Menene Begen Tashin Matattu Yake Nufi A Gare Ka?
‘Kana kuwa ba su isashe, kakan biya bukatarsu duka.’ —Zabura 145:16.
1-3. Wane bege wasu suke da shi don nan gaba? Ka ba da misali.
CHRISTOPHER ɗan shekara tara da wansa da kawunsa da gwaggonsa da yaransu maza biyu sun yi wa’azi na gida gida da safe a hidimarsu ta Kirista kusa da Mancesta ta Ingila. Jaridarmu Awake!, ta ba da bayanin abin da ya faru. “Da rana dukansu suka fita zuwa Blackpool wajen hutu na gaɓar teku don ganin wurare masu kyau. Dukansu shida suna cikin mutane 12 da hatsarin mota ya kashe a take, ’yan sanda sun kwatanta hatsarin da ‘hallaka mai girma.’ ”
2 Daddare kafin bala’in ya faru, iyalin sun halarci Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya, an tattauna batun mutuwa a taron. “Christopher yaro ne mai tunani sosai,” in ji babansa. “Daddaren nan ya yi bayani sosai game da sabuwar duniya da kuma begensa don nan gaba. Sa’ad da muka ci gaba da zancen, sai Chrisopher ya ce: ‘Zama Mashaidin Jehobah na da amfani sosai, ko da mutuwa na kawo baƙin ciki, mun san za mu sake ganin juna a duniya wata rana.’ Babu wani cikinmu da ke wajen da zai yi tsammanin cewa kalmomin nan abin da za a riƙa tunawa ne koyaushe.”a
3 Shekaru da suka shige, a shekara ta 1940, Franz, Mashaidi ɗan Austriya, ya san za a kashe shi don ya ƙi ya yi rashin aminci ga Jehobah. Franz ya rubuta wa mamarsa wasiƙa daga wani kurkuku a Berlin: “Na san cewa idan na yi rantsuwa na [soja], da na yi zunubin da ya dace in mutu. Wannan zai zama mini rashin aminci. Da ba za a tashe ni ba daga matattu. . . . Mamata ƙaunatacciya da dukan ’yan’uwana, yau aka gaya mini abin da zai faru da ni, kada ku firgita, mutuwa ce, gobe da safe za a kashe ni. Allah ya ƙarfafa ni, yadda ya ƙarfafa dukan Kiristoci na gaskiya na dā. . . . Idan kuka kasance da aminci har mutuwa, za mu sake saduwa a tashin matattu. . . . Sai mun sake saduwa.”b
4. Yaya labarai da aka ba da a nan ya shafe ka, menene za mu bincika a gaba?
4 Christopher da Franz sun ba da gaskiya ga begen tashin matattu. Da gaske yake a gare su. Babu shakka waɗannan labaran masu ban tausayi ne! Don mu ƙara nuna godiya ga Jehobah kuma mu ƙarfafa begenmu na tashin matattu, bari mu bincika abin da ya sa za a yi tashin matattu da kuma yadda wannan zai shafe mu ɗaiɗai.
Wahayin Tashin Matattu na Duniya
5, 6. Menene wahayin da manzo Yahaya ya rubuta a Wahayin Yahaya 20:12, 13 ya bayyana?
5 Manzo Yahaya ya ga matattu suna tashiwa a duniya a wahayin da ya gani na abubuwa da za su faru a lokacin Sarautar Alif na Kristi Yesu. Ya ce: “Na ga matattu manya da yara . . . Sai teku ta ba da matattun da ke cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da ke gare su.” (Wahayin Yahaya 20:12, 13) Ko menene matsayinsu—ko “manya” ko kuma “yara”—duk waɗanda suke cikin Hades (Sheol) wato inda matattu suke za su fito. Waɗanda suka mutu cikin teku za su dawo rai a lokacin. Wannan aukuwa mai ban al’ajabi yana cikin nufin Jehobah.
6 Sa’ad da Kristi ya soma sarauta na alif zai kama kuma ya ɗaure Shaiɗan. Shaiɗan ba zai iya yaudarar wani cikin waɗanda aka ta da daga matattu ko kuwa waɗanda suka tsira wa ƙunci mai girma a lokacin sarautarsa ba, ba zai iya kome ba. (Wahayin Yahaya 20:1-3) Shekara dubu za ta yi tsawo ainun a gare ka, amma a wajen Jehobah “kamar kwana ɗaya ne.”—2 Bitrus 3:8.
7. Bisa menene za a yi wa mutum hukunci a lokacin Sarautar Alif na Kristi?
7 Bisa wahayin, Sarautar Kristi ta Alif za ta zama lokacin hukunci. Manzo Yahaya ya rubuta: “Sai na ga matattu manya da yara, tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari’a bisa ga abin da ke rubuce cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi. . . . Aka kuwa yi wa kowa shari’a gwargwadon aikin da ya yi.” (Wahayin Yahaya 20:12, 13) Ya nuna cewa dalilin yin wannan shari’a ba don abin da mutumin ya yi ko kuma bai yi ba kafin ya mutu. (Romawa 6:7) Maimakon haka, game da “littattafai” ne da za a buɗe nan gaba. Ayyukan mutum ne bayan ya koyi abin da ke cikin littattafan zai sa a san ko za a rubuta sunansa a “Littafin Rai.”
“Tashin Rai” ko “Tashin Hukunci”
8. Wane yanayi biyu ne wataƙila waɗanda aka tashe su za su kasance ciki?
8 Da farko a cikin wahayin Yahaya, an kwatanta Yesu yana riƙe da “mabuɗan mutuwa da na Hades.” (Wahayin Yahaya 1:18) Shi ne “Tushen Rai,” na Jehobah, an ba shi iko ya yi wa “rayayyu da matattu” shari’a. (Ayyukan Manzanni 3:15; 2 Timoti 4:1) Ta yaya zai yi haka? Ta wajen ta da waɗanda suka rasu daga matattu. Yesu ya gaya wa taron da yake wa wa’azi: “Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk waɗanda ke kaburbura za su ji murya tasa, su kuma fito.” Ya daɗa cewa: “Waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.” (Yahaya 5:28-30) Wane bege ne maza da mata na dā masu aminci suke da shi?
9. (a) Idan suka dawo a tashin matattu, menene mutane da yawa za su koya? (b) Wane aikin ilimantarwa za a yi?
9 Sa’ad da waɗannan amintattu na dā suka dawo a tashin matattu, ba da daɗewa ba za su fahimci cewa alkawari da suke begensa ya kasance da gaske. Za su so su san ko waye Zuriyar macen Allah da aka ambata a cikin annabci na farko na Littafi Mai Tsarki a Farawa 3:15! Za su yi farin cikin jin cewa wannan Almasihu, Yesu da aka yi alkawarinsa ya kasance da aminci har mutuwa, ya ba da ransa hadayar fansa! (Matiyu 20:28) Waɗanda suke marabtarsu za su yi farin cikin taimakonsu su fahimci cewa wannan tanadin hadayar fansa alherin Jehobah ne da kuma jinƙansa. Babu shakka waɗanda aka tashe su daga matattu za su yabi Jehobah sa’ad da suka gane abin da Mulkin Allah yake cimmawa don a cika nufin Jehobah game da duniya. Za su sami zarafin nuna amincinsu ga Ubansu na samaniya mai ƙauna da kuma Ɗansa. Kowa da ke rayuwa lokacin zai yi farin cikin sa hannu a aikin ilimantarwa da ake bukata don a koyar da mutane masu yawa da suke fitowa daga kabari, su ma za su bukaci su amince da fansa da Allah ya yi tanadinsa.
10, 11. (a) Wane zarafi sarauta na Alif zai ba dukan mutane da suke duniya? (b) Yaya ya kamata wannan ya shafe mu?
10 Sa’ad da Ibrahim ya tashi zai yi farin cikin ganin cewa rayuwa a ƙarƙashin sarautar “birnin” nan da yake begensa ya kasance da gaske. (Ibraniyawa 11:10) Ayuba na dā mai aminci zai yi farin ciki sosai idan ya san cewa tafarkin rayuwarsa ya ƙarfafa sauran bayin Jehobah da suka fuskanci gwaji ga amincinsu! Daniyel zai so ya san game da cikar annabce annabce da aka hure shi ya rubuta!
11 Hakika, duk waɗanda za su yi rayuwa a sabuwar duniya, ko ta tashin matattu ko ta tsira wa ƙunci mai girma, za su koyi abubuwa da yawa game da nufin Jehobah don duniya da kuma mazaunanta. Begen rayuwa har abada da yabon Jehobah har fil azal babu shakka zai sa tsarin ilimantarwa na Alif abin farin ciki. Amma ya dangana a kan abin da muka yi ɗaiɗai ne sa’ad da muka koyi abin da ke cikin littattafan. Za mu aikata abin da muka koya kuwa? Shin za mu yi bimbini kuma mu yi amfani da bayani da zai ƙarfafa mu, mu yi tsayayya da ƙoƙarin Shaiɗan na ƙarshe don ya janye mu daga gaskiya?
12. Menene zai taimaki kowanne mutum ya sa hannu sosai a aikin ilimantarwa da kuma mai da duniya ta zama aljanna?
12 Bai kamata mu manta da albarka mai ban al’ajabi da yin amfani da hadayar fansa na Kristi zai kawo ba. Waɗanda aka tashe su daga matattu ba za su yi irin rashin lafiya ko naƙasa da ake yi yanzu ba. (Ishaya 33:24) Lafiyayyen jiki da begen zaman lafiya zai sa dukan mazaunan sabuwar duniya su sa hannu sosai a aikin ilimantarwa na koya wa biliyoyi da aka tashe su hanyar yin rayuwa. Waɗannan mazauna za su kuma sa hannu a aikin da ba a taɓa yi ba a duniya—na mai da dukan duniya aljanna ga yabon Jehobah.
13, 14. Don me za a saki Shaiɗan a gwaji na ƙarshe, wane sakamako ne za mu samu ɗaiɗai?
13 Idan aka saki Shaiɗan don ya yi gwadi na ƙarshe, zai yi ƙoƙari ya yaudari mutane. Bisa ga Wahayin Yahaya 20:7-9, dukan ‘al’ummai da aka yaudara’ ko kuma rukunin mutane da suka bi tasirin Shaiɗan za a yi musu shari’ar halaka: ‘Wuta za ta zubo daga sama ta lashe su.’ Wannan halakar za ta sa halaka waɗanda aka ta da daga matattu a sarautar Alif ya zama tashin hukunci. Akasarin haka, amintattu da aka tashe su za su sami kyautar rai madawwami. Hakika, nasu zai zama “tashin rai.”—Yahaya 5:29.
14 Ta yaya begen tashin matattu zai ƙarfafa mu a yanzu ma? Menene dole mu yi don mu tabbata mun sami amfaninsa a nan gaba?
Darussa da Za Mu Koya Yanzu
15. Ta yaya imani da tashin matattu zai taimake mu yanzu?
15 Mai yiwuwa ka yi rashin wanda kake ƙauna kwanan nan, kuma kana ƙoƙari ka daidaita damuwa da wannan rashin ya kawo. Begen tashin matattu zai taimake ka ka kasance da kwanciyar rai da ƙarfi da wasu ba su da shi domin ba su san gaskiya ba. Bulus ya yi wa Tasalonikawa ta’aziyya yana cewa: “Ba mā so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran ke yi, marasa sa zuciya.” (1 Tasalonikawa 4:13) Kana ganin kanka a cikin sabuwar duniya, kuma kana ganin ana tashin matattu? Idan haka ne, ka ƙarfafa kanka yanzu ta yin bimbini game da begen saduwa da waɗanda kake ƙauna.
16. Yaya wataƙila za ka ji sa’ad da aka yi tashin matattu?
16 Wataƙila a yanzu kana shan wahalar sakamakon tawayen Adamu, wataƙila ta wajen ciwo. Kada ka ƙyale baƙin cikin wannan ya sa ka manta da farin cikin begen tashin matattu da kuma na dawowa rai da cikakkiyar lafiya da kuzari a cikin sabuwar duniya. Sa’ad da idanunka suka buɗe kuma ka ga mutane suna farin cikin suna maka maraba, babu shakka za ka gode wa Allah domin alherinsa.
17, 18. Waɗanne darussa biyu masu muhimmanci ya kamata mu tuna?
17 Kafin lokacin, ka yi la’akari da darussa biyu da ya kamata mu tuna. Na ɗaya, yana da muhimmanci mu bauta wa Jehobah yanzu da dukan zuciyarmu. Ta yin koyi da Shugabanmu Kristi Yesu, sadaukar da kanmu na nuna muna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu. Idan hamayya ko kuma tsanantawa ya sa mun yi hasarar mallakarmu ko kuma ’yancinmu, za mu dage a bangaskiyarmu ko wane irin gwaji ne ya same mu. Idan masu hamayya suka yi mana barazana da mutuwa, begen tashin matattu zai sanyaya mana zuciya kuma ya ƙarfafa mu mu kasance da aminci ga Jehobah da kuma Mulkinsa. Hakika, yin himma ga aikin wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa zai sa mu sami albarka na har abada da Jehobah zai yi wa adalai.
18 Yadda muke bi da gwaji da ajizancinmu yake jawowa, shi ne darassi na biyu. Abin da muka sani game da tashin matattu da godiya ga alherin Jehobah na ƙarfafa mu mu dage a bangaskiyarmu. Manzo Yahaya ya yi kashedi: “Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da ke cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da ke duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” (1 Yahaya 2:15-17) Ba za mu so abubuwan duniya masu jan hankali ainun ba sa’ad da muka gwada su da “rai wanda yake na hakika.” (1 Timoti 6:17-19) Idan aka jarrabe mu mu yi lalata za mu yi tsayayya. Ya kamata mu san cewa idan muka ci gaba da yin abin da ke ɓata wa Jehobah rai kuma muka mutu kafin Armageddon, za mu kasance cikin yanayin waɗanda ba su da begen tashin matattu.
19. Bai kamata mu manta da wace gata mai girma ba?
19 Fiye da kome, kada mu manta da gata mai girma na faranta wa Jehobah rai yanzu da kuma har abada. (Karin Magana 27:11) Idan muka kasance da aminci har mutuwa ko kuma muka ci gaba da shi har ƙarshen wannan zamani, za mu nuna wa Jehobah wanda muke goyon bayansa a batun ikon mallakar dukan sararin samaniya. Zai zama abin farin ciki idan muka yi rayuwa cikin Aljanna ta duniya ta wajen tsira wa ƙunci mai girma ko kuma mu’ujizar tashin matattu!
Biyan Bukatarmu
20, 21. Menene zai taimake mu mu kasance da aminci ko idan muna da tambayoyi da ba a amsa ba game da tashin matattu? Ka ba da bayani.
20 Tattaunawarmu a kan tashin matattu bai amsa dukan tambayoyinmu ba. Yaya Jehovah zai yi da waɗanda suka yi aure kafin su mutu? (Luka 20:34, 35) Za a yi tashin matattu a wuraren da mutane suka mutu ne? Waɗanda suka mutu za su dawo rai kusa da gidajen iyalansu ne? Da tambayoyi da yawa game da tashin matattu da ba a amsa ba. Duk da haka, mu riƙa tunawa da kalmomin Irmiya: “Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa, da wanda ke nemansa kuma. Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa.” (Makoki 3:25, 26) A lokacin da Jehobah ya ga ya dace, za a amsa dukan tambayoyinmu yadda za mu gamsu. Me ya sa za mu tabbata da hakan?
21 Ka yi bimbini a kan hurarren kalmomin mai zabura sa’ad da ya rera wa Jehobah: “Yana kuwa ba su isashe, yakan biya bukatarsu duka.” (Zabura 145:16) Sa’ad da muke girma abubuwa da muke so suna canjawa. Ba ma son abin da muke so sa’ad da muke yara. Abubuwan da muke fuskanta da kuma waɗanda muka sa rai a kai na shafan ra’ayinmu game da rayuwa. Duk da haka, ko menene da ya dace da muke so a sabuwar duniya, Jehobah babu shakka zai biya mana muradinmu.
22. Me ya sa muke da ƙarfafan dalili na yabon Jehobah?
22 Abin da yake da muhimmanci yanzu shi ne kowannen mu ya kasance da aminci. “Abin da ake bukata ga mai riƙon amana, a same shi amintacce.” (1 Korantiyawa 4:2) Mu wakilai ne na bishara mai ɗaukaka na Mulkin Allah. Shelar wannan bishara ga dukan waɗanda muka sadu da su da himma zai sa mu sami rai. Koyaushe muna tuna cewa “sa’a, da tsautsayi” sukan sami kowannenmu. (Mai Hadishi 9:11) Don ka rage alhini da wannan rayuwa ke kawowa, ka dage ga bege mai ɗaukaka na tashin matattu. Idan kamar za ka mutu kafin Kristi ya soma Sarautarsa na Alif, tuna cewa sauƙi zai zo zai ƙarfafa ka. A lokacin da Jehobah ya ga ya dace za ka maimaita kalmomin da Ayuba ya yi ga Mahalicci: “Za ka yi kira, ni kuwa zan amsa.” Yabo ya tabbata ga Jehobah wanda yake son ya maido da dukan waɗanda yake tunawa da su zuwa rai!—Ayuba 14:15.
[Hasiya]
a Dubi Awake! 8 ga Yuli, 1988 shafi na 10, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafi na 662, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Ka Tuna?
• A kan me za a yi wa mutane shari’a a lokacin sarautar Shekara Dubu?
• Me ya sa wasu za su yi “tashin rai” wasu kuma “tashin hukunci”?
• Ta yaya begen tashin matattu zai sanyaya mana zuciya?
• Ta yaya kalmomin Zabura 145:16 za su taimake mu mu bi da amsoshi da ba amsa ba game da tashin matattu?
[Hotuna a shafi na 29]
Ta yaya imani ga tashin matattu zai taimake mu a yanzu?