Yadda Za a Kula da Tsofaffi
“’Ya’yana ƙanƙanana, kada mu yi ƙauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.”—1 YOH. 3:18.
1, 2. (a) Waɗanne matsaloli ne iyalai da yawa suke fuskanta kuma wace tambaya ce suke yi? (b) Ta yaya iyaye da kuma yara za su iya bi da matsalolin tsufa?
ABIN baƙin ciki ne ganin cewa iyayenka da a dā suke da ƙarfi kuma suke kula da kansu sun kasa yin hakan kuma. Mahaifiyarka ko mahaifinka zai iya faɗi kuma ya karye ko kuma ya yi ciwo mai tsanani. A wani ɓangare kuma, yana wa tsofaffi wuya su saba da yanayin jikinsu, musamman idan hakan ya hana su yin wasu abubuwa da suke yi a dā. (Ayu. 14:1) Ta yaya za mu iya taimaka musu?
2 Wani talifi da ya yi magana game da yadda za a kula da tsofaffi ya ce: “Ko da yana da wuya a tattauna matsalolin da tsofaffi suke fuskanta, amma iyalan da suka yi hakan za su fi sanin yadda za su bi da matsalolin.” Ya kamata mu san cewa ba za mu iya hana tsofaffi samun matsaloli ba. Shi ya sa yake da muhimmanci sosai iyalin baki ɗaya su shirya. Ta yaya iyalai za su iya kasancewa da haɗin kai don yanke wannan shawara mai wuya?
YIN SHIRI DON “MIYAGUN KWANAKI”
3. Mene ne iyalai za su iya yi idan iyayensu da suka tsufa suna bukatar taimako? (Ka duba hoton da ke shafi na 25.)
3 Akwai lokacin da tsofaffi ba za su iya kula da kansu ba kuma za su bukaci taimako. (Karanta Mai-Wa’azi 12:1-7.) Sa’ad da hakan ya faru, ya kamata iyayen da suka tsofe da kuma yaransu su tattauna yadda za su kula da tsofaffin. Ya fi dacewa iyalin baki ɗaya su zauna don tattauna abin da ake bukata da yadda za a yi hakan da kuma yadda kowa zai goyi bayan shawarar da aka yanke. Ya kamata kowa ya furta ra’ayinsa kuma ya faɗi batun daidai yadda yake. Shin iyayen za su iya ci gaba da zama a gida su kaɗai?a Ko kuma su tattauna yadda kowa a cikin iyalin zai iya taimaka wa iyayen. (Mis. 24:6) Alal misali, wasu za su iya ɗaukan nawayar yi musu aiki kowace rana, wasu kuma za su iya ba da kuɗi domin biyan bukatunsu. Ya kamata kowa ya san matsayinsa, amma da shigewar lokaci, za a iya yin wasu canje-canje ko kuma wani a cikin iyalin zai iya ɗaukan matsayin wani.
4. Mene ne zai iya taimaka wa iyalai yayin da yanayinsu yake canjawa?
4 Yayin da kake kula da iyayenka da suka tsufa, ka ƙoƙarta domin ka fahimci yanayin ciwonsu. Idan suna da ciwon da zai ci gaba da yin tsanani, ka san lokacin da hakan zai faru. (Mis. 1:5) Ka tuntuɓi asibitocin gwamnati da suke kula da tsofaffi. Ka yi bincike game da shirin kiwon lafiya a yankinku don sauƙaƙa aikin kula da su. Waɗannan canje-canjen da irin wannan yanayin zai kawo, zai iya sa ka baƙin ciki ko kuma ruɗewa. Idan hakan ya faru, za ka iya bayyana wa wani amininka damuwarka. Mafi muhimmanci, ka gaya wa Jehobah dukan abin da ke ci maka tuwo a ƙwarya a cikin addu’a. Zai sa ka kasance da kwanciyar hankali don ka jure kowane irin yanayin.—Zab. 55:22; Mis. 24:10; Filib. 4:6, 7.
5. Me ya sa ya dace a shirya yadda za a kula da tsofaffi tun da wuri?
5 Zai dace iyalai da kuma tsofaffinsu su nemi bayanai game da tsarin kiwon lafiya da za su bi. Suna iya yin bincike don sanin ko zai dace iyayen su zauna da wani daga cikin yaran ko a kai su gidan kula da tsofaffi ko kuma a yi musu wani tanadi dabam. Da hakan, iyalan za su yi shiri don ‘wahala da baƙin ciki’ da ke tattare da tsufa. (Zab. 90:10) Iyalan da ba su yi shiri ba tun da wuri za su tsai da shawara a garaje sa’ad da matsaloli suka taso. Wani masani ya ce: “Yanke shawara a irin wannan lokacin bai dace ba ko kaɗan.” Yanke shawara a irin wannan yanayin zai iya sa a sami saɓani sosai a cikin iyalin kuma ƙila ba za a cim ma kome ba. Amma dai, idan mun shirya tun da wuri, bi da kowace matsalar da ta taso za ta fi sauƙi.—Mis. 20:18.
6. Me za a cim ma idan aka tattauna yadda za a kula da iyaye tsofaffi?
6 Zai iya kasance da wuya ka gaya wa iyayenka cewa su yi wani canji a gidansu ko kuma za su ƙaura wata rana. Amma duk da haka, wasu sun ce wannan tattaunawar ta taimaka musu daga baya. Ta yaya? Domin yin magana a kan batutuwa masu wuya da saurarawa sosai da kuma yin shiri sosai kafin matsaloli su taso ya fi sauƙi. Idan iyalin suka tattauna tare hankali a kwance, hakan zai sa su faɗi ra’ayinsu kuma za su kusaci juna sosai. Wasu tsofaffi sun fi son zaman kansu. Saboda haka, idan suka faɗi abin da suka fi so, hakan zai taimaka wa kowa a cikin iyalin sa’ad da ake so a yanke shawara a kan yadda za a kula da su.
7, 8. Wane batu ne ya kamata iyalai su tattauna, kuma me ya sa?
7 A lokacin da ake wannan tattaunawar, ya kamata iyaye su gaya wa ’ya’yansu abin da suke bukata, yawan kuɗin da suke bukata da abin da suka fi so. Hakan zai sa su san shawarwarin da za su tsai da idan kuka tsufa. Babu shakka, yaranku za su so daraja ku kuma su sa ku sami ’yanci. (Afis. 6:2-4) Alal misali, shin za ku so wani cikin yaranku ya sa ku zo ku zauna tare da iyalinsa sa’ad da kuka tsufa? Ko kuwa kuna bukatar wani abu dabam? Ko da mene ne ya faru, ka tuna cewa ba kowa cikin iyalin ba ne zai amince da ra’ayinka ba. Za a ɗan daɗe kafin kowa ya daidaita ra’ayinsa.
8 Za a iya guje wa matsaloli da yawa idan aka yi shiri kuma aka tattauna batun da kyau. (Mis. 15:22) Ka tattauna batun jinya da iyalinka da kuma abin da ka fi so. Sa’ad da kuke wannan tattaunawar, zai dace ku yi magana a kan yadda kuke so a yi amfani da jininku a lokacin jinya da kuma matakan da za a ɗauka sa’ad da kuke bakin mutuwa. Hakan ya dace domin kowa a cikin iyalin zai san abin da kuke so. Kowane mutum yana da ’yancin sanin irin jinyar da za a yi masa da kuma ’yancin amince da jinyar ko a’a. Za a iya cika irin waɗannan bayanai a cikin katin DPA. Idan ka zaɓi mutumin da zai yi magana a madadinka sa’ad da kake jinya tun da wuri, hakan zai ba ka zarafin zaɓan wanda ka amince da shi. Ya kamata tsofaffin da masu kula da su da kuma waɗanda suka saka musu hannu a katin DPA ɗin su sami kofi guda na katin da aka cika.
YADDA ZA KA JIMRE IDAN YANAYINKA YA CANJA
9, 10. A wane lokaci ne iyaye za su fi bukatar yaransu su taimaka musu?
9 A yawancin lokaci, kowa a cikin iyalin yana so tsofaffi su kasance da ’yanci. Idan har ila iyayen sun iya girki da shara da wanke-wanke da shan magani da kuma yin magana sosai, zai dace yaran su bar su su sami ’yancin kansu. Amma da shigewar lokaci, idan ba su iya yin tafiya sosai ba ko cefane ko kuma suna saurin mantuwa, yaran za su iya yin wasu canje-caje da suka dace.
10 Tsofaffi suna iya rikicewa ko sanyin gwiwa ko mantuwa ko rashin ji sosai ko rashin gani da wasu matsalolin da ke tattare da tsufa. Idan wasu cikin waɗannan matsalolin suka taso, jinya zai iya sa ya ragu. Yara za su iya su riƙa kai iyayensu da suka tsufa wurin likita a kai a kai. Idan suna so iyayen su sami jinya mai kyau, zai dace su yi magana a madadinsu, su yi musu rubuce-rubuce, su kai su asibitin da dai sauransu.—Mis. 3:27.
11. Mene ne za a iya yi don tsofaffi su yi saurin sabawa da canji?
11 Idan iyayenku suna da ciwon da ba za a iya magance shi ba, za ku iya yin wasu canji a yadda kuke kula da su ko kuma ku canja musu wurin zama. Idan canjin bai da yawa sosai, zai fi musu sauƙin sabawa da shi. Idan kuna zama a wuri mai nisa daga iyayenku, wani Mashaidi ko kuma maƙwabci zai iya riƙa ziyartarsu a kai a kai kuma ya gaya muku yadda suke. Shin suna bukatar mutumin da zai riƙa yi musu shara da wanki da kuma girki? Idan an yi wasu canje-canje a tsarin gidan, shin hakan zai sa ya fi kasance musu da sauƙi su yi yawo a cikin gidan da wanka da dai sauransu? Wataƙila abu kawai da suke bukata shi ne mutumin da zai riƙa yi musu aikace-aikacen gida. Amma, idan zama su kaɗai zai jawo musu lahani, za a iya musu wani shirin da ya fi hakan. Ko da mene ne yanayin, ka yi bincike a kan abin da ya fi dacewa a yankin.b—Karanta Misalai 21:5.
YADDA WASU SUKE BI DA ƘALUBALEN
12, 13. Mene ne wasu yara da suka yi girma suke yi don su girmama da kuma kula da iyayensu da suke nesa da su?
12 Muna ƙaunar iyayenmu, saboda haka, muna so mu kula da su sosai. Yin hakan yana sa mu sami kwanciyar hankali. Amma, yawancin yara ba sa zama kusa da iyayensu. A irin wannan yanayin, wasu suna amfani da lokacin hutu domin su ziyarci iyayensu, kuma su taimaka su yi musu wasu abubuwa da ba su da ƙarfin yi kuma. Yin kira a waya kowace rana, ko kuwa aika wasiƙu yana tabbatar wa iyaye cewa yaran suna ƙaunarsu sosai.—Mis. 23:24, 25.
13 Ko da kowannenku yana zama a wuri mai nisa, zai dace ku tattauna abin da za ku riƙa yi musu kullum. Idan kuna zama nesa da su, kuma su Shaidu ne, za ku iya ce dattawan ikilisiyarsu su shawarce ku. Daɗin daɗawa kuma, ku yi addu’a ga Jehobah game da iyayenku. (Karanta Misalai 11:14.) Ko da iyayenku ba Shaidu ba ne, wajibi ne ‘ku ba da girma ga ubanku da uwarku.’ (Fit. 20:12; Mis. 23:22) Hakika, ba dukan iyalai ba ne za su tsai da shawara iri ɗaya ba. Wasu suna kawo iyayensu da suka tsufa gidajensu. Amma hakan ba ya cika faruwa a yau. Wasu iyaye sun fi so su zauna a gidajensu, maimakon su zauna tare da ’ya’yansu da kuma iyalinsu. Wasu za su fi so su riƙa biyan wani don ya kula da su.—M. Wa. 7:12.
14. Waɗanne irin matsaloli ne waɗanda suka fi kula da iyayensu tsofaffi suke fuskanta?
14 A iyalai da yawa, ana barin nawayar kula da iyaye da suka tsufa ga mutum ɗaya, musamman wanda yake zama kusa da su. Amma, ya kamata su daidaita yadda suke biyan bukatun iyalansu da kuma na iyayensu. Lokaci da kuma ƙarfin kowa ba ɗaya ba ne. Kuma idan yanayin mai kula da su ya canja, zai dace a yi wasu canje-canje. Shin hakkin kula da wani cikin yaran yake ɗauka ya yi yawa ainun? Shin sauran yaran za su iya zuwa su kula da iyayen bi da bi?
15. Ta yaya ’yan’uwa da abokai za su iya taimaka wa wanda ke kula da tsofaffi don kada ya gaji?
15 Mai kula da iyaye tsofaffi zai iya gaji tikis idan suna yawan bukatar taimako. (M. Wa. 4:6) Yara za su so su yi iya ƙoƙarinsu don su biya bukatun iyayensu, amma yin hakan zai iya nauyaya su sosai. Mutumin da ke kula da iyayen yana bukatar kasancewa da ra’ayin da ya dace kuma ya ce wani ya taimaka masa. Saboda haka, zai dace mai kula da tsofaffi ya nemi taimako daga wurin wasu. Hakan zai sa ya samu damar ci gaba da taimaka wa tsofaffin ba tare da yin gajiya ba.
16, 17. Waɗanne ƙalubale ne yara za su iya fuskanta yayin da suke kula da iyayensu, kuma ta yaya ne za su bi da ƙalubalen? (Ka duba akwatin nan “Ka Nuna Godiya don Yadda Aka Kula da Kai.”)
16 Abin baƙin ciki ne mutum ya ga matsalar da tsufa ta jawo wa iyayensa. A wasu lokuta, masu kula da tsofaffi suna baƙin ciki da sanyin gwiwa da taƙaici da kuma fushi. Iyaye tsofaffi za su iya faɗin abin da zai ɓata maka rai. Kada ka yi saurin fushi idan hakan ya faru. Wani likitan ƙwaƙwalwa ya ce: “Hanya mafi kyau na bi da wannan yanayin shi ne ka yarda cewa abin ba ya sa ka farin ciki. Kada ka yi fushi da kanka domin kana jin hakan.” Ka gaya wa miji ko matarka game da yadda kake ji, ko kuma wani danginka ko amininka. Irin wannan tattaunawar za ta taimaka maka ka san yadda za ka bi da irin wannan matsalar.
17 Akwai lokacin da mai yiwuwa iyalin ba za su sami kuɗin kula da iyayensu da suka tsufa kuma ba. A wasu ƙasashe, yaran za su iya yin wani tanadi don su kula da iyayensu. Wata ’yar’uwa tana ziyartar mahaifiyarta a gidan kula da tsofaffi kullum. Ta ce: “Mun kasa kula da mahaifiyarmu a kowane lokaci a gida. Bai zama mana da sauƙi mu kai ta gidan kula da tsofaffi ba. Amma, mun yi hakan domin abin da zai magance matsalar ke nan kuma ta yarda da hakan.”
18. Wane tabbaci ne masu kula da tsofaffi suke da shi?
18 Kula da iyayen da suka tsufa yana da wuya sosai. Wataƙila yadda aka kula da wani tsoho bai zai yiwu wa wani ba. Amma idan kun yi shiri sosai kun haɗa kai da iyalinku kuma kun tattauna sosai, mafi muhimmanci ma, idan kun yi addu’a ga Jehobah, za ku iya cim ma hakkinku na girmama iyayenku. Idan kuka yi hakan, za ku sami kwanciyar hankali da kuma farin ciki domin kuna kula da iyayenku. (Karanta 1 Korintiyawa 13:4-8.) Mafi muhimmanci, za ku sami kwanciyar hankali kuma Jehobah zai albarkace ku.—Filib. 4:7.
a A wasu wurare, iyaye suna zama tare da yaransu da suka yi girma idan iyayen sun fi son hakan.
b Idan har ila iyayenku suna gida, ku tabbata cewa mutumin da zai riƙa kula da su yana da makullin ɗakinsu domin ya iya taimaka musu idan suna bukatar jinyar gaggawa.