Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Agusta p. 3
  • Ku Tuna da Matar Lutu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Tuna da Matar Lutu
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Tuna da Matar Lutu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Matar Lutu Ta Dubi Baya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Na Tashi Cikin Talauci, Amma Yanzu Ni Mai Arziki Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Kada Ka Kalli Abubuwan Da Ke “Baya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Agusta p. 3
Matar Lutu ta juya ta kalli Saduma kuma ta zama tarin gishiri

RAYUWAR KIRISTA

Ku Tuna da Matar Lutu

Me ya sa matar Lutu ta kalli baya sa’ad da suke barin Saduma? Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin ba. (Fa 19:​17, 26) Amma gargaɗin da Yesu ya yi ya nuna cewa wataƙila ta tuna da abubuwan da ta bari a garin Saduma ne. (Lu 17:​31, 32) Ta yaya za mu guji bin misalinta? Wajibi ne mu guji saka kayan duniya farko a rayuwarmu. (Mt 6:33) Yesu ya ce ba za mu iya ‘sa ranmu ga bin Allah da kuma son kuɗi a lokaci ɗaya’ ba. (Mt 6:24) Amma me za mu yi idan muka ga cewa kayan duniya sun soma janye hankalinmu daga ibada? Mu yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mana mu ga inda muke bukatar mu yi gyara kuma ya ba mu ƙarfin hali don mu yi gyarar.

KU TUNA DA BIDIYON NAN KU TUNA DA MATAR LUTU, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Anna a wurin aiki; Gloria da kawunta; Brian da Gloria suna addu’a

    Ta yaya halayena zasu nuna cewa ina “tuna da matar Lutu”?

    Ta yaya matsin da aka yi wa Gloria ya shafi tunaninta da furucinta da kuma ayyukanta?

  • Ta yaya matar Lutu ta zama misali a gare mu yau?

  • Ta yaya bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Joe da iyalinsa?

  • Ta yaya abokan aikin Anna suka sa ta daina mai da hankali a ayyuka na ibada?

  • Me ya sa muke bukatar ƙarfin hali idan ana matsa mana mu nemi kuɗi ruwa a jallo?

  • Ta yaya Brian da Gloria suka soma bauta wa Jehobah kamar yadda suke yi a dā?

  • Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne aka yi amfani da su a bidiyon nan?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba