Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Sarakuna na Ɗaya
“SA’AD da masu adalci suke mulki, jama’a sukan yi murna, amma sa’ad da mugaye suke mulki, jama’a sukan yi nishi.” (Karin Magana 29:2) Littafin Sarakuna na Ɗaya na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta gaskiyar wannan ƙarin maganar sosai. Ya faɗi labarin rayuwar Sulemanu, wanda a lokacin mulkinsa Isra’ila ta dā ta mori kāriya da arziki. Littafin Sarakuna na Ɗaya ya kuma faɗi labarin raba al’ummar bayan mutuwar Sulemanu da kuma sarakuna 14 da suka yi mulki a bayansa, wasu a Isra’ila wasu kuma a Yahuza. Sarakuna biyu ne kawai a cikinsu suka riƙe amincinsu ga Jehobah. Ƙari ga haka, littafin ya ambata ayyukan annabawa shida, har da Iliya.
Annabi Irmiya ne ya rubuta shi a Urushalima da kuma Yahuza, labarin da ya ɗauki tsawon shekara 129—daga shekara ta 1040 K.Z. zuwa 911 K.Z. Sa’ad da yake harhaɗa littafin, babu shakka, Irmiya ya duba irin rubutun nan na dā kamar su “littafin tarihin Sulemanu.” Yanzu babu irin wannan littafin.—1 Sarakuna 11:41; 14:19; 15:7.
SARKI MAI HIKIMA YA ƊAUKAKA SALAMA DA ARZIKI
(1 Sarakuna 1:1–11:43)
Littafin Sarakuna na ɗaya ya soma ne da labari mai ban sha’awa game da ɗan Sarki Dauda Adonaija wanda ya so ya zama sarki. Matakin da Natan ya ɗauka ya ɓata shirin, kuma aka naɗa ɗan Dauda, Sulemanu ya zama sarki. Jehobah ya yi murna ƙwarai da roƙon da sabon sarkin da aka naɗa ya yi, kuma ya ba shi “zuciya ta hikima da ganewa” tare da “wadata da girma.” (1 Sarakuna 3:12, 13) Babu na biyun sarkin a hikima da arziki. Isra’ilawa sun sami salama da wadata.
Akwai haikalin Jehobah da gidajen gwamnati masu yawa a cikin gine-ginen da Sulemanu ya gina. Jehobah ya ba Sulemanu tabbaci: “Zan kafa gadon sarautarka a bisa Isra’ila har abada,” idan sarkin ya ci gaba da yin biyayya. (1 Sarakuna 9:4, 5) Allah na gaskiya ya kuma yi masa gargaɗi game da sakamakon rashin biyayya. Amma Sulemanu ya auri mata baƙi masu yawa. Sun rinjaye shi, kuma ya fara bauta ta ƙarya sa’ad da ya tsufa. Jehobah ya annabta cewa za a raba mulkinsa. Sulemanu ya mutu a shekara ta 997 K.Z., wanda hakan ya kawo ƙarshen mulkinsa na shekara 40. Ɗansa Yerobowam ya hau gadon sarauta.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
1:5—Me ya sa Adonaija ya so ya hau gadon sarauta duk da cewa Dauda na raye? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Amma, ya dace mu kammala cewa tun da yake yayyen Adonaija, Amnon da Absalom sun riga sun mutu, wataƙila har da ɗan Dawuda, Kileyab, Adonaija ya ga cewa yana da ikon zama sarki a matsayinsa na babban ɗan Dawuda da ya rage. (2 Sama’ila 3:2-4; 13:28, 29; 18:14-17) Tun da yake ya sami goyon bayan shugaban mayaƙa mai ƙarfi Yowab da kuma babban firist mai tasiri Abiyata, wataƙila Adonaija ya sami gaba gaɗin cewa manufarsa za ta cika. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana cewa ƙila yana sane da shirin Dauda na ɗaura Sulemanu a kan gadon sarauta ba. Amma, Adonaija bai gayyaci Sulemanu da waɗanda suka kusaci Dauda zuwa “hadaya” ba. (1 Sarakuna 1:9, 10) Hakan ya nuna cewa ya ɗauki Sulemanu abokin adawarsa.
1:49-53; 2:13-25—Me ya sa Sulemanu ya kashe Adonaija bayan ya gafarta masa? Ko da yake Bat-sheba ta ƙi fahimtar haka, Sulemanu ya gane manufar roƙon da Adonaija ya yi cewa ta roƙi sarki ya ba shi Abishag ta zama matarsa. Ko da yake Dauda bai kwanta da ita ba, an ɗauki Abishag kyakkyawa a matsayin ƙwarƙwarar Dauda. A kan al’adar lokacin, za ta iya zama matar magajin Dauda ne kawai. Wataƙila Adonaija ya yi tunanin cewa idan ya auri Abishag, zai iya sake biɗar sarauta. Da ya fahimci cewa Adonaija yana burin zama sarki, hakan ya sa Sulemanu ya fasa gafarta masa.
6:37–8:2—Yaushe ne aka keɓe haikalin? An kammala ginin haikalin a watan takwas na shekara ta 1027 K.Z., a shekara ta 11 ta sarautar Sulemanu. Kamar ɗauko kayan ado da kuma kammala sauran shirye-shiryen ya ɗauki watanni 11. Wataƙila an yi keɓewar a watan bakwai na shekara ta 1026 K.Z. Labarin ya kwatanta wasu gine-gine bayan an kammala ginin haikalin kafin ya ambata keɓewarta, domin ba da cikakken kwatanci game da ayyukan ginin.—2 Tarihi 5:1-3.
9:10-13—Kyautar garuruwa 20 a ƙasar Galili da Sulemanu ya yi wa Hiram Sarkin Taya ya jitu da Dokar Musa? Dokar da ke Littafin Firistoci 25:23, 24 wataƙila tana nuni ne kawai ga yankin Isra’ilawa. Ƙila garuruwa da Sulemanu ya ba Hiram ba na Isra’ilawa ba ne, ko da yake suna kusa da iyakar Ƙasar Alkawari. (Fitowa 23:31) Wataƙila abin da Sulemanu ya yi ya nuna ƙin bin Doka da ya yi, kamar sa’ad da ya “tattara wa kansa dawakai” kuma ya auri mata da yawa. (Maimaitawar Shari’a 17:16, 17) Ko yaya yake dai, Hiram ya raina kyautar. Wataƙila arnan da ke zaune a biranen ba su kula da su ba yadda ya kamata, ko kuwa ba sa wuraren da yake so.
11:4—Gigin-tsufa ne ya sa Sulemanu ya yi ridda sa’ad da ya tsufa? Kamar ba haka ba ne. Sulemanu matashi ne sa’ad da ya fara sarauta, ko da yake ya yi sarauta na shekara 40, bai tsufa ba sosai. Bugu da ƙari, bai daina bin Jehobah gabaki ɗaya ba. Amma ya soma wani salon bauta.
Darussa Dominmu:
2:26, 27, 35. Abin da Jehobah ya faɗa yana cika a kowane lokaci. Korar Abiyata, zuriyar Eli, ya cika “maganar da Ubangiji ya faɗa a kan gidan Eli.” Sanya Zadok na zuriyar Finehas a madadin Abiyata, ya cika Littafin Ƙidaya 25:10-13; Fitowa 6:25; 1 Sama’ila 2:31; 3:12; 1 Tarihi 24:3.
2:37, 41-46. Abin haɗari ne mutum ya yi tunanin cewa zai iya karya doka ba tare da wani sakamako ba! Waɗanda suka bijire da gangan daga bin ‘ƙunƙuntar ƙofar zuwa rai’ za su fuskanci sakamakon wannan mugun matakin.—Matiyu 7:14.
3:9, 12-14. Jehobah yana amsa addu’ar bayinsa na hikima, fahimi, da kuma ja-gora na tafiyar da hidimarsa.—Yakubu 1:5.
8:22-53. Sulemanu ya nuna godiya ga Jehobah—Allah mai nuna ƙauna ta alheri, Mai cika alkawura, da kuma Mai jin addu’a! Yin bimbini a kan addu’ar keɓewa da Sulemanu ya yi, zai faɗaɗa godiyarmu ga waɗannan da kuma sauran fasalolin halayen Allah.
11:9-14, 23, 26. Sa’ad da Sulemanu ya yi rashin biyayya a ƙarshen shekarunsa, Jehobah ya tayar masa da ’yan hamayya. “Allah na gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali’u alheri,” in ji manzo Bitrus.—1 Bitrus 5:5.
11:30-40. Sarki Sulemanu ya nemi ya kashe Yerobowam domin abin da Ahaija ya annabta game da Yerobowam. Hakan ya bambanta da yadda sarkin ya aikata shekaru 40 da suka shige, sa’ad da ya ƙi ɗaukan fansa a kan Adonaija da sauran ’yan tawaye! (1 Sarakuna 1:50-53) Halinsa ya canja a sakamakon ƙyale Jehobah da ya yi.
AN RABA MULKI MAI HAƊIN KAI
(1 Sarakuna 12:1–22:53)
Yerobowam da sauran mutane suka zo wurin Sarki Rehobowam suka roƙe shi ya sauƙaƙa musu wahalar da ubansa Sulemanu ya ɗora musu. Maimakon ya amsa roƙonsu, Rehobowam ya yi barazanar ƙara nawaita musu. Ƙabilun goma suka yi tawaye kuma suka naɗa Yerobowam ya zama sarkinsu. Haka ya raba mulkin. Rehobowam ya yi sarauta bisa kudancin mulkin, wanda ya ƙunshi ƙabilun Yahuza da Biliyaminu, kuma Yerobowam ya yi sarauta bisa arewacin ƙabila goma ta mulkin Isra’ila.
Domin ya hana mutanen zuwa Urushalima yin bauta, Yerobowam ya kafa gunki biyu—ɗaya a Dan ɗayan kuma a Betel. Sarakunan da suka yi sarauta a Isra’ila bayan Yerobowam su ne Nadab, Ba’asha, Ila, Zimri, Tibni, Omri, Ahab, da Ahaziya. Abaija, Asa, Yehoshafat, da kuma Yehoram ne suka gaji Rehobowam a Yahuza. Annabawa da suka wanzu a ranakun sarakunan sun haɗa da Ahaija, Shemaiya, da kuma wani annabin Allah da ba a ambata sunansa ba, da kuma Yehu, Iliya, da kuma Mikaiya.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
18:21—Me ya sa mutane suka yi tsit sa’ad da Iliya ya gaya musu cewa su bi Jehobah ko Ba’al? Wataƙila sun fahimci ƙin da suka yi su bauta wa Jehobah shi kaɗai kuma saboda haka suka ji cewa sun yi zunubi. Ko kuwa lamirinsu ya taurara har suna ganin cewa ba laifi ba ne su bauta wa Ba’al bayan suna da’awa cewa suna bauta wa Jehobah. Bayan Jehobah ya nuna musu ikonsa ne kawai suka ce: “Ubangiji shi ne Allah, Ubangiji shi ne Allah.”—1 Sarakuna 18:39.
20:34—Bayan Jehobah ya ba Ahab nasara bisa Suriyawa, me ya sa Ahab ya ƙyale sarkinsu, Ben-hadad? Maimakon ya kashe Ben-hadad, Ahab ya yi alkawari da shi domin Ben-hadad zai ba shi karauku da take a babban birnin Suriya, Dimashƙu, wataƙila domin ya kafa kasuwa. A farko, uban Ben-hadad ya bai wa kansa karauku a Suriya domin kasuwanci. Saboda haka, an saki Ben-hadad ne domin Ahab ya kafa kasuwanci a Dimashƙu.
Darussa Dominmu:
12:13, 14. Sa’ad da muke yanke shawarwari masu muhimmanci a rayuwa, mu nemi shawara daga mutane masu hikima kuma da suka manyanta waɗanda suka san Nassosi kuma suke daraja mizanan Allah sosai.
13:11-24. Shawara da ake shakka, ko sahihin mai bi ne ya yi ta, a gwada ta da lafiyayyar ja-gorar Kalmar Allah.—1 Yahaya 4:1.
14:13. Jehobah yana neman nagarin abu a cikinmu. Ko yaya ne ƙanƙantar wannan abu mai kyau, yana iya sa ta yi girma yayin da muke iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa.
15:10-13. Dole ne mu ƙi ridda da gaba gaɗi, maimako, mu ɗaukaka ibada ta gaskiya.
17:10-16. Gwauruwar da ke Zarefat ta fahimci cewa Iliya annabi ne kuma ta karɓe shi a haka, kuma Jehobah ya albarkaci ayyukanta na bangaskiya. A yau, Jehobah yana kula da ayyukanmu na bangaskiya, kuma yana sakawa waɗanda suke taimakawa aikin Mulki a hanyoyi masu yawa.—Matiyu 6:33; 10:41, 42; Ibraniyawa 6:10.
19:1-8. Sa’ad da muke fuskantar tsanantawa mai yawa, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana.—2 Korantiyawa 4:7-9.
19:10, 14, 18. Masu bauta ta gaskiya ba su taɓa kaɗaita ba. Jehobah yana tare da su da kuma ’yan’uwansu na dukan duniya.
19:11-13. Jehobah ba allahn yanayi ba ne.
20:11. Sa’ad da Ben-hadad ya yi barazanar halaka Samariya, sarkin Isra’ila ya amsa: “Sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa’an nan ya yi fariya, amma ba tun kafin a fara ba.” Sa’ad da muka fuskanci sabon aiki, dole ne mu ƙi yawan gaba gaɗi na mai fahariya.—Karin Magana 27:1; Yakubu 4:13-16.
Yana da Muhimmanci Sosai a Gare Mu
Sa’ad da yake ba da labarin Dokar da aka bayar a Dutsen Sinai, Musa ya gaya wa ’ya’yan Isra’ila: “Ga shi, yau na sa albarka da la’ana a gabanku. Za ku sami albarka idan kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau. Za ku zama la’anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau.”—Maimaitawar Shari’a 11:26-28.
Mun fahimci wannan gaskiyar da ke littafin Sarakuna na Ɗaya dalla-dalla! Kamar yadda muka gani, wannan littafin ya koyar da wasu darussa masu muhimmanci. Saƙonsa hakika rayayyiya ce kuma mai ƙarfi.—Ibraniyawa 4:12.