Babi Na Tara
Ikon Begen Tashin Matattu
1. Idan babu bege na tashin matattu, me zai kasance yanayin matattu?
KA TAƁA rashin wasu da kake ƙauna? Idan babu tashin matattu, babu begen sake ganinsu kuma. Za su kasance cikin yanayin da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta da ya ce: “Amma matattu ba su san kome ba, . . . gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.”—Mai-Wa’azi 9:5, 10.
2. Wane bege mai ban mamaki ne ya yiwu ta wurin tashin matattu?
2 Cikin jinƙai kuwa, ta wurin tashin matattu, Jehovah ya buɗe hanya mai tamani ga mutane da yawa da sun mutu su dawo daga mutuwa su more rai madawwami. Wannan yana nufin cewa muna iya kasancewa da bege mai daɗaɗa zuciya cewa wata rana, cikin sabuwar duniya ta Allah, za mu sake haɗuwa da waɗanda muke ƙauna da suka mutu.—Markus 5:35, 41, 42; Ayukan Manzanni 9:36-41.
3. (a) A waɗanne hanyoyi ne tashin matattu ya kasance da muhimmanci a cika nufin Jehovah? (b) Yaushe ne musamman bege na tashin matattu ke kasancewa tushen ƙarfi gare mu?
3 Saboda tashin matattu, ba ma bukatar kasancewa da tsoron mutuwa. Jehovah zai iya ƙyale Shaiɗan ya jaraba mugun tuhumarsa yadda ba zai kawo lahani na dindindin ba ga bayinsa masu aminci, na cewa “dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayuba 2:4) Yesu ya yi aminci ga Allah har mutuwarsa, saboda haka Allah ya ta da shi zuwa rai a samaniya. Domin haka, Yesu ya ba da darajar kamiltaccen hadayar ransa na mutum a gaban kursiyin Ubansa a sama, da albarkar rai na har abada dominmu. Ta wurin tashin matattu, waɗanda suke na “ƙaramin garke,” da suke magāda tare da Kristi, suke da begen haɗuwa da shi cikin Mulki na samaniya. (Luka 12:32) Ga wasu kuma, da akwai bege na tashin matattu zuwa rai na har abada a aljanna a duniya. (Zabura 37:11, 29) Dukan Kiristoci za su samu bege na tashin matattu, tushen ƙarfi “mafificin girman iko” ne yayin da suka fuskanci gwaji da ya kawo su dab da mutuwa.—2 Korinthiyawa 4:7.
Abin da Ya Sa Ya Kasance Tushen Bangaskiyar Kirista
4. (a) A wane azanci ne tashin matattu “koyarwar farko” ce? (b) Menene tashin matattu yake nufi ga duniya gabaki ɗayanta?
4 Tashin matattu, kamar yadda aka faɗa a Ibraniyawa 6:1, 2 (NW ), “koyarwar farko” ce. Ɓangare ne na tushen bangaskiya wanda idan babu shi ba za mu iya zama ƙwararrun Kiristoci ba. (1 Korinthiyawa 15:16-19) Amma, koyarwar Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu sabon al’amari ne ga duniya gabaki ɗayanta. Saboda rashin ruhaniya, mutane da yawa suna ɗaukan wannan rayuwa ita ke nan. Domin haka, suna rayuwa ta biɗan annashuwa. Sai kuma masu addinan al’adu—a ciki da kuma waje da Kiristendam—da suke jin suna da kurwa mara mutuwa. Amma ba a iya daidaita imanin nan da koyarwar Littafi Mai Tsarki ta tashin matattu, domin ba za a bukaci tashin matattu ba idan mutane suna da kurwa marar mutuwa. Ƙoƙarin daidaita koyarwa biyun nan yana rikitarwa maimakon ya ba da bege. Ta yaya za mu taimaki masu zuciyar kirki su san gaskiya?
5. (a) Kafin mutum ya fahimci tashin matattu, me yake bukatar ya sani? (b) Waɗanne nassosi za ka yi amfani da su ka bayyana yanayin matattu? (c) Me za a iya yi idan wani yana amfani da fassarar Littafi Mai Tsarki da kamar ta ɓoye gaskiya game da yanayin matattu?
5 Kafin irin waɗannan su fahimci cewa tashin matattu tanadi ne mai girma, suna bukatar su fahimci gaskiya game da yanayin matattu. Sau da yawa, ana bukatar nassosi kalilan ne kawai don bayyana al’amuran nan ga wanda yake da muradin sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki. (Farawa 2:7; Zabura 146:3, 4; Ezekiel 18:4) Amma, wasu fassara da bayani na Littafi Mai Tsarki sun ɓoye gaskiya game da yanayin matattu. Saboda haka, zai dace a bincika furcin a harshen asali na Littafi Mai Tsarki.
6. Ta yaya za ka iya ka taimake mutum ya fahimci abar da kurwa take nufi?
6 New World Translation ya yi taimako musamman a wannan domin ya yi amfani daidai da kalmar nan na Ibrananci neʹphesh da kuma madaidaiciyar ta a Helenanci psy·kheʹ da ke nufin “kurwa.” A wasu shafuffukan bayani na ƙarshen fassarar nan, an nuna ayoyi da yawa da za a iya samun wannan. Wasu fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa ba su daidaita su fassara kalmomi na asali “kurwa” kawai ba, amma “halitta,” “mutum,” da kuma “rai”; ana iya ce da “neʹphesh ɗina” “ni,” kuma a ce da “neʹphesh ɗinka,” “kai.” Gwada wasu fassarar Littafi Mai Tsarki da New World Translation za ta taimaki sahihan ɗalibai su fahimci furcin kalma ta asali da aka fassara “kurwa” cewa ana amfani da ita ga mutane da kuma dabbobi. Amma waɗannan furcin ba su taɓa nuna cewa kurwa marar ganuwa ba ce, abin da ba za a iya taɓa ta ba, da za ta iya barin jiki a lokacin mutuwa kuma ta ci gaba da rayuwa a wani waje.
7. Yaya za ka bayyana daga Littafi Mai Tsarki yanayin waɗanda suke cikin Sheol? cikin Hades? da cikin Jahannama?
7 New World Translation kuma ya daidaita a yadda ya yi amfani da kalmar nan “Sheol” an bayyana kalmar Ibrananci ta sheʼohlʹ a yadda kuma ya yi amfani da “Hades” don kalmar Helenanci ta haiʹdes da kuma “Jahannama” a Helenanci geʹen·na. Ma’anar “Sheol” ɗaya ce da kalmar nan “Hades.” (Zabura 16:10; Ayukan Manzanni 2:27, NW ) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Sheol da Hades suna nufin kabari makomar ’yan Adam kuma tana da nasaba da mutuwa ce, ba da rai ba. (Zabura 89:48; Ru’ya ta Yohanna 20:13) Nassosi ma sun nuna zaton komowa daga kabari makomar ’yan Adam ta wurin tashin matattu. (Ayuba 14:13; Ayukan Manzanni 2:31) Akasin haka, waɗanda suke Jahannama ba su da wani begen rai a nan gaba kuma, ba a yi zancen cewa kurwa tana rayuwa a nan ba.—Matta 10:28.
8. Ta yaya fahimtar tashin matattu da kyau zai rinjayi hali da kuma ayyukan mutum?
8 Yayin da an bayyana al’amuran nan dalla-dalla, sa’an nan za a iya taimakon mutumin ya fahimci abin da tashin matattu yake nufi a gare sa. Zai soma godiya ga ƙaunar da Jehovah ya nuna da ya yi tanadin nan mai girma. Baƙin cikin waɗanda suka yi rashin wani da suke ƙauna zai iya raguwa domin begen sake saduwa na farin ciki a sabuwar duniya ta Allah. Fahimtar waɗannan al’amura na da muhimmanci a fahimtar ma’anar mutuwar Kristi. Kiristoci na ƙarni na farko sun fahimci cewa ta da Yesu Kristi daga matattu shi ne tushen bangaskiyar Kirista, da yake buɗe hanyar tashin matattu ga wasu. Cikin himma suna yin wa’azi game da ta da Yesu da kuma begen da ya bayar. Saboda haka, a yau waɗanda suka fahimci haka kuma suke godiya ga tashin matattu suna gaya wa wasu gaskiyar nan mai tamani.—Ayukan Manzanni 5:30-32; 10:42, 43.
Yin Amfani da ‘Maƙullin Hades’
9. Yaya Yesu ya yi amfani da “maƙullai na mutuwa da na Kabari” da farko?
9 Dukan waɗanda za su yi tarayya da Kristi cikin Mulkinsa na samaniya dole ne su mutu. Amma sun san tabbaci da ya ba su da ya ce: “Na mutu, ga shi kuwa, ina da rai har abada, ina kuwa da maƙullai na mutuwa da na Kabari.” (Ru’ya ta Yohanna 1:18) Menene yake nufi? Yana magana ne game da abin da shi da kansa ya fuskanta. Shi ma ya mutu. Amma Allah bai bar shi a Hades ba. A rana ta uku, Jehovah kansa ya ta da shi zuwa rai na ruhu kuma ya mai da shi marar mutuwa. (Ayukan Manzanni 2:32, 33; 10:40) Ƙari ga haka, Allah ya ba shi “maƙullai na mutuwa da na Kabari,” ya yi amfani da su ya kwance wasu daga kabari makoma da kuma sakamakon zunubi na Adamu. Saboda yana da maƙullai ɗin, Yesu ya ta da mabiyansa masu aminci daga mutuwa. Ya ta da shafaffu da suke cikin ikilisiyar da farko, yana ba su kyauta mai tamani na rai marar matuƙa a sama, yadda Ubansa ya ba shi.—Romawa 6:5; Filibbiyawa 3:20, 21.
10. Yaushe ne ake ta da shafaffun Kiristoci masu aminci?
10 Yaushe ne shafaffun Kiristoci masu aminci za su tashi daga matattu zuwa sama? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an riga an fara. Manzo Bulus ya bayyana cewa za a ta da su ‘a bayyanar Kristi,’ bayyanarsa ta fara a shekara ta 1914. (1 Korinthiyawa 15:23) Yayin da shafaffu masu aminci suka gama hidimarsu a duniya yanzu da lokacin bayyanarsa ne, ba sa bukatar su kasance matattu har sai Ubangijinsu ya dawo. Da zarar sun mutu, ana ta da su cikin ruhu, a ‘ƙyaftar ido za su sāke.’ Suna farin ciki sosai, da yake nagargarun ayyukansu suna ‘tafiya tare da su’!—1 Korinthiyawa 15:51, 52; Ru’ya ta Yohanna 14:13.
11. Wane tashin matattu zai kasance ga mutane gabaki ɗaya, kuma yaushe za a fara?
11 Amma ta da matattu na magādan Mulkin zuwa rai a samaniya ba shi ne kawai tashin matattu ba. Da yake an kira shi “tashi na fari” a Ru’ya ta Yohanna 20:6 ya nuna cewa da akwai wani da zai biyo baya. Waɗanda za su amfana daga tashi na bayan nan suna da bege na farin ciki na rai na har abada a aljanna a duniya. Yaushe wannan zai faru? Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa zai kasance bayan—da an kawar da “duniya da sama”—wato, zamanin nan tare da masu mulkinsa. Ƙarshen tsohon zamanin nan ya kusa sosai. Bayan haka, a lokaci da Allah ya sanya, za a fara ta da matattu.—Ru’ya ta Yohanna 20:11, 12.
12. Su wa ke cikin masu aminci da za a ta da zuwa rai a duniya, kuma me ya sa wannan zato ne mai ban sha’awa?
12 Su wa za su kasance cikin tashin matattu na duniya? A tsakanin su zai kasance da bayi masu aminci ga Jehovah tun lokatan dā, maza da mata da domin bangaskiyarsu mai ƙarfi ga tashin matattu, “ba su karɓi fansarsu ba.” Wato, sun ƙi su karya amincinsu ga Allah don su guje wa fin ƙarfi, da mutuwar kadangatse. Zai zama abin farin ciki ne ƙwarai mu san su kuma mu ji daga bakinsu abubuwan da suka faru dalla-dalla da Littafi Mai Tsarki ya ɗan ba da labarinsu! Za a kuma tashi su Habila, mashaidin Jehovah na farko zuwa rayuwa a duniya; Ahnuhu da Nuhu, masu shelar saƙon kashedi na Allah da gaba gaɗi kafin Rigyawa; Ibrahim da Saratu, da suka marabci mala’iku; Musa, wanda aka ba da Doka ta hannunsa a Dutsen Sinai; annabawa masu ƙarfin zuciya irinsu Irmiya, da suka ga halakar Urushalima a shekara ta 607 K.Z.; da Yohanna Mai Baftisma, da kunnensa ya ji Allah ya ce Yesu Ɗansa ne. Ƙari kuma da akwai maza da mata masu aminci da sun mutu cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Ibraniyawa 11:4-38; Matta 11:11.
13, 14. (a) Me zai faru da Hades da kuma matattu na cikinsa? (b) Tashi daga matattu zai haɗa da su wa, kuma me ya sa?
13 A hankali, wasu ban da bayi masu aminci na Allah ma za a ta da su daga matattu, ba za a bar kowa cikin kabari ba. Yadda ba za a bar kome cikin kabari ba zai nuna yadda Yesu ya yi amfani da ‘maƙullai na Hades’ domin bil Adam. An nuna wannan ga manzo Yohanna cikin wahayi, inda ya ga Hades ‘aka jefa cikin ƙorama ta wuta.’ (Ru’ya ta Yohanna 20:14) Menene wannan ke nufi? Yana nufin cewa za a halaka Hades wato kabari, kwata-kwata. Ba zai kasance ba kuma, domin an fitar da dukan matattu daga cikinsa, ban da ta da masu bauta wa Jehovah da aminci, Yesu cikin jinƙai kuma zai ta da marasa adalci ma. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayukan Manzanni 24:15.
14 Babu wani cikin marasa adalcin nan da za a ta da shi domin kawai a yi masa hukuncin kisa. A cikin mahalli na adalci da zai kasance a duk faɗin duniya ƙarƙashin Mulkin Allah, za a taimake su su gyara rayuwarsu ta yi daidai da hanyoyin Jehovah. Wahayin ya nuna cewa za a buɗe “littafin rai.” Saboda haka, za su samu zarafin a rubuta sunayensu a ciki. Za a “yi musu shari’a” bisa abin da suka yi bayan an ta da su daga matattu. (Ru’ya ta Yohanna 20:12, 13) Saboda haka, idan aka bi sakamakonsa, nasu zai iya zama “tashi na rai” kuma ba zai zama dole “tashi na shari’a [ta hukunci ba].”—Yohanna 5:28, 29.
15. (a) Su wa ba za a ta da su daga matattu ba? (b) Yaya ya kamata sanin gaskiya game da tashin matattu ya shafe mu?
15 Amma, ba dukan waɗanda suka taɓa rayuwa kuma suka mutu ne za a ta da su ba. Wasu sun yi zunubi da ba a gafartawa. Irin waɗannan ba a Hades suke ba, a Jahannama suke, inda za su halaka har abada. Wannan zai haɗa da waɗanda aka halaka su a “ƙunci mai-girma” da yanzu ya kusa. (Matta 12:31, 32; 23:33; 24:21, 22; 25:41, 46; 2 Tassalunikawa 1:6-9) Saboda haka, ko da yake Jehovah ya nuna jinƙai ƙwarai a fitowa da matattu daga Hades, bege na tashin matattu ba dalili ne gare mu mu ƙi damuwa da yadda muke rayuwa a yanzu ba. Babu tashin matattu ga waɗanda suka yi tawaye da gangan ga ikon mallaka na Jehovah. Ya kamata wannan sani ya motsa mu mu nuna muna godiya sosai ga alherin Allah ta wajen rayuwa daidai da nufinsa.
Samun Ƙarfafa Daga Bege na Tashin Matattu
16. Ta yaya ne bege na tashin matattu ya kasance tushen ƙarfi mai girma?
16 Mu da muka amince da bege na tashin matattu, mun iya samun ƙarfafa mai yawa daga gare shi. A yanzu, idan muka kusa da ƙarshen ranmu, mun san ba za mu iya hana mutuwa ba har abada—kowacce irin magani muka yi amfani da shi. (Mai-Wa’azi 8:8) Idan muna bauta wa Jehovah cikin aminci a ƙungiyarsa, za mu iya zuba ido ga nan gaba da gaba gaɗi. Mun sani cewa ta wurin tashin matattu, za mu sake more rayuwa, a lokaci na Allah. Kuma lalle zai zama rayuwa mai daɗi! “Hakikanin rai,” haka manzo Bulus ya kira shi.—1 Timothawus 6:19; Ibraniyawa 6:10-12.
17. Me zai taimake mu mu riƙe amincinmu ga Jehovah?
17 Sanin cewa akwai tashin matattu kuma da sanin Wanda shi ne tushen wannan tanadin zai sa mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi. Wannan yana ƙarfafa mu mu zama da aminci ga Allah ko idan masu tsananta mana sun yi barazanar za su kashe mu. Da daɗewa Shaiɗan yake amfani da mutuwar kadangatse don ya riƙe mutane cikin bauta. Amma Yesu ba shi da irin wannan tsoron. Ya kasance da aminci ga Jehovah har mutuwarsa. Ta wurin hadayarsa ta fansa, Yesu ya yi tanadi na ’yantar da wasu daga irin wannan tsoron.—Ibraniyawa 2:14, 15.
18. Menene ya taimaki bayin Jehovah su kasance da irin tarihi na aminci haka?
18 Domin bangaskiyarsu cikin tanadi na hadayar Kristi da kuma cikin tashin matattu, bayin Jehovah suna da tarihi na masu riƙe aminci musamman. Yayin da suke cikin matsi, dole su tabbatar da cewa ‘ba sa ƙaunar ransu’ fiye da yadda suke ƙaunar Jehovah. (Ru’ya ta Yohanna 12:11) Cikin hikima, ba su yasar da ƙa’idodi na Kirista domin su ceci wannan rai na yanzu ba. (Luka 9:24, 25) Sun sani cewa ko sun yi rashin ransu yanzu domin suna ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah da aminci, zai albarkace su ta wurin ta da su daga matattu. Kana da irin bangaskiyar nan? Za ka iya samu, idan kana ƙaunar Jehovah da gaske kuma idan ka fahimci abin da bege na tashin matattu yake nufi da gaske.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Me ya sa mutum yake bukatar ya sami fahimi game da yanayin matattu kafin ya fahimci tashin matattu?
• Su wa za su dawo daga matattu, kuma ta yaya ya kamata wannan sani ya shafe mu?
• Ta yaya bege na tashin matattu ke ƙarfafa mu?
[Hoto a shafuffuka na 84 da 85]
Jehovah ya yi alkawarin cewa za a yi tashin masu adalci da na marasa adalci daga matattu