Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 2/1 pp. 27-31
  • Koyaushe Jehobah Na Yin Abin Da Ke Daidai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Koyaushe Jehobah Na Yin Abin Da Ke Daidai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Za Ka Yarda da Hukuncin Jehobah?
  • Me Ya Sa Lutu ya Ba da ’Ya’yansa Mata ga Taron ’Yan Iska da Suka Fusata?
  • Me Ya Sa Jehobah Ya Kashe Uzza?
  • Ƙarfafan Dalili na Kasancewa da Tabbaci
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Matar Lutu Ta Dubi Baya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Za Mu Iya Faranta wa Allah Rai Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 2/1 pp. 27-31

Koyaushe Jehobah Na Yin Abin Da Ke Daidai

“Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka.”—ZABURA 145:17.

1. Yaya za ka aikata sa’ad da wani ya faɗi abin da ba daidai ba ne game da kai, kuma wane darassi za mu koya daga wannan?

WANI ya taɓa faɗan abin da ba daidai ba ne game da kai, wataƙila yana shakkarka ba tare da samun cikakken labarinka ba? Mai yiwuwa ka yi fushi—kuma an fahimci hakan. Za mu iya koyan muhimmin darasi daga wannan: Ba shi da kyau mu kammala abu sa’ad da ba mu ji cikakken labarin ba.

2, 3. Yaya wasu suke aikatawa game da labaran Littafi Mai Tsarki da ba su ba da isashen bayani ba game da kowace tambaya, menene Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Jehobah?

2 Ya kamata mu tuna wannan darasin sa’ad da muke magana game da Jehobah Allah. Me ya sa? Domin da wasu labaran Littafi Mai Tsarki da za su sa mu yi mamaki da farko. Waɗannan labaran—wataƙila game da hukuncin Allah dā ko kuma yadda wasu bayinsa suka aikata—ba za su kasance da isashen bayani ga dukan tambayoyinmu ba. Abin baƙin ciki, wasu suna sūkan irin waɗannan labarai, suna ma shakkar ko Allah mai adalci ne. Amma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka.” (Zabura 145:17) Kalmarsa ta tabbatar mana cewa “ba zai aikata mugunta ba.” (Zabura 37:28; Ayuba 34:12) Ka yi tunanin yadda zai ji sa’ad da wasu suke faɗin abin da ba daidai ba ne game da shi!

3 Bari mu bincika dalilai biyar da ya sa za mu yarda da hukuncin Jehobah. Tare da waɗannan dalilai, za mu bincika labaran Littafi Mai Tsarki biyu da za su yi wa wasu wuyar fahimta.

Me Ya Sa Za Ka Yarda da Hukuncin Jehobah?

4. Me ya sa za mu kasance da tawali’u sa’ad da muke la’akari da ayyukan Allah? Ka ba da misali.

4 Na farko, domin Jehobah ya san abubuwa da ba mu sani ba, ya kamata mu kasance da tawali’u sa’ad da muke la’akari da ayyukan Allah. Alal misali: A ce alƙali da aka sani ba ya wariya wajen shari’a, ya yanke hukunci. Menene za ka ce game da wani da ya zargi hukuncin alƙalin ba tare da sanin abin da ya faru ba ko kuma bai fahimci dokoki da abin ya ƙunsa ba? Wauta ce mutum ya mai da martani ga batu kafin ya saurare shi. (Karin Magana 18:13) Wautar za ta wuci kima ga ’yan adam su zargi “Mahukuncin dukan duniya.”—Farawa 18:25.

5. Me ya kamata mu tuna sa’ad da muka karanta labaran Littafi Mai Tsarki game da hukuncin Allah a kan wasu mutane?

5 Dalili na biyu da ya sa za mu yarda da hukuncin Allah shi ne domin yana iya sanin abin da ke zuciya ba kamar ’yan adam ba. (1 Sama’ila 16:7) Kalmarsa ta ce: “Ni Ubangiji nakan bincike tunani, in gwada zuciya, domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al’amuransa, da kuma gwargwadon ayyukansa.” (Irmiya 17:10) Shi ya sa sa’ad da muka karanta labaran Littafi Mai Tsarki game da hukuncin Allah a kan wasu mutane kada mu manta cewa yana ganin kome har da tunani, muradi da nufi da ba a rubuta ba cikin Kalmarsa.—1 Tarihi 28:9.

6, 7. (a) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana manne wa mizanansa na adalci ko ma zai yi hasara? (b) Me ya kamata mu tuna idan muka karanta wani abu cikin Littafi Mai Tsarki da ya sa mu shakkar ko Allah ya aikata abin da ke daidai?

6 Ga dalili na uku da ya sa za mu yarda da hukuncin Jehobah: Yana bin mizanai na adalci ko zai yi hasara. Ga misali. Da ya ba da Ɗansa fansa don ya ceci ’yan adam daga zunubi da mutuwa, Jehobah ya bi mizanansa na adalci. (Romawa 5:18, 19) Amma ganin Ɗansa ƙaunatacce ya wahala ya kuma mutu a kan gungumen azaba ya sa Jehobah baƙin ciki sosai. Menene wannan ya nuna mana game da Allah? Game da “fansar da Almasihu Yesu ya yi,” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah kuwa ya yi haka domin ya nuna adalcinsa ne.” (Romawa 3:24-26) Wata fassara ta Romawa 3:25 ta ce: “Wannan ya nuna cewa koyaushe Allah na yin abin da ke daidai.” (New Century Version) Hakika, yadda Jehobah ya kasance a shirye ya yi tanadin fansa ya nuna cewa yana daraja “abin da ke daidai.”

7 Saboda haka, idan muka karanta wani abu cikin Littafi Mai Tsarki da ya sa mu shakkar ko Allah ya yi abin da ke daidai, ya kamata mu tuna wannan: Domin yana manne wa mizanansa na adalci da kuma yin gaskiya Jehobah bai hana Ɗansa ya mutu ba. Shin zai taka waɗannan mizanan a wasu batutuwa? Gaskiyar ita ce, Jehobah ba ya taka mizanansa na adalci. Saboda haka muna da ƙarfafan dalilin kasancewa da tabbaci cewa koyaushe yana yin abin da ke daidai.—Ayuba 37:23.

8. Me ya sa ba zai yi daidai ba ’yan adam su yi tunani cewa Jehobah zai riƙa rashin gaskiya da adalci?

8 Ka yi la’akari da dalili na huɗu da ya sa za mu amince da hukuncin Jehobah: Jehobah ya yi mutum cikin siffarsa. (Farawa 1:27) Da haka ’yan adam suna da halaye da Allah yake da su, har da azancin yin gaskiya da adalci. Ba zai yi daidai ba idan azancinmu na yin gaskiya da adalci zai sa muna tunanin cewa Jehobah zai yi rashin waɗannan halaye. Idan mun damu game da wani labarin Littafi Mai Tsarki, ya kamata mu tuna cewa domin mun gaji zunubi da mutuwa, ba za mu riƙa ɗaukan abin da ke daidai da kuma adalci yadda ya kamata ba. Jehobah Allah wanda ya yi mu cikin siffarsa mai gaskiya ne da kuma adalci. (Maimaitawar Shari’a 32:4) Wauta ce a yi tunani cewa ’yan adam sun fi Allah yin gaskiya da adalci!—Romawa 3:4, 5; 9:14

9, 10. Me ya sa bai kamata Jehobah ya ba da bayani ba ko kuma ya ba da dalilin ayyukansa ga ’yan adam?

9 Dalili na biyar da ya sa za mu yarda da hukuncin Jehobah shi ne domin shi “ne mamallakin dukan duniya.” (Zabura 83:18) Saboda haka bai kamata ya yi bayani ko ya ba da dalilin ayyukansa ga ’yan adam ba. Jehobah ne Babban Magini, muna kama da yumɓu da ake yin tukwane da shi, zai mulmula mu yadda ya ga dama. (Romawa 9:19-21) Waye ne mu—aikin hannunsa—da za mu tuhumi shawararsa ko kuma ayyukansa? Sa’ad da uban iyali Ayuba bai fahimci yadda Allah yake sha’ani da ’yan adam ba, Jehobah ya daidaita tunanin Ayuba, ya tambaye shi: “Kai kanka za ka sa mini laifi? Za ka kā da ni don kai ka barata?” Da ya fahimci cewa ya yi kuskure, sai Ayuba ya tuba. (Ayuba 40:8; 42:6) Kada mu yi kuskuren ɗaura wa Allah laifi!

10 Hakika, muna da ƙarfafan dalili na gaskata cewa Jehobah koyaushe yana abin da ke daidai. Da wannan taimako na fahimtar hanyoyin Jehobah, bari mu bincika labaran Littafi Mai Tsarki guda biyu da wasu za su iske da ban mamaki. Na farko, game da ayyukan wani bawan Allah ne, na biyun kuma game da hukuncin Allah ne.

Me Ya Sa Lutu ya Ba da ’Ya’yansa Mata ga Taron ’Yan Iska da Suka Fusata?

11, 12. (a) Ka ba da labarin abin da ya faru sa’ad da Allah ya aiki mala’iku biyu zuwa Saduma. (b) Wannan labarin ya sa wasu suna waɗanne tambayoyi?

11 A cikin Farawa sura 19, da labarin abin da ya faru sa’ad da Allah ya aiki mala’iku biyu zuwa Saduma. Lutu ya nace wa baƙin su zauna a gidansa. Amma daddare taron maza ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan suka ce a fito da baƙin su yi lalata da su. Lutu ya yi ƙoƙari ya lallashe taron amma sun ƙi. Tun da yana son ya kāre baƙinsa, Lutu ya ce: “Ina roƙonku ’yan’uwana, kada ku aikata mugunta haka. Ga shi, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.” Mutanen ba su ma saurara ba kuma suka kusan ɓalle kofar. Daga baya, mala’ikun suka makantar da mutanen.—Farawa 19:1-11.

12 Hakika, wannan labarin ya sa mutane sun yi tambayoyi. Suna mamaki: ‘Yaya Lutu zai kāre baƙinsa ta wajen ba da ’ya’yansa mata ga taron ’yan iska masu neman lalata? Bai yi wauta ba kuwa? Domin wannan labarin, me zai sa Allah ya hure Bitrus ya kira Lutu “adali”? Shin Allah ya amince da abin da Lutu ya yi? (2 Bitrus 2:7, 8) Bari mu yi magana a kan wannan batun domin mu kammala yadda ya dace.

13, 14. (a) Menene ya kamata mu lura game da labarin abin da Lutu ya yi da ke cikin Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya nuna cewa Lutu ba wawa ba ne?

13 Ya kamata a lura cewa maimakon a amince ko kuma zargi ayyukan Lutu, Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da ya faru kawai. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abin da Lutu yake tunaninsa ba ko kuma abin da ya sa shi ya yi haka. Sa’ad da ya dawo a tashin ‘matattu, na masu adalci,’ wataƙila zai ƙara ba da bayanin abin da ya faru dalla-dalla.—Ayyukan Manzanni 24:15.

14 Lutu ba matsoraci ba ne. Yana cikin yanayi ne mai wuya. Tun da ya ce baƙin “sun shiga ƙarƙashin inuwar” sa, Lutu ya nuna cewa dole ne ya kāre su kuma ya ba su mafaka. Amma wannan ba shi da sauƙi. Ɗan tarihi Bayahude Josephus, ya ce “Sadumawa marasa adalci ne ga mutane kuma ba sa daraja Allah . . . Sun tsani baƙi kuma sun shagala sosai cikin ayyukan lalata.” Amma, Lutu bai ji tsoron wannan taron ’yan iska masu ƙiyayya ba. Maimakon haka, ya fita waje ya yi magana da mutanen da suka fusata. Ya ma “rufe ƙofar a bayansa.”—Farawa 19:6.

15. Me ya sa za mu ce mai yiwuwa Lutu ya aikata hakan ne cikin bangaskiya?

15 Wasu har illa za su yi tambaya ‘me ya sa Lutu ya ba da ’ya’yansa mata ga taron ’yan iska?’ Maimakon mu kammala cewa manufarsa ba shi da kyau, ga wasu abubuwa da wataƙila ya sa ya yi hakan. Na farko, mai yiwuwa Lutu ya aikata hakan ne cikin bangaskiya. Ta yaya? Lutu babu shakka yana sane da yadda Jehobah ya kāre Saratu, matar Ibrahim, kawunsa. Ka tuna cewa domin Saratu kyakkyawa ce, Ibrahim ya gaya mata ta ce ita ƙanwarsa ce, yana tsoron kada a kashe shi dominta.a Domin haka aka kai Saratu gidan Fir’auna. Amma Jehobah ya hana Fir’auna yin lalata da Saratu. (Farawa 12:11-20) Wataƙila Lutu yana da bangaskiya cewa za a kāre ’ya’yansa mata hakan nan. Hakika, Jehobah ta mala’ikunsa ya sa hannu, kuma ba abin da ya sami ’yammatan.

16, 17. (a) A wace hanya ce Lutu ya yi ƙoƙari ya rikiɗar ko ya ba mazan Saduma mamaki? (b) Ko menene dalilin Lutu, za mu kasance da wane tabbaci?

16 Ga wani misali. Lutu mai yiwuwa yana ƙoƙari ya rikiɗar da mutanen ko kuma ya ba su mamaki. Wataƙila ya gaskata cewa taron ba za su so ’ya’yansa mata ba domin ayyukan luwaɗi da Sadumawa suka dulmuya ciki. (Yahuza 7) Ban da wannan, ’yammatan sun yi alkawarin aure da mazan birnin, saboda haka, dangi, abokai ko kuma abokan kasuwanci na surukan Lutu mai yiwuwa suna cikin taron. (Farawa 19:14) Lutu wataƙila ya sa rai cewa domin wannan nasaba wasu maza cikin taron za su yi magana a madadin ’ya’yansa mata. Taron da suke a rabe ba za su kasance da lahani ba.b

17 Ko menene dalilin Lutu da muradinsa, za mu kasance da wannan tabbacin: Tun da yake Jehobah koyaushe yana yin abin da ke daidai, yana da dalili mai kyau na ɗaukan Lutu “adali.” Idan muka yi la’akari da ayyukan taron ’yan iska na Sadumawa, shin da wani dalili na yin shakkar cewa Jehobah ya aikata daidai da ya zartar da hukunci a kan mazaunan wannan mugun birni?—Farawa 19:23-25.

Me Ya Sa Jehobah Ya Kashe Uzza?

18. (a) Menene ya faru sa’ad da Dauda yake son ya kai Akwatin Urushalima? (b) Wace tambaya ce wannan labarin ya ta da?

18 Wani labari da zai iya ba wasu mamaki ya faru sa’ad da Dauda ya sa aka ɗauko akwatin alkawari zuwa Urushalima. An ɗora akwatin a kan keken shanu, kuma Uzza da ɗan’uwansa ne suke korar shanun. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da suka zo masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa ya riƙa akwatin alkawarin Allah, gama takarkaran sun yi kwarangyasa. Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawari.” Bayan wasu watanni, an yi nasara wajen kawar da Akwatin domin an ɗauka yadda Allah ya ce a riƙa ɗauka, Lawiyawa na iyalin Kohat sun ɗauka a kafaɗunsu. (2 Sama’ila 6:6, 7; Littafin Ƙidaya 4:15; 7:9; 1 Tarihi 15:1-14) Wasu za su yi tambaya, ‘Me ya sa Jehobah ya yi fushi haka? Uzza ya yi hakan ne domin ba ya son Akwatin ya faɗi.’ Kafin mu kammala yadda bai dace ba, yana da kyau mu bincika wasu abubuwa cikin labarin.

19. Me ya sa ba zai yiwu ba Jehobah ya aikata abin da ba daidai ba?

19 Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ba ya mugunta. (Ayuba 34:10) Ba zai nuna ƙauna ba idan ya yi haka, kuma mun sani daga nazarin Littafi Mai Tsarki cewa “Allah shi ne ƙauna.” (1 Yahaya 4:8) Ƙari ga haka, Nassosi sun gaya mana cewa a kan “gaskiya da adalci aka kafa mulkin [Allah].” (Zabura 89:14) To, ta yaya Jehobah zai aikata abin da ba daidai ba? Idan zai yi haka, zai ɓata tushen ikon mallakarsa.

20. Don waɗanne dalilai ne ya kamata Uzza ya san dokoki game da Akwati?

20 Ka tuna cewa ya kamata Uzza ya san dokar. Akwatin yana wakiltar bayanuwar Jehobah. Doka ta ce wanda ba shi da izini kada ya taɓa shi, ta ba da gargaɗi cewa za a kashe wanda ya taka dokar. (Littafin Ƙidaya 4:18-20; 7:89) Saboda haka, mayar da akwatin zuwa wani waje ba abin da za a yi da wasa ba ne. Mai yiwuwa Uzza Balawi ne (ko da yake ba firist ba ne), ya kamata ya san Dokar sosai. Ban da haka, shekaru da suka shige an ajiye Akwatin a gidansu. (1 Sama’ila 6:20–7:1) Ya kasance a wurin shekara 70, har sai da Dauda ya ɗauke shi daga wajen. Saboda haka, wataƙila tun yana yaro Uzza yana sane da dokoki game da Akwatin.

21. Me ya sa yake da muhimmanci mu tuna cewa Jehobah yana ganin zuciya a batun Uzza?

21 Yadda aka faɗa da farko, Jehobah yana sanin abin da ke zuciya. Tun da Kalmarsa ta kira abin da Uzza ya yi ‘karambani,’ Jehobah ya ga muradinsa na son kai da ba a faɗa ba a labarin. Shin Uzza mai girman kai ne, da zai yi abin da ba a gaya masa ba? (Karin Magana 11:2) Shin ja-gorar Akwatin da iyalinsa ya kāre a ɓoye zai sa shi girman kai? (Karin Magana 8:13) Shin Uzza ya yi rashin bangaskiya da zai sa ya yi tunani cewa Jehobah ba zai iya tsayar da akwatin da ke wakiltar bayyanuwarsa ba? Ko menene dai, muna da tabbaci cewa Jehobah ya aikata abin da ya dace. Mai yiwuwa ya ga abin da ke cikin zuciyar Uzza da ya sa ya zartar da hukunci nan da nan.—Karin Magana 21:2.

Ƙarfafan Dalili na Kasancewa da Tabbaci

22. Ta yaya Kalmar Jehobah da ba ta ba da wasu bayani ba ta nuna hikimarsa?

22 Ana ganin hikimar Jehobah da babu na biyunsa a cikin Kalmarsa da wani lokaci ba ta ba da wasu bayani ba. Ta haka Jehobah na ba mu zarafi mu nuna mun dogara a gare shi. Ta abin da muka bincika, ba a bayane yake ba cewa muna da dalilin yarda da hukuncin Jehobah? Hakika, sa’ad da muka yi nazarin Kalmar Allah domin muna son mu san shi, muna ƙara koyan abubuwa da yawa game da Jehobah da zai sa mu tabbata cewa koyaushe yana aikata abin da ke daidai. Saboda haka, idan wasu labaran Littafi Mai Tsarki sun ta da wasu tambayoyi da ba za mu samu amsar nan da nan ba, bari mu kasance da tabbaci cewa koyaushe Jehobah yana aikata abin da ke daidai.

23. Wane tabbaci za mu kasance da shi game da ayyukan Jehobah na nan gaba?

23 Za mu kasance da irin wannan tabbaci game da abin da Jehobah zai yi a nan gaba. Saboda haka, za mu kasance da tabbaci cewa sa’ad da zai zartar da hukunci a lokacin matsananciyar wahala da ke zuwa, ba zai “hallaka adali tare da mugu” ba. (Farawa 18:23) Da yake yana son adalci da gaskiya ba zai taɓa yin haka ba. Za mu kuma kasance da tabbaci cewa a sabuwar duniya mai zuwa, zai biya dukan bukatunmu yadda ya dace.—Zabura 145:16.

[Hasiya]

a Daidai ne Ibrahim ya tsorata, don wani rubutu na dā ya yi maganar wani Fir’auna da ya sa rundunarsa suka ƙwace kyakkyawar mace kuma suka kashe mijinta.

b Don ƙarin bayani, ka dubi Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1979 shafi na 31 (Turanci).

Ka Tuna?

• Domin waɗanne dalilai za mu amince da hukuncin Jehobah?

• Menene zai taimake mu mu guji faɗan abin da ba daidai ba game da yadda Lutu ya ba da ’ya’yansa mata ga taron ’yan iska?

• Waɗanne abubuwa za su taimake mu mu fahimci abin da ya sa Jehobah ya kashe Uzza?

• Wane tabbaci muke da shi game da abin da Jehobah zai yi nan gaba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba