Ka Kusaci Allah
‘Jehobah Makiyayina Ne’
KA DUBA hoton da ke wannan shafin. Za ka iya kwatanta kwanciyar hankalin da ɗan ragon nan yake ji a ƙirjin makiyayinsa? A Zabura 23, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kamancen makiyayi da tumakinsa don ya kwatanta yadda Jehobah yake kula da masu bauta masa. Yana so mu samu kwanciyar hankali irin ta waɗanda kamar mai zabura Dauda, za su iya cewa da gaba gaɗi: ‘Jehobah Makiyayina ne.’a—Aya 1.
Dauda, marubucin wannan zaburar, makiyayi ne sa’ad da yake matashi. Ya san bukatun tumaki da kuma hakkokin makiyayi. Dauda, wanda ya more kulawar Allah a rayuwarsa, ya rubuta abin da aka kira “zaburar tabbaci ko gaskatawa.” Sunan Allah, Jehobah, ya bayyana a farko da kuma ƙarshen zaburar.b (Ayoyi 1, 6) Kalmomi da ke cikin zaburar sun kwatanta hanyoyi uku da Jehobah yake kula da mutanensa, kamar yadda makiyayi yake kula da tumakinsa.—Zabura 100:3.
Jehobah yana yi wa tumakinsa ja-gora. Idan tumaki ba sa tare da makiyayinsu, suna iya ɓacewa. Hakazalika, muna bukatar taimako don mu sami ja-gora mai kyau a rayuwa. (Irmiya 10:23) Dauda ya bayyana cewa Jehobah yana yi wa mutanensa ja-gora zuwa “makiyaya mai-ɗanya” da “ruwaye na hutawa.” Yana bishe su “cikin hanyoyin adalci.” (Ayoyi 2, 3) Waɗannan kwatanci na makiyayi da ke wurin da ke da dausayi suna tabbatar da mu cewa za mu iya dogara ga Allah. Idan muka bi ja-gorancin ruhunsa kamar yadda aka nuna a cikin Littafi Mai Tsarki, za mu iya biɗar rayuwar da za ta sa mu samu gamsuwa da ƙarfafawa da kuma kwanciyar hankali.
Jehobah yana kāre tumakinsa. Tumaki suna iya ruɗewa su kuma tsorata idan ba sa tare da makiyayinsu. Jehobah yana gaya ma mutanensa cewa ba sa bukatar su ji tsoro, ko da suna ‘tafiya a tsakiyar kwari na inuwar mutuwa,’ wato, lokacin da suke fuskantar masifu masu tsanani. (Aya 4) Jehobah yana kula da su, kuma a shirye yake a kowane lokaci don ya taimake su. Zai iya ba masu bauta masa hikima da ƙarfin da suke bukata don su jure wa gwaji.—Filibiyawa 4:13; Yaƙub 1:2-5.
Jehobah yana ciyar da tumakinsa. Tumaki sun dogara ne da makiyayinsu don samun abinci. Muna da bukata ta ruhaniya wadda Allah ne kaɗai zai iya biya mana ita. (Matta 5:3) Abin godiya, Jehobah Mai karimci ne ƙwarai, wanda yake yi wa mabiyansa tanadin abinci na ruhaniya a yalwace. (Aya 5) Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, kamar wannan mujallar da kake karantawa, duk hanyoyi ne na samun abinci na ruhaniya da ke biyan bukatunmu na sanin ma’anar rayuwa da kuma nufin Allah a gare mu.
Dauda ya samu kwanciyar hankali, don ya san cewa idan ya ci gaba da kasancewa kusa da Makiyayinsa na sama, zai more kulawar da ke cike da ƙauna daga Jehobah, ‘dukan kwanakin ransa.’ (Aya 6) Kana ɗokin samun irin wannan kwanciyar hankalin? Idan haka ne, ka koyi yadda za ka kusaci Jehobah. Da haka, za ka iya kasance da kwanciyar hankali a damtsen Babban Makiyayi, wanda yake yin ja-gora, yake kāre da kuma ciyar da waɗanda suka kasance da aminci a gare shi.—Ishaya 40:11.
[Hasiya]
a Masu karatu da yawa sun saba da wannan fassarar “UBANGIJI Makiyayina ne.” Don sanin dalilin da ya sa wasu fassarar suka cire sunan Allah, wato, Jehobah, daga nasu Littafi Mai Tsarki, ka duba littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Kalmar nan “Ubangiji” da ke cikin surorin nan, an rubuta ta ne a matsayin “Jehobah” a cikin rubutu na ainihi.