Maganar Jehovah Rayayyiya Ce
Taƙaici Daga Littafin Farawa—na I
“FARAWA” tana nufin “asali,” ko kuma “tushe.” Wannan sunan ya dace da littafin da ya faɗi yadda aka sami sararin halitta, yadda aka shirya duniya domin ’yan Adam, da kuma yadda mutane suka kasance a cikinta. Musa ya rubuta wannan littafin cikin dajin Sinai, ƙila ya gama shi a shekara ta 1513 K.Z.
Littafin Farawa ya gaya mana game da duniya da ke kafin Rigyawa, abin da ya faru bayan Rigyawa, da kuma yadda Jehovah Allah ya bi da Ibrahim, Ishaƙu, Yakubu, da kuma Yusufu. Wannan talifin zai taƙaita Farawa 1:1–11:9, watau har zuwa lokacin da Jehovah ya soma sha’ani da uban iyali, Ibrahim.
DUNIYA KAFIN RIGYAWA
(Farawa 1:1–7:24)
Kalmomin nan “a cikin farko,” da suka soma littafin Farawa, suna nufin biliyoyin shekaru ne can baya. An kwatanta aukuwa na ‘kwanaki’ shida na halitta ko kuma lokatai na musamman na ayyukan halitta daidai da idan mutum yana duniya a lokacin zai gane. Allah ya halicci mutum a rana ta shida. Ko da yake ba da daɗewa ba an yi hasarar Aljanna domin rashin biyayya ta mutum, Jehovah ya ba da bege. Annabci na farko cikin Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “zuriya” da zai kawar da sakamakon zunubi kuma ya ƙuje Shaiɗan a kai.
A cikin ƙarnuka 16 daga baya, Shaiɗan ya yi nasara a juyar da yawancin mutane daga Allah, kalilan ne masu aminci, kamar su Habila, Ahnuhu, da kuma Nuhu. Alal misali, Kayinu ya kashe adali, ɗan’uwansa Habila. Aka “fara kira bisa sunan Ubangiji,” a hanyar munafunci. Lamech ya rera waƙar yadda ya kashe wani mutum, cewa yana kāre kansa ne domin yana da halin mutanen zamanin. Yanayi ya suƙuƙuce sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwashi mata kuma suka haifi ’ya’ya ƙatta mugaye. Duk da haka, Nuhu amini ya gina jirgi, ya gargaɗe wasu game da Rigyawar da take zuwa, kuma ya tsira wa halakar tare da iyalinsa.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi
1:16—Ta yaya Allah ya ba da haske a rana ta farko tun da yake ba a yi manyan haske ba har sai kwana na huɗu? Kalmar Ibrananci da aka fassara “yi” a aya ta 16 ba daidai ba ne da kalmar da aka fassara “halitta” da aka yi amfani da ita a Farawa sura 1, ayoyi 1, 21, da 27. An halicci “sama” da ke da haske da daɗewa kafin a soma kwana na “farko.” Amma hasken bai kai nan duniya ba. A kwana na farko, “haske kuwa ya kasance” domin haske da ya haskaka cikin gajimare ya iya kai duniya. Da haka, zagayawar duniya ta sa aka soma samun dare da rana. (Farawa 1:1-3, 5) Har wa yanzu ba a iya ganin tushen wannan haske a duniya ba. Amma wani abu na musamman ya faru a kwana na huɗu na halitta. Rana, wata, da kuma taurari suka soma “bada haske a bisa duniya.” (Farawa 1:17) Yanzu “Allah ya yi” su da ake iya ganinsu daga duniya.
3:8—Jehovah Allah ya yi wa Adamu magana kai tsaye ne? Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa sa’ad da Allah yake wa mutane magana, yana yin haka ta wurin mala’ika ne. (Farawa 16:7-11; 18:1-3, 22-26; 19:1; Alƙalawa 2:1-4; 6:11-16, 22; 13:15-22) Babban kakakin Allah shi ne Ɗansa makaɗaici, da ake ce da shi “Kalma.” (Yohanna 1:1) Mai yiwuwa ne cewa Allah ya yi magana da Adamu da Hauwa’u ta wurin “Kalmar” ne.—Farawa 1:26-28; 2:16; 3:8-13.
3:17—A wace hanya ce aka la’antar da ƙasa, kuma har yaushe? La’ana da aka yi wa ƙasa tana nufin cewa ko a yanzu ma nome ƙasa za ta kasance da wuya. Zuriyar Adamu sun sha wahalar ƙayayuwa da sarƙaƙiya har da uban Nuhu, Lamech ya yi maganar ‘wahalar hannuwansu, da ya fito daga ƙasa wadda Ubangiji ya la’anta.’ (Farawa 5:29) Bayan Rigyawar, Jehovah ya albarkaci Nuhu da ’ya’yansa, ya gaya musu Ƙudurinsa su mamaye duniya. (Farawa 9:1) Lallai daga baya Allah ya kawar da la’anarsa a kan ƙasa.—Farawa 13:10.
4:15—Ta yaya Jehovah “ya yi ma Kayinu alama”? Littafi Mai Tsarki bai ce an sa wani taɓo ko alama a jikin Kayinu ba. Mai yiwuwa ne cewa alamar wani abin da Allah ya faɗa ne da aka sani kuma mutane suka yi biyayya da shi saboda kada su kashe shi a yin ramako.
4:17—Daga ina ne Kayinu ya sami matarsa? Adamu ya “haifi ’ya’ya maza da mata.” (Farawa 5:4) Kayinu ya ɗauki ɗaya cikin ƙanwarsa ko kuma ’yar ƙanensa da ta zama matarsa. A kwana a tashi, Dokar Allah ta daina yarda wa Isra’ilawa su auri ’yar ko kuwa ɗan ubansu.—Leviticus 18:9.
5:24—A wace hanya ce Allah ya ‘ɗauki Ahnuhu’? Ahnuhu yana cikin haɗarin mutuwa, amma Allah bai yarda ya sha wahala a hannun magabtansa ba. Manzo Bulus ya rubuta: “Aka ɗauki Ahnuhu domin kada ya ga mutuwa.” (Ibraniyawa 11:5) Wannan ba ya nufin cewa Allah ya kai shi sama, da zai ci gaba da rayuwa ba. Yesu ne na farko da ya hau sama. (Yohanna 3:13; Ibraniyawa 6:19, 20) “Aka ɗauki Ahnuhu domin kada ya ga mutuwa” ƙila wannan yana nufin Allah ya sa shi a yanayin annabci sai kuma ya ɗauki ransa sa’ad da yake cikin wannan yanayin. A cikin irin wannan yanayin, Ahnuhu bai sha wahala ko kuma “ga mutuwa” ba a hannun magabtansa.
6:6—A wane azanci ne za a ce Jehovah “ya tuba” da ya yi mutum? Kalmar Ibrananci da a nan aka fassara “ya tuba” canja hali ko kuma manufa ne. Jehovah kamiltacce ne saboda haka, bai yi kuskure ba a halittar mutum. Amma, manufarsa ya canja game da muguwar tsara da take kafin Rigyawar. Allah ya canja halinsa na Mahaliccin mutane zuwa na mai halaka su domin rashin amincinsu da kuma muguntarsu. Da yake ya ceci wasu mutane, ya nuna cewa nadamarsa a kan miyagu ne.—2 Bitrus 2:5, 9.
7:2—Menene tushen bambanci tsakanin dabobbi masu tsabta da marasa tsabta? Wannan ya dangana ga irin abin da za iya hadayarsa a bauta ba abin da za a iya ci ba ko kuma wanda aka hana ci. Kafin Rigyawa, mutum ba shi da izinin cin nama. Yadda aka samu abinci ‘tsarkake’ da ‘mai-ƙazanta’ a lokacin Dokar Musa ke nan, kuma hakan ya ƙare lokacin da aka kawar da dokar. (Ayukan Manzanni 10:9-16; Afisawa 2:15) Hakika, Nuhu ya san abin da ya dace don hadayar bauta ga Jehovah. Da zarar ya fito daga jirgin, ya “gina bagadi ga Ubangiji; ya ɗiba kuma daga cikin kowane irin tsatsabtan dabba, da kowane irin tsatsabtan tsuntsu, ya miƙa baiko na ƙonawa a bisa bagadi.”—Farawa 8:20.
7:11—Daga ina ne ruwan da aka yi Rigyawarsa a dukan duniya ya fito? A lokaci na biyu na halitta, ko kuma “kwana” na biyu, lokacin da aka yi ‘sararin’ duniya, akwai ruwa a “ƙarƙashin sarari,” da kuma a “bisa sararin.” (Farawa 1:6, 7) Ruwa da ke “ƙarƙashin” sarari wanda yake duniya ne dama. Ruwa da ke “bisa” sarari raɓa ne mai yawa da ke tattare a bisa duniya, da ya zama “maɓulɓulan zurfafa.” Waɗannan ruwaye ne suka zubo a zamanin Nuhu.
Darussa da Za Mu Koya:
1:26. Domin an yi mu cikin siffar Allah, mutane suna da iyawar su kasance da halaye na ibada. Hakika, ya kamata mu yi ƙoƙarin mu koyi irin halayen nan na ƙauna, jinƙai, alheri, nagarta, da kuma haƙuri, da suke nuna Wanda ya yi mu.
2:22-24. Aure tsarin Allah ne. Gamin aure na dindindin ne kuma tsarkake, maigidan ne shugaban iyali.
3:1-5, 16-23. Samun farin ciki ta dangana ga fahimtar ikon mallaka na Jehovah ne a rayuwarmu.
3:18, 19; 5:5; 6:7; 7:23. Maganar Jehovah kullum tana cikawa.
4:3-7. Jehovah ya amince da hadayar Habila saboda shi adali ne mai bangaskiya. (Ibraniyawa 11:4) A wata sassa kuma, ta halinsa Kayinu ya nuna ba shi da bangaskiya. Ayyukansa na mugunta ne, cike da kishi, ƙiyayya, da kuma kisan kai. (1 Yohanna 3:12) Ban da haka ma, ƙila bai ma yi tunanin kirki ba game da hadayar da yake yi, ya dai yi ne kawai. Bai kamata ba ne hadayunmu na yabo ga Jehovah ya zama daga zuciya ɗaya kuma mu kasance da halin kirki da ya dace ba?
6:22. Ko da an yi shekaru da yawa ana ginin jirgin, Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umurce shi. Saboda haka an ceci Nuhu da iyalinsa daga Rigyawar. Jehovah yana mana magana ta wurin rubutacciyar Kalmarsa kuma yana ba mu ja-gora ta wurin ƙungiyarsa. Mu za mu amfana idan muka saurara kuma muka yi biyayya.
7:21-24. Jehovah ba ya halaka adalai da miyagu tare ba.
’YAN ADAM SUN SHIGA SABON ZAMANI
(Farawa 8:1–11:9)
Da duniyar Rigyawar ta shige, ’yan Adam suka shiga sabon zamani. Aka ba wa ’yan Adam izinin su ci nama aka kuma umurce su su hanu daga jini. Jehovah ya ba da izinin a kashe wanda ya yi kisan kai kuma ya yi alkawari ta wurin bakan gizo, cewa ba zai sake halaka duniya da wata Rigyawa kuma ba. ’Ya’yan Nuhu uku ne suka zama tushen ’yan Adam, amma tattaɓa kunnensa Nimrod ya zama ‘ƙaƙarfan mai-farauta gāba da Ubangiji.’ Maimakon su warwatsa, mutane suka shawarta za su gina birni da sunansa Babel da kuma hasumiya don su yi wa kansu suna. Sa’ad da Jehovah ya ɗimauce yarensu ya ɓata musu sha’ani sai ya warwatsa su a duk duniya.
An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi
8:11—Idan Rigyawar ta halaka itatuwa, daga ina ne kurciya ta samo ganyen zaitun? Da akwai yanayi biyu da zai iya yiwuwa. Tun da yake zaitun itace ne mai ƙarfi, zai iya kasance a cikin ruwa na watanni a lokacin Rigyawar. Da ruwayen suka shanye, itacen zaitun da yake cikin ruwa yanzu ya fito kan ƙasa kuma zai iya toho ganye. Ganyen zaitun da kurciyar ta kai wa Nuhu ma ƙila daga wani ɗan ganye da ya toho ne bayan rigyawar.
9:20-25—Me ya sa Nuhu ya la’anci Kan’ana? Mai yiwuwa ne Kan’ana yana da laifin yi wa kakansa Nuhu wulakanci. Ko da yake uban Kan’ana, Ham, ya ga wannan, bai daina wulakancin ba amma kamar ya yaɗa labarin ne. Amma, sauran ’ya’yan Nuhu biyu, Shem da Japheth suka rufe babansu. Saboda wannan aka albarkace su, amma aka la’anci Kan’ana, Ham ya wahala domin kunya da ya jawo a kan ’ya’yansa.
10:25—Ta yaya aka “rarraba” duniya a kwanakin Feleg? Feleg ya rayu daga shekarun 2269 zuwa 2030 K.Z. A ‘kwanakinsa’ ne Jehovah ya ɗimauce yare na maginan Babel kuma ya warwatsa su a dukan fuskar duniya. (Farawa 11:9) Da haka ne aka “warwatsadda su bisa fuskar dukan duniya” a zamanin Feleg.
Darussa da Za Mu Koya:
9:1; 11:9. Babu wata dabara ko kuma wani ƙoƙarin mutane da zai iya kawar da ƙudurin Jehovah.
10:1-32. Labaran tsararraki da ke game da lokacin Rigyawa—sura 5 da 10—ya haɗa dukan zuriyar mutane da na mutum na farko, Adamu ta wurin ’ya’ya uku na Nuhu. Assuriyawa, Kaldiyawa, Ibraniyawa, Suriyawa, da wasu ƙabilan Arabiya sun fito ne daga zuriyar Shem. ’Yan Etofiya, Masarawa, Kan’aniyawa da wasu ƙabilan Afirka da na Arabiya sun fito ne daga Ham. Yawanci ƙabilan Turai sun fito ne daga zuriyar Japheth. Dukan mutane dangin juna ne, dukansu babu wanda ya fi wani a gaban Allah. (Ayukan Manzanni 17:26) Dole wannan gaskiya ya shafi yadda muke ɗaukan wasu kuma muke bi da su.
Kalmar Allah Tana da Ƙarfin Aiki
Sashen farko na littafin Farawa tana ɗauke da labarai cikakku game da tarihin ’yan Adam na farko. A cikin waɗannan shafofi, mun sami fahimin ƙudurin Allah da ya saka mutum cikin duniya. Abin gaba gaɗi ne mu ga cewa babu ƙoƙarce-ƙoƙarcen mutane kamar su Nimrod da zai iya hana cikarsa! Sa’ad da kake karatun Littafi Mai Tsarki naka na kowanne mako don Makarantar Hidima ta Allah, idan ka yi la’akari da sashen nan “An Ba da Amsar Tambayoyi na Nassi” zai taimake ka ka fahimci wasu wurare masu wuya na Nassi. Abin da aka ce a ƙarƙashin “Darussa da Za Mu Koya” yana nuna maka yadda za ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki na kowanne mako. A inda ya dace, suna iya zama wani bukatar yankinka a Taron Hidima. Maganar Jehovah da gaske rayayyiya ce kuma tana aiki ƙwarai cikin rayukanmu.—Ibraniyawa 4:12.