Iyaye Ku Kāre Kyautarku Mai Tamani
“Hikima mafaka ce, . . . takan yi wa mai ita [kāriya].” —Mai Hadishi 7:12.
1. Me ya sa ya kamata iyaye su ɗauki ’ya’yansu tamkar kyauta?
IYAYE sun kawo sabon mutum duniya da yake da hali da mutuntaka irin nasu. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan ‘kyauta daga wurin Ubangiji.’ (Zabura 127:3) Tun da shi ne Mafarin Dukan rai, lalle Jehobah yana kyauta ne da abin da shi kaɗai ya mallaka. (Zabura 36:9) Iyaye yaya kuke ɗaukan wannan kyautar daga wurin Allah?
2. Menene Manowa ya yi da ya sami labari cewa zai haifi ɗa?
2 Hakika ya kamata a ɗauki irin wannan kyautar da tawali’u da kuma godiya. Shekara 3,000 da ta shige, Ba’isra’ile Manowa ya faɗi haka sa’ad da mala’ika ya sanar da matarsa cewa za ta haifi ɗa. Da Manowa ya sami wannan albishir, ya yi addu’a yana cewa: “Ya Ubangiji, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.” (Littafin Mahukunta 13:8) Iyaye, menene za ku koya daga misalin Manowa?
Abin da Ya Sa Ake Bukatar Taimakon Allah a Yanzu
3. Me ya sa taimakon Allah wajen renon yara yake da muhimanci musamman ma a yau?
3 Fiye da dā iyaye suna bukatar taimakon Jehobah domin su yi renon ’ya’yansu. Me ya sa? Domin an jefo Shaiɗan da mala’ikunsa zuwa duniya. ‘Kaitonki, ke ƙasa,’ in ji Littafi Mai Tsarki, “don Iblis ya sauko gare ku da matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.” (Wahayin Yahaya 12:7-9, 12) “Kamar zaki mai ruri,” Littafi Mai Tsarki ya yi bayani, Shaiɗan “yana neman wanda zai lanƙwame.” (1 Bitrus 5:8) Galibi zakuna suna farautar dabba mai rauni, ko kuma ɗan ƙarami. Cikin hikima, iyaye Kiristoci suke zuba wa Jehobah idanu domin ja-gora wajen kāre ’ya’yansu. Kana yin ƙoƙari kuwa ka kāre ’ya’yanka?
4. (a) Idan da zaki mai ruri a unguwa, menene ya kamata iyaye su yi? (b) Menene yara suke bukata domin kāriya, ta yaya haka zai kāre rai?
4 Idan ka sani cewa da zaki da ya kuɓuce a unguwarku, kāre ’ya’yanka zai kasance abin damuwa a gare ka. Shaiɗan mafarauci ne. Yana ƙoƙari ya lalata mutanen Allah, ta haka ya sa ba su cancanci yardar Allah ba. (Ayuba 2:1-7; 1 Yahaya 5:19) Yara ba su da wuyar kamawa. Domin su guje wa tarkon Iblis, dole ne yara su san Jehobah kuma su yi masa biyayya. Sani na Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci. “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko,” in ji Yesu. (Yahaya 17:3) Bugu da ƙari, yara suna bukatar hikima—iya fahimta da kuma yin amfani da abin da suka koya. Tun da “hikima takan yi wa mai ita [kariya],” ku iyaye kuna bukatar ku cusa gaskiya a zukatan ’ya’yanku. (Mai Hadishi 7:12) Ta yaya za ku yi haka?
5. (a) Ta yaya za a koyar da hikima? (b) Ta yaya Karin Magana ya kwatanta tamanin hikima?
5 Za ka iya, kuma ya kamata, ka karanta wa ’ya’yanka Kalmar Allah. Amma taimaka musu su ƙaunaci Jehobah yana bukatar fiye da haka, yana bukatar su fahimta. Alal misali: Ana iya gaya wa yaro kada ya ƙetare hanya sai ya dubi dama da hagu. Duk da haka, wasu yara ba sa yin biyayya. Me ya sa? Ba a yi bayanin abin da yake faruwa idan mota ta bugi mutum da zai nuna wa yaron haɗarin haka, da kuma kauce wa “wauta” da za ta iya haddasa irin wannan haɗari. Koyar da hikima tana ɗaukan lokaci, kuma tana bukatar haƙuri. Amma hikima tana da tamani! “Hikima takan sa ka ji daɗin zama,” in ji Littafi Mai Tsarki, “ta kuma bi da kai lafiya a zamanka. Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da ’ya’ya.”—Karin Magana 3:13-18; 22:15.
Koyarwa da Ke Ba da Hikima
6. (a) Me ya sa yara sau da yawa suke abin da ba daidai ba? (b) Wace kokawa ce ake yi?
6 Sau da yawa yara suna yin abin da ba daidai ba, ba domin ba a koyar da su ba, amma domin koyarwar ba ta shiga zuciyarsu ba—halinsu. Iblis yana kokawa ya mallaki zukatan yara. Tarkonsa shi ne ya ga duniya ta rinjaye su. Yana kuma amfani da yanayin da suka gāda na son yin abin da ba shi da kyau. (Farawa 8:21; Zabura 51:5) Iyaye suna bukatar su fahimci cewa yana kokawa ƙwarai na neman ya mallaki zukatan ’ya’yansu.
7. Me ya sa ake bukatar fiye da gaya wa yaro kawai abin da yake da kyau da abin da ba shi da kyau?
7 Sau da yawa iyaye suna gaya wa yaro abin da ke mai kyau da abin da ba shi da kyau, suna tsammanin sun tarbiyyar da shi. Za su gaya wa yaron yin ƙarya ba shi da kyau, da sata, da yin jima’i da wanda ba su aura ba. Amma, yaron yana bukatar abin da zai motsa shi ya yi biyayya fiye da cewa iyayensa ne kawai suka faɗi haka. Waɗannan dokokin Jehobah ne. Ya kamata yaron ya fahimci cewa hikima ce ya yi wa dokokin Jehobah biyayya.—Karin Magana 6:16-19; Ibraniyawa 13:4.
8. Wace irin koyarwa ce take ba da hikima?
8 Girman sararin samaniya, bambancin abubuwa masu rai, canjin yanayi, dukan irin waɗannan abubuwa za su iya taimakon yaro ya fahimci cewa da Mahalicci mai hikima. (Romawa 1:20; Ibraniyawa 3:4) Bugu da ƙari, ya kamata a koyar da yaron cewa Allah yana ƙaunarsa kuma ya yi tanadi ta wajen hadayar Ɗansa domin ya ba shi rai madawwami kuma zai iya sa Allah ya yi farin ciki ta wajen yi masa biyayya. Ta haka, wataƙila yaron zai so ya bauta wa Jehobah, duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen Iblis ya hana shi.—Karin Magana 22:6; 27:11; Yahaya 3:16.
9. (a) Menene koyarwa mai kāre rai take bukata? (b) Menene aka umurci ubanni su yi, kuma menene wannan ya ƙunsa?
9 Irin koyarwa da take kāre yaro kuma take motsa shi ya yi abin da ke mai kyau tana bukatar lokaci, kula da kuma shiri. Yana bukatar iyaye su bi ja-gorar Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku ubanni, ku goye su [’ya’yanku] da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.” (Afisawa 6:4) Menene wannan take nufi? “Tarbiyya,” a ainihin Hellenanci, tana nufin “saka zuciya a ciki.” Saboda haka, an aririci ubanni ne su saka zuciyar Jehobah a cikin ’ya’yansu. Lalle wannan zai kasance kāriya ga yara! Idan yara suka kasance da tunanin Allah, wato yadda yake tunani, aka saka a zukatansu, an kāre su daga yin abin da ba shi da kyau.
Sha’awar da Ƙauna ta Motsa
10. Domin ka koyar da yaronka da kyau, menene yake da muhimmanci ka sani?
10 Domin ka cim ma muradinka na renon ’ya’yanka da kyau, ya kamata ƙauna ta motsa ka ka yi ƙoƙari. Wata aba da take da muhimmanci ita ce sadarwa. Ka bincika abin da yake faruwa a rayuwar ɗanka ko ’yarka da kuma ra’ayinsa game da wannan. A lokaci da ya dace, ka sa ya faɗi cikinsa. Wani lokaci abin da ya ce sai ya ba ka mamaki.a Ka yi hankali kada ka yi abin da zai wuce gona da iri. Maimakon haka, ka saurare shi da juyayi da ƙauna.
11. Ta yaya iyaye za su iya saka zuciyar Allah a cikin ’ya’yansu?
11 Hakika, wataƙila ka karanta wa yaronka daga Littafi Mai Tsarki game da dokar Allah da ta hana lalata, ƙila sau da yawa. (1 Korantiyawa 6:18; Afisawa 5:5) Wannan wataƙila ya nuna wa ’ya’yanka abubuwa da suke faranta wa Jehobah rai da waɗanda ba sa faranta masa rai. Duk da haka, saka zuciyar Jehobah a yaron yana bukatan wasu abubuwa. Yara suna bukatar taimako domin su yi tunani game da tamanin dokokin Jehobah. Suna bukatar su tabbata cewa dokokinsa daidai ne kuma suna da kyau, da kuma cewa yi musu biyayya daidai ne kuma abu ne mai kyau da mutum ya kamata ya yi. Sai ka sa ’ya’yanka sun yi tunani bisa Nassosi saboda su karɓi ra’ayin Allah, tukuna za a ce ka saka ‘zuciyarsa’ a ta su.
12. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa ɗansu ya san ra’ayin da ya dace game da jima’i?
12 Sa’ad da kake magana game da jima’i, kana iya tambaya, “Kana tsammanin bin dokar Jehobah, kada a yi jima’i kafin a yi aure zai hana mutum farin ciki ne?” Ka ƙarfafa ɗanka ya ba da bayani. Bayan ka maimaita tanadi mai ban sha’awa na Allah wajen haifan ɗan, kana iya tambaya, “Kana tsammanin Allahnmu mai ƙauna zai ba da doka domin ya hana mu farin ciki ne? Ko kana tsammani dokokinsa domin su faranta mana rai ne su kāre mu?” (Zabura 119:1, 2; Ishaya 48:17) Ka bincika tunanin ɗanka game da wannan batu. Sai ka jawo hankalinsa ga misalai game da yadda lalata ya kai ga baƙin ciki da damuwa. (2 Sama’ila 13:1-33) Ta wajen sa ɗanka ya yi tunani kuma ya fahimci ra’ayin Allah, ka riga ka yi ƙoƙari wajen saka zuciyar Allah a ta shi. Amma, har yanzu da wani abu da za ka iya yi.
13. Wane fahimi ne zai motsa yaro ya yi biyayya ga Jehobah?
13 Cikin hikima, ba za ka koya wa ɗanka kawai sakamakon rashin biyayya ga Jehobah ba amma kuma za ka yi bayani yadda rayuwarmu take shafar Jehobah. Ka nuna wa ɗanka daga Littafi Mai Tsarki cewa za mu iya ɓata wa Jehobah rai sa’ad da muka ƙi mu yi nufinsa. (Zabura 78:41) Kana iya tambaya, “Me ya sa ba za ka so ka ɓata wa Jehobah rai ba? Kuma ka yi bayani cewa: “Da’awar abokin gaban Allah Shaiɗan cewa muna bauta wa Jehobah ne kawai domin son kai ba domin muna ƙaunarsa ba ne.” Sai ka faɗi yadda ta wajen kasancewa da aminci Ayuba ya faranta wa Allah rai, ta haka ya ba da amsa ga zargin ƙarya na Shaiɗan. (Ayuba 1:9-11; 27:5) Yaronka yana bukatar ya fahimci cewa, faranta wa Jehobah rai da kuma baƙanta masa rai ya dangana ga halinsa. (Karin Magana 27:11) Wannan da kuma wasu darussa masu muhimmanci ana iya koya wa yaro ta wajen amfani da wannan littafin Ka Koya Daga Wurin Babban Malami.b
Sakamako Mai Kyau
14, 15. (a) Waɗanne darussa ne daga littafin nan Malami suka motsa yara? (b) Waɗanne sakamako masu kyau ka samu daga karanta littafin? (Ka dubi akwati a shafi na 30–31.)
14 Kakan wani yaro ɗan shekara bakwai daga birnin Croatia da yake karanta masa littafin nan Malami ya rubuta cewa yaron ya ce masa: “Mamata tana cewa in yi abu, amma ni ba na so in yi.’ Sai na tuna babin nan ‘Biyayya Tana Kāre Ka’ sai na je na gaya mata cewa zan yi mata biyayya.” Game da babin na “Abin da Ya Sa Bai Kamata Mu Yi Ƙarya ba,” wasu ma’aurata daga Florida ta Amirka, suka ce: “Da tambayoyi da suke sa yara su buɗe zukatansu kuma su yarda da laifinsu da idan ba haka ba ba za su yarda ba.”
15 Littafin nan Malami yana da hotuna fiye da 230, da kuma kwatanci ga kowane hoto ko kuma tarin hotuna. “Sau da yawa ɗana sai ya zuba wa hoton idanu ba ya so ya juya shafin,” in ji wata uwa mai godiya. “Hotunan suna da kyau kuma suna koyar da nasu darassi, ko kuma su sa yara su yi tambaya. A wani hoto inda yaro yake kallon telibijin a ɗaki mai duhu, ɗana ya yi tambaya, ‘Mama, menene wannan yaron yake yi?’ da muryar da ya nuna cewa ya sani da abin da ba daidai ba.” Kwatancin hoton ta ce: “Waye zai iya ganin dukan abin da muke yi?”
Ilimi Mai Muhimmanci a Yau
16. Menene yake da muhimmanci a koyar da yara a yau, kuma me ya sa?
16 Yara suna bukatar su san amfani da ya dace da wanda bai dace ba da jikinsu. Amma, yin magana game da wannan ba shi da sauƙi. Wata marubuciyar jarida ta lura cewa ita ta girma ne a lokacin da yin amfani da kalmomin da suke kwatanta al’aura laifi ne. Game da koyar da ’ya’yanta ta rubuta: “Dole ne sai na rufe wa kunya ido.” Hakika, idan domin kunya iyaye suka guji batun jima’i, ba ya kāre yaro. Masu ɓata yara suna amfani da jahilcin yara. Ka Koya Daga Wurin Babban Malami ya tattauna wannan batun da daraja. Sanar da yara game da jima’i ba ya ɓata yara, ƙin yin haka ne zai iya sa a ɓata su.
17. Ta yaya littafin nan Malami yake taimakon iyaye su koyar da ’ya’yansu game da jima’i?
17 A babi na 10, sa’ad da ake tattaunawa game da miyagun mala’iku da suka zo duniya suka haifi ’ya’ya, an tambayi yaron: “Menene ka sani game da jima’i?” Littafin ya ba da misali masu sauƙi masu kyau. Daga baya, a babi na 32 ya yi bayani game da yadda za a kāre yara daga malalata. Wasiƙu masu yawa sun nuna cewa irin wannan koyarwa tana da muhimmanci. Wata ta rubuta: “Makon da ya shige yarona Javan ya je ganin likitan yara, ta tambaye shi ko mun tattauna da shi yadda ake amfani da al’aura a yadda ya dace. Domin mun yi haka da sabon littafinmu ya burge ta ƙwarai.”
18. Ta yaya littafin nan Malami ya tattauna sara wa alamu na ƙasa?
18 Wani babi kuma ya yi magana game da labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na Ibraniyawa uku matasa Shadrak, Meshak, da Abed-nego, waɗanda suka ƙi su yi sujada ga gunkin da yake wakiltan ƙasar Babila. (Daniyel 3:1-30) Wasu ba za su ga nasaba tsakanin yi wa gunki sujada da kuma sara wa tuta ba, kamar yadda yake a littafin nan Malami. Amma, ka lura da abin da mawallafi Edward Gaffney ya ce a wani ganawa da ya yi da jaridar U.S. Catholic. Ya ce sa’ad da ’yarsa ta gaya masa ta koyi “sabuwar addu’a a makaranta” a ranarta ta farko a makarantar, ya ce mata ta yi addu’ar. “Ta ɗora hannunta a kirjinta,” in ji Gaffney, “ta fara da gaba gaɗi, ‘Na yi alkawarin cewa zan bauta wa tuta. . . ’ ” Ya ci gaba da cewa: “Farat ɗaya sai ya faɗo mini. Gaskiyar Shaidun Jehobah. Da akwai wani ɓangaren ruhaniya ta ƙasa da ake yaɗawa a makarantunmu tun yara suna ƙanana—aminci marar iyaka ga ƙasa.”
Ta Cancanci Dukan Ƙoƙari
19. Wane lada za a samu daga koyar da yara?
19 Hakika, koyar da ’ya’yanmu ta cancanci dukan ƙoƙari da za mu yi. Wata uwa ta yi hawaye sa’ad da ta sami wasiƙa daga wurin ɗanta a Kansas ta Amirka. Ya rubuta: “Ina ganin na yi sa’a ƙwarai da na sami reno da ya taimake ni na kasance cikin hankalina da kuma daidaito. Ke da baba hakika kun cancanci yabo.” (Karin Magana 31:28) Ka Koya Daga Wurin Babban Malami zai iya taimakon iyaye su koyar da ’ya’yansu saboda su kāre wannan kyauta mai tamani.
20. Me ya kamata iyaye su riƙa tunawa kullum, kuma yaya wannan ya kamata ya shafe su?
20 ’Ya’yanmu sun cancanci dukan lokaci, kula, da kuma ƙoƙari da za mu iya bayarwa. Babu wuya za su girma. Ku yi amfani da dukan zarafi ku kasance tare da su kuma ku taimake su. Ba za ku yi da na sani ba. Za su ƙaunace ku. Ku riƙa tunawa kullum cewa yaranku kyauta ne daga Allah. Kyauta ne masu tamani! (Zabura 127:3-5) Ku kula da su, tamkar za ku ba da amsa ga Allah game da yadda kuka rene su, hakika za ku ba da amsa.
[Hasiya]
a Alal misali, wani marubuci a New York City mai sunan Bill O’Reilly ya yi ƙaulin wani mai ba da rahoto da ya lura cewa: “Jima’i shi ne batu na ɗaya a tsakanin ’yan makaranta a yanzu. ’Yan shekara goma sun san kome game da shi da dā babu yaro ɗan ƙarami haka da zai fahimta ko hankalinsa ya ɗauka.”—New York Daily News, 22 ga Satumba, 2003.
b Shaidun Jehobah ne suka wallafa. Ka dubi babi na 40, “Yadda Za a Faranta wa Allah Rai.”
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa iyaye suke bukatar su kāre ’ya’yansu musamman ma a yanzu?
• Wace irin koyarwa ce take ba da hikima?
• Waɗanne abubuwa ne suke da muhimmanci ka tattauna da ’ya’yanka a yau?
• Ta yaya littafin nan Malami ya taimaki iyaye su koyar da ’ya’yansu?
[Box/Hotuna a shafuffuka na 30, 31]
Littafi Don Kowa
An tsara Ka Koya Daga Wurin Babban Malami domin ya taimaki iyaye ko kuma wasu manyan mutane su karanta su tattauna abin da Yesu Kristi ya koyar da yara. Amma kuma, manya da suka karanta littafin da kansu sun furta godiyarsu domin abin da suka koya.
Wani mutum a Texas, na Amirka, ya ce: “Ka Koya Daga Wurin Babban Malami yana da sauƙi kuma yana motsa mu ko shekara nawa muke da shi—har ni ma da nake ɗan shekara 76. Na gode muku ƙwarai, ni ma da na bauta wa Jehobah tun ina yaro.”
Wata mai karatu daga Landan ta Ingila ta ba da rahoto: “Kyawawan kwatanci tabbatacce ne da za su jawo hankali iyaye da yara. Yadda aka tsara tambayoyi abin sha’awa ne, kuma yana da kyau yadda aka yi magana a kan wasu batutuwa, kamar na Babi na 32, ‘Yadda Aka Kāre Yesu.’ ” Ta kammala da cewa: “Ko da yake ainihi an tsara wannan littafin domin yaran Shaidun Jehobah ne, na tabbata cewa malamai da wasu manya za su yi farin ciki ƙwarai su sami wannan littafin. Zan yi amfani da shi a yanzu da kuma lokaci mai zuwa.”
Wata mace daga Massachusetts ta Amirka, ta yi magana game da “hotuna” masu kyau da ke ciki. Ta lura cewa: “Ko da yake littafin nan domin yara ne, abubuwa da aka tattauna za su taimake mu mu manya mu yi tunani game da dangantakarmu da Jehobah.”
“Littafi mai ban sha’awa!” in ji wata mace daga Maine ta Amirka. “Ba kawai domin yara ba ne amma domin dukan ’ya’yan Jehobah ne. Ya taɓa mini zuciya ya motsa ni saboda haka na sami salama. Na kusaci Jehovah domin Ubana ne. Ya sanyaya mini zuciya daga baƙin ciki na shekaru masu yawa kuma ya bayyana nufinsa sarai.” Ta kammala da cewa: “Ina gaya wa kowa, ‘Don Allah ku karanta.’ ”
Wata mace daga Kyoto ta Japan, ta ba da rahoto cewa sa’ad da take karanta shi ga jikokinta, suna tambayoyi kamar haka: “ ‘Menene wannan yaron yake yi? Me ya sa ake tsawata wa wannan yarinyar? Menene wannan mamar take yi? Wannan zakin kuma fa?’ Yana koyar da abubuwa da muke so, saboda haka nake sonsa fiye da dukan wani littafi da yake laburare.”
Wani Uba daga Calgary ta Kanada, ya ce da ya sami littafin nan da nan ya fara karanta wa ’yarsa ’yar shekara shida da kuma ɗansa ɗan shekara tara. “Sakamakon haka abin sha’awa ne.” Ya ba da rahoton cewa “ ’ya’yana suna sauraro kuma suna ba da amsa daga zukatansu. Suka ji nazarin ya shafe su, kuma ya ba su zarafin su faɗi ra’ayinsu. Sun ci gaba da nuna kuzari, kuma ’yata ta ce tana so ta yi nazari littafin kowane dare.”
Bayan wani nazari, uban ya ce: “Ni da ɗana mun yi ta magana game da Jehobah da kuma nufinsa na awoyi. Yana da tambayoyi daga abin da littafin ya ce. Hawaye suka zubo daga idanuna sa’ad da ya ce mini sai da safe kuma ya yi tambaya: ‘Baba, za mu yi taɗi kuwa gobe? Ina da tambayoyi masu yawa kuma ina so in san kome game da Jehobah.’ ”
[Hoto a shafi na 27]
Iyaye menene za ku koya daga misalin Manowa?
[Hoto a shafi na 28]
Yara, menene za ku koya daga misalin Ibraniyawa uku?
[Hoto a shafi na 29]
Hotuna da kwatanci na littafin nan “Malami” kayan aiki ne masu kyau wajen koyarwa
[Hoto a shafi na 29]
Wace ƙarya Hananiya yake yi wa Bitrus?
[Hoto a shafi na 29]
Waye yake ganin dukan abin da muke yi?