Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 10/1 pp. 12-16
  • Ka Yi Irin Zaman Da Yesu Kristi Ya Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Irin Zaman Da Yesu Kristi Ya Yi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Kristi Yake Ja-gorar Mabiyansa
  • Ka Kasance da Sanin Ya Kamata Sa’ad da Kake Nuna Iko
  • Ka Kasance Mai Tausayi Mai Gafartawa
  • Ka Sa Al’amura ta Mulki Farko
  • Ka Kasance Mai Aminci
  • Ka Bi Gurbin Da Yesu Ya Kafa
  • Kristi Yana Ja-gorar Ikilisiyarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Kasance Da Hali Irin Na Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Yi Biyayya Ga Kristi Da Kuma Amintaccen Bawansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 10/1 pp. 12-16

Ka Yi Irin Zaman Da Yesu Kristi Ya Yi

“Kowa ya ce yana zaune cikinsa [Allah], ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da [Yesu] ya yi.”—1 YAHAYA 2:6.

1, 2. Menene zuba ido ga Yesu ya ƙunsa?

“MU KUMA yi tseren nan da ke gabanmu tare da jimiri,” in ji manzo Bulus, “muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma kammala ta.” (Ibraniyawa 12:1, 2) Muna bukatar mu zuba wa Yesu Kristi ido idan za mu bi tafarki na aminci.

2 Kalma ta yaren asali ta “zuba ido” yadda aka yi amfani da ita a Nassosin Kirista na Helenanci na nufin “mutum ya mai da hankali, kada ya raba hankali,” “a kawar da ido daga wani abu don a ga wani.” Wani bincike da aka yi ya nuna cewa: “Lokacin da mai tsere a filin wasa na Helas ya kau da hankalinsa daga tsere da kuma burin da yake son ya cim ma, kuma ya mai da hankalinsa ga masu kallo, sai ya ja da baya. Hakan yake ga Kirista.” Abubuwan raba hankali za su iya hana mu ci gaba a ruhaniya. Dole mu zuba ido ga Yesu Kristi. Menene muke nema wajen Shugaban? Kalmar Helenanci da aka fassara “shugaba” na nufin wanda yake ja-gora a kome kuma ta haka yana kafa misali.” Zuba ido ga Yesu na nufin bin misalinsa.

3, 4. (a) Yin zaman da Yesu Kristi ya yi na bukatar menene a gare mu? (b) Waɗanne tambayoyi ya kamata mu mai da wa hankali?

3 “Kowa ya ce yana zaune cikinsa [Allah], ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da [Yesu] ya yi,” in ji Littafi Mai Tsarki. (1 Yahaya 2:6) Dole ne mu zauna cikin Allah ta wajen kiyaye umurnin Yesu yadda ya kiyaye na Ubansa.—Yahaya 15:10.

4 Shi ya sa, don mu yi zaman da Yesu ya yi muna bukatar mu kiyaye umarninsa da yake shi ne Babban Shugaba kuma mu bi sawunsa a tsanake. Tambayoyi masu muhimmanci da za mu bincika game da wannan sune: Ta yaya Kristi ke shugabancin mu a yau? Ta yaya yin koyi da yadda ya yi zama zai shafe mu? Menene amfanin bin gurbin da Yesu Kristi ya kafa?

Yadda Kristi Yake Ja-gorar Mabiyansa

5. Kafin ya haura sama, wane alkawari Yesu ya yi wa almajiransa?

5 Kafin ya haura sama, Yesu Kristi da aka ta da daga matattu ya bayyana wa almajiransa kuma ya ba su aiki mai muhimmanci. Ya ce: “Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai.” A wannan lokacin Babban Shugaban ya yi alkawarin zai kasance da su sa’ad da suke cika wannan aikin, yana cewa: “Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har matuƙar zamani.” (Matiyu 28:19, 20) Ta yaya Yesu Kristi yake tare da manzanninsa a wannan matuƙar zamani?

6, 7. Ta yaya Yesu yake mana ja-gora ta ruhu mai tsarki?

6 “Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uban zai aiko da sunana,” in ji Yesu “shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.” (Yahaya 14:26) Ruhu mai tsarki da aka aika cikin sunan Yesu, yana yi mana ja-gora kuma yana ƙarfafa mu a yau. Yana wayar da mu a ruhaniya da kuma taimaka mana mu fahimci “har ma zurfafan al’amuran Allah.” (1 Korantiyawa 2:10) Ƙari ga haka, halaye na ibada kamar su “ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, da tawali’u da kuma kamunkai” sune “albarkar ruhu.” (Galatiyawa 5:22, 23) Da taimakon ruhu mai tsarki, za mu iya koyan irin waɗannan halaye.

7 Yayin da muke nazarin Nassosi kuma muke ƙoƙarin mu yi amfani da abin da muke koya, ruhun Jehobah zai taimake mu mu sami hikima, tsinkaya, fahimi, sani, da kuma gaskiya. (Karin Magana 2:1-11) Ruhu mai tsarki na taimakonmu mu jimre wa gwaji. (1 Korantiyawa 10:13; 2 Korantiyawa 4:7; Filibiyawa 4:13) An gargaɗi Kiristoci su ‘tsarkake kansu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, su kamalta cikin tsarki.’ (2 Korantiyawa 7:1) Za mu iya rayuwa cikin jituwa da farillan Allah game da tsarki, ko tsabta, ban da taimakon ruhu mai tsarki? Hanya ɗaya da Yesu ke amfani da ita a yau ya yi mana ja-gora ita ce ta ruhu mai tsarki, da Jehobah Allah ya ba Ɗansa iko ya yi amfani da shi.—Matiyu 28:18.

8, 9. Ta yaya Kristi yake shugabanci ta “amintaccen bawan nan mai hikima”?

8 Ka yi la’akari da wata hanya da Kristi ke wa ikilisiya ja-gora a yau. Da yake maganar bayyanuwarsa da ƙarewar zamani, Yesu ya ce: “Wanene amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangijinsa ya ba shi riƙon gidansa, yā riƙa ba su abincinsu a kan kari? Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangijinsa ya dawo zai samu yana yin haka. Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa.”—Matiyu 24:3, 45-47.

9 “Ubangijin” Yesu Kristi ne. “Bawan” kuma rukunin Kiristoci shafaffu ne a duniya. An ɗora wa rukunin bawan nan hakkin kula da mallakar Yesu na duniya da kuma tanadin abinci na ruhaniya a kan kari. Hukumar Mulki, wato ƙaramin rukuni na masu kula daga “amintaccen bawan nan mai hikima,” ne wakilan rukunin bawan. Sune suke ja-gorar aikin wa’azin Mulki da ake yi a dukan duniya da kuma ba da abinci na ruhaniya a lokacin da ya dace. Da haka, Kristi yana shugabancin ikilisiya ta Hukumar Mulki ta “amintaccen bawan nan mai hikima” da aka shafa da ruhu.

10. Yaya ya kamata mu ɗauki dattawa, kuma me ya sa?

10 Wani abu da ya nuna Kristi ne ke shugabancin shi ne ‘kyauta ga mutane’ wato, dattawa Kirista, ko kuma masu kula. Haka yake “domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar ikilisiya domin inganta jikin Almasihu.” (Afisawa 4:8, 11, 12) Ibraniyawa 13:7 ta ce game da su: “Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.” Dattawa suna shugabanci a cikin ikilisiya. Tun da yake suna yin koyi da Yesu Kristi, bangaskiyarsu ta dace a yi koyi da ita. (1 Korantiyawa 11:1) Za mu nuna godiyarmu ga tsarin dattawa ta yin biyayya da kuma ba da kai ga waɗannan ‘kyauta ga mutane.’—Ibraniyawa 13:17, Litafi Mai-Tsarki.

11. Ta yaya Kristi yake shugabancin mabiyansa a yau, kuma menene zama yadda ya yi ya ƙunsa?

11 Hakika, Yesu Kristi yana wa mabiyansa a yau shugabanci ta ruhu mai tsarki, “amintaccen bawan nan mai hikima,” da kuma dattawan ikilisiya. Domin mu yi irin zaman da Kristi ya yi, muna bukatar mu fahimci yadda yake ja-gora kuma mu yi biyayya. Muna bukatar mu yi koyi da irin zaman da ya yi. Manzo Bitrus ya rubuta: “Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.” (1 Bitrus 2:21) Ta yaya bin gurbin Yesu ya kamata ya shafe mu?

Ka Kasance da Sanin Ya Kamata Sa’ad da Kake Nuna Iko

12. Wane fanni na misalin Kristi musamman dattawa cikin ikilisiya za su bi?

12 Ko da Yesu ya samu iko da babu na biyunsa daga Ubansa, ya daidaita a yadda yake nuna ikon. Duka a cikin ikilisiya, musamman masu kula, ya kamata su “bari kowa ya san jimirin[su].” (Filibiyawa 4:5; 1 Timoti 3:2, 3) Tun da yake dattawa suna da ɗan iko a cikin ikilisiya, yana da muhimmanci su bi gurbin Kristi wajen nuna ikon.

13, 14. Ta ya ya dattawa za su iya yin koyi da Kristi sa’ad da suke ƙarfafa wasu su bauta wa Allah?

13 Yesu ya yi la’akari da kasawar almajiransa. Bai bukaci abin da ba za su iya yi ba a gare su. (Yahaya 16:12) Yesu bai matsa wa mabiyansa ba, amma ya ƙarfafa su su yi “faman” yin nufin Allah. (Luka 13:24) Ya yi hakan ta yin shugabanci kuma ya motsa zukatansu. Hakanan ma, dattawa a yau ba za su matsa wa wasu su bauta wa Allah ta wajen kunyatar da su ba. Maimakon haka, su ƙarfafa su su bauta wa Jehobah domin suna ƙaunarsa da kuma Yesu, da kuma ’yan’uwansu ’yan adam.—Matiyu 22:37-39.

14 Yesu bai ɓata ikon da aka ɗanka masa ba ta wajen yin shisshigi a rayuwar mutane. Bai kafa mizanai da ba za a iya bi ba ko kuma dokoki masu yawa. Ya taimaki mutane ta wajen motsa zukatansu da ƙa’idodi da suka goyi bayan dokoki da aka bayar ta hannun Musa. (Matiyu 5:27, 28) Ta yin koyi da Yesu Kristi, dattawa suna ƙin yin dokoki bisa abin da suke so ko kuma nace wa nasu ra’ayi. A batun tufafi da yin ado ko kuma nishaɗi, dattawa suna ƙoƙari su motsa zuciya ta yin amfani da ƙa’idodin da ke cikin kalmar Allah, kamar waɗanda suke Mika 6:8; 1 Korantiyawa 10:31-33; da 1 Timoti 2:9, 10.

Ka Kasance Mai Tausayi Mai Gafartawa

15. Yaya Yesu ya bi da kasawar almajiransa?

15 Kristi ya bar mana gurbi da za mu bi a yadda ya bi da kasawa da kurakuran almajiransa. Ka yi la’akari da abubuwa biyu da suka faru a darensa na ƙarshe a duniya. Da suka isa Gatsemani, Yesu ya “ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya” kuma ya gaya musu “ku zauna a faɗake.” “Da ya ci gaba kaɗan, sai ya faɗi ƙasa, ya yi addu’a.” Da ya dawo “ya samu suna barci.” Menene Yesu ya yi? Ya ce: “Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.” (Markus 14:32-38) Maimakon ya tsauta wa Bitrus, Yakubu, da Yahaya sosai, sai ya ji tausayinsu! A daren nan, Bitrus ya yi musun sanin Yesu sau uku. (Markus 14:66-72) Yaya Yesu ya bi da Bitrus bayan haka? “Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!” (Luka 24:34) “Ya kuma bayyana ga Kefas” in ji Littafi Mai Tsarki, “sa’an nan ga sha biyun.” (1 Korantiyawa 15:5) Maimakon ya yi ƙiyayya, Yesu ya gafarta wa manzon da ya tuba kuma ya ƙarfafa shi. Bayan haka, Yesu ya ɗanka wa Bitrus hakki mai girma.—Ayyukan Manzanni 2:14; 8:14-17; 10:44, 45.

16. Ta yaya za mu aikata yadda Yesu ya yi sa’ad da ’yan’uwanmu suka yi mana laifi?

16 Sa’ad da ’yan’uwanmu suka yi mana laifi domin ajizancin ’yan adam, ya kamata mu ji tausayinsu kuma mu gafarta musu yadda Yesu ya yi. Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi: “Dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar ’yan’uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali’u. Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka sai ku sa albarka.” (1 Bitrus 3:8, 9) Idan wani bai bi da mu yadda Yesu zai yi ba, yana ƙin jin tausayi da gafartawa kuma fa? Har ila wajibi ne mu yi ƙoƙari mu yi koyi da Yesu kuma mu aikata yadda zai yi.—1 Yahaya 3:16.

Ka Sa Al’amura ta Mulki Farko

17. Menene ya nuna cewa Yesu ya sa yin nufin Allah farko a rayuwarsa?

17 Da wata hanya kuma da ya kamata mu yi zaman da Yesu Kristi ya yi. Yin wa’azin Mulkin Allah ne ya fi muhimmanci ga Yesu. Bayan ya yi wa mace Basamariya wa’azi kusa da birnin Saikar a Samariya, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.” (Yahaya 4:34) Yin nufin Ubansa ya kiyaye Yesu; ya gamsar da shi kuma ya wartsake shi kamar abinci. Yin koyi da Yesu ta wajen mai da hankali ga yin nufin Allah zai sa mu yi rayuwa mai ma’ana mai gamsarwa kuma.

18. Waɗanne albarka ake samu ta ƙarfafa yara su soma hidima ta cikakkiyar lokaci?

18 Sa’ad da iyaye suka ƙarfafa yaransu su soma hidima ta cikakkiyar lokaci, su da ’ya’yansu na samun albarka mai yawa. Uban tagwaye maza ya ƙarfafa yaransa tun suna ’yan yara su sa aikin majagaba ya zama makasudinsu. Bayan sun gama makarantarsu, tagwayen sun zama majagaba. Da yake maganar farin cikinsa domin wannan, baban ya rubuta: “ ’Ya’yanmu ba su ba mu kunya ba. Da godiya za mu iya faɗa cewa ‘Ya’ya kyauta ne daga wurin Ubangiji.’ ” (Zabura 127:3) Ta yaya yara suke amfana daga biɗan hidima ta cikakkiyar lokaci? Uwa mai yara biyar ta ce: “Majagaba ya taimaki dukan yarana su ƙulla dangantaka ta kusa da Jehobah, ya kyautata yadda suke nazari na kansu, ya taimake su su koyi yadda za su yi amfani da lokacinsu da kyau, ya taimake su su koyi saka abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarsu. Ko da dukansu sun yi gyara da yawa, babu wani cikinsu da ya yi da na sani ga tafarkin da ya zaɓa.”

19. Wane shiri don nan gaba ya kamata matasa su yi la’akari da shi da kyau?

19 Matasa, menene kuke shirin yi a nan gaba? Kuna nema ku sami ci gaba a wata sana’a? Ko kuma kuna yin abin da zai sa ku shiga hidima ta cikakken lokaci? Bulus ya yi gargaɗi: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.” Ya daɗa: “Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da ke nufin Ubangiji.”—Afisawa 5:15-17.

Ka Kasance Mai Aminci

20, 21. Ta yaya Yesu ya kasance da aminci, ta yaya za mu yi koyi da amincinsa?

20 Don mu yi irin zaman da Yesu ya yi za mu yi koyi da amincinsa. Littafi Mai Tsarki ya yi maganar amincin Yesu yana cewa: “Ko da ya ke surar Allah yake, bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba, sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta [gungumen azaba].” Yesu da aminci ya ɗaukaka ikon mallakar Jehobah ta wajen yin nufin Allah dominsa. Ya kasance da aminci har mutuwa a kan gungumen azaba. Dole ne mu “ɗauki halin” nan kuma mu miƙa kai da aminci a yin nufin Allah.—Filibiyawa 2:5-8.

21 Yesu ya kuma kasance da aminci ga manzanninsa masu aminci. Duk da kumamancinsu da ajizancinsu, Yesu ya ƙaunace su “har matuƙa.” (Yahaya 13:1) Haka nan ma, bai kamata mu ƙyale ajizancin ’yan’uwanmu ya sa mu soma kushe mutane ba.

Ka Bi Gurbin Da Yesu Ya Kafa

22, 23. Waɗanne fa’idodi ne ake samu ta manne wa gurbin da Yesu ya kafa?

22 Da yake mu ajizai ne, ba za mu iya bin sawun wanda muke bin misalinsa daidai ba. Amma, muna iya ƙoƙari mu bi sawunsa a tsanake. Muna bukatar mu fahimci kuma mu yi biyayya ga yadda Kristi yake shugabanci kuma mu bi gurbin da ya kafa.

23 Yin koyi da Kristi zai sa mu sami albarka mai yawa. Domin muna mai da hankali ga yin nufin Allah maimakon namu, rayuwarmu za ta zama mai ma’ana kuma mai gamsarwa. (Yahaya 5:30; 6:38) Za mu kasance da lamiri mai tsabta. Rayuwarmu za ta zama abin koyi. Yesu ya gayyaci duka masu wahala, masu fama da kaya su zo gare shi kuma su sami kwanciyar rai. (Matiyu 11:28-30) Sa’ad da muka bi misalin Yesu, mu ma za mu wartsake wasu ta tarayyarmu da su. Bari mu ci gaba da yin irin zaman da Yesu ya yi.

Ka Tuna?

• Ta yaya Kristi ke shugabancin mabiyansa a yau?

• Ta yaya dattawa za su bi shugabancin Kristi sa’ad da suke nuna ikon da Allah ya ba su?

• Ta yaya za mu bi misalin Yesu sa’ad da muke bi da kasawar wasu?

• Ta yaya matasa za su sa al’amuran Mulki farko?

[Hoto a shafi na 13]

Dattawa na taimakonmu mu bi shugabancin Kristi

[Hotuna a shafuffuka na 14, 15]

Matasa, wane shiri kuke yi don ku sami rayuwa mai ba da lada?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba