Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/1 pp. 4-6
  • Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Kawo Ƙarshen Talauci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Kawo Ƙarshen Talauci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Hasashen da Aka Yi na Arziki ga Kowa
  • Tsarin Marshall Plan Zai Iya Kawar da Talauci Kuwa?
  • Abin da Ya Sa Agaji Daga Ƙasashen Waje Bai Kawar da Talauci Ba
  • Abin da Ya Jawo Talauci
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Albishiri Ga Talakawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Talauci—Samun Maganinsa na Dindindin
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Bi Misalin Yesu Kuma Ka Nuna Damuwa Ga Matalauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/1 pp. 4-6

Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Kawo Ƙarshen Talauci

MAWADATA sun riga sun yi bankwana da talauci. Amma dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcen da aka yi na kawar da talauci daga duniya sun ci tura. Me ya sa? Domin masu arziki ba sa son kowa ko kuma wani abu ya taɓa dukiyarsu da matsayinsu. Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā ya rubuta: “Duba, ga hawayen waɗannan da a ke zalumtassu, ba su da mai-taimako; a wajen masu-zalumtassu kuma ga iko.”—Mai-Wa’azi 4:1.

Shin mutanen da suke da iko za su iya kawar da talauci daga dukan duniya kuwa? An hura Sulemanu ya rubuta: “Ga shi kuwa, duka banza ne, cin iska kawai. Ba shi yiwuwa a miƙe abin da ya rigaya ya tanƙware.” (Mai-Wa’azi 1:14, 15) Bincika ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ake yi a yau na kawar da talauci ya tabbatar da hakan sosai.

Hasashen da Aka Yi na Arziki ga Kowa

A ƙarni na 19, sa’ad da wasu ƙasashe suka tara arziki ta hanyar cinikayya da masana’antu, wasu manyan mutane sun mai da hankali ga batun talauci. Zai yiwu a rarraba arzikin duniya daidai wa daida?

Wasu suna hasashen cewa tsarin siyasar kwaminisanci zai sa dukan al’ummar duniya su zama aji ɗaya inda za a raba dukiya daidai. Hakika, masu arziki ba su so irin waɗannan ra’ayoyin ba. Amma mutane da dama a faɗin duniya sun amince da ra’ayin nan wanda ya ce, “Kowa ya ba da gudummawa daidai da ƙarfinsa ga al’umma kuma ya karɓi daidai bukatunsa daga al’umma.” Mutane da yawa sun yi zaton cewa dukan ƙasashe za su rungumi ra’ayin kwaminisanci don duniya ta zama Mahalli Mai Kyau. Wasu ƙasashe masu arziki sun amince da fasalolin kwaminisanci kuma suka ƙafa gwamnatin da ta yi alkawarin ɗaukan nauyin kula da dukan bukatun jama’arta “daga haihuwa har mutuwa.” Sun yi da’awar cewa sun kawar da matuƙar talauci da ke jefa rayuwar mutanensu cikin haɗari.

Amma, kwaminisanci ba ta cim ma burinta na kawar da son kai daga jama’arta ba. Manufar da aka so a cim ma wa na cewa ’yan ƙasa za su yi aiki don al’ummar su su amfana maimakon kansu ya zama mafarki kawai. Wasu mutane sun ƙi jinin ba talakawa abin da suke bukata, sun ce wai irin waɗannan tanadodin ga talakawa za su iya sa wasu daga cikin su su yi zaman kashe wando. Hakan ya nuna gaskiyar waɗannan kalmomin da ke cikin Littafi Mai Tsarki: “Babu wani mai-adalci ko ɗaya cikin duniya, wanda yana aika nagarta, ba tare da zunubi ba. . . .  Allah ya yi mutum sosai; amma suna ta biɗebiɗe da yawa.”—Mai-Wa’azi 7:20, 29.

Wani tsari kuma da mutane suka sa rai a kansa shi ne American Dream, wato, wurin da duk wani mai son yin aiki tuƙuru zai iya zama mai arziki. Ƙasashe da yawa a duniya sun amince da waɗannan hanyoyin, wato, dimokuraɗiyya, yin kasuwanci kyauta ba tare da biyan haraji ba, abubuwan da ake ganin cewa su ne suka sa Amirka ta zama ƙasa mai arziki. Amma ba kowace ƙasa ce za ta iya yin nasara ta wajen bin tsarin American Dream ba, domin ba tsarin siyasarta ce kawai ta sa Amirka ta zama ƙasa mai arziki ba. Ɗimbin arzikin ƙasa da kuma yin kasuwanci da sauran ƙasashen duniya sun bunƙasa arzikin ƙasar Amirka. Bugu da ƙari, a tsarin cinikayya na duniya, akwai waɗanda suke samun riba kuma akwai waɗanda suke yin hasara. Za a iya ƙarfafa ƙasashe masu arziki su taimaki ƙasashe marasa arziki kuwa?

Tsarin Marshall Plan Zai Iya Kawar da Talauci Kuwa?

Bayan Yaƙin Duniya na biyu, ƙasar Turai ta shiga matsanancin hali kuma yunwa ta dami mazaunanta masu yawa. Yadda tsarin kwaminisanci ta samu karɓuwa a ƙasar Turai ya dami gwamnatin Amirka. Saboda haka, Amirka ta ba da kuɗi masu yawan gaske har tsawon shekara huɗu ga ƙasashen da suka amince da tsarinta domin farfaɗo da masana’antu da aikin noma. An ce wannan tsarin na European Recovery Program, wanda aka sani da sunan nan Marshall Plan, ya yi nasara. Tasirin Amirka ya ƙaru a Yammancin Turai, kuma matuƙar talauci ya ragu sosai. Wannan ita ce hanyar kawar da talauci a dukan duniya?

Nasarar da aka yi a tsarin Marshall Plan ya sa gwamnatin Amirka ta riƙa ba da agaji ga sauran ƙasashe marasa arziki, tana taimaka musu su bunƙasa aikin gona, lafiyar jiki, ilimi da kuma sufuri. Amirka ta yarda cewa tana yin hakan ne domin ta san cewa za ta amfana. Wasu ƙasashen sun yi ƙoƙarin faɗaɗa tasirin su ta wajen ba da taimakon agaji ga ƙasashen waje. Shekaru sittin bayan sun kashe kuɗi mai yawan gaske da ya wuce wanda aka kashe akan Marshall Plan, sakamakon da aka samu bai faranta musu rai ba. Hakika, wasu ƙasashen da suke cikin talauci a dā sun sami arziki sosai, musamman a Asiya ta Gabas. Amma, a wasu wuraren kuwa, duk da cewa agajin da ake samu ya rage mace-macen yara kuma yara da yawa sun sami ilimi, ƙasashe da yawa sun ci gaba da kasancewa cikin matuƙar talauci.

Abin da Ya Sa Agaji Daga Ƙasashen Waje Bai Kawar da Talauci Ba

Taimaka wa ƙasashe marasa arziki su fita daga cikin talauci ya kasance da wuya fiye da taimaka wa ƙasashe masu arziki su farfaɗo daga sakamakon yaƙi. Turai tana da masana’antu, kasuwanci da kuma sufuri. Abin da kawai take bukata ita ce farfaɗo da arzikin ƙasar. Ko da ana amfani da kuɗaɗen agajin da ake samu daga ƙasashen waje don taimakawa ƙasashe marar arziki su gina hanyoyi, makarantu, da asibitoci, mutane suna ci gaba da kasancewa cikin matuƙar talauci saboda waɗannan ƙasashen sun rasa aikin yi kuma ba su da arzikin ƙasa, da kuma hanyoyin zuwa wuraren yin kasuwanci.

Matsalolin da suke haddasa talauci da kuma waɗanda talauci yake haddasawa suna da wuyan warwarewa. Alal misali, cuta tana haddasa talauci, talauci kuma yana haddasa cuta. Yaran da ba su samu abincin da ke gina jiki ba suna iya raunana sosai a zahiri da kuma a tunani, kuma sa’ad da suka girma ba za su iya kula da ’ya’yansu ba. Ƙari ga haka, sa’ad da ƙasashe masu arziki suka kawo abinci mai yawa a ƙasashe marar arziki a matsayin “agaji,” ana kashe kasuwan manoman ƙasar da kuma masu saye da sayarwa, kuma hakan yana ƙara jawo talauci. Aika kuɗi zuwa ga gwamnatin ƙasashe marar arziki yana kuma jawo waɗannan abubuwa: Kuɗin da aka ba da don taimakon agaji yana da sauƙin sacewa, saboda haka yakan kai ga rashawa, kuma rashawa, yakan kai ga ƙarin talauci. Hakika, samun taimakon agaji daga ƙasashen waje ba ya kawar da ainihin abin da ke jawo talauci.

Abin da Ya Jawo Talauci

Abin da ke jawo matuƙar talauci shi ne son kai da al’ummai, gwamnatoci, da mutane suke nunawa. Alal misali, gwamnatocin ƙasashe masu arziki ba sa damuwa sosai da kawar da talauci a duniya domin an zaɓe su ne kuma dole ne su biya bukatun waɗanda suka jefa musu ƙuri’a. Da haka, suna hana manoman ƙasashe marar arziki su sayar da amfanin gonarsu a ƙasashe masu arziki don kada manoman ƙasashe masu arziki su rasa abin sayar wa. Kuma masu mulki a ƙasashe masu arziki suna ɗan ba da tallafi ga manomansu don su sayar da kayansu da araha fiye da manoman ƙasashe marasa arziki.

Babu shakka, ’yan Adam ne suke jawo talauci, domin mutane da gwamnatoci suna son su kāre muradin su ne kawai. Sulemanu ɗaya daga cikin marubutan Littafi Mai Tsarki ya bayyana yanayin kamar haka: “Waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu.”—Mai Hadishi 8:9, Littafi Mai Tsarki.

Saboda haka, akwai begen cewa za a taɓa kawar da talauci kuwa? Akwai gwamnatin da za ta iya canja halayen ’yan Adam kuwa?

[Akwati a shafi na 6]

Dokar da Za Ta Taimaka a Sha Kan Talauci

Jehobah Allah ya ba al’ummar Isra’ila ta dā jerin dokokin da idan suka bi su, ba za su faɗa cikin talauci ba. A ƙarƙashin Dokar, idan aka cire ƙabilar firistoci na Lawi, kowace iyali tana samun gadon fili. Domin an hana sayar da fili har abada, hakan yana kāre gadon iyali. A kowace shekara 50, za a mai da filin da aka saya ga ainihin mai filin ko iyalinsa. (Levitikus 25:10, 23) Idan mutum ya sayar da filinsa saboda rashin lafiya, bala’i ko ragwanci, za a mai da masa filin a Shekarar ’Yanci ba tare da biya bashin ba. Babu iyalin da za ta kasance cikin talauci daga tsara zuwa tsara.

Wani tanadi na rahama a cikin Dokar Allah ita ce, mutumin da ya faɗa cikin bala’i yana iya sayar da kansa cikin bauta. Zai karɓi kuɗin da aka saye shi kafin ya soma zaman bauta don ya biya bashin da ya ci. Idan bai fanshi kansa kafin shekara ta bakwai ba, za a ƙyale shi kuma za a ba shi hatsi da dabbobi don ya soma noma. Bugu da ƙari, idan talaka ya yi rancen kuɗi, Dokar ta haramta ’yan’uwansa Isra’ilawa su karɓi kuɗin ruwa. Dokar ta kuma hana mutanen girbe gefen gonakinsu domin talakawa su samu wajen yin kala. Da haka, babu wani ɗan Isra’ila da zai yi bara.—Kubawar Shari’a 15:1-14; Levitikus 23:22.

Amma, tarihi ya nuna cewa wasu Isra’ilawa sun faɗa cikin talauci. Me ya jawo hakan? Isra’ila ta ƙi bin Dokar Jehobah. Saboda haka, kamar yadda yake a yawancin ƙasashe, wasu mutane sun zama masu arziki da filaye, kuma wasu suka zama talakawa marasa fili. Talauci ya auku a tsakanin Isra’ilawa domin wasu a cikinsu sun yi watsi da Dokar Allah kuma suka nuna son kai.—Matta 22:37-40.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba