Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 8/1 pp. 4-7
  • Talauci—Samun Maganinsa na Dindindin

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Talauci—Samun Maganinsa na Dindindin
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Matakai Masu Kyau na Bi da Talauci
  • Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dalilin Bege
  • Za Ka Kasance a Wurin?
  • Ka Bi Misalin Yesu Kuma Ka Nuna Damuwa Ga Matalauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Kawo Ƙarshen Talauci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Albishiri Ga Talakawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 8/1 pp. 4-7

Talauci—Samun Maganinsa na Dindindin

DUK DA munanan labarai kewaye da duniya game da talauci, har ila akwai waɗanda suke da begen za a iya wani abin taimako. Alal misali, bisa ga wani jigo cikin jaridar Manila Bulletin, Bankin Bunƙasa na Asiya ya ba da rahoto cewa “Asiya za ta iya kawar da talauci nan da shekaru 25.” Bankin ya ce idan akwai kayan ciniki a kasuwai za a sami kuɗi kuma haka zai ’yantar da mutane daga mugun talauci.

Wasu ƙungiyoyi da gwamnatoci sun jera shawarwari da kuma shiri a ƙoƙarin warware matsalar. Ga wasu cikinsu: tsarin inshora na jama’a, ƙara ilimi, kawar da bashi da al’ummai da suke neman bunƙasawa suke bin al’ummai da suka bunƙasa, kawar da hani na shigar da kayayyaki saboda ƙasashe da suke da yawan matalauta su iya sayar da kayansu da sauƙi kuma su samu gidajen da gwamnati suka gina domin matalauta.

A shekara ta 2000, Taron Majalisar Ɗinkin Duniya sun kafa maƙasudai da za su cim ma a shekara ta 2015. Waɗannan sun haɗa da kawar da talauci da yunwa da kuma rashin samun kuɗi. Ko yaya maƙasudin suke da girma, mutane da yawa suna shakkar ko za a cim ma su a wannan duniya da ke rarrabe.

Matakai Masu Kyau na Bi da Talauci

Tun da yake samun ci gaba na gaske a dukan duniya kamar ba zai yiwu ba, daga ina ne mutum zai iya neman taimako? Kamar yadda aka ambata da farko, da akwai tushen hikima mai kyau da zai iya taimakon mutane a yanzu haka. Menene? Kalmar Allah ce, Littafi Mai Tsarki.

Menene ya sa Littafi Mai Tsarki ya bambanta daga dukan tushen koyarwa? Ya fito ne daga iko mafi girma, Mahaliccinmu. Da akwai abubuwa masu daraja cikinsa—ƙa’idodi da suke amfanar dukan mutane, a dukan wurare, kuma a dukan lokatai. Idan aka bi waɗannan ƙa’idodi, za su taimaki matalauta su more rayuwa mai gamsarwa ko a yanzu ma. Bari mu bincika misalai kalilan.

Ka kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hikima, kamar dukiya, kāriya ce; amma fikon sani ke nan, hikima ta kan kiyaye ran mai-ita.” (Mai-Wa’azi 7:12) Menene wannan yake nufi? Kuɗi ba shi ne kome ba. Alhali, yana ba da ɗan kāriya. Muna iya sayan abubuwa da muke bukata da shi, amma akwai iyakarsa. Da akwai abubuwa da suka fi muhimmanci da kuɗi ba zai iya saya ba. Idan mun fahimci wannan zai sa mu sa abin duniya a matsayin da ya dace, muna guje wa baƙin cikin da waɗanda suka kafa rayuwarsu domin samun kuɗi suke da shi. Kuɗi ba zai iya sayan rai ba, amma aikatawa da hikima zai kāre rai a yanzu kuma yana iya buɗe hanyar rai marar matuƙa.

Ka yi rayuwa daidai da aljihunka. Abubuwan da muke so ba lallai bukatarmu ce ba. Ya kamata mu sa muhimmanci a kan bukatunmu. Yana da sauƙi mu ce wa kanmu muna bukatar wani abu, alhali kuwa abin da muke so ne ba abin biyan bukata ba ne. Mutum mai hikima da farko zai yi lissafin kuɗinsa domin bukatu masu muhimmanci—abinci, sutura, mafaka, da sauransu. Kafin ya kashe kuɗi a kan wani abu, zai bincika sauran kuɗinsa ko zai iya sayan wasu abubuwa. A cikin wani misalinsa, Yesu ya ce yana da kyau mutum ya “fara zaunawa tukuna, ya yi lissafin tamanin . . . , ko yana da abin da zai gama shi.”—Luka 14:28.

A ƙasar Philippines, Eufrosina, gwauruwa mai yara uku suna wahalar samun na biyan bukata kuma suna lallaɓa da ɗan kuɗin da suke da shi domin maigidanta ya bar ta shekaru da daɗewa. A yin wannan, ta koyar da yaranta su fahimci abin da ya fi muhimmanci. Alal misali, yaran za su iya ganin wani abin da suke so. Maimakon kawai ta ce a’a, sai ta tattauna da su ta ce: “To, idan kana so kana iya saya, amma za ka yi zaɓe. Muna da kuɗin abu guda ne kawai. Za mu iya sayan wannan abin da kake so, ko kuma mu sayi ɗan nama ko ganye da za mu dafa shinkafa da shi wannan mako. Yanzu wanne kake so? Ka zaɓa.” Sau da yawa, yaran sukan fahimta, sai su yarda sun fi son abinci maimakon abin.

Ka gamsu. “Da shi ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci,” in ji wata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki. (1 Timothawus 6:8) Kuɗi ba ya kawo farin ciki. Mutane da yawa da suke da arziki ba sa farin ciki, sa’in nan kuma matalauta da yawa suna farin ciki sosai. Waɗannan sun koyi su gamsu da abubuwa kalilan da suke bukata a rayuwa. Yesu ya yi maganar ‘ido ya zama sosai’ bisa abubuwa da suka fi muhimmanci. (Matta 6:22) Wannan yana sa mutum ya gamsu. Matalauta da yawa suna gamsuwa domin sun gina dangantaka mai kyau da Allah kuma suna da rayuwar iyali mai farin ciki—abubuwa da kuɗi ba zai iya saya ba.

Waɗannan misalai kalilan ne kawai na shawarwari masu kyau na Littafi Mai Tsarki da za su taimaki matalauta su jure da yanayinsu. Da akwai wasu da yawa. Alal misali, ka guje wa munanan abubuwa kamar shan taba da caca, da ke cin kuɗi; kana iya kafa abubuwa masu muhimmanci a rayuwa, musamman ka kafa makasudai na ruhaniya; a wurare da babu aiki, ka yi ƙoƙarin samun fasaha ko aikin hannu da mutane suke bukata. (Misalai 22:29; 23:21; Filibbiyawa 1:9-11) Littafi Mai Tsarki ya ce a yi amfani da “sahihiyar hikima da hankali” domin za su “zama rai ga ruhunka.”—Misalai 3:21, 22.

Ko da yake shawarwari na Littafi Mai Tsarki zai yi tanadin sauƙaƙawa mai kyau ga waɗanda suke kokawa da talauci, tambayoyi game da nan gaba har ila suna nan. Matalauta za su kasance cikin talauci ne har abada? Za a iya kawar da bambanci kuwa tsakanin masu arziki ƙwarai da waɗanda suke talauci ƙwarai? Bari mu bincika wasu abin taimako da mutane da yawa ba su sani ba.

Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dalilin Bege

Mutane da yawa sun yarda cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne mai kyau. Amma, sau da yawa ba su sani ba cewa yana wasu koyarwa na ainihi da ke nuna canje-canje na musamman da za su auku ba da daɗewa ba.

Allah ya yi niyyar ya ɗauki matakai na warware matsalolin mutane, har da talauci. Tun da yake gwamnatocin mutane sun kasa ko kuma ba sa son su yi, Allah yana nufin ya sake su. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki ya faɗa da gaba gaɗi a Daniel 2:44: “Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.”

Bayan an kawar da waɗannan “mulkoki,” ko gwamnatoci, Sarkin da Allah ya naɗa zai soma aiki. Sarkin nan ba ɗan Adam ba ne amma halitta mai iko ne na samaniya kamar Allah, yana da iyawar kawo canje-canje na musamman da ake bukata a kawar da bambanci na wannan lokaci. Allah ya zaɓi Ɗansa ya yi wannan. (Ayukan Manzanni 17:31) Zabura 72:12-14 ta kwatanta abin da wannan Sarkin zai yi, tana cewa: “Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai. Za ya fanshi ransu daga zalunci da ƙwace; a ganinsa kuma jininsu mai-daraja ne.” Lallai wannan bege ne mai girma! A ƙarshe za a sami sauƙi! Sarki da Allah ya naɗa zai aika domin matalauta da fakirai.

Matsaloli da yawa da ke tattare da talauci za su ƙare a lokacin. Aya ta 16 ta Zabura 72 ta ce: “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.” Ba za a yi karancin abinci ba kuma domin yunwa, rashin kuɗi, ko kuma wata kasawar gwamnati.

Za a yi maganin wasu matsaloli kuma. Alal misali, yau yawancin mazaunan duniya ba su da gidan kansu. Amma Allah ya yi alkawari: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; gama kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama, zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.” (Ishaya 65:21, 22) Kowa zai sami gidan kansa kuma more aikinsa. Saboda haka, Allah ya yi alkawari zai magance talauci dindindin. Ba za a sami bambanci mai girma kuma ba tsakanin mawadata da matalauta, ba za a sake samun mutane da suke fama kawai don su samu su tsira ba.

A jin waɗannan alkawura na Littafi Mai Tsarki, mutum zai iya jin cewa ba za su iya faruwa ba. Amma, idan aka bincika Littafi Mai Tsarki da kyau ya nuna cewa dukan alkawuran Allah a dā sun cika. (Ishaya 55:11) Saboda haka, ba batun wataƙila za su cika ba. Maimako, tambayar ya kamata ta zama, Menene dole ka yi domin ka amfana sa’ad da za su cika?

Za Ka Kasance a Wurin?

Tun da yake gwamnatin ta Allah ce, dole mu kasance irin mutane da Allah zai amince da su su zama mazauna cikin sarautar. Bai ƙyale mu babu ja-gora ba game da yadda za mu cancanta. Farillan suna cikin Littafi Mai Tsarki.

Mai adalci ne Sarki da aka naɗa, Ɗan Allah. (Ishaya 11:3-5) Saboda haka, waɗanda aka amince da su don su rayu cikin gwamnatin ana bukatar su zama masu adalci. Misalai 2:21, 22 ta ce: “Masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”

Da akwai yadda za a koya a cika waɗannan farillan ne? E, da akwai. Ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yin amfani da ja-gorarsa, za ka iya moran rayuwa mai kyau nan gaba. (Yohanna 17:3) Shaidun Jehovah za su yi murnan taimakonka ka yi nazarin. Muna gayyatarka ka yi amfani da wannan zarafin ka haɗa cikin jam’iyya wadda ba za ta sake shaida talauci da rashin gaskiya ba.

[Hoto a shafi na 5]

Eufrosina: “Yin amfani da kuɗin da muke da shi a kan abubuwa masu muhimmanci ya taimake iyalita ta sami abin biyan bukata”

[Hotuna a shafi na 6]

Kuɗi ba zai iya sayan dangantaka mai kyau da Allah da rayuwar iyali mai farin ciki ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba