Albishiri Ga Talakawa
KALMAR ALLAH ta ba mu wannan tabbacin: “Ba kullum za a manta da matalauta ba.” (Zabura 9:18) Littafi Mai Tsarki ya ce game da Mahaliccinmu: “Kana buɗe hannunka, kana biya wa kowane mai-rai muradinsa.” (Zabura 145:16) Wannan begen da ke cikin Kalmar Allah ba mafarki ba ne. Allah Maɗaukaki zai iya tanadar da abin da ake bukata don kawar da talauci. Mene ne talakawa suke bukata?
Wata masaniyar tattalin arziki daga Afirka ta ce ƙasashe marasa arziki suna bukatar “mai mulkin kama-karya da zai taimaki mutane.” Abin da ake nufi shi ne, idan ana son a kawar da talauci, ana bukatar mutumin da ke da ƙarfin yin canji wanda zai nuna kula da kuma alheri. Za mu iya daɗa cewa mai mulkin da zai iya kawar da talauci zai zama wanda ke mulkin duniya gabaki ɗaya, domin sau da yawa talauci mai tsanani yana aukuwa ne a sakamakon arzikin da wasu ƙasashe suke morewa fiye da wasu. Bugu da ƙari, mai mulkin da ke da ƙarfin kawar da talauci zai zama wanda zai iya ɗaukan mataki a kan abin da ke jawo talauci, wato, halin son kai na ’yan Adam. A ina ne za a iya samun irin wannan mai mulkin da ya dace?
Allah ya aiko Yesu da albishiri ga talakawa. Sa’ad da Yesu ya tashi don ya karanta saƙon da Allah ya ba shi, ya ce: “Ruhun Ubangiji yana bisa na, gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa.”—Luka 4:16-18.
Mene ne Albishirin?
Allah ya naɗa Yesu a matsayin Sarki. Hakika, wannan albishiri ne. Shi ne Sarkin da zai iya kawar da talauci domin (1) zai yi sarauta bisa dukan ’yan Adam kuma yana da ikon ɗaukan mataki nan da nan; (2) yana bi da talakawa cikin tausayi kuma yana koya wa mabiyansa su kula da su; kuma (3) zai iya kawar da sanadin talauci, wato, halin son kai da muka gāda. Bari mu duba waɗannan fasaloli guda uku na bisharar.
1. Ikon da Yesu yake da shi bisa dukan al’umma Kalmar Allah ta ce game da Yesu: “Aka ba shi sarauta . . . domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa.” (Daniyel 7:14) Ka yi tunanin irin albarkar da dukan ’yan Adam za su samu idan aka ce gwamnati guda ce kacal take sarauta. Ba za a ƙara yin jayayya da kuma gwagwarmaya bisa arzikin ƙasa ba. Kowa zai more albarka daidai wa daida. Yesu da kansa ya ba da tabbacin cewa zai kasance Sarkin duniya wanda yake da ikon ɗaukan mataki. Ya ce: ‘An ba ni dukan hukunci a cikin sama da ƙasa.’—Matta 28:18.
2. Yesu ya tausaya wa talakawa Gabaki ɗayan hidimarsa a duniya, Yesu ya tausaya wa talakawa. Alal misali, wata mace da ta yi amfani da dukan abin da take da shi wajen yin jinya, ta taɓa tufafin Yesu da fatan warkewa. Ta yi shekara 12 tana zubar da jini kuma babu shakka cewa ba ta da jini sosai a jikinta. Bisa Doka, duk wanda ta taɓa zai zama marar tsarki. Amma Yesu ya tausaya mata. Ya ce: ‘Ɗiya, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.’—Markus 5:25-34.
Abubuwan da Yesu ya koyar suna da ikon canja halayen mutane don su ma su nuna tausayi. Alal misali, ka yi la’akari da amsar da Yesu ya ba wani mutumin da yake son ya san yadda zai faranta wa Allah rai. Mutumin ya san cewa Allah yana son mu ƙaunaci maƙwabcinmu, amma ya tambayi Yesu: “Wanene maƙwabcina?”
Don ya amsa tambayar, Yesu ya ba da sanannen misalin nan game da wani mutumin da yake tafiya daga Urushalima zuwa Jericho wanda aka yi wa fashi kuma aka bar shi “tsakanin rai da mutuwa.” Wani firist da yake tafiya a kan hanyar ya rāɓa ta wancan gefe, ya wuce. Haka kuma wani Balawi. ‘Amma wani Ba-samariye yana cikin tafiya, ya kawo wurin da ya ke: sa’an da ya gan shi, ya yi juyayi.’ Ya ɗaure raunukan mutumin, ya kai shi inda za a yi jinyarsa, kuma ya biya kuɗin jinyar. “Wa . . . ya zama maƙwabci ga wanda ya gamu da mafasa?” in ji Yesu. Amsar ita ce, “wannan da ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce: “Je ka, ka yi hakanan.”—Luka 10:25-37.
Mutanen da suka zama Shaidun Jehobah sun yi nazarin irin waɗannan koyarwar ta Yesu kuma sun canja halinsu game da taimaka wa mabukata. Alal misali, a cikin littafinta Women in Soviet Prisons wata mawallafiya ’yar Latviya ta rubuta game da rashin lafiyar da ta yi sa’ad da take aiki a kurkukun Potma a tsakanin shekarar 1965 da 1969. “A dukan lokacin da na yi rashin lafiya, [Shaidun] sun yi jinya ta sosai. Babu wata irin kulawar da za ta wuce wadda na samu.” Ta daɗa: “Shaidun Jehobah suna ganin cewa hakkin su ne su taimaki kowa, ko da mene ne addininsa ko ƙasar mutumin.”
Sa’ad da gurguncewar tattalin arziki ya jefa wasu daga cikin Shaidun Jehobah da ke garin Ancon a ƙasar Ecuador cikin rashin aiki da abin kashewa, ’yan’uwansu Shaidu sun yi shawarar yadda da za su harhaɗa musu kuɗi; suna dafa abinci don su sayar da shi ga masuntan da suke dawowa daga kamun kifi da daddare (ga hoton nan a hannun dama). Dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar sun amince da hakan, har da yara. Suna soma dahuwar ne da ƙarfe ɗaya na dare a kowace rana domin su gama girkin kafin jiragen ruwan su iso da ƙarfe huɗu na asubar fari. An rarraba kuɗin da Shaidun suka samu daidai da bukatar kowannensu.
Irin waɗannan labaran sun nuna cewa misalin da Yesu ya kafa da kuma koyarwarsa suna da ikon canja halayen mutane game da taimaka wa mabukata.
3. Yesu yana da ikon canja muradin yin zunubi da muka gāda Sanannen abu ne a dukan duniya cewa ’yan Adam suna da muradin nuna son kai. Littafi Mai Tsarki ya kira shi zunubi. Manzo Bulus ma ya rubuta: “Na iske wannan ka’ida fa a wurina, ni da na ke nufi in aika nagarta, ga mugunta gareni.” Sai ya ƙara: “Wanene zai tsamo ni daga cikin jikin nan na mutuwa? Na gode Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Romawa 7:21-25) A nan Bulus yana nuni ne ga yadda Allah, ta hanyar Yesu, zai ceci masu bauta ta gaskiya daga ajizin muradin da suka gāda, ɗaya daga cikin su shi ne son kai, tushen talauci. Ta yaya hakan zai yiwu?
Bayan baftismar Yesu, Yohanna Mai Yin Baftisma ya gabatar da Yesu, yana cewa: “Duba, ga Ɗan Rago na Allah, mai ɗauke zunubin duniya!” (Yohanna 1:29, Littafi Mai Tsarki) Ba da daɗewa ba, duniya za ta cika da mutanen da aka ’yanta daga zunubin da suka gāda, har da muradin nuna son kai. (Ishaya 11:9) A lokacin, Yesu zai kawar da abin da ke jawo talauci.
Sa’ad da muka yi tunani cewa lokaci na zuwa da kowa zai samu abin da yake bukata, hakan yana sa mu farin ciki! Kalmar Allah ta ce: “Kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratar da su.” (Mikah 4:4) Kalmomin nan suna kwatanta lokacin da dukan mutane za su sami aiki mai gamsarwa, kwanciyar hankali, da kuma cikakken zarafin more duniyar da babu talauci, yabo ya tabbata ga Jehobah.