Jehobah Yana Kula Da Bayinsa Tsofaffi
“Gama Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa” ba.—IBRAN. 6:10.
1, 2. (a) Idan ka ga mutum mai furfura yana tuna maka da menene? (b) Yaya Jehobah yake ɗaukan tsofaffi Kirista?
IDAN ka ga tsofaffi masu furfura a cikin ikilisiya, hakan na tuna maka da wani labari a cikin littafin Daniel na Littafi Mai Tsarki kuwa? A cikin wani wahayi da ya nuna wa Daniel, Jehobah Allah ya kwatanta kansa da mai furfura. Daniel ya rubuta: “Ina nan ina dubawa, har na ga an kafa kursiyai, wani kuma wanda shi ke mai-zamanin dā yana zaune: tufafinsa farifat kamar snow su ke: gashin kansa kuma kamar tsatsabtar ulu.”—Dan. 7:9.
2 Ainihi ulu fari ne. Da haka, furfura da laƙabin nan “mai-zamanin dā” suna bayyana girman Allah da hikimarsa, da muke bukata mu daraja su. To, ta yaya ne mai zamanin dā, Jehobah yake ɗauka tsofaffi maza da mata masu aminci? Kalmar Allah ta ce, “furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.” (Mis. 16:31) Hakika, idan wani amintaccen Kirista yana da furfura, da ke nuna ya manyanta hakan yana da kyau a gaban Allah. Kana ɗaukan ’yan’uwanka tsofaffi kamar yadda Jehobah yake ɗaukansu?
Me Ya Sa Suke da Tamani?
3. Me ya sa bayi tsofaffi suke da tamani a gare mu?
3 A cikin waɗannan bayin Allah tsofaffi akwai waɗanda suke cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah, masu kula masu ziyara na dā da na yanzu, majagaba masu ƙwazo, ’yan’uwa maza da mata masu shelar Mulki da suke hidima da aminci a ikilisiyarmu. Wataƙila ka san wasu da suka yi shelar bishara da ƙwazo shekaru masu yawa kuma misalinsu ya taimaka wajen motsa matasa kuma ya gyara rayuwarsu. Wasu tsofaffi masu bi sun ɗauki hakki masu girma kuma sun jimre gwaji don shelar bishara. Jehobah da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suna godiya ga dukan abubuwan da suka yi dā da waɗanda suke yi yanzu a aikin Mulki.—Mat. 24:45.
4. Me ya sa ya kamata mu daraja tsofaffi Kiristoci kuma mu riƙa yi musu addu’a?
4 Waɗannan tsofaffi masu aminci sun cancanci sauran bayin Jehobah Allah su yaba musu kuma su daraja su. Hakika, Dokar da Allah ya ba Musa ta nuna cewa idan mutum yana tsoron Jehobah zai kula kuma ya daraja tsofaffi. (Lev. 19:32) Ya kamata mu riƙa yi wa waɗannan amintattu addu’a a kai a kai kuma mu yi godiya ga Allah don ayyukansu na ƙauna. Manzo Bulus ya yi addu’a ga abokan aikinsa matasa da tsofaffi.—Ka karanta 1 Tasalonikawa 1:2, 3.
5. Ta yaya za mu amfana ta yin tarayya da tsofaffi masu bauta wa Jehobah?
5 Bugu da ƙari, duka mutane a ikilisiya za su amfana ta wajen yin tarayya da tsofaffi Kiristoci. Ta wajen nazari, da lura, da kuma abin da suka fuskanta, tsofaffi amintattu masu bauta wa Jehobah suna da ilimi mai tamani. Sun koyi su jimre da kuma jin tausayi, hakan ya sa suna koya wa tsara ta gaba abin da suka koya ta haka za su sami farin cikin da gamsuwa. (Zab. 71:18) Matasa ku kasance da hikima kuma ku yi amfani da wannan tushen ilimi kamar yadda za ku amfana ta wajen jawo ruwa daga rijiya mai zurfi.—Mis. 20:5.
6. Ta yaya za ka nuna wa tsofaffi cewa kana daraja su?
6 Kana gaya wa tsofaffi cewa kana ƙaunarsu kamar yadda Jehobah yake ƙaunarsu kuwa? Hanya ɗaya da za ka iya yin haka ita ce ta wurin gaya musu cewa kana ƙaunarsu don amincinsu kuma kana daraja ra’ayinsu. Bugu da ƙari, ta wurin amfani da abin da ka koya daga gare su, kana nuna cewa kana daraja su sosai. Tsofaffi Kiristoci da yawa za su iya tuna shawara mai kyau da suka samu daga tsofaffi masu aminci da kuma yadda yin aiki da su ya amfane su a dukan rayuwarsu.a
Ka Nuna Ƙauna a Hanyoyi Dabam Dabam
7. Wanene Jehobah ya ba ainihin aikin kula da tsofaffi?
7 Allah ya ba iyalin da suke da tsofaffi hakkin kula da su. (Ka karanta 1 Timothawus 5:4, 8.) Jehobah yana farin ciki idan iyalai suka cika hakkinsu game da danginsu tsofaffi kuma su nuna cewa sun damu da tsofaffi kamar yadda ya damu da su. Allah yana taimakon waɗannan iyalan kuma yana yi musu albarka don ƙoƙarinsu da duka sadaukarwar su.b
8. Me ya sa ya kamata ikilisiyoyi su damu da tsofaffi Kiristoci?
8 Hakazalika, Jehobah yana farin ciki sa’ad da ikilisiyoyi suka taimaki tsofaffi amintattu waɗanda suke bukatar taimako amma ba su da iyalai masu bi ko kuma waɗanda za su so su kula da su. (1 Tim. 5:3, 5, 9, 10) Ta yin haka ikilisiyoyi suna nuna cewa suna da ‘juyayi suna yin ƙauna kamar ’yan’uwa, masu taushin zuciya’ ga tsofaffi. (1Bit. 3:8) Bulus ya kwatanta kula da tsofaffi na ikilisiya sa’ad da ya ce idan gaɓa ɗaya na jikin mutum ya sha wuya, “dukan gaɓaɓuwa suna shan raɗaɗi tare da shi.” (1 Kor. 12:26) Yin abubuwa don kula da tsofaffi yana kwatanta ƙa’idar da ke cikin shawarar da Bulus ya bayar: “Ku ɗauki kayan junanku, ku cika shari’ar Kristi hakanan.”—Gal. 6:2.
9. Menene tsofaffi suke fuskanta?
9 Menene tsofaffi suke fuskanta? Wasu suna gajiya da sauri. Za su ga kamar ba za su iya zuwa wajen likita ba, rubuce-rubuce, sharan gida, da kuma yin girki. Tun da tsufa yakan zo da rashin jin marmarin cin abinci da shan ruwa, za su yi tunani cewa ba sa bukatar su ci ko su sha kamar yadda ya kamata su yi. Yana iya kasance hakan da abincinsu na ruhaniya. Idanun tsofaffi da kunnuwansu na iya sa ya kasance da wuya su yi karatu kuma su saurari abubuwa na ruhaniya, kuma shirya taro na Kirista na iya zama aiki mai gajiyarwa ƙwarai. To, menene wasu za su iya yi wa tsofaffi?
Yadda Za Ka Iya Ba da Taimako
10. Menene ya kamata dattawa su yi don su tabbata ana biya bukatar tsofaffi?
10 A ikilisiyoyi da yawa ana kula da tsofaffi a hanyoyi dabam dabam. ’Yan’uwa suna taimakonsu da cefane, girke-girke, da kuma shara. Suna taimakon tsofaffi su yi nazari, su yi shiri don taro, kuma su riƙa fita hidima a kai a kai. Matasa suna tafiya tare da su kuma su ɗauke su a mota. Idan tsofaffi ba sa iya barin gida ana iya saka musu shi a tef. Idan zai yiwu, dattawa su tabbata cewa ana kula da bukatun tsofaffi a ikilisiya.c
11. Ka faɗi yadda wata iyali ta taimaki wani ɗan’uwa.
11 Kiristoci ma za su iya nuna halin karɓan baƙi da karimci. Da matar wani ɗan’uwa tsoho ta rasu, bai iya biyan kuɗin gidansa ba don ba ya karɓan kuɗin fenshonta kuma. Shi da matarsa sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wata iyali masu ’ya’ya mata biyu da suke da babban gida. Sun ba shi ɗakuna biyu ya zauna a ciki. Sun ci abinci tare, sun yi hira, kuma sun nuna ƙauna ta ’yan’uwa na shekara 15. Yaran sun koyi abubuwa daga bangaskiyarsa da kuma abin da ya fuskanta a rayuwa, shi kuma ya amfana daga cuɗanyarsu. Wannan ɗan’uwa tsoho ya zauna tare da su har ya mutu yana shekara 89. Har ila iyalin na gode wa Allah don albarka da suka samu ta wurin tarayya da shi. Ba su yi hasarar ‘ladar’ da suka samu na taimakon almajirin Yesu Kristi ba.—Mat. 10:42.d
12. Menene za ka yi don ka nuna kana ƙaunar ’yan’uwa tsofaffi?
12 Wataƙila ba ka da halin taimakon ɗan’uwa ko ’yar’uwa tsofaffi yadda wannan iyalin ta yi, amma kana iya taimakonsu su je taro su kuma fita hidimar fage. Kana iya gayyatarsu zuwa gidanka da kuma idan za ka je yawon shakatawa. Kana iya ziyararsu sa’ad da suke ciwo ko kuma ba sa iya tashiwa. Bugu da ƙari, ya kamata ka bi da su a matsayin manya. Muddin suna da hankali, ya kamata a haɗa tsofaffi Kiristoci a dukan shawarwari da suka shafe su. Har da waɗanda ba su da cikakken hankalinsu suna sanin lokacin da ake daraja su.
Jehobah ba Zai Manta da Aikinka Ba
13. Me ya sa yin la’akari da yadda tsofaffi Kiristoci suke ji yake da muhimmanci?
13 Yana da muhimmanci a yi la’akari da yadda tsofaffi suke ji. Sau da yawa tsofaffi suna baƙin ciki domin ba sa iya yin abubuwa da suke yi sa’ad da suke matasa kuma suke da kuzarinsu. Alal misali, wata ’yar’uwa da ta bauta wa Jehobah shekara 50 kuma ta yi hidimar majagaba na kullum ta soma ciwo da ke raunana ta kuma hakan na sa ya kasance da wuya ta halarci taro. Sa’ad da ta gwada hidimarta ta dā da kasawarta na yanzu, sai ta soma kuka. Ta sunkuyar da kanta tana kuka, ta ce, “Ba na iya yin kome kuma.”
14. Ta yaya zabura za ta ƙarfafa tsofaffi bayin Jehobah?
14 Idan ka tsufa, ka taɓa jin hakan? Da akwai lokacin da kake jin Jehobah ya yashe ka? Wataƙila mai zabura ya ji hakan sa’ad da ya tsufa, don ya roƙi Jehobah: “Kada ka yashe ni cikin kwanakin tsufa; kada ka yarfarda ni lokacin da ƙarfina ya ƙare. I, har lokacinda na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah.” (Zab. 71:9, 18) Hakika, Jehobah ba zai yasar da wanda ya rubuta wannan zaburar ba, kuma ba zai yasar da kai ba. A wata zabura, Dauda ya furta tabbacinsa cewa Allah zai taimake shi. (Ka karanta Zabura 68:19.) Idan kai Kirista ne mai aminci da ya tsufa, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana tare da kai kuma zai ci gaba da kiyaye ka kullum.
15. Menene zai taimake tsofaffi su kasance da ra’ayin da ya dace?
15 Allah ba ya mantawa da dukan abin da tsofaffi Shaidun Jehobah suka yi kuma suke yi yanzu don su ɗaukaka shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” (Ibr 6:10) Saboda haka, ku daina kasancewa da ra’ayin da bai dace ba, kuna tunanin cewa domin kun tsufa ba ku da amfani kuma a gaban Jehobah. Ku yi ƙoƙari ku canja mummunan ra’ayi ku kasance da ra’ayi masu kyau. Ku yi farin ciki don albarkarku da kuma begenku na nan gaba! Muna da “bege mai-kyau a ƙarshe” wanda ya fi kyau, kuma Mahaliccinmu ne ya ba da tabbacin wannan. (Irm 29:11, 12; A. M. 17:31; 1Ti 6:19) Ka yi tunani a kan begenka, ka yi ƙoƙari ka kasance da ƙarfi a ruhaniya, kuma ka da ka ga kamar ba ka da muhimmanci a taron ikilisiya!e
16. Me ya sa wani dattijo ya yi tunani ya sauke aikinsa na dattijo, amma yaya rukunin dattawa suka ƙarfafa shi?
16 Ga misalin, Johan, mai shekara 80 da ke kula da Sannief matarsa mai aminci da ba ta iya tashiwa yanzu. ’Yan’uwa mata suna zama da Sannie don Johan ya je taro da kuma hidima. Ba da daɗewa ba, Johan ya ji ya gaji sarai kuma ya soma tunani cewa ba zai iya zama dattijo kuma ba. “Menene amfanin zama dattijo?” in ji shi, idanunsa cike da hawaye. “Ba na yin wani aikin kirki kuma a ikilisiya.” Dattawan ikilisiyarsu suka tabbatar masa cewa abin da ya fuskanta a rayuwa da yadda yake bi da batutuwa suna da muhimmanci. Suka aririce shi ya ci gaba da hidimarsa na dattijo, ko idan abin da yake yi kaɗan ne. Da yake sun ƙarfafa shi sosai, Johan ya ci gaba da hidimarsa na dattijo, kuma wannan albarka ce ga ikilisiya.
Jehobah Yana Kula da Ku Sosai
17. Wane tabbaci ne Littafi Mai Tsarki ya ba tsofaffi Kiristoci?
17 Nassosi ya bayyana sarai cewa tsofaffi za su iya ci gaba a ruhaniya duk da matsaloli da ke tattare da tsufa. Mai zabura ya ce: “Waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji . . . Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai: Za su kasance cike da romo da ɗanyantaka.” (Za 92:13, 14) Manzo Bulus, wanda wataƙila ya yi fama da wani ciwo bai ‘yi yaushi ba; ko da mutumi da yake a waje yana lalacewa.’—Ka karanta 2 Korinthiyawa 4:16-18.
18. Me ya sa tsofaffi ’yan’uwa masu bi da waɗanda suke kula da su suke bukatar taimako?
18 Misalai da yawa na zamani sun nuna cewa tsofaffi “za su yi ta ’ya’ya.” Amma ƙalubale da ciwo da tsufa suke kawo wa suna sa mutum sanyin gwiwa, har ga waɗanda suke da iyalai masu kula da su. Waɗanda suke kula da tsofaffi ma suna iya gajiya. Ikilisiya tana da gata da kuma hakkin nuna ƙaunarta ga tsofaffi da waɗanda suke kula da su. (Ga 6:10) Irin wannan taimako na nuna cewa ba ma gaya wa irin waɗannan su tafi ‘su ji ɗumi, su ƙoshi’ ba tare da taimaka musu ba.—Yaƙ 2:15-17.
19. Me ya sa ya kamata Kiristoci shafaffu masu aminci su ɗauki nan gaba da tabbaci?
19 A wata hanya, tsufa na iya canja ayyukan Kirista, amma wucewar lokaci ba ya rage ƙaunar Jehobah ga bayinsa tsofaffi masu aminci. A wani ɓangare, dukan waɗannan Kiristoci masu aminci suna da tamani a idanunsa, kuma ba zai taɓa yashe su ba. (Za 37:28; Ish 46:4) Jehobah zai kiyaye kuma ya yi musu ja-gora a duk shekarun tsufansu.—Za 48:14.
[Hasiya]
a Ka dubi talifin nan “Tsofaffi Albarka ne ga Matasa,” a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuni, 2007.
b Ka duba Awake shafuffuka na 3-10 na 8 ga Fabrairu, 1994!
c A wasu ƙasashe, hakan zai ƙunshi taimakon tsofaffi su karɓi gudummawar da gwamnati take bayarwa. Ka dubi talifin nan “Allah Yana Kula da Tsofaffi,” a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuni, 2006.
d Ka dubi talifin nan “Jehovah Always Cares for Us,” Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 2003.
e Ka duba talifin nan “The Splendor of Gray-Headedness,” a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 1993.
f An canja sunaye.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa kake ɗaukan Kiristoci tsofaffi masu aminci da tamani?
• Ta yaya za mu nuna wa tsofaffi ’yan’uwa masu bi ƙauna?
• Menene zai taimaki bayin Jehobah da suka tsufa su kasance da ra’ayin da ya dace?
[Hotuna a shafi na 18]
Waɗanda suke cikin ikilisiya suna daraja tsofaffi sosai