Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 10/1 pp. 8-13
  • Yin Taɗi Na Ruhaniya Yana Ƙarfafawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Taɗi Na Ruhaniya Yana Ƙarfafawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Mai da Hankali ga Zuciya
  • “Ku Mai da Hankali ga Waɗannan”
  • Ka Yi Taɗi da ke Ƙarfafawa
  • Yin Taɗi na Ruhaniya Yana Kawo Fa’idodi
  • Sabon Talifi don Soma Tattaunawa da Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Yadda Za A Bi Bayanin da Ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Ku Riƙa Farin Cikin Soma Tattaunawa da Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Yadda Za Mu Yi Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 10/1 pp. 8-13

Yin Taɗi Na Ruhaniya Yana Ƙarfafawa

“Kada kowanne ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda a ke bukata, domin shi bada alheri ga waɗanda su ke ji.”—AFISAWA 4:29.

1, 2. (a) Yaya iya magana na ɗan Adam yake da muhimmanci? (b) Yaya bayin Jehovah suke son su yi amfani da furcinsu?

“IYA magana na ɗan Adam asiri ne; kyautar Allah ce, mu’ujiza kuma.” Haka Ludwig Koehler mawallafin ƙamus ya rubuta. Wataƙila ba ma ɗaukan wannan kyautar Allah da muhimmanci. (Yaƙub 1:17) Amma ka yi tunanin girman hasara da ake yi sa’ad da gazawar jiki ta sa wanda muke ƙauna bai iya magana ba. “Muna magana sosai da ya sa muka yi kusa da juna,” in ji Joan, wadda mijinta yanzu yake wahalar gazawar jiki. “Na yi rashin taɗin da muke yi ƙwarai!”

2 Taɗi yana ƙarfafa abokantaka, ya sa a daina jayayya, yana ƙarfafa wanda ya kasala, yana ƙarfafa bangaskiya, kuma yana kyautata rayuwa—amma taɗi ba ya cim ma waɗannan abubuwa haka kawai ba. Sarki Sulemanu mai hikima ya lura: “Akwai wanda ya kan yi magana da garaje kamar sussukan takobi: Amma harshen mai-hikima lafiya ne.” (Misalai 12:18) Da yake mu bayin Jehovah ne, muna son taɗinmu ya warkar kuma ya ƙarfafa, maimakon ya yi lahani ko kuma baƙanta rai. Muna kuma son mu yi amfani da furcinmu mu yabi Jehovah, a hidimarmu ta fage da kuma a taɗinmu. Mai Zabura ya rera: “A cikin Allah mun yi fahariyarmu dukan yini, za mu yi godiya ga sunanka kuma har abada.”—Zabura 44:8.

3, 4. (a) Wace matsala dukanmu muke fuskanta game da furcinmu? (b) Me ya sa ya dace mu damu da furcinmu?

3 Almajiri Yaƙub ya yi gargaɗi: “Harshe, babu mutum wanda ya ke da iko ya hore shi.” Ya tuna mana: “A cikin abu dayawa dukanmu mu kan yi tuntuɓe. Idan wani ba ya yi tuntuɓe ga wajen magana ba, wannan cikakken mutum ne, mai-ikon sarrafa dukan jiki kuma.” (Yaƙub 3:2, 8) Dukanmu ajizai ne. Saboda haka, duk da ƙoƙarinmu, ba koyaushe ba ne furcinmu yake ƙarfafa wasu ko kuma yabi Mahaliccinmu. Saboda haka, dole mu koyi mai da hankali ga abin da muke faɗa. Ban da haka, Yesu ya ce: “Kowacce maganar banza da mutane ke faɗi, a cikin ranar shari’a za su bada lissafinta. Gama bisa ga zantattukanka za ka barata, bisa ga zantattukanka kuma za a kāshe ka.” (Matta 12:36, 37) Hakika, Allah na gaskiya zai yi mana hisabi domin furci da muke yi.

4 Hanya ɗaya na guje wa furci mai lahani ita ce koyan halin yin taɗi na ruhaniya. Wannan talifin zai bincika yadda za mu yi haka, irin darussa da za mu yi taɗinsu, da fa’idodi da za mu samu daga furci mai ƙarfafawa.

Ka Mai da Hankali ga Zuciya

5. Yaya zuciya take da muhimmin matsayi a tokara wa taɗi mai ƙarfafawa?

5 A koyan halin yin taɗi mai ƙarfafawa, dole mu fahimta cewa furcinmu na bayyana abin da yake cikin zuciyarmu. Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Matta 12:34) Wato, muna son yin taɗi game da abin da ke da muhimmanci gare mu. To, muna bukatar yi wa kanmu tambaya: ‘Me taɗina ke bayyana game da yanayin zuciyata? Sa’ad da nake tare da iyalina ko kuma ’yan’uwa masu bi, taɗina game da abubuwa na ruhaniya ne ko kuma game da wasan guje-guje, tufafi, silima, abinci, saye-saye na zamani, ko kuma a kan wasu abubuwa da ba su da muhimmanci?’ Wataƙila ba da saninmu ba, rayuwarmu da tunaninmu sun kasance a kan abubuwa marasa muhimmanci. Gyara abubuwa da muka sa farko zai kyautata taɗinmu da kuma rayuwarmu.—Filibbiyawa 1:10.

6. Wane hakki bimbini ke da shi a taɗinmu?

6 Bimbini mai kyau wata hanya ce ta kyautata abin da muke faɗa. Idan da son rai muka yi ƙoƙarin yin tunani game da abubuwa na ruhaniya, za mu iske cewa za muna yin taɗi na ruhaniya. Sarki Dauda ya ga wannan nasabar. Ya rera: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji.” (Zabura 19:14) Sai mai Zabura Asaph ya ce: “Zan yi ta bimbinin dukan aikin [Allah], in yi maganar zuci a kan aike aikenka.” (Zabura 77:12) Zuciya da azanci da ke damuwa game da gaskiyar Kalmar Allah za ta riƙa furci na yabo. Irmiya bai iya daina magana game da abubuwa da Jehovah ya koya masa ba. (Irmiya 20:9) Mu ma za mu yi haka idan muna bimbini a kan al’amura na ruhaniya a kai a kai.—1 Timothawus 4:15.

7, 8. Waɗanne darussa suke da kyau don taɗi mai ƙarfafawa?

7 Kasance da tsari na ruhaniya mai kyau na sa mu samu darussan taɗi mai ƙarfafawa da yawa. (Filibbiyawa 3:16) Manyan taro, taron gunduma, taron ikilisiya, littattafai, da kuma nassin yini da kalaminsa, dukansu tamani ne na ruhaniya da za mu gaya wa wasu. (Matta 13:52) Abubuwa da muke shaidawa daga hidimarmu ta Kirista suna motsa mu a ruhaniya!

8 Itatuwa iri-iri, dabbobi, tsuntsaye, da kifaye da Sarki Sulemanu ya gani a Isra’ila sun burge shi. (1 Sarakuna 4:33) Yana farin cikin taɗi game da halittun Allah. Mu ma za mu iya haka. Bayin Jehovah suna jin daɗin magana a kan batutuwa dabam dabam, amma mutane masu ruhaniya taɗinsu a kan abubuwa na ruhaniya ne.—1 Korinthiyawa 2:13.

“Ku Mai da Hankali ga Waɗannan”

9. Wane gargaɗi ne Bulus ya ba wa Filibbiyawa?

9 Ko menene muke tattaunawa, taɗinmu zai ƙarfafa wasu idan sun yi daidai da gargaɗin manzo Bulus zuwa ga ikilisiyar Filibbi. Ya rubuta: “Iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan.” (Filibbiyawa 4:8) Abubuwan da Bulus ya ambata suna da muhimmanci da ya sa ya ce ‘ku maida hankali ga waɗannan.’ Ya kamata mu cika azantanmu da zukatanmu da su. Saboda haka, bari mu ga yadda mai da hankali ga kowanne cikin abubuwa takwas da Bulus ya ambata za su taimake mu a taɗinmu.

10. Ta yaya taɗinmu zai kasance yana ɗauke da abubuwa da ke na gaskiya?

10 Abin da ke mai gaskiya ba kawai yana nufin abin da ke daidai ko kuma a ce ba ƙarya ba ce. Yana nufin wani abin da ke daidai da ake gaskata shi a ce, gaskiyar Kalmar Allah ce. Shi ya sa, sa’ad da muke gaya wa mutane game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki da ta burge mu, jawabai da suka ƙarfafa mu, ko kuma gargaɗi na Nassi da ya taimake mu, muna mai da hankali ke nan da abin da ke na gaskiya. A wata sassa, muna ƙi da “ilimin da ana ce da shi hakanan a ƙaryace,” da ake gani kamar gaskiya. (1 Timothawus 6:20) Kuma za mu guje maimaita gulma ko kuma ba da labari da ba gaskiya ba ne.

11. Waɗanne abubuwa masu muhimmanci za mu iya taɗinsu?

11 Abubuwa da suka isa bangirma batutuwa ne masu daraja da ke da muhimmanci ba marasa muhimmanci ba. Sun ƙunshi damuwa game da hidimarmu ta Kirista, miyagun zamanu da muke ciki, da bukatar mu kasance da hali mai kyau. Sa’ad da muke tattauna batutuwa masu muhimmanci, muna ƙarfafa ƙudurinmu mu kasance a faɗake a ruhaniya, mu riƙe amincinmu, kuma mu ci gaba da wa’azin bishara. Hakika, labarai masu kyau a hidimarmu da aukuwa na kwanan nan da suke tuna mana cewa muna zama cikin kwanaki na ƙarshe suna sa mu sami abin taɗi da ke da ban ƙarfafa.—Ayukan Manzanni 14:27; 2 Timothawus 3:1-5.

12. Bisa gargaɗin Bulus a mai da hankali ga abubuwa na adalci da tsabta, menene ya kamata mu guje su?

12 Kalmar nan adalci tana nufin abin da ke daidai a idanun Allah—bisa mizanansa. Abin da ke mai tsabta yana da ma’anar tunani da hali mai tsarki. Tsegumi, maganganun banza, ko kuma habaici na lalata ba su dace ba a taɗinmu. (Afisawa 5:3; Kolossiyawa 3:8) A wajen aiki ko kuma a makaranta, Kiristoci da hikima ba sa sa baki sa’ad da aka soma irin wannan taɗi.

13. Ka ba da misalan taɗi game da abubuwa na ƙauna da na kyakkyawan ambato.

13 Sa’ad da Bulus ya ce mu mai da hankali ga abubuwa na ƙauna, yana nufin batutuwa masu kyau da suka dace ko kuma ke motsa ƙauna, maimakon waɗanda suke ta da ƙiyayya, baƙin ciki, ko kuma jayayya. Abubuwa na kyakkyawan ambato bayani da labari ne masu kyau. Irin labaran nan masu kyau game da labaran rayuwa na ’yan’uwa masu aminci ne da suke fitowa a kai a kai a jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! Me ya sa ba za ka gaya wa mutane abubuwa da suka burge ka muddin ka karanta waɗannan talifofi masu ƙarfafa bangaskiya ba? Abin ban ƙarfafa ne a ji abin da wasu suka cim ma a ruhaniya! Irin wannan taɗi zai sa a kasance da ƙauna da haɗin kai cikin ikilisiya.

14. (a) Menene yin kirki ke bukata a gare mu? (b) Ta yaya furcinmu zai haɗa da abubuwa da suka cancanci yabo?

14 Bulus ya yi zancen “idan akwai kirki.” Kirki yana nufin nagarta ko kuma ɗabi’a mai kyau. Dole mu mai da hankali, ƙa’idodin Nassi su yi wa furcinmu ja-gora domin kada su bijire daga abin da ke na adalci, tsabta, da kirki. Abin da yake na yabo yana nufin “yabawa.” Idan ka saurari jawabi mai kyau ko kuma ka lura da misali na aminci cikin ikilisiya, ka yi maganarsu—ga mutumin da kuma wasu. Sau da yawa manzo Bulus yana yaba wa hali mai kyau na ’yan’uwansa masu bi. (Romawa 16:12; Filibbiyawa 2:19-22; Filimon 4-7) Babu shakka, abubuwa da Mahaliccinmu ya yi sun cancanci yabo. A ciki za mu samu abubuwan yin taɗi mai ƙarfafawa da yawa.—Misalai 6:6-8; 20:12; 26:2.

Ka Yi Taɗi da ke Ƙarfafawa

15. Wane umurni na Nassi ya bukaci iyaye su yi taɗi mai kyau da yaransu?

15 Kubawar Shari’a 6:6, 7 ta ce: “Waɗannan zantattuka fa, da ni ke umurce ka yau, za su zauna cikin zuciyarka: kuma za ka koya ma ’ya’yanka su da anniya, za ka riƙa faɗinsu sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” A bayyane, wannan umurni na bukatar iyaye su yi taɗi mai kyau na ruhaniya da yaransu.

16, 17. Menene iyaye Kiristoci za su koya daga misalan Jehovah da Ibrahim?

16 Muna iya tunanin dogon taɗi da Yesu ya yi da Ubansa na samaniya sa’ad da suke tattaunawa game da hidimarsa a duniya. Yesu ya gaya wa almajiransa: “Uba wanda ya aiko ni, shi ne ya ba ni umurni, abin da zan faɗi, da magana da zan yi kuma.” (Yohanna 12:49; Kubawar Shari’a 18:18) Ibrahim uban iyali ya ɓad da sa’o’i masu yawa yana gaya wa ɗansa Ishaƙu game da yadda Jehovah ya yi musu albarka da kuma kakaninsu. Irin wannan taɗi babu shakka ya taimaki Yesu da Ishaƙu su yi biyayya da nufin Allah cikin tawali’u.—Farawa 22:7-9; Matta 26:39.

17 Yaranmu ma suna bukatar taɗi mai ƙarfafawa. Dole iyaye su nemi lokaci su yi magana da yaransu. Idan zai yiwu, me ya sa ba za ku shirya ku zauna cin abinci na iyali tare aƙalla sau ɗaya a rana ba? A lokacin ko kuma bayan cin abinci za a samu zarafin taɗi mai ƙarfafawa domin lafiyar iyalin na ruhaniya.

18. Ka ba da labari da ya nuna amfanin taɗi mai kyau tsakanin iyaye da yara.

18 Alejandro, majagaba wanda yake farkon shekarunsa na 20, ya tuna shakkar da yake yi da yake ɗan shekara 14. Ya ce: “Domin tasirin abokan makaranta da malamai, na yi shakkar Allah ya wanzu da kuma gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Iyayena sun ɓad da sa’o’i da yawa suna magana da ni cikin haƙuri. Taɗin nan ya taimake ni ba kawai na daina shakka ba a wannan mawuyancin lokaci amma kuma na tsai da shawarwari masu kyau a rayuwata.” Yanzu kuma fa? Alejandro ya ci gaba: “Har ila ina gida. Amma yawan aikinmu ya sa ya kasance da wuya ni da babana mu yi taɗi mu kaɗai. Saboda haka, mu biyu mukan ci abinci tare wajen aikinsa sau ɗaya kowane mako. Ina ji daɗin irin taɗin nan.”

19. Me ya sa dukanmu muke bukatar taɗi na ruhaniya?

19 Ba ma jin daɗin zarafin taɗi na ruhaniya da ’yan’uwanmu masu bi ne? Muna da irin wannan zarafi na taɗi a taro, sa’ad da muke hidimar fage, a wurin liyafa da kuma sa’ad da muke tafiya. Bulus yana ɗokin ya yi magana da Kiristoci a Roma. Ya rubuta musu: “Ina marmarin ganinku . . . ni da ku mu sami ƙarfafawa a wurinku, kowannenmu ta wurin bangaskiyar junanmu, taku da tawa kuma.” (Romawa 1:11, 12) “Taɗi na ruhaniya da Kiristoci masu bi yana biyan bukata mai muhimmanci,” in ji Johannes, dattijo Kirista. “Yana daɗaɗa zuciya kuma sauƙaƙa damuwa na yau da kullum. Nakan tambaye tsofaffi su gaya mini game da rayuwarsu da abin da ya taimake su su kasance da aminci. Cikin shekaru, na yi taɗi da tsofaffi da yawa, na samu hikima ko wayewar kai da ya kyautata rayuwata.”

20. Menene za mu iya yi idan muka sadu da wanda yake kunya?

20 Idan wani ba ya son taɗi na ruhaniya da ka soma fa? Kada ka kasala. Wataƙila nan gaba za ka sami zarafi mai kyau. Sulemanu ya lura: “Magana a kan kari tana kāma da tuntuwa na zinariya cikin kwanduna na azurfa.” (Misalai 25:11) Ka nuna fahimi wajen waɗanda suke kunya. “Shawara a cikin zuciyar mutum tana kama da ruwa mai-zurfi: Amma mutum mai-fahimi za ya jawo ta.”a (Misalai 20:5) Fiye da haka, kada ka ƙyale halayen wasu su hana ka magana game da abubuwan da suka motsa zuciyarka.

Yin Taɗi na Ruhaniya Yana Kawo Fa’idodi

21, 22. Waɗanne fa’idodi muke samu daga yin taɗi na ruhaniya?

21 Bulus ya yi gargaɗi: “Kada kowanne ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda a ke bukata, domin shi bada alheri ga waɗanda su ke ji.” (Afisawa 4:29; Romawa 10:10) Yana bukatar ƙoƙari a yi taɗi mai ƙarfafawa, amma fa’idodin suna da yawa. Taɗi na ruhaniya yana taimakon mu mu gaya wa mutane imaninmu kuma mu ƙarfafa ’yan’uwanmu.

22 Saboda haka, bari mu yi amfani da kyautar iya magana mu ƙarfafa mutane kuma mu yabi Allah. Irin taɗin nan yana kawo mana gamsuwa kuma yana ƙarfafa wasu. Fiye da haka, zai faranta zuciyar Jehovah domin yana saurara taɗinmu kuma yana farin ciki sa’ad da muka yi amfani da harshenmu a hanyar da ta dace. (Zabura 139:4; Misalai 27:11) Idan taɗinmu na ruhaniya ne, za mu tabbata cewa Jehovah ba zai manta da mu ba. Da yake magana game da waɗanda suke bauta wa Jehovah a zamaninmu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu-tunawa da sunansa.” (Malachi 3:16; 4:5) Lallai yana da muhimmanci taɗinmu ya kasance da ban ƙarfafa a ruhaniya!

[Hasiya]

a Wasu rijiyoyi a Isra’ila suna da zurfi sosai. A Gibiyon, masu tonan ƙasa sun ga wata rijiya mai zurfin kafa 80. Tana da matakala da mutane suke takawa su kai gindin rijiyar domin su jawo ruwa.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene taɗinmu ke bayyana game da mu?

• Waɗanne abubuwan ƙarfafawa ne za mu yi taɗinsu?

• Wane muhimmanci taɗi yake da shi cikin iyali da cikin ikilisiyar Kirista?

• Waɗanne fa’idodi ne taɗi mai ƙarfafawa ke kawowa?

[Hotuna a shafi na 10]

Taɗi mai ƙarfafawa yana game da . . .

“abin da ke mai-gaskiya”

“abin da ya isa bangirma”

“idan akwai yabo”

“abin da ke da kyakkyawan ambato”

[Inda aka Daukos]

Video cover, Stalin: U.S. Army photo; Creator book cover, Eagle Nebula: J. Hester and P. Scowen (AZ State Univ.), NASA

[Hoto a shafi na 11]

Lokacin cin abinci zarafi ne mafi kyau a yi taɗi na ruhaniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba