Mene Ne Matuƙar Talauci?
MATUƘAR talauci yana jefa rayuwa cikin haɗari. Yana nufin rashin samun isashen abinci, ruwa, māi, wurin kwana, kula da lafiyar jiki da kuma ilimi. Ya shafi wajen mutane biliyan ɗaya, wajen yawan jama’ar Afirka gabaki ɗaya. Amma, yawancin mutanen da ke zaune a irin su Yammancin Turai da Amirka ta Arewa ba su taɓa ganin mutumin da ke cikin matuƙar talauci ba. Bari mu ji daga bakin wasu.
Mbarushimana yana da zama a Rwanda, a Afirka, tare da matarsa da ’ya’ya biyar. Ɗansa na shida ya mutu saboda zazzaɓin cizon sauro. Ya ce: “Mahaifina ya rarraba filinsa a tsakanin mu shida. Nawa rabon filin ɗan ƙarami ne sosai, hakan ya sa ni da iyalina muka ƙaura zuwa wani gari. Ni da matata muna aikin ɗaukan buhunan duwatsu da ƙasa. Gidanmu bai da taga. Muna ɗebo ruwa ne daga wata rijiya a ofishin ’yan sanda. Muna cin abinci ne sau ɗaya a rana, amma a ranar da ba mu samu aikin yi ba, ba za mu samu abinci ba. Idan hakan ya faru, ina ficewa ne daga gida, domin ba zan iya tsayawa ba ina kallon yarana suna kukan yunwa.”
Victor da Carmen suna sana’ar gyaran takalmi. Suna zaune ne a wani gari da ke ware a ƙasar Bolivia tare da ’ya’yansu guda biyar. Suna zaman haya ne a ɗaki guda cikin wani tsohon gidan soro wanda rufin ke yoyo kuma babu wutar lantarki. Yaran makarantar da ke wannan ɓangaren duniyar suna zama ne a kan kujeru. Amma kujerun da ke wannan makarantar a yankin da iyalin Victor take da zama ta cika maƙil wanda hakan ya sa Victor ya yi wa ɗiyarsa kujerar zama, domin ta samu ta shiga makarantar. Waɗannan ma’auratan suna yin tafiyar mil shida (10 km) da ƙafa don su saro itacen yin dahuwa da tafasa ruwan sha. Carmen ta ce: “Ba mu da wurin yin ba-haya. Sai dai mu je gefen kogi inda ake zubar da shara, kuma ana wanka da ruwan kogin. Yaranmu suna yawan rashin lafiya.”
Francisco da Ilídia suna zaune ne a wata karkara a Mozambique. Suna da yara biyar amma ɗaya ya mutu bayan wani asibiti ya ƙi kwantar da shi sa’ad da ya yi zazzaɓin cizon sauro. Ma’auratan suna shuka shinkafa da dankali ne a cikin ’yar ƙaramar gonarsu don samun abincin da za su ci har tsawon wata uku. In ji Francisco: “A wasu lokatai ba ma samun amfanin gona domin rashin ruwan sama ko kuma saboda ɓarayin da ke sace amfanin gonarmu, ina samun ’yan kuɗaɗe ne ta wajen saro da sayar da icen gora da ake gini da shi. Muna kuma yin tafiyar awa biyu da ƙafa don samun itace daga cikin daji. Ni da matata muna ɗauko dami guda-guda, muna dahuwa da dami guda, muna kuma sayar da ɗayan.”
Mutane da yawa suna jin cewa bai dace ba kuma rashin adalci ne a ce a duniyar nan, mutum 1 cikin 7 yana rayuwa irin ta Mbarushimana, Victor da Francisco, yayin da biliyoyin mutane suke more arziki fiye kima. Wasu sun ƙoƙarin yin wani abu game da wannan batun. Talifin da ke gaba ya tattauna ƙoƙarce-ƙoƙarcensu da kuma begensu.
[Hoto a shafi na 3]
Carmen da yaranta biyu suna ɗiban ruwa daga kogi