Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 3/15 pp. 20-24
  • Ku Girmama Tsofaffi da ke Tare da Ku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Girmama Tsofaffi da ke Tare da Ku
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “KADA KA YASHE NI”
  • HAKKIN IYALI
  • HAKKIN IKILISIYA
  • KA ƘARFAFA TSOFAFFI DA FURUCINKA
  • Kula Da Tsofaffi Hakki Ne Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Yana Kula Da Bayinsa Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yadda Za a Kula da Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kula da Iyaye da Suka Tsufa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 3/15 pp. 20-24

Ku Girmama Tsofaffi da Suke Tare da Ku

“Ku girmama tsofaffi.”—LEV. 19:32, Littafi Mai Tsarki.

MECE CE AMSARKA?

  • Yaya Jehobah yake ɗaukan ’yan’uwa tsofaffi?

  • Wane hakki ne yara da suka girma suke da shi ga iyayensu tsofaffi?

  • Ta yaya ’yan’uwa a cikin ikilisiyoyi za su girmama ’yan’uwa tsofaffi?

1. A wane yanayin baƙin ciki ne ’yan Adam suka sami kansu?

JEHOBAH bai nufi ’yan Adam da tsufa da kuma wahalar da ke tattare da hakan ba. Akasin haka, nufinsa ne ’yan Adam su ji daɗin rayuwa cikin ƙoshin lafiya a Aljanna. Amma yanzu, “dukan halitta na nishi, na shan azaba.” (Rom. 8:22, LMT) Yaya kake gani Allah yake ji sa’ad da ya ga ’yan Adam suna shan wahala saboda zunubi? Abin baƙin ciki ne cewa ana watsi da tsofaffi da yawa a wannan lokacin da ya kamata a kula da su sosai.—Zab. 39:5; 2 Tim. 3:3.

2. Me ya sa Kiristoci suna godiya cewa suna tare tsofaffi a cikin ikilisiya?

2 Mutanen Jehobah suna farin cikin cewa suna tare da tsofaffi a cikin ikilisiyoyinsu. Muna amfana daga hikimarsu kuma muna son mu yi koyi da bangaskiyarsu. Wataƙila waɗannan tsofaffin danginmu ne. Amma ko da ce su danginmu ne ko a’a, ya kamata mu damu da lafiyarsu kuma mu kula da su da kyau. (Gal. 6:10; 1 Bit. 1:22) Bari mu tattauna yadda Allah yake ɗaukan tsofaffi don hakan zai taimaka mana. Ƙari ga haka, za mu tattauna hakkin da ke kan iyalai da kuma ’yan’uwa a cikin ikilisiya wajen kula da tsofaffinmu.

“KADA KA YASHE NI”

3, 4. (a) Wace addu’a mai muhimmanci ce marubucin Zabura ta 71 ya yi ga Jehobah? (b) Mene ne tsofaffi da ke cikin ikilisiya za su iya roƙan Jehobah?

3 Zabura 71:9 ta ce: “Kada ka yashe ni cikin kwanakin tsufa; kada ka yarfar da ni lokacin da ƙarfina ya ƙare.” Wataƙila Dauda ne ya rubuta wannan zaburar. Ya bauta wa Allah a dukan rayuwarsa kuma Jehobah ya yi amfani da shi wajen yin abubuwa masu ban al’ajabi. (1 Sam. 17:33-37, 50; 1 Sar. 2:1-3, 10) Dauda ya tsufa kuma ya roƙi Jehobah ya ci gaba da nuna masa alheri.—Karanta Zabura 71:17, 18.

4 Mutane da yawa a yau suna nan kamar Dauda. Duk da cewa sun tsufa kuma suna fuskantar “miyagun kwanaki,” suna iya ƙoƙarinsu a bauta wa Allah. (M. Wa. 12:1-7) Da yawa daga cikinsu ba su da ƙwazo kamar dā, har ma a wa’azi. Amma su ma za su iya roƙi Jehobah ya ci gaba da kula da su kuma ya albarkace su. Ƙari ga haka, Jehobah zai amsa addu’o’insu. Mun san hakan gaskiya ne don Jehobah ya hure Dauda ya yi addu’a game da irin waɗannan matsalolin.

5. Yaya Jehobah yake ɗaukan tsofaffi?

5 Jehobah yana ɗaukan tsofaffi masu aminci da mutunci kuma ya bukaci bayinsa su daraja su. (Zab. 22:24-26; Mis. 16:31; 20:29) Littafi Mai Tsarki ya ce “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsoro na. Ni ne Ubangiji.” (Lev. 19:32, LMT) Hakika, girmama tsofaffi hakki ne mai muhimmanci a lokacin da aka rubuta waɗannan kalaman, kuma haka yake a yau. Amma wane ne ke da hakkin kula da su?

HAKKIN IYALI

6. Wane misali ne Yesu ya kafa a kula da iyaye?

6 Kalmar Allah ta ce: “Ka ba da girma ga ubanka da uwarka.” (Fit. 20:12; Afis. 6:2) Yesu ya nuna cewa wannan dokar tana da muhimmanci sa’ad da yake tsauta wa Farisawa da marubuta da suka ƙi kula da iyayensu. (Mar. 7:5, 10-13) Yesu ya kafa misali mai kyau. Alal misali, sa’ad da yake gab da mutuwa a gungumen azaba, ya yi tanadi don a kula da mahaifiyarsa, wadda a lokacin gwauruwa ce. Ya tabbata cewa almajirinsa, wato Yohanna wanda abokinsa ne na kud da kud, ya kula da ita.—Yoh. 19:26, 27.

7. (a) Wace ƙa’ida ce game da kula da iyali manzo Bulus ya ambata? (b) Mene ne ya yi magana a kai kuma?

7 An hure manzo Bulus ya rubuta cewa ya kamata masu bi su kula da iyalansu. (Karanta 1 Timotawus 5:4, 8, 16.) Sa’ad da yake magana game da waɗanda suka cancanta ikilisiya ta tallafa musu, ya ambaci wannan ƙa’idar. Ƙari ga haka, ya bayyana cewa yara da jikoki da kuma wasu da ke cikin dangi ne ke da hakkin kula da gwauraye da suka tsufa. Ta haka, za a guji nawaita wa ikilisiya. Hakazalika, hanya ɗaya da muke nuna cewa muna ƙaunar Allah a yau ita ce ta wajen biyan bukatun iyali da kuma danginmu.

8. Me ya sa Littafi Mai Tsarki bai ba da takamaiman umurni game da kula da tsofaffi ba?

8 ’Ya’ya da suka manyanta ne ke da hakkin kula da iyayensu. Bulus yana nufin danginmu da Shaidu ne, amma bai kamata mu yi watsi da iyayenmu ba ko da su ba Shaidun Jehobah ba ne. Yadda yara za su cika wannan hakkin ya bambanta domin yanayin kowace iyali ba ɗaya ba ne. Wasu tsofaffi suna da ’ya’ya da yawa, wasu kuma ɗaya kawai suke da shi. Wasu za su iya samun tallafi daga gwamnati, wasu kuma ba za su iya ba. Ƙari ga haka, kowa yana da nasa bukata. Saboda haka, ba zai dace a yi sūkar waɗanda suke kula da iyayensu ko kuma danginsu da suka tsufa ba. Jehobah zai iya sa duk wata shawara da ke bisa Littafi Mai Tsarki ta yi nasara kamar yadda ya yi a zamanin Musa.—Lit. Lis. 11:23.

9-11. (a) Wane yanayi mai wuya ne wasu za su iya fuskanta? (Ka duba hoton da ke farkon talifin nan.) (b) Me ya sa bai kamata waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci su yi saurin barin hidimarsu don kula da iyayensu ba? Ka ba da misali.

9 Idan inda yara suke zama ya yi nisa da inda iyayensu suke, kula da iyaye zai iya zama da ƙalubale. Yara za su bukaci ziyarar iyayensu sakamakon faɗuwa, karayar gaɓa ko kuma wata matsala mai tsanani. Bayan haka, iyayen za su bukaci a kula da su na wani ɗan lokaci ko na tsawon lokaci.a

10 Waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci da ke hidima nesa da gida za su iya fuskantar ƙalubale sosai a irin wannan yanayin. Waɗanda suke hidima a Bethel da masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma masu kula masu ziyara suna ɗaukan hidimarsu da tamani, tamkar albarka daga Jehobah. Duk da haka, sa’ad da iyayensu suka yi rashin lafiya, za su iya soma tunani cewa, ‘muna bukatar mu bar hidimarmu mu koma gida don mu kula da iyayenmu.’ Amma zai dace mu yi addu’a game da ainihin abubuwan da iyayenmu suke bukata. Kada mu yi saurin barin ayyukan da muke yi a ƙungiyar Jehobah, kuma yin hakan ma ba wajibi ba ne a wani lokaci. Shin rashin lafiyar na wani ɗan lokaci ne? Wasu a cikin ikilisiya za su so su taimaka ne?—Mis. 21:5.

11 Ka yi la’akari da misalin wani yaya da ƙane da suke hidima nesa da gida. Ɗaya mai wa’azi a ƙasashen waje ne kuma yana hidima a ƙasar Paraguay, ɗayan kuma yana hidima a babban hedkwatarmu da ke Brooklyn, a birnin New York. Iyayensu da suka tsufa sun bukaci taimako. ’Yan’uwa biyun da matansu sun je garinsu don su san yadda za a iya taimaka wa iyayensu. Bayan wani lokaci, sai wanda yake wa’azi a ƙasashen waje da matarsa suka soma tunanin barin hidimarsu don kula da tsofaffin. Sai dattawa da ke ikilisiyar da iyayen suke suka yi musu waya. Dattawan suka nazarci batun kuma suka ce suna so ɗan’uwan da matarsa su ci gaba da hidimarsu. Dattawan sun yaba wa waɗannan ma’auratan kuma sun ce za su kula da iyayensu. Babu shakka, kowa a cikin wannan iyalin ya ji daɗi cewa dattawan sun taimaka!

12. Mene ne ya kamata iyalin Kirista su fi mai da wa hankali sa’ad da suke shawara game da yadda za su kula da tsofaffi?

12 Ya kamata dukan Kiristoci da suke so su kula da iyayensu su tabbata cewa matakin da suke so su ɗauka don yin hakan ya girmama sunan Allah. Kada mu yi kamar shugabannin addinai na zamanin Yesu. (Mat. 15:3-6) Muna son shawarar da muka yanke ta sa a yabi Allah da kuma ikilisiya.—2 Kor. 6:3.

HAKKIN IKILISIYA

13, 14. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ikilisiyoyi suna da hakkin kula da ’yan’uwa tsofaffi?

13 Ba kowa ne zai iya taimaka wa waɗanda suke hidima ta cikakken lokaci kamar yadda aka ambata a baya ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya kamata ikilisiyoyi su yi iya ƙoƙarinsu don taimaka wa tsofaffi masu aminci. A cikin ikilisiyar Urushalima ta dā, “ba wanda yake da rashi.” Ba wai duk wanda ke cikin ikilisiyar mai arziki ba ne. A bayyane yake cewa wasu mabukata ne, amma “an kuwa rarraba wa kowa gwargwadon bukatarsa.” (A. M. 4:34, 35, LMT) Daga baya, aka sami wata babbar matsala a cikin ikilisiyar. An yi watsi da wasu gwauraye sa’ad da ake raba “abinci kowace rana.” Saboda haka, manzannin suka naɗa wasu mazaje da suka cancanta don tabbatar da cewa waɗannan gwaurayen suna samun abinci kamar sauran. (A. M. 6:1-5) A ranar Fentakos ta shekara ta 33 a zamaninmu ne aka yi wannan tanadin don baƙi da yawa da suka zama Kiristoci sun kasance a Urushalima don ƙarfafa bangaskiyarsu. Duk da cewa wannan tanadin rarraba abinci na ɗan lokaci ne, matakin da manzannin suka ɗauka ya nuna cewa ikilisiya za ta iya kula da amintattun ’yan’uwa da suka tsufa.

14 Bulus ya bayyana wa Timotawus cewa zai dace ikilisiya ta taimaka wa Kiristoci gwauraye. (1 Tim. 5:3-16) An hure Yaƙub ya rubuta cewa Kiristoci suna da hakkin kula da marayu da gwauraye da wasu da suke shan wahala. (Yaƙ. 1:27; 2:15-17) Manzo Yohanna ya ƙara da cewa: “Amma wanda ya ke da dukiyar duniya, yana kuwa ganin ɗan’uwansa da tsiya [rashi], ya hana masa tausayi, ƙaƙa ƙaunar Allah tana zaune a cikinsa?” (1 Yoh. 3:17) Saboda haka, idan Kirista yana da hakkin kula da mabukata, ikilisiyoyi ma suna da wannan hakki har ila.

15. Waɗanne abubuwa ne za su iya shafan yadda ake kula da ’yan’uwa tsofaffi?

15 A wasu ƙasashe, gwamnati tana ba da fensho da wasu tanadodi don taimaka wa tsofaffi. (Rom. 13:6) A wasu kuma, ba a yin irin wannan tanadin. Saboda haka, irin taimakon da dangi da kuma ikilisiya za su tanadar wa tsofaffi ya dangana ga yanayin. Idan yara masu bi suna zama nesa da iyayensu, hakan zai iya shafan yawan taimakon da za su iya bayarwa. Zai dace ’ya’yan tsofaffin su tattauna da dattawan da ke ikilisiyar iyayensu don tabbata cewa kowa ya fahimci yanayin iyalinsu. Alal misali, dattawa za su iya taimaka wa iyayen yadda za su amfana daga wani tsarin gwamnati don kula da tsofaffi. Za su kuma lura da wasu abubuwan da ya kamata yaran su sani, kamar wasiƙun da ba a buɗe ba da kuma magungunan da iyayen ba su yi amfani da su ba kuma su gaya wa ’ya’yansu. Idan yaran da dattawan suna tuntuɓar juna kowane lokaci, hakan zai rage munin yanayin kuma zai iya magance wasu matsaloli. Idan akwai wani kusa da ke taimaka wa tsofaffin ko kuma yana gaya wa yaransu da ke nesa abin da iyayensu suke bukata, hakan zai taimaka sosai kuma ba za su riƙa yawan damuwa ba.

16. Ta yaya wasu Kiristoci suke taimaka wa tsofaffi da ke cikin ikilisiya?

16 Wasu Kiristoci sun ba da lokacinsu don su kula da waɗannan tsofaffin a duk yadda za su iya domin suna ƙaunar su sosai. Suna kula da waɗannan tsofaffin kamar danginsu. Wasu kuma suna haɗa kai da wasu cikin ikilisiya wajen kula da tsofaffi, wataƙila suna yin hakan juyi-juyi. Ko da yake yanayinsu ba zai bar su su yi hidima ta cikakken lokaci ba, waɗannan ’yan’uwan suna farin cikin taimaka wa don ’ya’yan ’yan’uwa tsofaffi su ci gaba da hidima ta cikakken lokaci. Wannan hali ne mai kyau ’yan’uwa suke nunawa! Duk da haka, alherin da suke yi ba zai sa yaran su yi watsi da hakkinsu na taimaka wa iyayensu ba.

KA ƘARFAFA TSOFAFFI DA FURUCINKA

17, 18. Ta yaya kasancewa da ra’ayi mai kyau yake shafan tsofaffi da kuma waɗanda suke kula da su?

17 Tsofaffi da kuma waɗanda ke kula da su za su iya mai da yanayi mai muni ya kasance da sauƙi idan sun kasance da ra’ayi mai kyau. Wani lokaci tsufa zai iya sa mutum baƙin ciki. Saboda haka, ana bukatar a yi ƙoƙari sosai don a girmama da kuma ƙarfafa ’yan’uwa tsofaffi. Mene ne za ka iya yi? Ku riƙa tattaunawa mai ban ƙarfafa da su. Waɗannan ’yan’uwan sun kasance da aminci ga Jehobah kuma ya kamata mu yaba musu. Jehobah ba zai manta da ayyukan da suka yi a bautarsa ba, mu ma ba za mu manta ba.—Karanta Malakai 3:16; Ibraniyawa 6:10.

18 Ƙari ga haka, ayyukan yau da kullum zai kasance da sauƙi idan ana wasa da dariya a lokacin da ya dace. (M. Wa. 3:1, 4) Tsofaffi da yawa suna ƙoƙari don kada su cika damun ’yan’uwa da matsalolinsu. Sun fahimci cewa za a kula da su sosai idan sun kasance da fara’a. Mutane da yawa da suke ziyarar tsofaffi sukan ce, “Na je ƙarfafa wani abokina da ya tsufa, amma kuma ya ƙarfafa ni.”—Mis. 15:13; 17:22.

19. Mene ne zai taimaka wa matasa da tsofaffi su kasance da bangaskiya sosai a mawuyacin lokaci?

19 Muna ɗokin ganin ranar da za a kawo ƙarshen tsufa da wahala da kuma ajizanci. Kafin lokacin, wajibi ne bayin Allah su kasance da bege cewa lokaci yana zuwa da za mu rayu har abada. Idan muka ba da gaskiya ga alkawuran Allah, za mu jure a lokaci ma wuya. Da yake muna da bangaskiya, “ba mu yi yaushi ba; amma ko da mutumin namu na waje yana lalacewa, mutumin namu na ciki yana sabuntuwa yau da gobe.” (2 Kor. 4:16-18; Ibran. 6:18, 19) Mene ne kuma zai taimaka wa waɗanda suke da hakkin kula da tsofaffi? Za a tattauna wasu shawarwari da za su taimaka musu a talifi na gaba.

a Za mu tattauna wasu hanyoyin kula da yara za su iya bi don kula da tsofaffinsu a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba