Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 10/1 pp. 16-20
  • Ka Kasance Da Gaba Gaɗi Ta Wurin Bangaskiya Da Tsoron Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Gaba Gaɗi Ta Wurin Bangaskiya Da Tsoron Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mutane Marasa Bangaskiya da ba Su da Gaba Gaɗi
  • Kada Ka ‘Noƙe’
  • Gaskatawa Cewa Akwai Allah Bai Isa Ba
  • Mutumin da Ya “Game Allah Ne Sarai”
  • Kasancewa da Gaba Gaɗi Don Tsoron Allah
  • “Ka Ƙarfafa, Ka Yi Ƙarfin Zuciya Ƙwarai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Ƙarfafa​—Jehobah Yana Tare da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Yi Tafiya Da Allah A Wannan Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • ‘Ku Yi Ƙarfi Ku Yi Gaba Gaɗi!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 10/1 pp. 16-20

Ka Kasance Da Gaba Gaɗi Ta Wurin Bangaskiya Da Tsoron Allah

“Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma . . . Ubangiji Allahnka yana tare da kai.”—JOSHUA 1:9.

1, 2. (a) Bisa ra’ayin ’yan adam, Isra’ilawa za su iya yin nasara bisa Kan’aniyawa ne? (b) Yaya aka ƙarfafa Joshua?

ASHEKARA ta 1473 K.Z., al’ummar Isra’ila tana shirye ta shiga Ƙasar Alkawari. Musa ya gaya wa mutanen wahalar da za su sha, yana cewa: “Yau kana ƙetaren Urdun garin ka shiga ka ci al’ummai waɗanda sun ɗara ka girma da ƙarfi kuma; birane kuwa manya manya masu-shimge har sama, mutane manya manya, dogaye, ’ya’yan Anaƙim, waɗanda . . . ka ji labarinsu, cewa, Wa ke iya tsaya ma ’ya’yan Anaƙim?” (Kubawar Shari’a 9:1, 2) Hakika, waɗannan jarumai ƙattai sanannu ne! Ƙari ga haka, wasu Kan’aniyawa suna da ƙwararrun sojoji, da dawakai da karusai na ƙarfe.—Alƙalawa 4:13.

2 Isra’ila kuma al’ummar bayi ne da suka yi shekaru 40 a cikin jeji. Saboda haka, bisa ra’ayin ’yan adam, da kyar ne su ci nasara. Duk da haka, Musa yana da bangaskiya, ya ‘ga’ cewa Jehobah ne yake musu ja-gora. (Ibraniyawa 11:27) Musa ya gaya wa mutanen: “Ubangiji Allahnka shi ne mai-ƙetare a gabanka, . . . za ya kuwa hallaka su, ya ƙasƙanta su a gabanka.” (Kubawar Shari’a 9:3; Zabura 33:16, 17) Bayan mutuwar Musa, Jehobah ya sake ƙarfafa Joshua cewa zai tallafa masa, yana cewa: “Yanzu fa ka tashi, ka ƙetare wannan Urdun, da kai, da dukan wannan al’umma, zuwa cikin ƙasa wadda ni ke ba su, su ’ya’yan Isra’ila. Babu mutum da za ya iya tsaya gabanka dukan kwanakin ranka: kamar yadda ina tare da Musa, hakanan zan yi tare da kai.”—Joshua 1:2, 5.

3. Me ya taimaki Joshua ya kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi?

3 Don ya sami taimakon Jehobah da ja-gorarsa, dole ne Joshuwa ya karanta kuma ya yi bimbini bisa Dokar Allah kuma ya yi amfani da ita. Jehobah ya ce: “Hakanan za ka sa hanyarka ta yi albarka, da hakanan kuma za ka yi nasara. Ban rigaya na umurce ka ba? Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma; kada ka tsorata, kada ka yi fargaba kuma: gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai dukan inda ka nufa.” (Joshua 1:8, 9) Domin Joshua ya saurari Allah, ya kasance da gaba gaɗi, ya ƙarfafa, kuma ya ci nasara. Amma, yawancin mutane na tsaransa ba su saurara ba. Domin haka, ba su yi nasara ba kuma suka mutu a cikin jeji.

Mutane Marasa Bangaskiya da ba Su da Gaba Gaɗi

4, 5. (a) Yaya halin ’yan leƙen asiri goma yake idan aka gwada da na Joshua da Kaleb? (b) Yaya Jehobah ya aikata ga rashin bangaskiyar mutanen?

4 Shekara arba’in da ta shige sa’ad da Isra’ila ta isa Kan’ana, Musa ya aiki mutane 12 su je su leƙo asirin ƙasar. Goma sun dawo sun tsorata. Suka ce: “Dukan mutanen da muka iske a nan mutane ingantattu ne. Can fa mun ga Nephilim, ’ya’yan Anak, zuriyar Nephilim; har mu, ga ganinmu, muka zama kamar ƙwanso, haka fa mu ke a wurinsu.” Ba “dukan mutanen” ba ne ƙattai da gaske, mutanen Anak ne kaɗai. ’Ya’yan Anak zuriyar Nephilim ne da suka rayu kafin Rigyawa? A’a! Duk da haka, domin wannan muguwar ƙarya, tsoro ya kama dukan mutanen da suke sansanin. Mutanen suka so su koma ƙasar Masar inda suka yi bauta!—Litafin Lissafi 13:31–14:4.

5 Amma, mutane biyu cikin masu leƙen asirin, wato, Joshua da Kaleb suna ɗokin shigan Ƙasar Alkawari. Suka ce: Kan’aniyawa “abincinmu ne; an kawarda kāriyarsu, Ubangiji yana tare da mu: kada ku ji tsoronsu.” (Litafin Lissafi 14:9) Hakan yana nufin cewa gaba gaɗin Joshua da Kaleb ba shi da tushe ne? Ko kaɗan. Su da sauran mutanen al’ummar, sun ga yadda Jehobah ya kunyatar da Masar da allolinta ta wurin Annoba Goma. Sun ga yadda Jehobah ya sa ruwa ya ci Fir’auna da rundunarsa a Jan Teku. (Zabura 136:15) A bayyane yake cewa ’yan leƙen asiri goma da waɗanda suka rinjaya ba su da hujjar jin tsoro. Jehobah ya furta baƙin cikinsa, yana cewa: “Har yaushe kuma za su ƙi gaskanta ni, ga kuwa dukan alamun da na aikata a wurinsu?”—Litafin Lissafi 14:11.

6. A wace hanya ce gaba gaɗi yake da nasaba da bangaskiya, yaya wannan ya kasance hakan a wannan zamani?

6 Jehobah ya faɗi ainihin tushen matsalar cewa tsoro da mutanen suka ji ya nuna cewa ba su da bangaskiya. Hakika, bangaskiya da gaba gaɗi suna da nasaba ƙwarai da ya sa manzo Yohanna ya rubuta game da ikilisiyar Kirista da yaƙinta na ruhaniya: “Nasara wadda ta ci duniya ke nan, bangaskiyarmu.” (1 Yohanna 5:4) A yau, bangaskiya kamar irin ta Joshua da Kaleb ta sa Shaidun Jehobah fiye da miliyan shida, yara da manya, masu ƙarfi, da raunannu su riƙa wa’azin bisharar Mulki a dukan duniya. Ba magabcin da zai iya sa waɗannan sojoji masu gaba gaɗi su yi shuru.—Romawa 8:31.

Kada Ka ‘Noƙe’

7. Menene “noƙewa” yake nufi?

7 Bayin Jehobah a yau suna wa’azin bishara da gaba gaɗi dominnufinsu ɗaya ne da na manzo Bulus wanda ya rubuta: “Mu ba mu cikin masu-noƙewa zuwa hallaka ba; amma cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibraniyawa 10:39) Kamar yadda Bulus ya ambata, “noƙewa” ba ta nufin jin tsoro na ɗan lokaci, domin bayin Allah da yawa masu aminci wani lokaci suna jin tsoro. (1 Samuila 21:12; 1 Sarakuna 19:1-4) Maimakon haka, wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ba da bayani cewa noƙewa tana nufin “ja da baya” da yin “sakaci game da gaskiya.” Ya kuma daɗa cewa za a iya kwatanta “noƙewa” wato, “ja da baya” a hidimar Allah da “rage gudun kwalekwale.” Hakika, waɗanda suka da bangaskiya sosai ba sa tunanin “ja da baya” sa’ad da matsala ta taso, ko tsanantawa, rashin lafiya, ko kuma wani gwaji. Maimakon haka, suna nacewa a hidimar Jehobah, sun sani cewa yana kula da su sosai kuma ya san kasawarsu. (Zabura 55:22; 103:14) Kana da irin wannan bangaskiyar?

8, 9. (a) Ta yaya ne Jehobah ya ƙarfafa bangaskiyar Kiristoci na farko? (b) Menene za mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

8 Akwai lokacin da manzannin suka ga cewa ba su da bangaskiya, sai suka gaya wa Yesu: “Ka ƙara mana bangaskiya.” (Luka 17:5) An ba su abin da suka roƙa, musamman a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka aiko wa almajiran ruhu mai tsarki da aka yi musu alkawarinsa, wannan ya ba su ƙarin fahimi game da Kalmar Allah da kuma nufinsa. (Yohanna 14:26; Ayukan Manzanni 2:1-4) An ƙarfafa bangaskiyarsu, almajiran suka soma aikin wa’azi kuma duk da hamayya, sun yi wa’azin bishara ga “dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.”—Kolossiyawa 1:23; Ayukan Manzanni 1:8; 28:22.

9 Domin mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu nace a hidimarmu, dole ne mu ma mu yi nazari mu yi bimbini bisa Nassosi kuma mu yi addu’a don samun ruhu mai tsarki. Sai ta wurin cusa gaskiyar Allah a cikin zuciyar mu kamar yadda Joshua, Kaleb, da almajirai Kirista na farko suka yi ne za mu kasance da bangaskiya da za ta ba mu gaba gaɗi da muke bukata mu jimre a yaƙinmu na ruhaniya kuma mu yi nasara.—Romawa 10:17.

Gaskatawa Cewa Akwai Allah Bai Isa Ba

10. Menene bangaskiya ta gaske ta ƙunsa?

10 Kamar yadda mutane masu aminci na dā suka nuna, bangaskiya da ke sa mutum ya kasance da gaba gaɗi da jimiri ta fi gaskatawa kawai cewa akwai Allah. (Yaƙub 2:19) Muna bukatar mu san kowane irin mutum ne Jehobah kuma mu dogara a gare shi. (Zabura 78:5-8; Misalai 3:5, 6) Tana nufin gaskatawa da dukan zuciyarmu cewa za mu amfana idan muka yi biyayya ga dokokin Allah da kuma ƙa’idodinsa. (Ishaya 48:17, 18) Bangaskiya ta ƙunshi kasancewa da cikakken tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan alkawarinsa kuma ya zama “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.”—Ibraniyawa 11:1, 6; Ishaya 55:11.

11. Ta yaya aka albarkaci Joshua da Kaleb don bangaskiyarsu da gaba gaɗi?

11 Irin wannan bangaskiya tana ƙaruwa. Za mu iya ƙara bangaskiyarmu yayin da muke bin gaskiya a rayuwarmu, sa’ad da muka “ɗanɗana” amfaninta, muka ga amsar addu’o’inmu, kuma a wasu hanyoyi muka fahimci cewa Jehobah yana ja-gorar rayuwarmu. (Zabura 34:8; 1 Yohanna 5:14, 15) Mun tabbata cewa bangaskiyar Joshua da Kaleb ta ƙaru sa’ad da suka ɗanɗana alherin Allah. (Joshua 23:14) Ka yi la’akari da waɗannan darussa: Sun tsira wa tafiya ta shekara 40 a cikin jeji, kamar yadda Allah ya yi musu alkawari. (Litafin Lissafi 14:27-30; 32:11, 12) Sun yi aiki sosai a yaƙin cin nasara na shekara shida da suka yi bisa Kan’ana. A ƙarshe suka more doguwar rayuwa da koshin lafiya kuma suka sami gado na kansu. Jehobah yana saka wa waɗanda suka bauta masa cikin aminci da gaba gaɗi!—Joshua 14:6, 9-14; 19:49, 50; 24:29.

12. Ta yaya Jehobah yake ‘girmama kalmarsa’?

12 Ƙauna ta alheri da Allah ya nuna wa Joshua da Kaleb ta tuna mana kalmomin mai zabura: “Ka girmama kalmarka bisa ga dukan sunanka.” (Zabura 138:2) Idan Jehobah ya yi amfani da sunansa don ya ba da tabbacin alkawari, yana “girmama” cikar wannan alkawarin domin ya fi dukan abin da ake tsammaninsa. (Afisawa 3:20) Hakika, Jehobah ba ya yasar da waɗanda suka “faranta zuciyar[su]” a gare shi.—Zabura 37:3, 4.

Mutumin da Ya “Game Allah Ne Sarai”

13, 14. Me ya sa Anuhu yake bukatar bangaskiya da gaba gaɗi?

13 Za mu koyi abubuwa da yawa game da bangaskiya da kuma gaba gaɗi ta wajen yin la’akari da misalin da Anuhu wani mashaidi ya kafa kafin lokacin Kiristanci. Kafin ya soma yin annabci, mai yiwuwa Anuhu ya san cewa za a gwada bangaskiyarsa da kuma gaba gaɗinsa. Ta yaya? Domin Jehobah ya faɗa a lambun Adnin cewa ƙiyayya za ta kasance tsakanin waɗanda suke bauta wa Allah da waɗanda suke bauta wa Shaiɗan Iblis. (Farawa 3:15) Anuhu kuma ya san cewa wannan ƙiyayya ta soma tun farkon tarihin ’yan adam sa’ad da Kayinu ya kashe ɗan’uwansa Habila. Hakika, babansu Adamu ya yi rayuwa kusan shekaru 310 bayan an haifi Anuhu.—Farawa 5:3-18.

14 Duk da waɗannan abubuwa, Anuhu da gaba gaɗi ya ci gaba da “tafiya tare da Allah” kuma ya la’anta “baƙaƙen maganganu” da mutane suke faɗa game da Jehobah. (Farawa 5:22; Yahuda 14, 15) Wannan gaba gaɗi don bauta ta gaskiya ya sa Anuhu ya yi magabta da yawa kuma ya saka ransa cikin haɗari. A wannan yanayin, Jehobah ya kāre annabinsa don kada a kashe shi. Bayan da aka bayyana wa Anuhu cewa shi “mai-game Allah ne sarai,” Jehobah ya “ɗauke” ransa, ƙila ya sa shi a yanayin annabci sai kuma ya ɗauki ransa sa’ad da yake cikin wannan yanayin.—Ibraniyawa 11:5, 13; Farawa 5:24.

15. Wane misali ne mai kyau Anuhu ya kafa wa bayin Jehobah a yau?

15 Bayan da ya ambata cewa an ɗauke Anuhu, Bulus ya kuma nanata muhimmancin bangaskiya, yana cewa: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:6) Kasancewa da bangaskiya ya sa Anuhu ya kasance da gaba gaɗi wajen yin tafiya da Jehobah kuma ya sanar da saƙon hukuncinsa ga duniya marar ibada. Ta yin hakan, Anuhu ya kafa mana misali mai kyau. Muna da irin wannan aikin a wannan duniya da ke cike da kowane irin mugunta kuma tana hamayya da bauta ta gaskiya.—Zabura 92:7; Matta 24:14; Ru’ya ta Yohanna 12:17.

Kasancewa da Gaba Gaɗi Don Tsoron Allah

16, 17. Wanene Obadiah, a wane yanayi ne ya sami kansa?

16 Ban da bangaskiya, tsoron Allah wani hali ne da ke sa mu kasance da gaba gaɗi. Bari mu bincika wani fitaccen misali na wani mutum mai tsoron Allah da ya yi rayuwa a kwanakin annabi Iliya da Sarki Ahab wanda ya yi sarautar arewancin Isra’ila. A lokacin sarautar Ahab, bautar Ba’al ta lalata masarauta ta arewa sosai. Annabawan Ba’al 450 da kuma annabawa 400 na gunki mai kama da azzakarin mutum suna “ci a table na Jezebel” matar Ahab.—1 Sarakuna 16:30-33; 18:19.

17 Jezebel wadda maƙiyar Jehobah ce, ta yi ƙoƙarin ta kawar da bauta ta gaskiya a ƙasar. Ta kashe wasu cikin annabawan Jehobah kuma ta yi ƙoƙarin ta kashe Iliya, wanda Allah ya ba shi umurni ya gudu ya nufi gabashin Urdun ya ɓuya. (1 Sarakuna 17:1-3; 18:13) Lallai zai kasance da wuya a ɗaukaka bauta ta gaskiya a masarauta ta arewa na lokacin. Zai ma fi wuya idan kana aiki a fadar sarki. Obadiah,a ma’aikacin Ahab, mai jin tsoron Allah yana cikin irin wannan yanayin.—1 Sarakuna 18:3.

18. Me ya sa Obadiah ya yi fice a bautarsa ga Jehobah?

18 Babu shakka, Obadiah mai azanci ne da kuma hikima a bautarsa ga Jehobah. Duk da haka, bai bar bautarsa ba. Littafin 1 Sarakuna 18:3 ta gaya mana: ‘Obadiah dai mai-tsoron Ubangiji ne ƙwarai.’ Hakika, Obadiah mutum ne mai tsoron Allah sosai. Wannan tsoron ya sa ya kasance da gaba gaɗi na musamman kamar yadda ya nuna nan da nan bayan Jezebel ta kashe annabawan Jehobah.

19. Menene Obadiah ya yi da ya nuna yana da gaba gaɗi?

19 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya zama, lokacin da Jezebel ta hallaka annabawan Ubangiji, shi Obadiah ya ɗauki annabawa guda ɗari, ya ɓoye su, hamsin hamsin, cikin wani kogon dutse, ya yi kiwonsu da gurasa da ruwa.” (1 Sarakuna 18:4) Ciyar da mutane ɗari a ɓoye aiki ne mai haɗari. Obadiah ya mai da hankali kada Ahab da Jezebel su kama shi, kuma kada annabawan ƙarya 850 da suke zuwa fadan koyaushe su gane abin da yake yi. Ban da haka, masu bautar ƙarya da yawa da ke ƙasar, talakawa da mawadata za su yi amfani da kowane zarafi su fallasa Obadiah don su sami farin jini a wurin sarkin da kuma sarauniyar. Duk da haka, a gaban dukan waɗannan masu bautar gumaka, Obadiah da gaba gaɗi ya biya bukatun annabawan Jehobah. Lallai tsoron Allah yana da iko.

20. Ta yaya tsoron Allah ya taimaki Obadiah, kuma yaya misalinsa ya taimaka maka?

20 Domin Obadiah ya nuna gaba gaɗi don tsoron Allah, Jehobah ya kāre shi daga magabtansa. Misalai 29:25 ta ce: “Tsoron mutum ya kan kawo tarko, amma wanda ya sa danganarsa ga Ubangiji za ya zauna lafiya.” Obadiah mutumi ne kawai; yana jin tsoron kada a kama shi kuma a kashe shi, kamar yadda muke jin tsoro. (1 Sarakuna 18:7-9, 12) Duk da haka, tsoron Allah ya sa ya kasance da gaba gaɗi kuma ya sha kan kowane tsoron mutum da yake ji. Obadiah ya kafa wa dukanmu misali mai kyau, musamman waɗanda ba su da ’yancin bauta wa Jehobah ko kuma suna hakan ta wajen sa ransu cikin haɗari. (Matta 24:9) Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu bauta wa Jehobah “tare da ladabi da saduda.”—Ibraniyawa 12:28.

21. Menene za a tattauna a talifi na gaba?

21 Bangaskiya da tsoron Allah ba su ba ne kawai halayen da ke sa gaba gaɗi ba, ƙauna ma tana da iko sosai. Bulus ya rubuta: “Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo.” (2 Timothawus 1:7) A talifi na gaba, za mu ga yadda ƙauna za ta taimake mu mu bauta wa Jehobah da gaba gaɗi a wannan miyagun kwanaki na ƙarshe.—2 Timothawus 3:1.

[Hasiya]

a Wannan ba annabi Obadiah ba ne.

Za Ka Iya Amsawa?

• Me ya sa Joshua da Kaleb suka kasance da gaba gaɗi?

• Menene bangaskiya ta gaske ta ƙunsa?

• Me ya sa Anuhu ya kasance da gaba gaɗi sa’ad da yake shelar saƙon hukunci na Allah?

• Ta yaya tsoron Allah ke sa mutum ya kasance da gaba gaɗi?

[Hoto a shafi nas 16, 17]

Jehobah ya ba Joshua umurni: “Ka ƙarfafa; ka yi ƙarfin zuciya kuma”

[Hoto a shafi na 18]

Obadiah ya kula da annabawan Allah kuma ya kāre su

[Hotuna a shafi na 19]

Anuhu ya faɗi maganar Allah da gaba gaɗi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba