Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 4/1 pp. 11-14
  • “Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Farilla Mai Muhimmanci
  • Su Waye Ya Kamata Su Zama Abokanmu?
  • Zaɓan Aiki
  • “A Cikin Dukan Al’amuranka ka Shaida Shi”
  • Ka Biɗi Hikima ta Allah
  • Koyaushe Ne Sakamakon Yake da Kyau?
  • Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Riƙa Tsai da Shawarwari Masu Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 4/1 pp. 11-14

“Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa”

“Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.”—ROMAWA 14:12.

1. Wane hakki ne Ibraniyawa uku suka cika da kyau?

MATASA Ibraniyawa uku da ke da zama a Babila sun fuskanci batun da ya shafi rayuwarsu. Za su bauta wa wani babban gunki, yadda dokar ƙasar ta ce a yi ne? Ko kuwa za su ƙi bauta masa kuma a jefa su cikin tanderun gagarumar wuta? Shadrak, Meshak, da Abednego ba su da lokacin neman shawarar kowa, kuma ba sa bukatar yin haka. Babu ɓata lokaci suka ce: “A sanashe ka, ya sarki, ba za mu bauta ma allohinka ba, ba kuwa za mu yi sujada ga gunki na zinariya wanda ka kafa.” (Daniel 3:1-18) Ibraniyawan uku sun ɗauki kayan kansu.

2. Wanene ainihi ya tsai da wa Bilatus shawara game da Yesu Kristi, hakan zai hana wannan gwamna ne daga Roma ya ba da lissafi?

2 Ƙarnuka shida bayan haka, gwamnan ya ji tuhumar da aka yi wa mutumin. Da ya bincika batun, ya ga cewa mutumin ba shi da laifi. Amma, taron sun ce a kashe shi. Bayan ya ɗan yi ƙoƙarin ya ƙi bin abin da suka faɗa, gwamnan ya yi jinkiri ya cika hakkinsa kuma ya faɗa wa matsi. Ya wanke hannuwansa ya ce: “Baratace ni ke daga jinin wannan mai-adalci.” Sai ya miƙa shi a tsire. Hakika, maimakon ya cika hakkinsa ya tsai da shawara game da Yesu Kristi, Bilatus Babunti ya bar wasu su tsai da masa shawara. Ba yawan ruwan da zai kuɓutar da shi daga ba da lissafin zartar da hukuncin da bai dace ba a kan Yesu.—Matta 27:11-26; Luka 23:13-25.

3. Me ya sa bai kamata mu ƙyale mutane su tsai da mana shawara ba?

3 Kai kuma fa? Idan za ka tsai da shawara, kana kama da Ibraniyawa uku, ko kuwa kana ƙyale wasu su tsai da maka shawara? Tsai da shawara ba shi da sauƙi. Mutum na bukatar ya manyanta don ya yi zaɓe da ya dace. Alal misali, iyaye suna bukatar su tsai da wa yaransu ƙanƙanana shawara mai kyau. Hakika, tsai da shawara yana da wuya idan yanayin mai wuya ne kuma za a bincika wasu abubuwa. Amma, hakkin tsai da shawara ba shi da wuya ainun da za a haɗa shi cikin “kaya” ko abubuwa masu ban wahala da “masu-ruhaniya” za su taya mu ɗauka. (Galatiyawa 6:1, 2) Maimakon haka, kaya ne da “kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Romawa 14:12) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane mutum za ya ɗauki kayan kansa.” (Galatiyawa 6:5) To, ta yaya, za mu tsai da shawara mai kyau a rayuwa? Na farko, dole ne mu fahimci cewa muna da kasawa kuma mu koyi abin da ake bukata don mu daidaita su.

Farilla Mai Muhimmanci

4. Wane darasi mai muhimmanci ne ya kamata mu koya daga rashin biyayyar ma’aurata na farko?

4 Ba da daɗewa ba bayan somawar tarihin ’yan adam, ma’aurata na farko sun tsai da shawara da ta kawo mugun sakamako. Sun zaɓi su ci ’ya’yan itace na sanin nagarta da mugunta. (Farawa 2:16, 17) Me ya sa suka tsai da wannan shawara? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima, sai ta ɗiba ’ya’yansa, ta ci; ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci.” (Farawa 3:6) Hauwa’u ta yi zaɓe bisa son kai. Abin da ta yi ya sa Adamu ya bi ta. Shi ya sa zunubi da mutuwa suka “bi kan dukan mutane.” (Romawa 5:12) Ya kamata rashin biyayyar Adamu da Hauwa’u su koya mana darasi mai muhimmanci game da kasawar ’yan adam. Darasin shi ne, idan ’yan adam suka ƙi bin ja-gorar Allah, ba za su tsai da shawarar da ta dace ba.

5. Wane ja-gora ne Jehobah ya yi mana tanadinsa, menene dole ne mu yi don mu amfana daga ja-gorar?

5 Abin farin ciki ne cewa Jehobah Allah yana mana ja-gora! Nassosi sun gaya mana: “Kunnuwanka kuma za su ji magana daga bayanka, tana cewa, wannan ita ce hanya, ku bi ta; yayinda ku ke juyawa ga dama, da yayinda ku ke juyawa ga hagu.” (Ishaya 30:21) Jehobah yana mana magana ta wurin hurarriyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Dole ne mu yi nazarin Nassosi kuma mu samu cikakken sani. Don mu yi zaɓen da ya dace, ya kamata mu ci abinci “mai-ƙarfi domin isassun mutane.” Idan muka yi hakan, za mu koyar da hankalinmu don “rabewar nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Za mu iya koyar da hankalinmu ta yin amfani da abin da muka koya daga Kalmar Allah.

6. Menene ake bukata don lamirinmu ya yi aiki da kyau?

6 Lamirinmu yana da muhimmanci ga tsai da shawara. Wannan lamiri na iya zartar da hukunci, kuma yana iya ‘kai ƙara ko kawo hujja’ game da mu. (Romawa 2:14, 15) Don lamirinmu ya yi aiki da kyau, dole ne a koyar da shi da cikakken sanin Kalmar Allah kuma a sa ya kasance mai aiki ta bin abin da Kalmar ta ce. Al’adu da halaye na iya rinjayar lamiri da ba a koyar ba da sauƙi. Mahallinmu da kuma ra’ayin mutane zai iya yaudararmu. Menene ke faruwa da lamirinmu sa’ad da muka yi banza da abin da yake gaya mana a kai a kai kuma muka taka mizanan Allah? Da shigewar lokaci, lamirin zai iya yin lalas sai ka ce an soke shi da “ƙarfe mai-wuta,” ya zama kamar tabo a jiki. (1 Timothawus 4:2) A wata sassa, lamiri da aka koyar da Kalmar Allah ja-gora ne mai kyau.

7. Menene farilla mafi muhimmanci wajen tsai da shawara mai kyau?

7 Farilla na musamman don tsai da shawara mai kyau, shi ne samun cikakken sani na Nassosi da kuma yin amfani da shi. Maimakon mu tsai da shawara da gaggawa, ya kamata mu ba da lokaci sosai mu bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma mu yi amfani da hankalinmu. Ko idan ya zama dole mu tsai da shawara nan da nan kamar Shadrak, Meshak, da kuma Abednego, za mu kasance a shirye idan mun san Kalmar Allah sosai kuma mun koyar da lamirinmu da ita. Don mu ga yadda manyantarmu zai iya kyautata tsai da shawararmu, bari mu bincika wurare biyu na rayuwa.

Su Waye Ya Kamata Su Zama Abokanmu?

8, 9. (a) Waɗanne farillai suka nuna bukatar guje wa tarayya da miyagu? (b) Yin abokantaka kawai da mutane marasa ƙa’ida ne tarayya da miyagu? Ka ba da bayani.

8 Manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) Yesu Kristi ya gaya wa almajiransa: “Ku ba na duniya ba ne.” (Yohanna 15:19) Da yake mun koyi waɗannan farillan, hakan ya sa mun fahimci bukatar guje wa tarayya da masu fasikanci, mazinata, ɓarayi, masu maye, da sauransu. (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Yayin da muka ci gaba da sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki, za mu fahimci cewa zama da irin waɗannan mutane ta kallonsu a bidiyo, a talabijin, a kwamfuta ko kuma karanto game da su a littattafai yana da lahani. Haka yake kuma da tarayya da “masu-makirci” a wurin hira na Intane.—Zabura 26:4.

9 Yin tarayya da waɗanda suke da tsabtaccen ɗabi’a amma ba su ba da bangaskiya ga Allah na gaskiya kuma fa? Nassosi sun gaya mana: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Mun fahimci cewa tarayya da miyagu ba kawai mutane da suke da mummunar ɗabi’a ba ne. Saboda haka, yana da kyau mu yi abokantaka kaɗai da waɗanda suke ƙaunar Jehobah.

10. Menene ke taimakonmu mu tsai da shawara mai kyau game da yin sha’ani da duniya?

10 Ba zai yiwu ba a guje wa tarayya gabaki ɗaya da mutanen duniya kuma bai dace ba. (Yohanna 17:15) Za mu yi tarayya da mutanen duniya sa’ad da muke wa’azi, a makaranta, da kuma wajen aiki. Kirista da abokiyar aurensa marar bi ce zai fi tarayya da duniya. Amma da yake mun koyar da hankalinmu za mu fahimci cewa ɗan sha’ani da duniya da kuma abokantaka da ita sosai sun bambanta. (Yaƙub 4:4) Da haka, za mu iya tsai da shawara mai kyau ko za mu sa hannu cikin ayyuka da ake yi idan aka tashi daga makaranta, kamar su guje guje da rawa, da zuwa liyafa da dina da aka shirya wa abokan aiki.

Zaɓan Aiki

11. Menene abu na farko da za mu yi la’akari da shi sa’ad da muka tsai da shawarar neman aiki?

11 Yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a hanyar da ta dace na taimakonmu wajen tsai da shawara game da yadda za mu cika hakkinmu na ‘tattalin iyalinmu.’ (1 Timothawus 5:8) Abu na farko da za mu mai da hankali shi ne irin aikin da za mu yi, da abin da yake bukata mu yi. Zaɓan aikin da ke tallafa wa abin da Littafi Mai Tsarki ya hana kai tsaye ba shi da kyau. Shi ya sa Kiristoci na gaskiya ba sa ayyuka da suka ƙunshi bautar gumaka, sata, wasa da jini ko wasu ayyuka da ba na nassi ba. Ba za mu yi ƙarya ba ko kuma mu cuci wasu, ko idan shugaban aikinmu ya ce mu yi hakan.—Ayukan Manzanni 15:29; Ru’ya ta Yohanna 21:8.

12, 13. Ban da irin aikin da za mu yi, waɗanne abubuwa ne suke da muhimmanci wajen tsai da shawara game da aiki?

12 Idan aikin ainihi bai taka kowace farilla na Allah kuma fa? Yayin da muka ƙara sanin gaskiya kuma hankalinmu ya koyu, za mu ga wasu abubuwa da ya kamata mu bincika. Idan aikin zai sa mu sa hannu a wasu ayyuka da ba na nassi ba fa, kamar amsa tarho a gidan caca? Ya kamata mu yi la’akari da inda ake samun kuɗin da kuma wurin aikin. Alal misali, Kirista da yake aikin kwangila zai karɓi aiki da ya ƙunshi shafa fenti a cocin Kiristendam, ta haka ya taimaka wajen ɗaukaka addinin ƙarya?—2 Korinthiyawa 6:14-16.

13 Idan shugaban aikinmu ya karɓi aikin adana wurin addinin ƙarya kuma fa? A irin wannan yanayi, muna bukatar mu yi la’akari da yawan yadda muke mai da hankali ga abin da ake yi da kuma yadda muke sa hannu. Yin aikin da Littafi Mai Tsarki bai hana ba kuma fa, kamar, idar da wasiƙu ko’ina a yankin, har da wurare da ake mummunan abubuwa? Ya kamata ƙa’ida da ke Matta 5:45 ta shafi irin shawarar da za mu tsai da. Ya kamata mu yi la’akari da yadda yin aikinmu kullum zai shafi lamirinmu. (Ibraniyawa 13:18) Hakika, ɗaukan hakkinmu wajen tsai da shawara mai kyau game da aiki na bukatar mu watsa hankalinmu kuma mu koyar da lamirinmu.

“A Cikin Dukan Al’amuranka ka Shaida Shi”

14. Sa’ad da muke tsai da shawara, waɗanne abubuwa ya kamata mu bincika?

14 Shawarwari da muke yi game da wasu batutuwa, kamar zuwan babban makaranta da kuma karɓa ko kuma ƙin wasu jinya kuma fa? Sa’ad da muke tsai da shawara, dole mu bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka dace, sai mu yi amfani da tunaninmu mu aikata su. Sarki Sulemanu mai hikima na Isra’ila ta dā ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.

15. Menene muka koya daga Kiristoci na ƙarni na farko game da tsai da shawara?

15 Sau da yawa zaɓen da muke yi na shafan wasu, kuma muna bukatar mu yi la’akari da wannan. Alal misali, Kiristoci na ƙarni na farko ba sa bin hani na abinci na Dokar Musa. Suna iya cin wasu abinci da a ƙarƙashin Dokar ba su da tsabta amma suna da kyau a wasu hanyoyi. Amma, manzo Bulus ya rubuta game da nama da aka miƙa wa gunki a haikali: “Idan abinci za ya sa ɗan’uwana shi yi tuntuɓe, ba ni cin nama har abada, domin kada in sa ɗan’uwana shi yi tuntuɓe.” (1 Korinthiyawa 8:11-13) An ƙarfafa Kiristoci na farko su yi la’akari da lamirin wasu don kada su sa su tuntuɓe. Bai kamata shawarwarinmu su sa mu zama “sanadin tuntuɓe.”—1 Korinthiyawa 10:29, 32.

Ka Biɗi Hikima ta Allah

16. Ta yaya addu’a ke taimakawa wajen tsai da shawara?

16 Abin da ke taimakawa wajen tsai da shawara ita ce addu’a. Almajiri Yaƙub ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) Idan muna da aminci, za mu yi wa Jehobah addu’a mu roƙi hikima da muke bukata don mu tsai da shawara da ta dace. Sa’ad da muka yi wa Allah na gaskiya magana game da damuwarmu kuma muka nemi ja-gorarsa, ruhu mai tsarki zai taimake mu mu fahimci nassosi da muka bincika da kyau kuma ya tuna mana abubuwa da ba mu lura da su ba.

17. Ta yaya mutane za su taimake mu wajen tsai da shawara?

17 Wasu za su iya taimakonmu wajen tsai da shawara ne? Jehobah ya yi tanadin mutane da suka manyanta a cikin ikilisiya. (Afisawa 4:11, 12) Za mu iya zuwan wajensu, musamman idan shawarar da za mu tsai da mai muhimmanci ce. Mutane da suke da fahimi na ruhaniya sosai kuma sun fuskanci abubuwa da yawa a rayuwa za su iya jawo hankalinmu ga ƙarin ƙa’idodi na ibada da za su shafi shawararmu kuma su taimake mu mu “zaɓi abubuwa mafifita.” (Filibbiyawa 1:9, 10) Amma mu lura da wannan gargaɗi: Mu mai da hankali kada mu bar wasu suna tsai da mana shawara. Mu ne za mu ɗauki kayan kanmu.

Koyaushe Ne Sakamakon Yake da Kyau?

18. Menene za a ce game da sakamakon shawara mai kyau da muka tsai da?

18 Koyaushe ne shawara da aka tsai da bisa ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki kuma aka yi su daidai yake kawo sakamako mai kyau? E, a ƙarshe yana kawo sakamako mai kyau. Amma, wani lokaci yana kawo wahala na ɗan lokaci. Shadrak, Meshak, da Abednego sun sani cewa sakamakon shawararsu na ƙin bauta wa gunki mai girma yana iya zama mutuwa. (Daniel 3:16-19) Hakanan ma, bayan da manzannin suka gaya wa Majalisa na Yahudawa cewa dole su fi yin biyayya ga Allah da mutane, an dūke su kafin a sake su. (Ayukan Manzanni 5:27-29, 40) Bugu da ƙari, ‘lokaci da zarafi’ na iya shafan sakamakon kowace shawara da muka tsai da. (Mai-Wa’azi 9:11) Idan muka wahala a wata hanya duk da shawara mai kyau da muka tsai da, mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimake mu mu jimre kuma zai albarkace mu a ƙarshe.—2 Korinthiyawa 4:7.

19. Ta yaya za mu ɗauki kayan kanmu da gaba gaɗi sa’ad da muke tsai da shawara?

19 Shi ya sa, sa’ad da muke yanke shawara, dole ne mu nemi ƙa’idodin Nassosi kuma mu yi amfani da hankalinmu wajen yin amfani da su. Ya kamata mu yi godiya don taimakon Jehobah ta wurin ruhunsa mai tsarki da kuma waɗanda suka manyanta a cikin ikilisiya! Ta irin wannan ja-gora da taimako, bari mu ɗauki kayan kanmu da gaba gaɗi ta wajen tsai da shawara mai kyau.

Menene Ka Koya?

• Menene ainihi ake bukata don a tsai da shawara mai kyau?

• Ta yaya manyantarmu zai shafi waɗanda muka zaɓa abokai?

• Waɗanne abubuwa masu muhimmanci ya kamata mu yi la’akari da su sa’ad da muke tsai da shawara game da aiki?

• Wane taimako ne muke da shi don tsai da shawara?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba