Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 1/1 p. 7
  • Tambayoyi daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Makamantan Littattafai
  • An Jejjefi Istafanus
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Sani?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • 3 | Ka Cire Kiyayya Daga Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 1/1 p. 7

Tambayoyi daga Masu Karatu

Shin furcin Istifanas a Ayyukan Manzanni 7:59 ya nuna cewa ya kamata a yi addu’a ga Yesu ne?

Ayyukan Manzanni 7:59 ta ce: “Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu’a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” Waɗannan kalmomi sun sa wasu suna tambaya, tun da Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah shi ne mai “amsa addu’o’i.” (Zabura 65:2) Shin da gaske ne Istifanas ya yi addu’a ga Yesu? Wannan ya nuna cewa Yesu daidai yake da Jehobah?

Littafi Mai Tsarki na King James ya ce Istifanas yana “kira ga Allah.” Saboda haka, mutane da yawa suka ce kamar yadda mai bayani a kan Littafi Mai Tsarki Matthew Henry ya ce: “Istifanas a nan ya yi addu’a ga Kristi ne, kuma dole mu ma mu yi haka.” Amma wannan ra’ayin ba daidai ba ne. Me ya sa?

Bayanin Barnes a kan Sabon Alkawari ya yi wannan bayanin: “Kalmar nan Allah ba ta cikin na asali, kuma bai kamata ya kasance cikin fassarar ba. Kalmar ba ta cikin littattafai na dā.” Ta yaya aka saka wannan kalmar “Allah” a wannan ayar? Manazarci Abiel Abbot Livermore ya kira wannan “misali ne na son kai na masu fassara.” Yawancin fassara na zamani sun cire Allah da aka sa a wurin da bai dace ba.

Duk da haka, fassara da yawa sun ce Istifanas ya yi “addu’a” ga Yesu. Kuma hasiya na New World Translation ya nuna cewa “roƙo” yana iya nufin “addu’a.” Shin wannan bai nuna ba ne cewa Yesu shi ne Allah Maɗaukaki? A’a. Littafin nan Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words, ya yi bayani cewa a irin wannan yanayi, kalmar ainihi ta Helenanci, e·pi·ka·leʹo, tana nufin: “Kira, roƙo; . . . a roƙi masu iko.” Bulus ya yi amfani da wannan kalmar sa’ad da ya ce: Na “ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.” (Ayyukan Manzanni 25:11) Litafi Mai-Tsarki ya fassara shi daidai da ya ce Istifanas ya yi “kira” ga Yesu.

Me ya sa Istifanas ya yi irin wannan kiran? In ji Ayyukan Manzanni 7:55, 56, Istifanas, “cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye dama ga Allah.” Hakika, da Istifanas ya yi roƙonsa ne ga Jehobah cikin sunan Yesu. Amma da yake ya ga Yesu da aka ta da daga matattu cikin wahayi, Istifanas wataƙila ya ga ya dace ya yi kira ga Yesu kai tsaye, yana cewa: “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” Istifanas ya sani cewa an ba Yesu ikon ta da matattu. (Yahaya 5:27-29) Saboda haka, ya roƙi Yesu ya kāre ruhunsa, ko kuma ransa, har sai ranar da Yesu zai tashe shi zuwa rai marar mutuwa a samaniya.

Shin wannan ɗan furci na Istifanas ya kafa misali ne na yin addu’a ga Yesu? A’a. Domin a bayyane yake cewa Istifanas ya bambanta tsakanin Yesu da Jehobah, domin labarin ya ce ya ga Yesu a “damar Allah.” Ƙari ga haka, wannan yanayin ya bambanta. Wani yanayi kuma da aka yi kira kai tsaye ga Yesu wanda manzo Yahaya ya yi ne, wanda ya ga Yesu a wahayi kuma ya kira shi kai tsaye.—Wahayin Yahaya 22:16, 20.

Ko da yake Kiristoci a yau suna addu’arsu kamar yadda ya dace ga Jehobah Allah, su ma suna da bangaskiya mai ƙarfi cewa Yesu ‘ne tashin matattu, shi ne kuma rai.’ (Yahaya 11:25) Kamar yadda Istifanas ya yi, haka bangaskiya ga iyawar Yesu ya ta da mabiyansa daga matattu zai taimaka kuma ya kiyaye mu a lokacin gwaji.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba