Ka Gaskata Da Begen Tashin Matattu Kuwa?
“Za a yi tashin matattu.”—AYUKAN MANZANNI 24:15.
1. Me ya sa mutuwa ta kasance da tabbaci?
“BABU abin da ke da tabbaci a duniyar nan kamar mutuwa da haraji.” Wannan kalami da Benjamin Franklin wani fitaccen ɗan siyasa a Amirka ya yi a shekara ta 1789 yana cike da hikima. Duk da haka, wasu mutane ba sa biyan harajinsu. Mutuwa ce take da tabbaci. Ba za mu iya guje wa mutuwa ba, sai da taimako. Ba za a iya guje wa mutuwa ba. Sheol wato kabari na dukan ’yan adam yana cin mutane da muke ƙaunarsu. (Misalai 27:20) Ka yi la’akari da wani abu mai ban ƙarfafa.
2, 3. (a) Me ya sa mutane da yawa ba su fahimci cewa ba kowa ba ne zai mutu? (b) Menene za mu tattauna a wannan talifi?
2 Kalmar Jehobah ta ba mu tabbataccen bege na tashin matattu kuma. Wannan ba mafarki ba ne, kuma babu wani mai iko da zai iya hana Jehobah ya cika wannan begen. A yau mutane da yawa ba su fahimci cewa ba kowa ba ne zai mutu. Me ya sa? Saboda “taro mai-girma” zai tsira daga “babban tsananin,” da za ya zo ba da jimawa ba. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, 14) Za su yi rayuwa da begen rai madawwami a nan gaba. Saboda haka, ba za su mutu ba. Bugu da ƙari, ‘za a kawar da mutuwa.’—1 Korinthiyawa 15:26.
3 Ya kamata mu gaskata da tashin matattu kamar yadda manzo Bulus ya yi, wanda ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Bari mu tattauna tambayoyi uku game da tashin matattu. Na farko, menene ya sa wannan bege tabbatacce ne? Na biyu, ta yaya za ka sami ƙarfafa daga begen tashin matattu? Na uku, ta yaya wannan begen zai shafi rayuwarka yanzu?
Tabbacin Tashin Matattu
4. Ta yaya ne tashin matattu ya kasance da muhimmanci ƙwarai a nufin Jehobah?
4 Akwai wasu abubuwa da suka sa tashin matattu zai tabbata. Fiye da kome, yana da muhimmanci ƙwarai a nufin Jehobah. Ka tuna cewa Shaiɗan ne ya rinjayi ’yan adam zuwa zunubi da mutuwa. Saboda haka, Yesu ya ce ma Shaiɗan: “Shi mai-kisan kai ne tun daga farko.” (Yohanna 8:44) Amma Jehobah ya yi alkawari cewa “macen,” ko kuma ƙungiyarsa mai kama da mace a sama, za ta haifi “zuriya” wanda zai ƙuje “tsohon maciji” a kai, ya halaka Shaiɗan. (Farawa 3:1-6, 15; Ru’ya ta Yohanna 12:9, 10; 20:10) Yadda Jehobah ya bayyana manufarsa game da wannan Ɗa Almasihu sannu a hankali, ya bayyana sarai cewa abin da Ɗan zai yi ya wuce halaka Shaiɗan kawai. Kalmar Allah ta ce: “Dalilin bayyanuwar Ɗan Allah ke nan, shi halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) Jehobah zai yi amfani da Yesu Kristi ya kawar da mutuwa da zunubin da muka gāda daga Adamu wanda Shaiɗan ya rinjaya da farko. Game da wannan, fansar Yesu da tashin matattu suna da muhimmanci.—Ayukan Manzanni 2:22-24; Romawa 6:23.
5. Me ya sa tashin matattu zai ɗaukaka sunan Jehobah?
5 Jehobah ya ƙudura zai ɗaukaka sunansa mai tsarki. Shaiɗan ya ɓata sunan Allah kuma ya ɗaukaka yin ƙarya. Ya yi ƙarya cewa idan Adamu da Hauwa’u suka ci ’ya’yan itace da Allah ya ce kada su ci, ‘lallai ba za su mutu ba.’ (Farawa 2:16, 17; 3:4) Tun daga lokacin, Shaiɗan ya ci gaba da irin wannan ƙarya, kamar su koyarwa ta ƙarya da ta ce kurwa ba ta mutuwa bayan gangan jiki ya mutu. Duk da haka, ta wurin tashin matattu, Jehobah zai fallasa dukan ƙarya da Shaiɗan ya yi. Zai nuna cewa shi ne kaɗai Mai rayarwa Mai bayar da rai.
6, 7. Menene ra’ayin Jehobah game da tashin matattu, kuma ta yaya muka san ra’ayinsa?
6 Jehobah yana marmarin ta da matattu. Littafi Mai Tsarki ya bayyana ra’ayin Jehobah a wannan batu. Alal misali, ka yi la’akari da hurarrun kalaman Ayuba mai aminci: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa? Dukan kwanakin yaƙina sai in jira, har a karɓe ni in huta. Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Ayuba 14:14, 15) Menene ma’anar waɗannan kalamai?
7 Ayuba ya san cewa bayan ya mutu, zai yi barci yana jira na ɗan lokaci. Ya ɗauki lokacin nan ‘kwanakin yaƙi,’ lokacin da zai jira har hutunsa ya zo. A gare shi, hutunsa zai tabbata. Ayuba ya fahimci cewa hutunsa zai zo. Me ya sa? Saboda ya san ra’ayin Jehobah. Jehobah zai yi “marmarin” ganin amintattun bayinsa kuma. Hakika, Allah yana marmarin dawo da dukan mutane masu adalci. Jehobah kuma zai ba waɗansu zarafin yin rayuwa a Aljanna ta duniya har abada. (Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29) Tun da nufin Allah ke nan, wa zai iya hana shi?
8. Ta yaya ne Jehobah ya ‘bada shaidar’ begenmu na nan gaba?
8 Begenmu na gaba ya tabbata a tashin Yesu daga matattu. Sa’ad da Bulus ya yi jawabi a Atina, ya ce: “[Allah] ya sanya rana, inda za ya yi ma duniya duka shari’a mai-adalci ta wurin mutum wanda ya ƙadara; wannan fa ya bada shaidarsa ga mutane duka, yayinda ya tashe shi daga matattu.” (Ayukan Manzanni 17:31) Wasu daga cikin masu sauraran Bulus sun yi masa ba’a sa’ad da suka ji maganar tashin matattu. Amma, kaɗan ne daga cikinsu suka zama masu bi. Wataƙila tunanin cewa wannan begen zai tabbata ne ya jawo ra’ayinsu. Jehobah ya yi ma’ujiza mafi girma, sa’ad da ya ta da Yesu daga matattu. Ya ta da Ɗansa daga matattu don ya rayu a matsayin babban ruhu. (1 Bitrus 3:18) Sa’ad da Yesu ya tashi daga matattu ya sami iko fiye da lokacin da yake ɗan adam. Bayan Jehobah shi ne na biyu wajen iko, ba zai mutu ba, yanzu Yesu ya cancanta ya karɓi aiki mai ban al’ajabi daga wurin Ubansa. Ta wurin Yesu ne Jehobah zai yi dukan sauran tashin matattu, zuwa rayuwa a sama ko kuma a duniya. Yesu da kansa ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai.” (Yohanna 5:25; 11:25) Jehobah ya tabbatar wa dukan mutane masu aminci irin wannan bege sa’ad da ya ta da ɗansa daga matattu.
9. Ta yaya ne labari na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tashin matattu zai tabbata?
9 A gaban shaidu an nuna yadda tashin matattu zai kasance kuma an rubuta a Kalmar Allah. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da kwatanci dalla-dalla game da mutane takwas da aka tashe su daga matattu. A gaban shaidu aka yi waɗannan mu’ujiza, ba a ɓoye ba. Yesu ya ta da Li’azaru da ya mutu bayan kwanaki huɗu, a gaban taron mutane masu makoki, babu shakka sun haɗa da iyalan mutumin, abokansa, da maƙwabtansa. Wannan ya tabbatar da cewa Allah ne ya aiki Yesu, hakan kuwa ya sa ’yan addini maƙiyan Yesu ba su taɓa musanta cewa hakan ya faru ba. Maimakon haka, suka shirya su kashe Yesu da Li’azaru! (Yohanna 11:17-44, 53; 12:9-11) Hakika, muna da tabbaci cewa tashin matattu zai tabbata. Allah ya gaya mana tashin matattu da aka yi a dā don su ƙarfafa mu kuma su sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi.
Samun Ta’aziyya Daga Begen Tashin Matattu
10. Menene zai taimake mu mu sami ta’aziyya daga labarin tashin matattu na Littafi Mai Tsarki?
10 Kana bukatar ta’aziyya sa’ad da mutuwa ta kusa? Za mu sami ta’aziyya daga labarin tashin matattu da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Karanta irin waɗannan labarai, da yin bimbini a kan su da kuma tunanin yadda suka auku zai iya sa begen tashin matattu ya zama da gaske a gare ka. (Romawa 15:4) Waɗannan ba tatsuniya ba ne. Hakika hakan ya faru da mutane kamar mu, da suka yi rayuwa a wani zamani. Bari mu ɗan tattauna game da wani misalin tashin matattu na farko a cikin labari na Littafi Mai Tsarki.
11, 12. (a) Wane bala’i ne ya sami gwauruwa a Zarefat, me ta yi da farko? (b) Ka kwatanta abin da Jehobah ya ba annabinsa Iliya ikon ya yi wa gwauruwar.
11 Ka ƙaga yadda yanayin ya kasance. A wasu ’yan kwanaki annabi Iliya yana baƙunci a gidan gwauruwa da ke Zarefat, yana zama a cikin ɗaki na bene. Ana baƙin ciki a garin saboda rashin ruwa da abinci. Mutane da yawa suna mutuwa. Jehobah ya yi amfani da Iliya ya yi mu’ujiza da za ta daɗe don ya albarkaci bangaskiyar wannan gwauruwa mai tawali’u. Ita da ɗanta sun kusa shiga lokacin yunwa, saboda abincinsu na ƙarshe ne kawai gare su, sa’ad da AIlah ya ba Iliya ikon yin mu’ujiza don garinta da mai su ciyar da su. Bayan haka, bala’i ta same ta. Ciwo ya kama yaron, nan da nan sai ya daina numfashi. Baƙin ciki ya kama gwauruwar. Rashin taimako da ƙarfafa na maigidanta ma ya ishe ta, kuma gashi yanzu ta rasa ɗanta. Saboda baƙin ciki, ta ga laifin Iliya da Allahnsa, Jehobah! Menene annabin zai yi?
12 Iliya bai tsauta wa gwauruwar saboda zargin da ta yi ba. Maimakon haka, ya ce: “Ba ni ɗanki.” Bayan da ya ɗauki ɗan zuwa cikin ɗakin kwana, Iliya ya yi addu’a a kai a kai don ran yaron ya dawo. Daga ƙarshe, Jehobah ya amsa! Ka yi tunanin irin farin cikin da Iliya ya yi sa’ad da ya ga yaron yana numfashi. Idanun yaron suka buɗe suna haske. Iliya ya kawo yaron wurin mahaifiyarsa ya ce: “Ga ɗanki, yana da rai.” Ba za a iya kwatanta farin cikin ta ba. Ta ce: “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne; maganar Ubangiji kuwa a bakinka gaskiya ne.” (1 Sarakuna 17:8-24) Bangaskiyarta ga Jehobah da kuma wakilinsa ya ƙarfafa fiye da dā.
13. Me ya sa labarin Iliya game da ta da ɗan gwauruwa yana ta’aziyyar da mu a yau?
13 Hakika, yin bimbini bisa ga irin wannan labarin yana kawo ta’aziyya sosai. Wannan ya tabbatar mana cewa Jehobah yana iya yin galaba bisa maƙiyinmu mutuwa! Ka yi tunanin ranar da mutane da yawa za su yi farin ciki irin na gwauruwar nan a ranar tashin matattu! Za a yi farin ciki a sama sosai sa’ad da Jehobah ya ja-goranci Ɗansa ya ta da matattu a dukan duniya. (Yohanna 5:28, 29) Ka taɓa rasa wani da kake ƙaunarsa kuwa? Abin al’ajabi ne ka sani cewa Jehobah zai iya kuma zai ta da matattu!
Begenka da Rayuwarka na Yanzu
14. Ta yaya ne begen tashin matattu zai iya shafan rayuwarka?
14 Ta yaya ne begen tashin matattu zai shafi yadda kake rayuwa yanzu? Za ka sami ƙarfafa daga wannan begen idan kana fuskantar wahala, matsaloli, ko kuma tsanantawa. Shaiɗan yana so ka ji tsoron mutuwa har ka yi musanyar amincinka da alkawarin ceto da ba za a iya cikawa ba. Ka tuna cewa Shaiɗan ya ce wa Jehobah: “Dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayuba 2:4) Ta wannan furcin, Shaiɗan ya zargi dukanmu, har da kai. Da gaske ne za ka daina bauta wa Allah idan ka fuskanci matsala? Ta wurin yin tunanin begen tashin matattu, za ka iya yin ƙuduri mai ƙarfi don ka ci gaba da nufin Ubanka na samaniya.
15. Ta yaya ne kalaman Yesu da aka rubuta a Matta 10:28 za su kawo mana ta’aziyya idan muna fuskantar matsala?
15 Yesu ya ce: “Kada ku ji tsoron waɗannan da su ke kisan jiki, ba su kuwa da iko su kashe rai: gwamma dai ku ji tsoron wannan wanda yana da iko ya hallaka rai duk da jiki cikin Jahannama.” (Matta 10:28) Kada mu ji tsoron Shaiɗan ko kuma mutanensa. Hakika, wataƙila wasu suna da ikon yin mugunta, har da kisa. Duk da haka, duk wani mugunta da za su iya yi na ɗan lokaci ne. Jehobah zai iya kuma zai cire dukan mugunta da aka yi wa amintattun bayinsa, har ya tashe su daga matattu. Jehobah ne kaɗai ya kamata mu ji tsoronsa, mu girmama kuma mu daraja shi. Shi ne kaɗai yake da ikon ya ɗauki rai da kuma dukan begen rayuwa na nan gaba, wanda zai halaka rai da jiki a cikin Jahannama. Hakika, Jehobah ba ya son hakan ya same ka a nan gaba. (2 Bitrus 3:9) Saboda begen tashin matattu, mu bayin Allah za mu tsira. Za mu sami rai madawwami idan muka ci gaba da amincinmu, kuma babu abin da Shaiɗan da mabiyansa za su iya yi game da haka.—Zabura 118:6; Ibraniyawa 13:6.
16. Ta yaya ne ra’ayinmu yake shafan abubuwa na musamman da muka kafa?
16 Idan muka yarda cewa begen tashin matattu gaskiya ne, zai iya gyara halinmu game da rayuwa. Mun fahimci cewa ‘ko mu rayu, ko mu mutu, na Ubangiji mu ke.’ (Romawa 14:7, 8) A wurin kafa abubuwa da suka fi muhimmanci, ya kamata mu bi umurnin Bulus: “Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sake ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.” (Romawa 12:2) Mutane da yawa suna sauri su cim ma kowane muradi, buri, da kuma kowane nufi. Saboda sun ɗauki rayuwa ba ta da tsawo, sun nace wa biɗan nishaɗi, kuma idan suna da wata hanyar bauta, hakika bai dace da “abin da Allah ke so” ba.
17, 18. (a) Ta yaya ne Kalmar Jehobah ta nuna cewa rayuwa ba ta da tsawo, amma menene nufin Allah a gare mu? (b) Menene yake motsa mu mu yabi Jehobah koyaushe?
17 Hakika, rayuwa ba ta da tsawo. “Da sauri ya kan wuce, mu kan tashi,” wataƙila a shekaru 70 ko kuma 80. (Zabura 90:10) ’Yan adam suna shuɗewa kamar ɗanyar ciyawa, kamar inuwa wadda take wucewa, kamar numfashi. (Zabura 103:15; 144:3, 4) Amma ba nufin Allah ba ne mu yi girma, mu sami hikima, bayan wasu shekaru kaɗan sai mu yi ciwo kuma mu mutu. Jehobah ya halicci ’yan adam da sha’awar su rayu har abada. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: ‘Ya sa madawaman zamanai a cikin zuciyarsu.’ (Mai-Wa’azi 3:11) Allah azzalumi ne da zai ba mu irin wannan muradi, sannan ya ƙi cika wa? A’a, hakika “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Zai yi amfani da tashin matattu don ya sa rai madawwami ta tabbata ga waɗanda suka mutu.
18 Saboda begen tashin matattu, za mu sami rayuwa mai kyau a nan gaba. Kada mu damu cewa dole sai mun cika dukan ingancinmu yanzu. Kada mu yi amfani da wannan duniya da za ta shuɗe don mu “cika moriyatata.” (1 Korinthiyawa 7:29-31; 1 Yohanna 2:17) Ba kamar waɗanda ba su da bege ba, muna da wannan kyauta: mun san cewa idan muka riƙe amincinmu ga Jehobah Allah, za mu zauna har abada mu bauta masa kuma mu mori rayuwa. Saboda haka, bari koyaushe mu yabi Jehobah wanda ya sa begen tashin matattu ya tabbata!
Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya ya kamata mu ɗauki begen tashin matattu?
• Waɗanne abubuwa ne suka sa begen tashin matattu ya tabbata?
• Ta yaya za ka sami ta’aziyya daga begen tashin matattu?
• Ta yaya ne begen tashin matattu zai shafi yadda kake rayuwa yanzu?
[Hoto a shafi na 18]
Ayuba ya san cewa Jehobah yana marmari ya ta da amintattun mutane
[Hoto a shafi na 19]
“Ga ɗanki, yana da rai”