Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 20-24
  • Jehobah Ne Makiyayinmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ne Makiyayinmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kwatancin da Ya Dace
  • “Yana Bi da Ni”
  • ‘Ba Zan Ji Tsoro Ba, Gama Kana Tare da Ni’
  • “Ka Shirya Mini Liyafa”
  • ‘Haikalin Jehobah Zai Zama Gidana’
  • ‘Jehobah Makiyayina Ne’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Inda Za Ka Sami Ta’aziyya
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Yesu Yana Kula da Tumakinsa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 20-24

Jehobah Ne Makiyayinmu

“Ubangiji makiyayina ne, ba zan rasa kome ba.”—Zabura 23:1.

1-3. Me ya sa ba abin mamaki ba ne da Dauda ya kwatanta Jehobah da makiyayi?

IDAN aka ce ka kwatanta yadda Jehobah yake kula da mutanensa, me za ka ce? Da wa za ka kwatanta shi da zai nuna yadda yake kula da bayinsa masu aminci cikin ƙauna? Fiye da shekara 3,000 da ta shige, Sarki Dauda mai zabura ya rubuta kyakkyawan kwatanci na Jehobah, ya yi amfani da kwatanci daga aikin da ya yi sa’ad da yake yaro.

2 Sa’ad da yake yaro, Dauda makiyayi ne. Saboda haka, ya san yadda ake kula da tumaki. Ya san cewa tumaki, idan aka ƙyale su ba makiyayi, babu wuya za su ɓata, ɓarayi su sace su ko kuma namun daji su cinye su. (1 Sama’ila 17:34-36) Idan ba tare da makiyayi mai kula ba, ba za su iya samun wurin kiwo ba. Sa’ad da ya manyanta babu shakka Dauda yana tuna awoyi masu yawa da ya yi yana ja-gorar tumaki kuma yana kāre su.

3 Ba abin mamaki ba ne da aikin makiyayi ya faɗo zuciyar Dauda sa’ad da aka hure shi ya kwatanta yadda Jehobah yake kula da mutanensa. Zabura ta 23, da Dauda ya rubuta, ta fara ne da waɗannan kalmomi: “Ubangiji makiyayina ne, ba zan rasa kome ba.” Bari mu bincika abin da ya sa wannan furcin ya dace. Sa’an nan, da taimakon Zabura ta 23, za mu ga hanyoyi dabam dabam da Jehobah yake kula da masu bauta masa kamar yadda makiyayi yake kula da tumakinsa.—1 Bitrus 2:25.

Kwatancin da Ya Dace

4, 5. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta halin tumaki?

4 Jehobah yana da laƙabi masu yawa a cikin Nassosi, amma laƙabin nan “Makiyayi” yana cikin waɗanda suke nuna ƙauna. (Zabura 80:1) Domin mu fahimci da kyau dalilin da ya sa kiran Jehobah Makiyayi ya dace, yana da kyau mu fahimci wasu abubuwa biyu: na farko yanayin tumaki, na biyu kuma ayyuka da kuma halin makiyayin kirki.

5 Littafi Mai Tsarki sau da yawa ya yi magana game da halin tumaki, ya kwatanta su cewa suna da saurin amsa ƙaunar makiyayi (2 Sama’ila 12:3), ba su da faɗa (Ishaya 53:7), kuma ba su da kāriya. (Mika 5:8) Wani marubuci da ya yi kiwon tumaki na shekaru masu yawa ya lura cewa: “Tumaki ba sa ‘kula da kansu’ kamar yadda wasu za su yi tunani. Suna bukatar kula fiye da dukan wani garken dabbobi.” Domin su rayu waɗannan halittu suna bukatar makiyayi mai kula.—Ezekiyel 34:5.

6. Yaya wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta aiki da makiyayi na dā yake yi a yini?

6 Wane aiki makiyayi na dā yake yi a rana? Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya ba da bayani: “Da safe sai ya fito da tumakin ya sa su gaba zuwa wurin da za su yi kiwo. A nan zai yini yana lura da su saboda kada waninsu ya ɓace, amma idan ya ɓace, zai je ya neme shi har sai ya same shi ya mai da shi garke. . . . Da yamma zai mai da dabbobin gida, zai ƙirga su sa’ad da suke shiga garke domin ya tabbata cewa babu wadda ta ɓata. . . . Sau da yawa dole ne ya tsaya tsaro daddare domin ya kāre tumakin daga namun daji, ko kuma ɓarawo.a

7. Me ya sa wani lokaci makiyayi yake bukatar nuna ƙarin haƙuri da ƙauna?

7 Wani lokaci kuma tumaki, musamman tunkiya mai ciki ko jariri, suna bukatar a yi haƙuri da su kuma a nuna musu ƙauna. (Farawa 33:13) Wani littafi game da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Haihuwa ga tumaki sau da yawa yana faruwa ne nesa da gida. Makiyayin zai kāre uwar kuma ya ɗauki jaririn zuwa garke. Har sai ya fara tafiya da kansa makiyayin zai riƙa ɗaukan jaririn.” (Ishaya 40:10, 11) Hakika, makiyayin kirki ya kamata ya kasance mai ƙarfin hali kuma mai ƙauna.

8. Dauda ya ba da waɗanne dalilai ne game da tabbacinsa ga Jehobah?

8 “Ubangiji makiyayina ne”—wannan ba kwatanci ba ne da ya dace da Ubanmu na samaniya? Sa’ad da muka bincika Zabura 23, za mu ga yadda Allah yake kula da mu da ƙarfin hali da kuma ƙauna na makiyayi. A aya ta 1, Dauda ya furta tabbacinsa cewa Allah zai biya bukatun dukan tumakinsa kuma ba za su “rasa kome ba.” A ayoyin da suka biyo baya, Dauda ya ba da dalilai uku na tabbacinsa: Jehobah yana yi wa tumakinsa ja-gora, yana kāre su, yana ciyar da su. Bari mu tattauna wannan ɗaɗɗaya.

“Yana Bi da Ni”

9. Wane yanayi na salama Dauda ya kwatanta, kuma yaya tumaki za su kasance a irin wannan wurin?

9 Da farko, Jehobah yana bi da mutanensa. Dauda ya rubuta: “Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa, yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif. Yana ba ni sabon ƙarfi. Yana bi da ni a hanyar da ke daidai kamar yadda ya alkawarta.” (Zabura 23:2, 3) Tumaki kwance cikin salama da yalwar abinci, a nan Dauda yana kwatanta yanayi ne na wadatar zuci, wartsakewa, da kwanciyar hankali. Kalmar Ibrananci da aka fassara “ɗanyar ciyawa” tana iya nufin “wuri mai ni’ima.” Wataƙila, tumakin ba za su iya samun wuri mai wartsakewa ba domin su kwanta cikin kwanciyar hankali. Makiyayinsu dole ne ya kai su irin wannan “wuri mai ni’ima.”

10. Ta yaya Allah ya nuna yardarsa da mu?

10 Ta yaya Jehobah yake yi mana ja-gora a yau? Hanya ɗaya da yake yin haka ta wajen misali ne. Kalmarsa ta aririce mu mu “zama masu koyi da Allah.” (Afisawa 5:1) Waɗannan kalmomi sun ƙunshi tausayi, yin gafara, da kuma ƙauna. (Afisawa 4:32; 5:2) Babu shakka, Jehobah ya kafa misali mafi kyau ƙwarai na nuna irin waɗannan halayen kirki. Yana bukatar abin da ya fi ƙarfinmu ne da ya ce mu yi koyi da shi? A’a. Wannan shawarar daga Allah tabbaci ce ta yardarsa da mu. A wace hanya? An halicce mu a kamanin Allah, wato, an halicce mu da halaye na ɗabi’a da kuma iyawa na kasancewa da ruhaniya. (Farawa 1:26) Saboda haka, Jehobah ya sani cewa duk da ajizancinmu, muna iya koyon wasu halayensa. Ka yi tunani, mahaliccinmu yana da tabbacin cewa muna iya zama kamarsa. Idan muka bi misalinsa, zai yi mana ja-gora, zuwa wuri mai ni’ima ‘na hutu.’ A duniya ta fin ƙarfi, mu za mu ‘zauna cikin kwanciyar hankali,’ mu sami salama da take samuwa daga sanin cewa Allah ya yarda da mu.—Zabura 4:8; 29:11.

11. Sa’ad da yake yi wa tumakinsa ja-gora, menene Jehobah yake yin la’akari da shi, kuma ta yaya wannan yake shafar abin da yake bukata a gare mu?

11 Sa’ad da yake mana ja-gora, Jehobah yana da ƙauna da haƙuri. Makiyayi yana yin la’akari da kasawar tumakinsa, saboda haka, yana ja-gora ‘bisa saurin tumakin.’ (Farawa 33:14) Haka ma Jehobah yana ja-gora “bisa saurin” tumakinsa. Yana la’akari da iyawarmu da kuma yanayinmu. Wato, yana rage sawunsa, ba ya bukatar fiye da abin da za mu iya bayarwa. Abin da yake bukata shi ne mu kasance da zuciya ɗaya. (Kolosiyawa 3:23) Amma idan ka tsufa kuma ba ka iya yin hidima kamar yadda ka saba yi fa? Ko kuma idan rashin lafiya ya rage abin da kake yi? A nan kyaun bukatar mu kasance da zuciya ɗaya yake. Babu mutane biyu masu zuciya iri ɗaya. Hidima da zuciya ɗaya tana nufin cewa mutum ya yi amfani da dukan ƙarfinsa iyaka yadda ya yiwu a gare sa wajen hidimar Allah. Duk da matsaloli da muke fuskanta, Jehobah yana ɗaukan bautarmu da zuciya ɗaya da muhimmanci.—Markus 12:29, 30.

12. Wane misali ne daga Dokar Musa ya nuna cewa Jehobah yana ja-gora ne “bisa saurin” tumakinsa?

12 Domin a kwatanta cewa Jehobah yana ja-gora ne bisa ga “saurin” tumakinsa, ka yi la’akari da wani abin da aka faɗa game da hadaya na zunubi a Dokar Musa. Jehobah yana bukatar kyauta ne mai kyau ta nuna godiya. Duk da haka, kyautar ta dangana ne bisa ƙarfin mai bayarwa. Dokar ta ce: “Idan ’yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.” Idan kurciyoyin ma sun fi ƙarfinsa fa? Sa’an nan zai iya kawo “gari mai laushi.” (Littafin Firistoci 5:7, 11) Wannan ya nuna cewa Allah ba ya bukatar abin da ya fi ƙarfin mai bayarwa. Tun da Allah har a yau bai canja ba, muna iya samun ƙarfafa daga sanin cewa ba ya bukatar abin da ya fi ƙarfinmu; maimakon haka, yana farin ciki da dukan abin da za mu iya bayarwa. (Malakai 3:6) Abin farin ciki ne ƙwarai irin wannan Makiyayi ya yi mana ja-gora!

‘Ba Zan Ji Tsoro Ba, Gama Kana Tare da Ni’

13. A Zabura 23:4, ta yaya Dauda ya yi magana da ya nuna ya shaƙu da Allah, kuma me ya sa wannan ba abin mamaki ba ne?

13 Dauda ya ba da dalili na biyu na dogararsa: Jehobah yana kāre tumakinsa. Mun karanta: “Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka suna kiyaye lafiyata.” (Zabura 23:4) Yanzu Dauda ya nuna ya shaƙu da Jehobah har yana kiransa da wakilin suna “ka.” Dauda yana magana ne game da yadda Allah ya taimake shi ya jimre bala’i. Dauda ya bi cikin wurare masu duhu da yawa, a wasu lokatai ransa ma a cikin haɗari take. Amma bai ƙyale tsoro ya kama shi ba, domin ya fahimci cewa Allah, da ‘sandansa’ da ‘kerensa’ yana tare da shi. Hakika, fahimtar Allah yana tare da shi, ya ƙarfafa Dauda kuma ya sa ya matsa kusa da Jehobah.b

14. Wane tabbaci ne Littafi Mai Tsarki ya ba mu game da kāriyar Jehobah, kuma menene wannan ba ya nufi?

14 Ta yaya Jehobah yake kiyaye tumakinsa a yau? Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa babu ɗan hamayya, aljani ko ɗan adam, da zai yi nasara wajen shafe tumakinsa daga duniya. Jehobah ba zai ƙyale haka ba. (Ishaya 54:17; 2 Bitrus 2:9) Amma fa, wannan ba ya nufin cewa Makiyayinmu zai kāre mu daga dukan bala’i. Muna fuskantar masifu da mutane suke fuskanta, kuma muna fuskantar hamayya da dukan Kiristoci na gaskiya suke fuskanta. (2 Timoti 3:12; Yakubu 1:2) Da lokatai da muke, inda za a iya kira wurare masu “duhu.” Alal misali, yana iya kasancewa saura kaɗan mu mutu domin tsanantawa ko kuma wani ciwo. Ko kuma wani na kusa da mu ya kusan mutuwa ko kuwa ya mutu. A irin wannan lokaci da zai kasance mai duhu, Makiyayinmu yana tare da mu, kuma zai kāre mu. Ta yaya?

15, 16. (a) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimakonmu mu jimre wa matsaloli da muke fuskanta? (b) Ka ba da labarin da ya nuna cewa Jehobah yana taimakonmu a lokacin matsaloli.

15 Jehobah bai yi alkawarin mu’ujiza ba.c Muna iya tabbatawa da wannan: Jehobah zai taimake mu mu fi ƙarfin dukan wata matsala da za mu fuskanta. Zai ba mu hikima da za mu jimre wa “gwaje-gwaje iri iri.” (Yakubu 1:2-5) Makiyayi yana amfani da sandarsa ko kuma kerensa ba kawai domin ya kori namun daji ba amma kuma domin ya ja-goranci tumakinsa. Jehobah yana iya “nuna” mana hanya, wataƙila ta wurin wani ɗan’uwa mai bi, domin mu yi amfani da wani gargaɗin Littafi Mai Tsarki da zai canja rayuwarmu ƙwarai. Ƙari ga haka, Jehobah yana iya ba mu ƙarfin da za mu jure. (Filibiyawa 4:13) Ta wurin ruhunsa mai tsarki, yana iya ba mu “mafificin ikon.” (2 Korantiyawa 4:7) Ruhun Allah yana iya sa mu jimre dukan wani gwaji da Shaiɗan zai kawo a gare mu. (1 Korantiyawa 10:13) Ba abin farin ciki ba ne mu sani cewa Jehobah yana shirye a kowane lokaci ya taimake mu?

16 Hakika, kowane irin duhu muka sami kanmu a ciki, ba za mu yi tafiya a cikinsa mu kaɗai ba. Makiyayinmu yana tare da mu, yana taimakonmu a hanyoyin da da farko ba za mu fahimta da wuri ba. Ka yi la’akari da misalin wani dattijo Kirista da aka gwada shi aka ga yana da kumburi a ƙwaƙwalwa. “Da farko, ina ta tunani ko Jehobah ya yi fushi da ni ne, ko kuwa ba ya ƙaunata. Amma na ƙuduri aniya ba zan janye ba daga Jehobah. Maimakon haka, na gaya masa damuwata. Kuma Jehobah ya taimake ni, sau da yawa yana ƙarfafa ni ta wurin ’yan’uwa maza da mata. Yawancinsu sun gaya mini yadda suka jimre da cututtuka masu tsanani. Kalamansu sun tuna mini cewa abin da nake fuskanta ba wani sabon abu ba ne. Taimako na zahiri, da suka haɗa da wasu alheri masu taɓa zuciya, sun tabbatar mini cewa Jehobah bai yi fushi da ni ba. Hakika, dole ne in ci gaba da fama da ciwona, kuma ban san sakamakon haka ba. Amma na tabbata cewa Jehobah yana tare da ni kuma zai ci gaba da taimakona a wannan gwaji da nake fuskanta.”

“Ka Shirya Mini Liyafa”

17. Yaya Dauda ya kwatanta Jehobah a Zabura ta 23:5, kuma me ya sa wannan bai saɓa wa kwatancin makiyayi ba?

17 Dauda ya faɗi dalili na uku na dogarar shi ga Makiyayinsa: Jehobah yana ciyar da tumakinsa, kuma yana yin haka a yalwace. Dauda ya rubuta: “Ka shirya mini liyafa inda maƙiyana duk za su iya ganina, ka marabce ni, ka shafe kaina da mai, ka cika tanduna fal da mai.” (Zabura 23:5) A wannan ayar, Dauda ya kwatanta makiyayinsa cewa magidanci ne mai karimci wanda yake yin tanadin abinci da abin sha a yalwace. Kwatancin biyu na makiyayi mai ƙauna da kuma magidanci mai karimci ba su saɓa wa juna ba. Tun da ma makiyayin kirki dole ne ya san inda zai sami wajen kiwo mai kyau da kuma wurin da ake samun isashen ruwa domin kada tumakinsa su “rasa kome.”—Zabura 23:1, 2.

18. Menene ya nuna cewa Jehobah magidanci ne mai karimci?

18 Makiyayinmu shi ma magidanci ne mai karimci? Wannan haka yake! Ka yi tunanin inganci, yawa, da kuma ire-iren abinci na ruhaniya da muke mora. Ta wajen amintaccen bawan nan mai hikima, Jehobah yana yi mana tanadin littattafai masu taimako da kuma tsari mai kyau a taro, da manyan taro, da taron gunduma, kuma duka suna biya mana bukatunmu na ruhaniya. (Matiyu 24:45-47) Hakika ba ma karancin abinci na ruhaniya. “Amintaccen bawan nan mai hikima” ya yi tanadin miliyoyin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai domin taimako a yi nazarinsa, kuma irin waɗannan littattafai ana samunsu cikin harsuna 413. Jehobah yana yin tanadin wannan abinci na ruhaniya iri-iri, daga “madara” wato, koyarwa masu sauƙi na Littafi Mai Tsarki, zuwa “abinci mai tauri,” wato, koyarwa masu zurfi na ruhaniya. (Ibraniyawa 5:11-14) Domin haka, sa’ad da muke fuskantar matsaloli, za mu sami daidai abin da muke bukata. Idan ba tare da waɗannan abinci na ruhaniya ba za mu wahala. Makiyayinmu hakika mai karimci ne ƙwarai da gaske!—Ishaya 25:6; 65:13.

‘Haikalin Jehobah Zai Zama Gidana’

19, 20. (a) A Zabura 23:6, wane tabbaci Dauda ya furta, kuma ta yaya za mu kasance da irin wannan tabbaci? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

19 Bayan ya yi bimbini bisa hanyoyin Makiyayinsa kuma Mai ba shi, Dauda ya ce: “Hakika, alherinka da ƙaunarka, za su kasance tare da ni muddin raina. Haikalinka zai zama gidana har abada.” (Zabura 23:6) Dauda ya furta zuciyarsa ce da take cike da godiya da bangaskiya, godiya domin abin da ya shige da kuma bangaskiya kuwa domin abin da ke zuwa. Wannan makiyayi na dā yana da kwanciyar hankali, domin ya sani cewa idan ya ci gaba da kasancewa kusa da Makiyayinsa, kamar a ce yana da zama a haikalinsa, zai kasance abin ƙaunar Jehobah.

20 Muna masu godiya domin waɗannan kalmomi da suke rubuce cikin Zabura ta 23! Babu wata hanya da za ta fi wannan da Dauda zai samu ya kwatanta yadda Jehobah yake ja-gora, kāre, da kuma yadda yake ciyar da tumakinsa. An kiyaye furcin Dauda domin su ba mu tabbaci cewa mu ma za mu iya dogara ga Jehobah Makiyayinmu. Hakika, muddin muka kasance kusa da Jehobah, zai kula da mu “har abada.” Amma kuma mu tumakin, muna da hakkin bin Makiyayinmu mai girma, Jehobah. Za mu tattauna abin da wannan ya ƙunsa a talifi na gaba.

[Hasiya]

a Dubi Farawa 29:7; Ayuba 30:1; Irmiya 33:13; Luka 15:4; Yahaya 10:3, 4.

b Dauda ya rera waƙoƙi da ya yabi Jehobah domin ya cece shi daga haɗari.—Alal misali, dubi kan magana na Zabura 18, 34, 56, 57, 59, 63 na NW.

c Dubi talifin nan “Divine Intervention—What Can We Expect?” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2003 na Turanci.

Ka Tuna?

• Me ya sa kwatanta Jehobah da makiyayi da Dauda ya yi ya dace?

• Ta yaya Jehobah yake mana ja-gora da sanin ya kamata?

• A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake taimakonmu mu jimre matsaloli?

• Menene ya nuna cewa Jehobah magidanci ne mai karimci?

[Hoto a shafi na 22]

Kamar makiyayi a Isra’ila, Jehobah yake ja-gorar tumakinsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba