Kula Da Tsofaffi Hakki Ne Na Kirista
“Har tsufarku kuma, ni ne shi, har zuwa furfuranku kuma ni zan ɗauke ku.”—ISHAYA 46:4.
1, 2. Ta yaya ne kulawar Ubanmu na samaniya ya bambanta da na iyaye?
IYAYE da suka keɓe kansu suna renon ’ya’yansu tun suna jarirai, sa’ad da suke yarantaka, da kuma sa’ad da suka balaga. Har ma sa’ad da matasa suka yi girma kuma suka sami iyalan kansu, iyayensu suna ci gaba da kula da su da kyau kuma suna taimaka musu.
2 Ko da yake akwai iyakar abin da mutane za su iya yi wa yaransu, Ubanmu na samaniya yana kula da bayinsa amintattu da kyau kuma yana taimaka musu. Sa’ad da yake yi wa zaɓaɓɓun mutanensa na dā magana, Jehovah ya ce: “Har tsufarku kuma, ni ne shi, har zuwa furfuranku kuma ni zan ɗauke ku.” (Ishaya 46:4) Wannan kalmomi ne na tabbatarwa ga Kiristoci tsofaffi! Jehovah ba ya watsi da waɗanda suka kasance da aminci gare shi. Maimakon haka, ya yi alkawarin zai kiyaye su, zai taimake su, kuma zai yi musu ja-gora a dukan rayuwarsu, har sa’ad da suka tsufa ma.—Zabura 48:14.
3. Menene za mu yi la’akari da shi a cikin wannan talifi?
3 Ta yaya za mu yi koyi da ƙauna mai kyau da Jehovah yake nuna wa tsofaffi? (Afisawa 5:1, 2) Bari mu yi la’akari da hanyoyin da yara, masu kula a cikin ikilisiya, da kuma kowane Kirista za su iya kula da bukatun tsofaffi da suke cikin ’yan’uwancinmu a dukan duniya.
Hakkinmu Mu Yara
4. Wane hakki ne yaran Kiristoci suke da shi ga iyayensu?
4 “Ka girmama ubanka da uwarka.” (Afisawa 6:2; Fitowa 20:12) Da wannan nassi mai sauƙi amma kuma mai ma’ana daga Nassosin Ibrananci, manzo Bulus ya tunasar da yara hakkin da suke da shi ga iyayensu. Amma ta yaya ne waɗannan kalmomi suka shafi kula da tsofaffi? Wani misali mai daɗaɗa rai kafin zamanin Kiristanci zai taimaka mana mu amsa wannan tambayar.
5. (a) Me ya nuna cewa Yusufu bai manta da hakkinsa na iyali ba? (b) Menene ake nufi da mu daraja iyayenmu, kuma wane misali mai kyau ne Yusufu ya kafa mana game da wannan?
5 Fiye da shekara 20, Yusufu bai haɗu da ubansa tsoho ba, Yakubu uban iyali. Amma, Yusufu bai manta da ƙaunar da yake yi wa Yakubu ba. Hakika, sa’ad da Yusufu ya faɗi gaskiya wa ’yan’uwansa game da kansa, ya tambaye su: “Ubana yana da rai har yanzu?” (Farawa 43:7, 27; 45:3) A wannan lokacin, ƙasar Kan’ana tana cikin yunwa mai tsanani. Saboda haka, Yusufu ya aika wa ubansa, yana cewa: “Ka zo wurina, kada ka tsaya: za ka zauna cikin ƙasar Goshen, kana kusa da ni ke nan . . . Daga nan kuma za ni kiwonka.” (Farawa 45:9-11; 47:12) Hakika, girmama iyaye tsofaffi ya ƙunshi kāre su da kuma tanadar musu abubuwan biyan bukata sa’ad da ba sa iya kula da kansu. (1 Samuila 22:1-4; Yohanna 19:25-17) Da farin ciki, Yusufu ya yarda da wannan hakkin.
6. Ta yaya ne Yusufu ya nuna ƙauna ta gaskiya ga ubansa, kuma ta yaya ne za mu yi kwaikwayon misalinsa?
6 Albarkacin Jehovah, Yusufu ya zama ɗaya cikin masu kuɗi kuma mafi ƙarfi a cikin ƙasar Masar. (Farawa 41:40) Amma bai ɗauki kansa mafi muhimmanci ba ko kuwa ya taƙure ainun da ba zai iya daraja ubansa tsoho mai shekara 130 ba. Sa’ad da ya ji cewa Yakubu (ko kuwa Isra’ila) ya kusa, “Yusufu kuma ya shirya karusassa, ya hau domin shi tarbi ubansa Isra’ila, a Goshen; ya fa isa a gabansa, ya faɗa ma wuyansa, ya yi kuka a wuyansa da daɗewa.” (Farawa 46:28, 29) Wannan marabci ya wuce nuna ƙauna kawai. Yusufu yana ƙaunar ubansa tsoho sosai kuma bai ji kunyar nuna wannan ƙaunar ba. Idan muna da iyaye tsofaffi, muna nuna ƙaunarmu sosai a gare su kuwa?
7. Me ya sa Yakubu ya ba da umurni a binne shi a Kan’ana?
7 Ibadar Yakubu wajen Jehovah ta kasance da ƙarfi har ƙarshen rayuwarsa. (Ibraniyawa 11:21) Saboda imaninsa ga alkawarin Allah, Yakubu ya umurta a binne gawarsa a Kan’ana. Yusufu ya daraja umurnin ubansa, ko da hakan zai bukaci kuɗi mai yawa da kuma ƙoƙari.—Farawa 47:29-31; 50:7-14.
8. (a) Menene babban dalilinmu na kula da iyaye tsofaffi? (b) Menene wani bawa mai hidima na cikakken lokaci ya yi domin ya kula da iyayensa tsofaffi? (Duba akwati a shafi na 13.)
8 Menene ya motsa Yusufu ya kula da ubansa? Ko da yake ƙauna da hakkin da yake da shi ga wanda ya ba shi rai kuma wanda ya yi renonsa su ne abubuwa da suka sa ya yi hakan, babu shakka Yusufu yana son ya faranta wa Jehovah rai. Mu ma ya kamata mu yi hakan. Bulus ya ce: “Idan kowacce gwauruwa tana da ‘ya’ya ko jikoki, bari su koya su fara gwada ibada wajen iyalin gida nasu, su sāka ma iyayensu: gama wannan abin karɓa ne a wurin Allah.” (1 Timothawus 5:4) Hakika, ƙauna ga Jehovah da kuma tsoronsa zai sa mu kula da iyayenmu tsofaffi, duk da matsalar da yin hakan ya ƙunsa.a
Yadda Dattawa Suke Nuna Kulawarsu
9. Wanene Jehovah ya naɗa ya kula da garkensa, har da Kiristoci tsofaffi?
9 Kusan ƙarshen doguwar rayuwarsa, Yakubu ya yi nuni ga Jehovah cewa “Allah wanda ya kiyaye ni dukan kwanakin raina har wa yau.” (Farawa 48:15) A yau, Jehovah yana kiyaye bayinsa a nan duniya ta wurin Kiristoci masu kula, ko kuma dattawa, ƙarƙashin ja-gorar Ɗansa, Yesu Kristi, “babban Makiyayi.” (1 Bitrus 5:2-4) Ta yaya masu kula za su iya kwaikwayon Jehovah sa’ad da suke kula da tsofaffi waɗanda suke cikin garke?
10. Menene aka yi domin a yi wa Kiristoci tsofaffi agaji? (Duba akwati a shafi 15.)
10 Ba da daɗewa ba bayan an kafa ikilisiyar Kirista, manzanni sun naɗa “mutum bakwai . . . cike da Ruhu Mai-tsarki da hikima kuma,” domin su sanya su a “bisa wannan sha’ani” na rarraba abinci tsakanin Kiristoci gwauraye mabukata. (Ayukan Manzanni 6:1-6) Daga baya, Bulus ya umarci Timothawus mai kula ya sa mata gwauraye masu hali mai kyau a cikin waɗanda za su karɓi kayan agaji. (1 Timothawus 5:3, 9, 10) Haka nan ma, masu kula da ikilisiya a yau suna ba da taimako mai kyau ga Kiristoci tsofaffi sa’ad da ya dace a yi haka. Amma, kula da tsofaffi ya ƙunshi abubuwa masu yawa.
11. Menene Yesu ya ce game da gwauruwa mabukaciya da ta ba da gudummawa ɗan ƙarami?
11 Kusan ƙarshen hidimarsa a duniya, Yesu ya zauna a haikali kuma ya “duba taron suna zuba kuɗi a cikin ma’ajin kuɗi.” Sai wata ta kwashi hankalinsa. Labarin ya ce: “Wata gwauruwa matalauciya ta zo, ta zuba anini biyu.” Yesu ya kira almajiransa ya ce masu: “Gaskiya ni ke faɗa muku, abin da wannan gwauruwa matalauciya ta zuba ya fi nasu duka da suka zuba cikin ma’aji: gama waɗannan duka daga cikin falalassu suka zuba a ciki; amma ita daga tsiyatta ta zuba abin da ta ke da shi duka, iyakar abin zaman garinta ke nan.” (Markus 12:41-44) A batun kuɗi, gudummawar da gwauruwa ta ba da kaɗan ne, amma Yesu ya san yadda Ubansa na samaniya yake daraja ibada ta zuciya ɗaya. Ko yaya shekarun gwauruwar matalauciyar suke, Yesu bai manta da abin da ta yi ba.
12. Ta yaya ne dattawa za su iya nuna godiya ga abin da Kiristoci tsofaffi suke yi?
12 Kamar Yesu, masu kula Kiristoci ba sa manta da abubuwan da tsofaffi suka yi domin yaɗa bauta ta gaskiya. Dattawa suna da dalilin yaba wa tsofaffi domin sa hannunsu a hidima, domin furci da suke yi a taron Kirista, domin tasirin mai kyau da suke da shi a cikin ikilisiya, da kuma jimrewarsu. Sahihan kalamai masu ƙarfafawa suna iya taimaka wa tsofaffi su ‘sami taƙama’ a tsarkakkar hidima, da haka, wannan zai kau musu da sanyin gwiwar gwada abin da wasu Kiristoci suke yi da kuma abubuwan da suka cim ma a dā.—Galatiyawa 6:4.
13. A waɗanne hanyoyi ne dattawa za su iya amfana daga labari da kuma iyawar tsofaffi?
13 Dattawa za su iya nuna godiya ga abin da Kiristoci tsofaffi suke yi ta hanyar saurarar labarinsu da kuma iyawarsu. Ana iya yin amfani da tsofaffi masu misalin kirki a wasu lokatai a wajen nuni ko kuwa ganawa. “Mutane suna mai da hankali sosai su saurara sa’ad da nake ganawa da ɗan’uwa tsoho ko kuwa ’yar’uwa da suka yi renon yaransu a cikin gaskiya,” in ji wani dattijo. Dattawa a wata ikilisiya sun faɗi cewa wata ’yar’uwa majagaba mai shekaru 71 ta yi nasara a taimaka wa masu shelar Mulki su zama masu zuwa hidimar fage a kai a kai. Kuma ta ƙarfafa su su yi “muhimman” abubuwa, karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nassosin yini, su kuma yi bimbini a kan abin da suka karanta.
14. Ta yaya ne wani rukunin dattawa suka nuna godiya ga wani dattijo mai kula?
14 Dattawa suna daraja abin da ’yan’uwa tsofaffi da su masu kula ne suke yi. José, wanda yake a cikin shekarunsa na 70 kuma ya yi hidima na dattijo na shekaru da yawa, an yi masa fiɗa mai tsanani. Domin yana ganin ba zai warke da wuri ba, sai ya yi tunanin tuɓe gatarsa ta shugaban ikilisiya. “Abin da sauran dattawan suka yi ya ba ni mamaki,” in ji José. “Maimakon su yarda da shawarata, sun tambaye ni irin taimakon da nake bukata domin na ci gaba da kula da hakki na.” Da taimakon wani dattijo matashi, José ya ci gaba da yin hidimar shugaban ikilisiya da farin ciki, kuma wannan ya zama albarka ga ikilisiyar. Wani dattijo ya ce: “ ’Yan’uwa suna daraja aikin José na dattijo. Suna ƙaunarsa suna kuma daraja shi saboda hikima da kuma misalinsa na bangaskiya. Ya kyautata ikilisiyarmu.”
Kula da Juna
15. Me ya sa dukan Kiristoci za su damu da lafiyar tsofaffi da ke tsakaninsu?
15 Ba yara da suke da iyaye tsofaffi da bayin da aka naɗa kawai ne za su damu da tsofaffi ba. Sa’ad da yake gwada ikilisiyar Kirista da jikin mutum, Bulus ya rubuta: “Allah ya harhaɗa jiki, yana ƙara mafificiyar daraja ga gaɓan da ya ke tauyeye; domin kada tsaguwa ta kasance a jiki, amma dukan gaɓaɓuwa su yi ma juna tattali ɗaya.” (1 Korinthiyawa 12:24, 25) Domin ikilisiyar Kirista ta ci gaba da haɗin kai, dole ne kowa ya damu da lafiyar kowane mai bi, har da tsofaffi.—Galatiyawa 6:2.
16. Ta yaya ne za mu iya nuna muna ƙaunar tsofaffi sa’ad da muka halarci taron Kirista?
16 Taron Kirista yana ba mu dama mai kyau da za mu nuna ƙaunarmu ga tsofaffi. (Filibiyawa 2:4; Ibraniyawa 10:24, 25) Muna ɗaukan lokaci mu tattauna da tsofaffi a wannan lokacin? Ko da yake yana da kyau mu tambaye su game da lafiyar jikinsu, muna iya ‘ba su wani baiko mai ruhaniya,’ ƙila ma ta faɗin labarai masu ƙarfafawa ko kuwa na Nassi? Tun da wasunsu ba su da ƙarfin yin tafiya sosai, zai fi kyau mu je wurinsu maimakon mu ce su zo wurinmu. Idan ba sa ji sosai, muna iya yin magana a hankali kuma mu faɗi yadda za su gane sosai. Idan za a “sami ƙarfafawa,” dole ne mu saurari abin da tsofaffi suke faɗi sosai.—Romawa 1:11, 12.
17. Ta yaya ne za mu iya nuna ƙaunarmu ga Kiristoci tsofaffi da suke kulle a gida?
17 Idan wani tsoho ba ya iya halarta taron Kirista fa? Yaƙub 1:27 ta nuna cewa hakkinmu ne mu “ziyarci marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu.” Wata ma’anar aikatau na Helenanci da aka fassara ‘kula da’ yana nufin “a ziyarci.” (Ayukan Manzani 15:36) Hakika tsofaffi suna jin daɗin ziyararmu! Sa’ad da yake a kurkuku a Roma kusan 65 A.Z., Bulus “tsoho” ya iske kansa ya kaɗaita. Yana marmarin ya ga abokin aikinsa Timothawus kuma ya rubuta: “Ka yi hanzari ka zo wurina ba da jinkiri ba.” (Filimon 9; 2 Timothawus 1:3, 4; 4:9) Ko da yake su ba fursunoni ba ne a zahiri, wasu tsofaffi suna kulle a gida saboda rashin lafiya. Watau, suna iya cewa, ‘Don Allah ka yi ƙoƙari ka ziyarce ni ba da jinkiri ba.’ Muna saurarar irin wannan roƙon?
18. Wane fa’idodi muke samu sa’ad da muka ziyarci tsofaffi?
18 Ya kamata mu ga amfanin ziyarar ’yan’uwa tsofaffi na ruhaniya maza ko mata. Sa’ad da wani Kirista mai suna Onisifurus yake a Roma, ya nemi Bulus, ya gan shi, bayan haka kuma, ‘ya kan wartsakadda da shi.’ (2 Timothawus 1:16, 17) “Ina jin daɗin ɓatar da lokaci tare da matasa,” in ji wata ‘yar’uwa tsohuwa. “Abin da na fi so shi ne suna bi da ni kamar ɗaya ne cikin iyalinsu. Wannan yana ƙarfafa ni sosai.” Wani Kirista tsoho ya ce: “Ina jin daɗi sosai sa’ad da wani ya aiko mini da katin gaisuwa, aka yi mini waya na ‘yan mintoci, ko kuma aka ziyarce ni na ɗan lokaci. Yana kama da sheƙar iska mai daɗi.”
Jehovah Yana Yi wa Waɗanda Suke Kula Albarka
19. Wace albarka ake samu wajen kula da tsofaffi?
19 Kula da tsofaffi yana kawo albarka mai yawa. Yin tarayya da tsofaffi kuma yin amfani da saninsu da labarinsu gata ce mai girma. Masu kula da majiyata sun shaida farin ciki mai yawa da ake samu wajen bayarwa, da kwanciyar rai da suke samu daga abin da suka cim ma domin sun cika hakkinsu na Nassi. (Ayukan Manzanni 20:35) Bugu da ƙari, waɗanda suke kula da tsofaffi kada su ji tsoron cewa su ma za a yi watsi da su sa’ad da suka tsufa. Kalmar Allah ta ba mu tabbaci: “Rai mai-alheri za ya yi ƙiba: Kuma mai-ban ruwa shi kansa za a yi masa ban ruwa.”—Misalai 11:25.
20, 21. Ta yaya Jehovah yake ɗaukan waɗanda suke kula da tsofaffi, kuma menene zai zama ƙudurinmu?
20 Jehovah yana yi wa yara masu tsoron Allah, masu kula, da kuma wasu Kiristoci waɗanda da son rai suke kula da bukatun ’yan’uwa tsofaffi masu bi albarka. Irin wannan halin ya yi daidai da wannan misalai: “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” (Misalai 19:17) Idan ƙauna ta sa muka nuna alheri ma taliki da fakiri, Allah yana ɗaukan irin wannan bayarwa kamar rance ne da zai biya mu da albarka. Yana kuma biyanmu domin kula da ’yan’uwanmu tsofaffi masu-bi da kyau, yawancinsu da suke ‘fakirai a duniya amma mawadata cikin bangaskiya.’—Yaƙub 2:5.
21 Sakaiyar Allah tana da karimanci! Ta haɗa da rai na har abada. Yawancin bayin Jehovah, za su sami rai madawwami a cikin aljanna a duniya, inda za a kawar da sakamakon zunubin da muka gada kuma tsofaffi masu aminci za su ji daɗin maido da ƙarfin ƙuruciyarsu. (Ru’ya ta Yohanna 21:3-5) Sa’ad da muke jiran wannan lokaci na albarka, bari mu ci gaba da cika hakkinmu na Kirista na kula da tsofaffi.
[Hasiya]
a Domin shawarwari masu kyau don kula da iyaye tsofaffi, duba Awake! na 8 ga Fabrairu, 1994, shafi na 3-10.
Menene Amsoshinka?
• Ta yaya yara za su iya daraja iyayensu tsofaffi?
• Ta yaya dattawa suke nuna godiya ga tsofaffi cikin garken?
• Menene kowane Kirista zai yi ya nuna ƙauna wa tsofaffi?
• Waɗanne albarka za a samu wajen kula da Kiristoci tsofaffi?
[Akwati a shafi na 13]
Sa’ad da Iyayensa ke Bukatar Taimako
Philip yana yin hidima na waɗanda suka ba da kansu wajen aikin gine-gine a Liberiya a shekara ta 1999 sa’ad da ya sami labarin cewa ubansa yana ciwo sosai. Sanin cewa mamarsa ba za ta iya jurewa ba tare da taimako ba, sai ya yanke shawarar ya koma gida domin ya kula da rashin lafiyar ubansa.
“Komawa gida ba abu ba ne mai sauƙi,” in ji Philip, amma na san cewa hakki na na farko yana ga iyayena.” Bayan shekaru uku, ya mai da iyayensa gida mai kyau, da taimakon ’yan’uwa Kiristoci na yankinsu, ya gyara gidan domin biyan bukatun ubansa.
Yanzu mamar Philip tana shirye sosai domin ta jimre rashin lafiya mai tsanani na mijinta. Ba da daɗewa ba, Philip ya iya karɓan takardar gayyata zuwa aikin ba da kai a ofishin reshe na Shaidun Jehovah a Makidoniya.
[Akwati a shafi na 15]
Ba Su Yi Watsi da Bukatunta Ba
Sa’ad da Ada, wata Kirista mai shekaru 85 a Australia, ba ta iya fita daga gidanta saboda rashin lafiya, dattawa a ikilisiya sun yi shirin taimaka mata. Sun tsara rukunin ’yan’uwa da za su iya taimaka mata. Waɗannan ’yan’uwa maza da mata sun yi farin cikin kula da irin waɗannan ayyuka, shara, wanke-wanke, dahuwa, da kuma wasu ayyuka.
An soma ba da wannan taimako kusan shekaru goma da suka wuce. Har yanzu, fiye da ’yan’uwana Shaidun Jehovah guda 30 sun taimaka wajen kula da Ada. Sun ci gaba da ziyararta, suna karanta mata littattafai na Littafi Mai Tsarki, suna kuma gaya mata yadda ‘yan ikilisiyar ke ci gaba a ruhaniya, kuma suna addu’a da ita a kowane lokaci.
Wani dattijo Kirista ya ce: “Waɗanda suke kula da Ada sun ɗauki taimaka mata gata ne. Hidimarta da aminci na shekaru mai yawa ya motsa mutane da yawa, kuma sun ga cewa bai dace ba su yi watsi da bukatunta.”
[Hoto a shafi na 12]
Muna nuna muna ƙaunar iyaye tsofaffi sosai ta furcinmu kuwa?
[Hotuna a shafi na 14]
Duka a cikin ikilisiya suna iya nuna ƙaunarsu wa ’yan’uwa masu bi tsofaffi