare.’ (Zabura 72:7) Ana talauci a duniya domin jayayya da kuma yaƙe-yaƙe na ’yan adam. Kristi zai kawo cikakkiyar salama ga duniya, ta haka zai kawar da ainihin abin da ke kawo talauci.
JUYAYI: ‘Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.’ (Zabura 72:12-14) Fakirai, matalauta, da waɗanda ake zalunta za su zama sashen iyalin ’yan adam mai farin ciki, su kasance da haɗin kai a ƙarƙashin shugabancin Sarki Yesu Kristi.
NI’IMA: ‘Za a yi albarkar hatsi a ƙasa.’ (Zabura 72:16) A sarautar Kristi, za a yi wadata da abubuwan biyan bukata masu yawa. Mutane ba za su sha wahalar ƙarancin abinci da kuma yunwa da ke kawo talauci a kai a kai a yau ba.