Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 9/1 pp. 21-25
  • Ka Yi Tafiya Da Allah A Wannan Lokacin Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Tafiya Da Allah A Wannan Lokacin Wahala
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Tafiya da Allah, Ba da Al’ummai Ba
  • Ta Yaya Za Mu Yi Tafiya da Allah Kuma Don Me?
  • Anuhu Ya Yi Tafiya da Allah a Lokacin Wahala
  • Menene ya Ƙarfafa Anuhu ya Yi Tafiya da Allah?
  • Ka Yi Koyi da Misalin Anuhu
  • “Ya Faranta wa Allah Rai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Gwarzon Mutum
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Kasance Da Gaba Gaɗi Ta Wurin Bangaskiya Da Tsoron Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Taƙaici Daga Littafin Farawa—na I
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 9/1 pp. 21-25

Ka Yi Tafiya Da Allah A Wannan Lokacin Wahala

“Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.”—FARAWA 5:24.

1. Waɗanne abubuwa ne suka sa zamaninmu ya kasance da masifu?

LOKACIN wahala! Wannan furci ya kwatanta shekarun hargitsi da mugunta da ’yan adam suka fuskanta tun lokacin da aka kafa Mulkin Almasihu a shekara ta 1914. Tun lokacin, ’yan adam suna cikin “zamanin ƙarshe.” Masifu kamar su yunwa, annoba, girgizar ƙasa, da yaƙe-yaƙe sun wahalar da mutane sosai. (2 Timoti 3:1; Wahayin Yahaya 6:1-8) Waɗanda suke bauta wa Jehobah su ma sun sha wahala sosai. Har ila, dukanmu muna jimre wa rashin tabbaci da wahala na wannan lokacin. Wahalar tattalin arziki, hargitsi na siyasa, mugunta, da ciwo suna cikin abubuwa da ke sa rayuwa take da wuya ainun.

2. Waɗanne kaluɓale bayin Jehobah suke fuskanta?

2 Ban da haka, bayin Jehobah da yawa sun jimre wa tsanantawa a kai a kai yayin da Shaiɗan ya ci gaba da yaƙi da “waɗanda ke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.” (Wahayin Yahaya 12:17) Ko da yake ba dukanmu muka fuskanci tsanantawa kai tsaye ba, dukan Kiristoci na gaskiya suna kokawa da Shaiɗan Iblis da halin da yake yaɗawa tsakanin ’yan adam. (Afisawa 2:2; 6:12) Muna bukatar mu kasance a faɗake ko da yaushe don kada wannan ruhun ya shafe mu, da yake muna fuskantarsa a wajen aiki, a makaranta, da kuma ko’ina da muke saduwa da waɗanda ba sa son bauta mai tsarki.

Ka Yi Tafiya da Allah, Ba da Al’ummai Ba

3, 4. A wace hanya ce Kiristoci suka bambanta da duniya?

3 Hakanan ma a ƙarni na farko, Kiristoci sun yi kokawa sosai don su tsayayya wa ruhun wannan duniya, kuma wannan ya sa sun kasance dabam da waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista. Bulus ya kwatanta bambancin sa’ad da ya rubuta: “To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku cikin Ubangiji, cewa kada ku sāke zama irin na al’ummai, masu azancin banza da wofi. Duhun zuciya gare su, bare suke ga rai wanda Allah ke bayarwa, sabili da jahilcin da ke gare su, saboda taurinkansu. Zuciya tasu ta yi kanta, sun dulmuya cikin fajirci, sun ɗokanta ido rufe ga yin kowane irin aikin lalata.”—Afisawa 4:17-19.

4 Wannan furcin ya kwatanta sarai duhu na ruhaniya da kuma na ɗabi’a da wannan duniya take ciki, a zamanin Bulus da kuma namu! Kamar yadda yake a ƙarni na farko, Kiristoci a yau ba sa “zama irin na al’ummai.” Maimakon haka, suna more babban gatar yin tafiya da Allah. Hakika, wasu mutane za su ce ko ya dace a ce ’yan adam ajizai raunannu suna tafiya da Jehobah. Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za su iya yin haka. Ƙari ga haka, Jehobah yana bukatar su yi hakan. A ƙarni na takwas kafin Zamaninmu, annabi Mika ya rubuta hurarrun kalmomin nan na gaba: ‘Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, ka bi Allah da tawali’u.’—Mika 6:8.

Ta Yaya Za Mu Yi Tafiya da Allah Kuma Don Me?

5. Ta yaya ’yan adam ajizai za su yi tafiya da Allah?

5 Ta yaya za mu yi tafiya da Allah marar ganuwa mafi iko? A bayane yake cewa ba yadda muke tafiya da mutane ba ne. A Littafi Mai Tsarki furcin nan ‘a yi tafiya’ yana iya nufin “bin wani tafarki.”a Da haka mun fahimci cewa wanda yake tafiya da Allah yana bin wani tafarkin rayuwa da Allah ya tsara kuma yana gamsar da shi. Bin irin wannan tafarki na sa mu kasance dabam da yawancin mutane da suka kewaye mu. Har ila, shi kaɗai ne zaɓi da ya dace Kirista ya yi. Me ya sa? Da dalilai masu yawa.

6, 7. Me ya sa yin tafiya da Allah tafarki ne mafi kyau?

6 Na farko, Jehobah ne Mahaliccinmu, Tushen rayuwarmu da kuma mai Tanadin dukan abubuwa da muke bukata don rayuwa. (Wahayin Yahaya 4:11) Saboda haka, shi kaɗai ne yake da ikon gaya mana yadda za mu yi tafiya. Ƙari ga haka, tafiya da Allah tafarki ne da ya fi amfani. Jehobah ya yi tanadin gafarta zunubi kuma ya ba da begen rai madawwami ga waɗanda suke tafiya da shi. Ubanmu na samaniya mai ƙauna na ba da gargaɗi mai kyau da ke taimakon waɗanda suke tafiya da shi su yi nasara a rayuwarsu yanzu, ko da su ajizai ne kuma suna zama a duniya da ke cikin ikon Shaiɗan. (Yahaya 3:16; 2 Timoti 3:15, 16; 1 Yahaya 1:8; 2:25; 5:19) Ƙarin dalili na yin tafiya da Allah shi ne cewa yin hakan na kawo salama da haɗin kai a cikin ikilisiya.—Kolosiyawa 3:15, 16.

7 Dalili na ƙarshe kuma mafi muhimmanci shi ne, idan muna tafiya da Allah muna nuna matsayinmu a batu mai girma da aka tayar can cikin lambun Aidan, wato, batun ikon mallaka. (Farawa 3:1-6) Muna nuna ta tafarkin rayuwarmu cewa muna gefen Jehobah gaba ɗaya, kuma muna shela babu tsoro cewa shi kaɗai ne Mamallaki da ya dace. (Zabura 83:18) Da haka muna aikata cikin jituwa da addu’armu cewa a tsarkake sunan Allah kuma a yi nufinsa. (Matiyu 6:9, 10) Waɗanda suka zaɓi su yi tafiya da Allah masu hikima ne! Suna da tabbacin cewa suna bin tafarkin da ya dace, da yake Jehobah ne “makaɗaicin hikima.” Ba ya kuskure.—Romawa 16:27.

8. Ta yaya zamanin Anuhu da Nuhu suka yi kama da namu?

8 To, ta yaya zai yiwu Kiristoci su yi rayuwa yadda ya kamata a lokaci mai wuya ƙwarai da yawancin mutane ba sa son bauta wa Jehobah? Za mu sami amsar sa’ad da muka yi la’akari da mutane na dā masu aminci da suka kasance da aminci a lokaci mai wuya ƙwarai. Biyu cikinsu Anuhu ne da Nuhu. Sun yi rayuwa a lokaci kamar wanda muke zama ciki a yanzu. Mugunta ta zama ruwan dare gama gari. A zamanin Nuhu duniya ta cika da mugunta da lalata. Duk da haka, Anuhu da Nuhu sun tsayayya wa ruhun duniya na zamaninsu kuma suka yi tafiya da Jehobah. Me ya sa suka iya yin hakan? Don mu sami amsar wannan tambayar, za mu tattauna misalin Anuhu a wannan talifin. A talifi na gaba, za mu tattauna na Nuhu.

Anuhu Ya Yi Tafiya da Allah a Lokacin Wahala

9. Wane bayani muke da shi game da Anuhu?

9 Anuhu ne mutum na farko da aka kwatanta cikin Nassosi cewa ya yi tafiya da Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah.” (Farawa 5:22) Bayan ya faɗi tsawon rayuwar Anuhu da bai kai yawan na zamani da suka riga shi ba amma yana da yawa idan aka gwada da tsawon rayuwarmu, labarin ya ce: “Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.” (Farawa 5:24) A bayane yake, Jehobah ya ɗauke Anuhu daga ƙasar masu rai zuwa mutuwa kafin magabta su yi masa lahani. (Ibraniyawa 11:5, 13) Ban da waɗannan ayoyin, akwai wurare kaɗan da aka yi magana game da Anuhu a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma, daga bayani da kuma wasu nuni da aka yi, muna da dalili mai kyau na cewa lokacin Anuhu na wahala ne.

10, 11. (a) Ta yaya mugunta ta yaɗu bayan Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye? (b) Wane saƙo na annabci ne Anuhu ya yi wa’azinsa, yaya mutane suka aikata ga saƙonsa?

10 Alal misali, ka yi la’akari da yadda ɓatanci ya yaɗu a tsakanin ’yan adam bayan Adamu ya yi zunubi. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Kayinu, ɗan farin Adamu, ya zama mai kisa na farko sa’ad da ya kashe ɗan’uwansa Habila. (Farawa 4:8-10) Bayan mutuwar Habila, Adamu da Hauwa’u suka haifi wani ɗa da suka kira Shitu. Mun karanta game da shi cewa: “Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.” (Farawa 4:25, 26) Abin baƙin ciki, sun yi “kira bisa sunan Ubangiji” ta wajen ridda.b Shekaru da yawa bayan haihuwar Enosh, wani daga zuriyar Kayinu mai suna Lamek ya rera wa matansa biyu waƙa, yana cewa ya kashe wani mutum da ya ji masa rauni. Ya kuma yi kashedi: “Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba’in da bakwai.”—Farawa 4:10, 19, 23, 24.

11 Irin wannan ɗan bayani ya nuna cewa ɓatanci da Shaiɗan ya gabatar a lambun Aidan ya sa mugunta ta yaɗu tsakanin ’ya’yan Adamu. A irin wannan zamani ne Anuhu ya zama annabi na Jehobah kuma hurarrun kalmominsa suna da amfani har a yau. Yahuza ya ba da rahoto cewa Anuhu ya yi annabci: “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa, don ya zartar da hukunci kan kowa, yā kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.” (Yahuza 14, 15) Waɗannan kalmomi za su cika a Armageddon. (Wahayin Yahaya 16:14, 16) Duk da haka, za mu tabbata cewa har ma a zamanin Anuhu, da akwai “masu zunubi marasa bin Allah” da suka yi fushi sa’ad da suka ji annabcin Anuhu. Yana da kyau da Jehobah ya ɗauki annabin don kada su ji masa!

Menene ya Ƙarfafa Anuhu ya Yi Tafiya da Allah?

12. Me ya sa Anuhu ya bambanta da mutanen zamaninsa?

12 Can cikin gonar Aidan, Adamu da Hauwa’u suka saurari Shaiɗan, kuma Adamu ya yi wa Jehobah tawaye. (Farawa 3:1-6) Ɗansu Habila ya bi wani tafarki dabam, Jehobah kuwa ya yi farin ciki da shi. (Farawa 4:3, 4) Abin baƙin ciki, yawancin zuriyar Adamu ba kamar Habila suke ba. Amma, Anuhu da aka haifa shekaru ɗarurruwa bayan haka ya bi tafarkin Habila. Wane bambanci ne yake tsakanin Anuhu da sauran zuriyar Adamu da yawa? Manzo Bulus ya amsa wannan tambayar sa’ad da ya rubuta: “Saboda bangaskiya ce aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi a kan ya faranta wa Allah rai.” (Ibraniyawa 11:5) Anuhu yana cikin “taron shaidu” masu yawa da misalai ne masu kyau na bangaskiya kafin lokacin Kirista. (Ibraniyawa 12:1) Bangaskiya ce ta taimaki Anuhu ya jimre da halinsa na kirki a fiye da shekara 300 na rayuwarsa, fiye da shekarar rayuwar yawancinmu a yau sau uku!

13. Wace irin bangaskiya ce Anuhu yake da ita?

13 Bulus ya kwatanta bangaskiyar Anuhu da wasu shaidu sa’ad da ya rubuta: “Bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da aka sa zuciya a kai, ita ce kuma tabbatawar abubuwan da ba a gani ba.” (Ibraniyawa 11:1) Hakika, bangaskiya ainihin abin da muka sa rai za su faru ne. Ta ƙunshi bege mai ƙarfi da zai shafi abin da muke ɗauka da muhimmanci a rayuwarmu. Irin wannan bangaskiya ta taimaki Anuhu ya yi tafiya da Allah ko da yake mutane da suka kewaye shi ba su yi hakan ba.

14. Bisa wane sani ne mai yiwuwa Anuhu ya kafa bangaskiyarsa?

14 Bangaskiya ta gaske na bisa cikakken sani. Wane irin sani ne Anuhu yake da shi? (Romawa 10:14, 17; 1 Timoti 2:4) Hakika, ya san abubuwa da suka faru a Aidan. Wataƙila ya ji yadda rayuwa take cikin lambun Aidan. Kuma wataƙila a lokacin Aidan yana nan ko da an hana mutane shiga. (Farawa 3:23, 24) Kuma yana sane da nufin Allah cewa ’ya’yan Adamu za su cika duniya kuma su mai da dukan doron ƙasa kamar Aljanna ta asali. (Farawa 1:28) Ƙari ga haka, Anuhu ya yi sha’awar alkawarin da Jehobah ya yi can baya cewa za a haifi Ɗa da zai ƙuje kan Shaiɗan kuma ya kawar da mugun sakamakon ruɗu na Shaiɗan. (Farawa 3:15) Hakika, annabcin Anuhu da aka hure da ke cikin littafin Yahuza, ya annabta halakar zuriyar Shaiɗan. Tun da yake Anuhu yana da bangaskiya, mun san cewa ya bauta wa Jehobah wanda yana “sakamako ga masu nemansa.” (Ibraniyawa 11:6) Ko da Anuhu bai da dukan ilimi da muke da shi, yana da isashe na kafa bangaskiya mai ƙarfi. Da irin wannan bangaskiya ya kasance da aminci a lokacin wahala.

Ka Yi Koyi da Misalin Anuhu

15, 16. Ta yaya za mu bi tafarkin Anuhu?

15 Tun da yake kamar Anuhu muna son mu faranta wa Jehobah rai a lokacin wahala da muke ciki yanzu, yana da kyau mu bi misalin Anuhu. Muna bukatar mu sami kuma mu riƙe cikakken sani na Jehobah da nufinsa. Amma da ƙari. Muna bukatar mu ƙyale wannan cikakken sani ya yi mana ja-gora. (Zabura 119:101; 2 Bitrus 1:19) Muna bukatar tunanin Allah ya yi mana ja-gora, mu riƙa ƙoƙari koyaushe mu faranta masa rai da dukan hankalinmu da ayyukanmu.

16 Ba mu da labarin wani kuma a zamanin Anuhu da ya bauta wa Jehobah, a bayane yake cewa shi kaɗai ne ko kuma yana cikin mutane kalilan. Mu ma kaɗan ne a duniya, amma wannan ba ya sa mu sanyin gwiwa. Jehobah zai goyi bayanmu ko waye ne yake gāba da mu. (Romawa 8:31) Anuhu da gaba gaɗi ya yi kashedi game da halakar miyagu. Mu ma a yau muna da gaba gaɗi sa’ad da muke yin “bisharan nan ta Mulkin” duk da ba’a, hamayya, da tsanantawa. (Matiyu 24:14) Anuhu bai yi rayuwa kamar mutane da yawa na zamaninsa ba. Duk da haka, bai sa rai a wannan duniya ba. Ya mai da hankalinsa a kan abin da ya fi muhimmanci. (Ibraniyawa 11:10, 35) Mu ma a yau muna mai da hankali ga cikar nufin Jehobah. Shi ya sa ba ma cika more wannan duniya. (1 Korantiyawa 7:31) Maimakon haka, muna amfani da ƙarfinmu da dukiyarmu musamman a hidimar Jehobah.

17. Wane sani muke da shi da Anuhu ba shi da shi, saboda haka me ya kamata mu yi?

17 Anuhu yana da bangaskiya cewa Ɗa da Allah ya yi alkawarinsa zai bayyana a lokacin da Jehobah ya ga ya dace. Shekaru 2,000 ne yanzu tun lokacin da wannan Ɗa, Yesu Kristi ya bayyana, ya yi tanadin fansa, kuma ya buɗe hanya dominmu, da kuma irin waɗannan shaidu masu aminci na dā kamar Anuhu, su gaji rai madawwami. Wannan Ɗa, da yanzu an naɗa shi Sarkin Mulkin Allah, ya jefo Shaiɗan daga sama zuwa wannan duniya, mun ga sakamakon haka kewaye da mu. (Wahayin Yahaya 12:12) Hakika muna da ƙarin ilimi fiye da Anuhu. Bari mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi yadda ya yi. Bari amincinmu a cikar alkawuran Allah ya shafi kome da muke yi. Kamar Anuhu, bari mu yi tafiya da Allah ko da yake muna rayuwa a lokacin wahala.

[Hasiya]

a Dubi kundin sanin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafi na 220, sakin layi na 6, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

b Kafin zamanin Enosh, Jehobah ya yi magana da Adamu. Habila ya miƙa hadaya da Jehobah ya amince da ita. Allah ya yi magana ma da Kayinu kafin kishi ya sa Kayinu ya yi kisa. Saboda haka, soma “kira bisa sunan Ubangiji” ta wata hanya ce dabam, ba na bauta mai tsarki ba.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Menene tafiya da Allah yake nufi ?

• Me ya sa yin tafiya da Allah tafarki ne da ya fi kyau?

• Menene ya taimaki Anuhu ya yi tafiya da Allah ko da yake lokacin wahala ne?

• Ta yaya za mu yi koyi da Anuhu?

[Hoto a shafi na 23]

Cikin bangaskiya “Anuhu ya yi tafiya tare da Allah”

[Hoto a shafi na 25]

Mun gaskata cewa alkawuran Jehobah za su cika

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 21]

Woman, far right: FAO photo/B. Imevbore; collapsing building: San Hong R-C Picture Company

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba