Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 4/1 pp. 12-16
  • “Ka Cika Hidimarka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Cika Hidimarka”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Nuna Ɗaukakar Allah
  • Bari Haskenka Ya Haskaka a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Gida
  • Ka Taimaki Ɗalibai Su Fahimta Misalai
  • Ka Yi Tambayoyi Masu Sa Tunani
  • Dukiya da Za a Daraja
  • Ka Taimaka Wa Mutane Su Yi Biyayya Da Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Mai Da Hankali Ga ‘Iyawarka Ta Koyarwa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Kana Cika Hidimarka ga Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 4/1 pp. 12-16

“Ka Cika Hidimarka”

“Ka cika hidimarka sosai.”—2 TIMOTHAWUS 4:5, Byington.

1, 2. Ko da dukan Kiristoci masu bishara ne, menene Nassi ke bukata daga dattawa?

KAI mai shelar Mulki ne? Idan haka ne, ka gode wa Jehovah Allah don wannan gata mai girma. Kai dattijo ne cikin ikilisiya? Wannan ƙarin gata ce daga Jehovah. Amma kada mu manta cewa makaranta ko kuwa ƙwarewa wajen magana ba zai isar da kowannenmu ba a yin hidima ko kuma kula da ikilisiya. Jehovah ne yake isar da mu don hidimar, kuma domin wasu maza tsakaninmu sun cika mizanai na Nassi ne ya sa suke da gatar hidima na masu kula.—2 Korinthiyawa 3:5, 6; 1 Timothawus 3:1-7.

2 Dukan Kiristoci da suka keɓe kansu masu aikin wa’azin bishara ne, dattawa musamman suna bukatar su kafa misali mai kyau na fita hidima. Allah da Kristi da kuma ’yan’uwa Shaidun Jehovah suna lura da dattawa “da ke aiki cikin kalma da koyarwa.” (1 Timothawus 5:17; Afisawa 5:23; Ibraniyawa 6:10-12) A dukan yanayi, koyarwa ta dattawa dole ta ɗaukaka lafiya ta ruhaniya na masu sauraronsu, domin manzo Bulus ya gaya wa mai kula Timothawus: “Kwanaki za su zo inda ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu; za su kawarda kunnuwansu ga barin gaskiya, su karkata zuwa wajen tatsuniyoyi. Amma kai, sai ka natsu cikin dukan abu, ka daure shan wuya, ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.”—2 Timothawus 4:3-5.

3. Menene ake bukata a yi don kada koyarwar ƙarya ta shafi ruhaniya ta ikilisiyar?

3 Don a tabbata cewa koyarwar ƙarya ba ta shafi ruhaniya ta ikilisiyar ba, dole dattijo ya bi gargaɗin Bulus: “Ka natsu cikin dukan abu, . . . ka cika hidimarka sosai.” (2 Timothawus 4:5, Byington) Hakika, dattijo yana bukatar ya ‘cika hidimarsa.’ Dole ya yi ta sosai. Dattijo da yake hidimarsa sosai zai mai da hankali da ya dace ga dukan hakkinsa, ba zai ƙyale kome ba ko kuma ya yi rabi da rabi. Irin wannan mutum yana da aminci har a ƙananan abubuwa.—Luka 12:48; 16:10.

4. Menene zai taimake mu mu yi hidimar sosai?

4 Cika hidimarmu ba koyaushe yake bukatar ƙarin lokaci ba, amma a yi amfani da lokacin da ake da shi da kyau. Fita hidima a kai a kai zai taimaki dukan Kiristoci su cim ma abubuwa a hidimar. Domin ya ƙara ba da lokaci a hidimar fage, dattijo yana bukatar ya tsara abubuwa da kyau don ya daidaita tsarinsa kuma ya san abin da zai ba wasu su yi da kuma yadda zai yi hakan. (Ibraniyawa 13:17) Dattijo da ake daraja shi zai sa hannu a hidimar, kamar Nehemiya da ya sa hannu a sake gina bangon Urushalima. (Nehemiah 5:16) Kuma ya kamata dukan bayin Jehovah su sa hannu a aikin wa’azin Mulki a kai a kai.—1 Korinthiyawa 9:16-18.

5. Yaya ya kamata mu ji game da hidimar?

5 Muna aiki da ke kawo farin ciki saboda mu masu shelar Mulki ne da aka kafa a sama! Babu shakka, muna son gatarmu ta sa hannu a wa’azin bishara a dukan iyakar duniya kafin ƙarshen ya zo. (Matta 24:14) Ko da mu ajizai ne, kalmomin Bulus zai ƙarfafa mu: “Muna da wannan kaya mai-daraja [na hidima] cikin tukwane na ƙasa, domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.” (2 Korinthiyawa 4:7) Hakika, za mu ba da karɓaɓɓiyar hidima—amma sai da ƙarfin da Allah yake bayarwa da kuma hikima.—1 Korinthiyawa 1:26-31.

Nuna Ɗaukakar Allah

6. Wane bambanci ya kasance tsakanin al’ummar Isra’ila da Isra’ila ta ruhaniya?

6 Da yake maganar shafaffun Kiristoci, Bulus ya ce Allah “ya kuma isarda mu muna masu-hidiman sabon alkawari.” Manzon ya nuna bambancin sabon alkawari da aka yi da Isra’ila ta ruhaniya ta wurin Yesu Kristi da Dokar tsohon alkawari da aka yi da al’ummar Isra’ila ta wurin Musa. Bulus ya daɗa cewa sa’ad da Musa ya sauƙo daga Dutsen Sinai da allon duwatsu da ya ƙunshi Dokoki Goma, fuskarsa tana walƙiya da ta sa Isra’ilawa ba su iya kallonsa ba. Amma da shigewar lokaci, abu mai tsanani ya faru domin “hankalinsu ya taurare” kuma lulluɓi ya rufe zuciyarsu. Amma, sa’ad da suka juya ga Jehovah da dukan zuciyarsu, sai aka kawar da lulluɓin. Da yake magana game da hidimar da aka ce waɗanda suke cikin sabon alkawari su yi, Bulus ya ce: “Dukanmu, da fuska ba lulluɓi muna juya darajar Ubangiji kamar madubi.” (2 Korinthiyawa 3:6-8, 14-18; Fitowa 34:29-35) “Waɗansu tumaki” na Yesu a yau suna da gatar nuna ɗaukakar Jehovah.—Yohanna 10:16.

7. Ta yaya mutane za su nuna ɗaukakar Allah?

7 Ta yaya mutane masu zunubi za su nuna ɗaukakar Allah, yayin da ba mutum da zai ga fuskarsa ya kuma rayu? (Fitowa 33:20) Dole mu fahimta cewa, ban da cewa Jehovah mutum ne mai ɗaukaka, yana da ƙuduri mai girma na kunita ikon mallakarsa ta wurin Mulkinsa. Gaskiya game da Mulkin yana cikin “ayyuka masu-girma na Allah” da waɗanda aka zuba musu ruhu mai tsarki a Fentakos na 33 A.Z., suka soma shelarsa. (Ayukan Manzanni 2:11) Da ja-gorar ruhun, za su iya cika hidimar da aka danƙa musu.—Ayukan Manzanni 1:8.

8. Game da hidimar, menene Bulus ya ƙudura niyyar yi?

8 Bulus ya ƙudura niyya ba kome da zai hana shi daga cika hidimarsa sosai. Ya rubuta: “Da shi ke fa muna da wannan hidima, kamar yadda muka sami jinƙai, ba mu yi yaushi ba: amma mun kakkaɓe ɓoyayyun al’amura na kunya, ba mu yi tafiya cikin kirsa ba, ba mu gudana maganar Allah da algus kuma; amma bisa ga bayyanawar gaskiya muna koɗa kanmu ga lamirin kowane mutum a gaban Allah.” (2 Korinthiyawa 4:1, 2) Ta abin da Bulus ya kira “wannan hidimar,” an bayyana gaskiyar kuma an yaɗa haske na ruhaniya a dukan duniya.

9, 10. Ta yaya zai yiwu mu nuna ɗaukakar Jehovah?

9 Game da Tushen haske na zahiri da na ruhaniya, Bulus ya rubuta: “Da shi ke Allah ne, wanda ya ce, Haske daga cikin duhu za ya haskaka, shi ne ya haskaka cikin zukatanmu, domin a bada haske na sanin darajar Allah cikin fuskar Yesu Kristi.” (2 Korinthiyawa 4:6; Farawa 1:2-5) Tun da yake an danƙa mana gata da babu na biyunta na zama masu hidima na Allah, bari mu ci gaba da tsabtace kanmu domin mu walƙa ɗaukakar Jehovah kamar madubi.

10 Mutane da suke cikin duhu ba za su iya ganin ɗaukakar Jehovah ko kuma walƙiyarta daga Yesu Kristi, Musa Mafi Girma ba. Da yake mu bayin Jehovah ne, muna samun haske na ɗaukaka daga Nassosi kuma muna gaya wa wasu. Idan waɗanda yanzu suna cikin duhu na ruhaniya za su tsira wa halaka, suna bukatar haske daga Allah. Da farin ciki mai yawa da kuma himma, muna biyayya da umurnin Allah mu bar haske shi haskaka cikin duhu zuwa ga ɗaukakar Jehovah.

Bari Haskenka Ya Haskaka a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Gida

11. Menene Yesu ya faɗa game da barin haskenmu ya haskaka, kuma wace hanya ɗaya ce za mu yi wannan a hidimarmu?

11 Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Ku ne hasken duniya. Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi ɓoyuwa. Kuma ba a kan kunna fitila, a sa ta ƙarƙashin akushi ba, amma bisa [teburi]; sai ta haskaka ma dukan waɗanda ke cikin gida. Hakanan ku kuma ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.” (Matta 5:14-16) Halinmu mai kyau zai sa wasu su ɗaukaka Allah. (1 Bitrus 2:12) Kuma fannoni dabam dabam na aikinmu na bishara yana ba mu zarafi da yawa na sa haskenmu ya haskaka. Ɗaya cikin muradinmu na musamman shi ne mu walƙa haske na ruhaniya daga Kalmar Allah ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da kyau. Wannan hanya ce mai muhimmanci na cika hidimarmu sosai. Waɗanne shawarwari zai taimake mu mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da ke motsa zukatan masu neman gaskiya?

12. Ta yaya addu’a take da nasaba da aikin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida?

12 Yin addu’a ga Jehovah game da wannan ya nuna muna son mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau. Ya kuma nuna cewa mun san muhimmancin taimakon wasu su samu sanin Allah. (Ezekiel 33:7-9) Babu shakka Jehovah zai amsa addu’o’inmu kuma ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a hidimar. (1 Yohanna 5:14, 15) Amma ba ma addu’a kawai don mu samu wanda za mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba. Bayan mun soma nazarin, addu’a da bimbini game da ainihin bukatun ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu gudanar da kowane nazari da kyau.—Romawa 12:12.

13. Menene zai iya taimakonmu mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da kyau?

13 Don mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da kyau, dole mu shirya kowane nazari da kyau. Idan muna ji ba mu iya sosai ba, lura da yadda mai kula da Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya yake gudanar da darasi na kowane mako zai iya taimakonmu. Wani lokaci, muna iya bin masu shelar Mulki da suka samu sakamako mai kyau a gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida. Hakika, ya dace mu yi la’akari da halin Yesu Kristi da yadda yake koyarwa.

14. Ta yaya za mu motsa zuciyar ɗalibi na Littafi Mai Tsarki?

14 Yesu yana farin cikin yin nufin Ubansa na samaniya da kuma gaya wa mutane game da Allah. (Zabura 40:8) Shi mai tawali’u ne kuma ya yi nasara a motsa zukatan waɗanda suka saurare shi. (Matta 11:28-30) Saboda haka, bari mu yi ƙoƙari mu motsa zukatan ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki. Domin mu yi haka, muna bukatar mu shirya kowane nazari da tunani game da ainihin yanayin ɗalibin. Alal misali, idan yana bin wata al’ada da ba ta da tushe daga Littafi Mai Tsarki, za mu huɗubantar da shi cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce shi ne gaskiya. Sa’annan za mu karanta nassosi da yawa kuma mu bayyana su.

Ka Taimaki Ɗalibai Su Fahimta Misalai

15, 16. (a) Ta yaya za mu iya taimakon wani ɗalibi da bai fahimci wani misali da aka yi amfani da shi cikin Littafi Mai Tsarki ba? (b) Menene za mu iya yi idan littattafanmu suka yi amfani da misali da yake da wuya wani ɗalibi na Littafi Mai Tsarki ya fahimta?

15 Ɗalibin Littafi Mai Tsarki ƙila bai san wani misali da aka yi amfani da shi cikin Nassosi ba. Alal misali, mai yiwuwa ba zai fahimci abin da Yesu yake nufi sa’ad da ya ce an saka fitila a kan maɗorinta ba. (Markus 4:21, 22) Yesu yana maganar fitila na dā mai ci bal-bal da lagwani. Ana saka irin wannan fitila a kan maɗori na musamman, ta haka kuma ya haskaka wani gefen gidan. Ana bukatar bincike a kan jigogi “Fitila” da “Maɗori” a cikin littattafanmu na Kirista don a bayyana misalin Yesu sosai. Amma yana da ban albarka a yi shiri don a bayyana abin da ɗalibin zai fahimta kuma ya yi farin ciki a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki!

16 Littafin da ake amfani da shi a nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya amfani da misali da yake da wuya wani ɗalibi ya fahimta. Ka ɗauki lokaci don ka bayyana shi, ko kuma ka yi amfani da wani misali da ya bayyana batun. Wataƙila wani littafi yana nanata cewa abokin aure da ya dace da kuma haɗin kai cikin aure suna da muhimmanci. Don a ba da misalin wannan, za a iya ba da misalin mutum da aka saka wani doguwar igiya a gabansa yana riƙe da wani abu a hannunsa ya yi ta adungure, idan ya saki hannunsa, zai dogara da wani ɗan wasan ya kama shi. Kana iya sake ba da wani misali na yadda ma’aikata suke aiki da haɗin kai ta sauke kwalaye na kayan kasuwa daga kwalekwale, ɗayan yana jefo wa ɗayan kwalayen, shi kuma yana cafe su yana ajiyewa bi da bi.

17. Menene za mu koya daga Yesu game da misalai?

17 Yin amfani da wani misali dabam na bukatar shiri tun da wuri. Amma, ta haka ne za mu nuna muna son ɗalibi na Littafi Mai Tsarki. Yesu ya yi amfani da misalai masu sauƙi don ya bayyana batutuwa masu wuyan ganewa. Huɗubarsa bisa Dutse ya ba da misalan wannan, kuma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa koyarwarsa ya motsa masu sauraronsa da kyau. (Matta 5:1–7:29) Yesu ya bayyana abubuwa da haƙuri domin yana son mutane sosai.—Matta 16:5-12.

18. Menene aka ce a yi game da nassosi da aka rubuta cikin littattafanmu?

18 Son mutane, zai motsa mu mu riƙa ‘muhawwara daga Nassosi.’ (Ayukan Manzanni 17:2, 3) Wannan yana bukatar nazari sosai tare da addu’a da kuma yin amfani da kyau da littattafai da “wakili mai-aminci,” yake tanadinsa. (Luka 12:42-44) Alal misali, littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada ya yi amfani da nassosi da yawa.a Domin babu isashen wuri, an rubuta wasu nassosi kawai. A lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki, yana da muhimmanci a karanta kuma bayyana aƙalla wasu cikin waɗannan nassosi da aka rubuta. Ballantana ma, koyarwarmu daga Kalmar Allah ce, kuma tana da iko sosai. (Ibraniyawa 4:12) Ka yi nuni ga Littafi Mai Tsarki a kowane nazari, kana amfani a kai a kai da nassosi da ke cikin sakin layin. Ka taimaki ɗalibin ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wani darasi ko kuma hali. Ka yi ƙoƙari ka nuna masa yadda zai amfana ta yi wa Allah biyayya.—Ishaya 48:17, 18.

Ka Yi Tambayoyi Masu Sa Tunani

19, 20. (a) Me ya sa za ka yi tambayoyi na bincike sa’ad da kake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida? (b) Menene za a iya yi idan wani darasin yana bukatar ƙarin bincike?

19 Yesu ya taimaki mutane su yi tunani ta amfani da tambayoyi da kyau. (Matta 17:24-27) Idan mun yi tambayoyin bincike da ba su sa ɗalibin Littafi Mai Tsarki kunya ba, amsoshinsa zai nuna ra’ayinsa game da wani batu. Muna iya gani cewa har ila yana da ra’ayi da ba na nassi ba. Alal misali, ƙila yana imani da Allah-Uku-Cikin Ɗaya. A cikin babi na 3, littafin nan Sanin ya nuna cewa koyarwar ‘Allah-Uku-Cikin Ɗaya’ ba ya cikin Littafi Mai Tsarki. Littafin ya yi ƙaulin kuma nuna nassosi da suka nuna cewa Jehovah dabam yake da Yesu kuma cewa ruhu mai tsarki ikon aiki na Allah ne, ba mutum ba. Karanta da kuma tattauna waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki ƙila zai isa. Idan ana bukatar ƙarin bayani fa? Wataƙila bayan nazari na gaba, za a ɗauki lokaci a tattauna wannan batun yadda aka bayyana a wani littafin Shaidun Jehovah, mujallar nan Ya Kamata Ka Gaskata da Dunƙulin-Alloli-Uku? Bayan haka, za mu sake soma nazarin ta yin amfani da littafin nan Sanin.

20 A ce amsar da aka bayar ga tambayar bincike yana da ban mamaki ko kuma sa sanyin gwiwa. Idan ya ƙunshi batu mai tsanani kamar shan taba ko kuma wasu, za mu iya ce a ci gaba da nazarin kuma a tattauna batun wani lokaci. Sanin cewa ɗalibin har ila yana shan taba zai taimake mu mu nemi littafin da zai taimake shi ya ci gaba a ruhaniya. Yayin da muke ƙoƙari mu motsa zuciyar ɗalibin, za mu iya yi wa Jehovah addu’a ya taimake shi ya ƙara ruhaniyarsa.

21. Menene zai faru idan mun daidaita hanyoyin koyarwarmu ga ainihin bukatun ɗalibin Littafi Mai Tsarki?

21 Da shiri mai kyau da kuma taimakon Jehovah, babu shakka za mu iya daidaita hanyoyin koyarwarmu domin ya dace da ainihin bukatun ɗalibin Littafi Mai Tsarki. Da shigewar lokaci, za mu iya taimakonsa ya koyi ƙaunar Allah sosai. Za mu iya samun nasara idan muka sa ya koyi daraja da kuma godiya ga ƙungiyar Jehovah. Kuma abin farin ciki ne sa’ad da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka san cewa ‘hakika Allah yana wurinmu’! (1 Korinthiyawa 14:24, 25) Bari mu gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau kuma mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu taimake mutane su zama almajiran Yesu.

Dukiya da Za a Daraja

22, 23. Menene ake bukata idan za mu cika hidimarmu sosai?

22 Don mu cika hidimarmu sosai, dole mu dogara ga ƙarfi da Allah yake bayarwa. Da yake maganar hidima, Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci shafaffu: “Muna da wannan kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa, domin mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.”—2 Korinthiyawa 4:7.

23 Ko shafaffu ne ko kuma “waɗansu tumaki,” muna kama da tukwane na ƙasa. (Yohanna 10:16) Amma, Jehovah zai ba mu ƙarfi da muke bukata domin mu cika ayyukanmu duk da matsi da muke da shi. (Yohanna 16:13; Filibbiyawa 4:13) Saboda haka, bari mu dogara ga Jehovah ƙwarai, mu daraja gatar hidima, kuma mu cika hidimarmu sosai.

[Hasiya]

a Shaidun Jehovah ne suka buga.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene dattawa za su iya yi don su cika hidimarsu sosai?

• Ta yaya za mu kyautata nazarinmu na Littafi Mai Tsarki na gida?

• Menene za ka yi idan ɗalibin Littafi Mai Tsarki bai fahimci wani misali ba ko kuma yana bukatar ƙarin bayani a kan wani batu?

[Hoto a shafi na 13]

Dattawa Kirista suna koyarwa cikin ikilisiya kuma suna taimakawa a koyar da ’yan’uwa masu bi a hidimar

[Hoto a shafi na 15]

Gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida hanya ɗaya ce na sa haskenmu ya haskaka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba