Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • my labari na 15
  • Matar Lutu Ta Dubi Baya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matar Lutu Ta Dubi Baya
  • Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Ɗauki Alkawari da Ibrahim
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Ka Taimaka wa Mutane Su Jimre da Matsaloli
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
my labari na 15

LABARI NA 15

Matar Lutu Ta Dubi Baya

LUTU da iyalinsa suka zauna tare da Ibrahim a ƙasar Kan’ana. Wata rana Ibrahim ya ce wa Lutu: ‘Ka ga babu isashen wuri a nan domin dabbobinmu duka. Don Allah ka ga gara mu rabu. Idan ka bi nan, sai ni in bi can.’

Lutu ya dubi duka ƙasar. Ya ga gefe mai kyau na ƙasar wanda yake da ruwa da kuma ciyayi da yawa domin dabbobinsa. Wato Gunduman Urdun. Sai Lutu ya ƙaura tare da iyalinsa da dabbobinsa zuwa can. A ƙasar suka zauna a birnin Saduma.

Mutanen Saduma miyagu ne ƙwarai. Wannan ya ɓata wa Lutu rai ƙwarai, domin shi mutumin kirki ne. Ran Allah ma ya ɓaci. A ƙarshe sai Allah ya aiki mala’iku biyu su yi wa Lutu gargaɗi cewa zai halaka Saduma da kuma Gwamarata birnin da ke kusa da shi domin muguntarsu.

Mala’ikun suka gaya wa Lutu: ‘Maza! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka mata biyu ka fita daga nan!’ Amma Lutu da iyalinsa suna ɗan jinkiri, saboda haka mala’ikun suka kama hannunsu suka fitar da su daga cikin birnin. Sai ɗaya daga cikin mala’ikan ya ce: “Ku gudu don ranku! Kada ku dubi baya. Ku gudu zuwa duwatsu saboda kada ku mutu.”

Lutu da ’ya’yansa mata suka yi biyayya suka gudu daga Saduma. Ba su tsaya ba ko na ɗan lokaci, kuma ba su dubi baya ba. Amma matar Lutu ta yi rashin biyayya. Bayan sun yi ɗan nisa da Saduma, ta tsaya ta dubi baya. Sai matar Lutu ta zama umudin gishiri. Ka ganta a wannan hoton?

Za mu iya koyon darassi mai kyau daga wannan. Wannan ya nuna mana cewa Allah yana ceton waɗanda suka yi masa biyayya, amma waɗanda suka ƙi yi masa biyayya za su rasa ransu.

Farawa 13:5-13; 18:20-33; 19:1-29; Luka 17:28-32; 2 Bitrus 2:6-8.

Tambayoyi na Nazari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba