Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 pp. 13-17
  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Muke Tsai da Shawarwari?
  • Dalilin da Ya Sa Tsai da Shawarwari Yake da Wuya
  • Matakai Shida na Tsai da Shawarwari Masu Kyau
  • Ka Koyar da Mutane Su Tsai da Shawarwari da Ke Ɗaukaka Allah
  • Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Yadda Za Ka Tsai da Shawarwari Masu Kyau
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Riƙa Tsai da Shawarwari Masu Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • “Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 pp. 13-17

Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah

“Mai-hankali ya kan lura da al’amuransa da kyau.”—MIS. 14:15.

1, 2. (a) Mene ne ya kamata ya zama ainihin damuwarmu game da dukan shawarwari da muke tsai da? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi la’akari da su?

MUNA tsai da shawarwari masu yawa a kowacce rana. Da yawa suna ɗan kawo sakamako na dindindin. Amma, wasu, suna shafanmu sosai a rayuwa. Ɗaukaka Allah ne ainihin abin da ya fi muhimmanci a dukan shawarwarin da muke tsai da.—Karanta 1 Korintiyawa 10:31.

2 Yana yi maka sauƙi ka tsai da shawarwari, ko kuma yana yi maka wuya ka yi hakan? Idan za mu samu ci gaba har mu manyanta, dole ne mu koya rarrabe nagarta da mugunta kuma mu tsai da shawarwari da suka jitu da tabbacinmu, ba na wani ba. (Rom. 12:1, 2; Ibran. 5:14) Waɗanne dalilai ne ya sa muke bukatar mu koya tsai da shawarwari masu kyau? Me ya sa yake da wuya mu tsai da shawarwari a wasu lokatai? Waɗanne matakai ne za mu iya ɗauka don mu tabbata cewa shawarwari da muke tsai da suna ɗaukaka Allah?

Me Ya Sa Muke Tsai da Shawarwari?

3. Mene ne bai kamata mu ƙyale ya shafi yadda muke tsai da shawarwari ba?

3 Idan muna shakka in ya zo ga batun da ya shafi mizanan Littafi Mai Tsarki, abokan makarantarmu ko abokan aikinmu za su iya kammala cewa ba mu gaskata da imaninmu ba kuma za a iya rinjayarmu da sauƙi. Suna iya yin ƙarya da cuci ko kuma sata kuma su rinjaye mu mu “bi bayan taron jama’a” ta wajen bin su ko kuma mu taimaka musu su ɓoye abin da suke yi. (Fit. 23:2) Amma, mutumin da ya san yadda ake tsai da shawarwari da ke ɗaukaka Allah ba zai ƙyale tsoro ko kuma son a amince da shi ya sa ya aikata a hanyar da ta saɓa wa lamirinsa da Littafi Mai Tsarki ya koyar ba.—Rom. 13:5.

4. Me ya sa wasu za su so su tsai da mana shawarwari?

4 Ba dukan waɗanda suke son su tsai da mana shawarwari ne suke son su yi mana lahani ba. Abokai masu nufin kirki za su iya nace mu bi shawararsu. Ko idan mun bar gida, danginmu suna iya damuwa sosai game da zaman lafiyarmu kuma suna iya ci gaba da sa baki a shawarwari masu muhimmanci da muke son mu tsai da. Alal misali, ka yi la’akari da batun jinya. Littafi Mai Tsarki ya haramta yin amfani da jini yadda bai dace ba. (A. M. 15:28, 29) Ko da yake ba a faɗa wasu batutuwa da ya shafi jinya dalla-dalla ba kuma hakan yana bukata kowannenmu ya tsai da shawara da kansa game da jinya da zai karɓa ko kuma zai ƙi.a Waɗanda muke ƙauna suna iya kasancewa da ra’ayoyi da ba su jitu da namu ba a kan waɗannan batutuwa. Amma sa’ad da muke tsai da shawara game da waɗannan batutuwa, kowanne Kirista da ya yi baftisma yana bukatar ya ɗauki “kayan kansa.” (Gal. 6:4, 5) Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu kasance da lamiri mai kyau a gaban Allah ba a gaban mutane ba.—1 Tim. 1:5.

5. Ta yaya za mu guji lalata bangaskiyarmu?

5 Ƙin tsai da shawara zai iya sa mu cikin mugun haɗari. Almajiri Yaƙub ya rubuta cewa mutum da ba ya iya tsai da shawara, ba ya “tsayawa a cikin dukan al’amuransa.” (Yaƙ. 1:8) Kamar mutum da ke cikin kwalekwale da ba shi da kwangwala da ke cikin teku mai hadari, ra’ayoyin ’yan Adam da suke canjawa za su riƙa jujjuya shi. Zai kasance da sauƙi irin wannan mutum ya lalatar da bangaskiyarsa kuma ya ga laifin wasu don mugun yanayinsa! (1 Tim. 1:19) Ta yaya za mu guji irin wannan sakamakon? Dole ne mu zama ‘kafaffu cikin bangaskiya.’ (Karanta Kolosiyawa 2: 6, 7.) Don mu tsaya da ƙarfi, dole ne mu koya tsai da shawarwari da suka nuna cewa muna da bangaskiya ga hurarriyar Kalmar Allah. (2 Tim. 3:14-17) Mene ne zai iya hana mu mu tsai da shawarwari masu kyau?

Dalilin da Ya Sa Tsai da Shawarwari Yake da Wuya

6. Ta yaya tsoro zai iya shafan mu?

6 Tsoron tsai da shawara da ba ta dace ba da tsoron kasawa da kuma tsoron zama wawaye a gaban mutane zai iya kama mu. Irin wannan damuwan daidai ne. Ba wanda yake son ya tsai da shawara da ba ta da kyau da za ta kawo masa damuwa ko kuma kunya. Ko da hakan, ƙauna da muke wa Allah da Kalmarsa za ta taimaka mana mu rage jin tsoro. A waɗanne hanyoyi? Ƙaunar da muke wa Allah za ta motsa mu a ko da yaushe mu karanta Kalmarsa da kuma littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki kafin mu tsai da shawarwari masu muhimmanci. Ta hakan za mu iya rage kurakuran da muke yi. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki zai iya “bada azanci ga marasa-wayo, ilimi da hankali ga saurayi.”—Mis. 1:4.

7. Mene ne misalin Sarki Dauda zai iya koya mana?

7 A kowanne lokaci ne za mu iya tsai da shawara da ta dace? A’a. Dukanmu muna kuskure. (Rom. 3:23) Alal misali, Sarki Dauda mutum ne mai hikima da kuma aminci. Amma, a wasu lokatai ya tsai da shawarwari da ba su dace ba da suka sa shi da wasu shan wahala. (2 Sam. 12:9-12) Duk da haka, Dauda bai bar kurakurensa su hana shi tsai da shawarwari da Allah yake amincewa da su ba. (1 Sar. 15:4, 5) Kamar Dauda, za mu iya tsai da shawara duk da cewa a dā mun yi kuskure, idan muka tuna cewa Jehobah zai mance da kurakuranmu kuma ya gafarta zunubanmu. Zai ci gaba da tallafa wa waɗanda suke ƙaunarsa kuma suke yi masa biyayya.—Zab. 51:1-4, 7-10.

8. Mene ne muka koya daga furcin manzo Bulus a kan aure?

8 Idan muna son mu tsai da shawarwari, ta yaya za mu iya rage yin alhini? Ta wajen ganewa a wasu lokatai cewa za mu iya yin zaɓi daga tafarku da yawa da suka dace. Ka yi la’akari da yadda manzo Bulus ya yi magana a kan batun aure. An hure shi ya rubuta: “Amma ga marasa-mata da gwauraye ina cewa, Ya yi kyau garesu su zama kamar yadda na ke. Amma idan ba su da daurewa, su yi aure; gama da a ƙuna gwamma a yi aure.” (1 Kor. 7:8, 9) Bulus ya ce ya fi kyau kada a yi aure, amma wannan ba zaɓin da muke da shi kaɗai ba ne.

9. Shin ya kamata mu riƙa damuwa game da yadda wasu suke ɗaukan shawarwarinmu? Ka ba da bayani.

9 Shin ya kamata mu riƙa damuwa game da yadda wasu suke ɗaukan shawarwari da muka yi? Babu shakka. Ka lura da abin da Bulus ya faɗa game da batun cin abinci da aka miƙa hadaya ga gumaka. Ya yarda cewa mutum yana iya tsai da shawara mai kyau, amma zai iya kasance da lahani ga mutum mai raunanan lamiri. Mene ne Bulus ya ƙudurta aniya zai yi? Ya rubuta: “Ni fa, idan abinci zai sa ɗan’uwana ya yi tuntuɓe, ba ni cin nama har abada, domin kada in sa ɗan’uwana ya yi tuntuɓe.” (1 Kor. 8:4-13) Mu ma muna bukatar mu yi la’akari da yadda shawarwarinmu za su shafi lamirin wasu. Hakika, ainihin damuwarmu shi ne yadda shawarwarinmu za su shafi dangantakarmu da Jehobah. (Karanta Romawa 14:1-4.) Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka mana mu tsai da shawarwari da suke ɗaukaka Allah?

Matakai Shida na Tsai da Shawarwari Masu Kyau

10, 11. (a) Ta yaya za mu guji yin girman kai cikin iyali? (b) Mene ne ya kamata dattawa su riƙa tuna wa da shi sa’ad da suke tsai da shawarwari da suka shafi ikilisiya?

10 Ka guji girman kai. Kafin mu ɗauki wani mataki, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Ina da ikon tsai da wannan shawara ne?’ Sarki Sulemanu ya rubuta: “Lokacin da girman kai ya zo, kunya tana nan tafe: Amma wurin masu-tawali’u akwai hikima.”—Mis. 11:2.

11 Iyaye suna iya ba yaransu zarafin tsai da wasu shawarwari, amma kada yara su ɗauki wannan matsayin. (Kol. 3:20) Mata suna da ɗan iko a cikin iyali amma yana da kyau su amince da ikon maigidansu. (Mis. 1:8; 31:10-18; Afis. 5:23) Hakazalika, magidanta suna bukatar su fahimci cewa ikonsu yana da iyaka kuma za su miƙa kai ga Kristi. (1 Kor. 11:3) Dattawa suna tsai da shawarwari da suka shafi ikilisiya. Amma suna tabbata cewa ba su “zarce abin da an rubuta” a cikin Kalmar Allah ba. (1 Kor. 4:6) Suna bin ja-gorar bawan nan mai aminci sosai. (Mat. 24:45-47) Za mu guji sa wa kanmu da wasu alhini da kuma baƙin ciki idan muka tsai da shawarwari sa’ad da aka ba mu ikon yin hakan.

12. (a) Me ya sa za mu yi bincike? (b) Ka bayyana yadda mutum zai iya yin irin wannan binciken.

12 Ka yi bincike. Sulemanu ya rubuta: “Tunanin mai-himma zuwa yalwata kaɗai su ke nufa: Amma kowane mai-garaje wajen tsiya ya ke nufa.” (Mis. 21:5) Alal misali, kana tunanin tayi na kasuwanci da aka yi maka? Kada yadda kake ji ya ja-gorance ka. Ka nemi shawara daga waɗanda suka san irin waɗannan abubuwa, kuma ka bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana a kan batun. (Mis. 20:18) Ka shirya binciken da kake son ka yi ta wajen lissafa abubuwa biyu da kake son ka sani, ɗaya zai yi magana a kan fa’idojin kasuwancin ɗayan kuma a kan matsalolin. Kafin ka tsai da shawara ka “yi lissafin tamanin.” (Luk 14:28) Ka yi tunanin yadda shawararka za ta shafi yanayin arzikinka da kuma dangantakarka da Jehobah. Yin bincike yana ɗaukan lokaci kuma ana bukatar ƙoƙari sosai don a yi hakan. Ta yin hakan, za ka guji saurin tsai da shawarwari da za su kawo matsaloli da kuma alhini a nan gaba.

13. (a) Yaƙub 1:5 yana ɗauke da wane tabbaci? (b) Ta yaya yin addu’a don samun hikima zai taimake mu?

13 Ka yi addu’a don samun hikima. Shawarwarinmu za su ɗaukaka Allah idan muka gaya masa ya taimaka mana mu tsai da su. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙ. 1:5) Ba abin kunya ba ne mu yarda cewa muna bukatar hikimar Allah ta taimaka mana mu tsai da shawarwari. (Mis. 3:5, 6) Ballantana ma, dogara a kan namu fahimi zai yi saurin yaudararmu. Sa’ad da muka yi addu’a don samun hikima kuma muka bincika ƙa’idodin Kalmar Allah da suka shafi batun, muna barin ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu fahimci ainihin muradinmu don son bin wani tafarki.—Ibran. 4:12; karanta Yaƙub 1:22-25.

14. Me ya sa za mu guje wa shiririta?

14 Ka tsai da shawarar. Kada ka yi saurin ɗaukan wannan matakin kafin ka yi bincike da kuma yin addu’a don samun hikima. Mutum mai hikima yana ɗaukan lokaci sosai don ya “lura da al’amuransa da kyau.” (Mis. 14:15) A wani ɓangaren kuma, kada ka yi yawan shiririta. Mai yin shiririta yakan fito da hujjoji da ba su da muhimmanci don ɗauka wani mataki. (Mis. 22:13) Amma har ila yana tsai da shawara, yana barin wasu su ja-goranci rayuwarsa.

15, 16. Mene ne ake bukata don a aikata wata shawara?

15 Ka aikata shawarar da ka tsai da. Idan muka tsai da shawara kuma ba mu aikata ta ba, shawarar ba za ta kasance da amfani ba. Sulemanu ya rubuta: “Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka.” (M. Wa. 9:10) Don mu yi nasara, dole ne mu kasance a shirye mu yi abubuwa da ake bukata don mu tsai da shawarwarinmu. Alal misali, mai shela zai iya tsai da shawara ya yi hidimar majagaba. Zai yi nasara kuwa? Zai yi nasara idan bai ƙyale yawan aiki da nishaɗi su gajiyar da shi kuma su cinye lokacin da zai yi amfani da shi don ya kula da hidimarsa ba.

16 Ba shi da sauƙi a tsai da shawarwari masu kyau. Me ya sa? Domin “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” (1 Yoh. 5:19) Dole ne mu yi kokawa “da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afis. 6:12) Manzo Bulus da almajiri Yahuda sun nuna cewa waɗanda suka tsai da shawara su ɗaukaka Allah za su yi kokawa.—1 Tim. 6:12; Yahu. 3.

17. Mene ne Jehobah yake bukata a gare mu, idan ya zo ga tsai da shawarwari?

17 Ka sake duba shawarar kuma ka yi gyara da ake bukata. Ba dukan shawarwari ba ne da aka tsai da suke yin nasara ba. “Sa’a, da tsautsayi, sukan sami” dukanmu. (M. Wa. 9:11, Littafi Mai Tsarki) Duk da haka, Jehobah ba ya son mu yi sanyin gwiwa sa’ad da muka tsai da shawarwari ko da za mu iya fuskanci gwaje-gwaje. Idan mutum ya keɓe kansa ga Jehobah ko kuma ya yi wa’adin aure, ba zai iya canja hakan ba. Allah yana bukatar mu yi rayuwa da ta jitu da irin waɗannan shawarwari. (Karanta Zabura 15:1, 2, 4.) Amma, yawancin shawarwari ba su da wuya sosai. Mutum mai hikima zai sake duba shawarwari da ya tsai da a lokaci lokaci. Ba zai ƙyale fahariya ko kuma taurin kai su hana shi yin gyara ko kuma sake shawararsa ba. (Mis. 16:18) Kasancewa da tabbaci cewa irin rayuwar da yake yi yana ci gaba da ɗaukaka Allah ne ya kamata ya fi muhimmanci a gare shi.

Ka Koyar da Mutane Su Tsai da Shawarwari da Ke Ɗaukaka Allah

18. Ta yaya iyaye za su iya koyar da yaransu su tsai da shawarwari masu kyau?

18 Iyaye suna iya taimaka wa yaransu su koya yadda ake tsai da shawarwari da ke ɗaukaka Allah. Ɗaya daga cikin abubuwa da suka fi kyau shi ne kafa misali mai kyau. (Luk 6:40) A lokacin da ya dace, iyaye za su iya bayyana wa yaransu yadda su da kansu suka tsai da wata shawara. Za su iya ƙyale yaransu su tsai da wasu shawarwari da kansu kuma su yaba musu idan shawarar ta yi nasara. Idan yaro bai tsai da shawara mai kyau kuma ba fa? Da farko iyayen za su so su kāre yaron daga sakamakon, amma ba a koyaushe hakan zai taimaki yaron ba. Alal misali, iyaye suna iya barin yaronsu ya samu lasisin direbobi. A ce yaron ya karya dokar hanya kuma aka kama shi aka ce ya biya wasu kuɗaɗe. Iyayen suna iya biyan kuɗaɗen. Amma yaron zai fi koyi hankali sosai idan aka bar shi ya yi aiki don ya biya kuɗaɗen.—Rom. 13:4.

19. Mene ne ya kamata mu koya wa ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki, kuma yaya za mu iya yin hakan?

19 Yesu ya gaya wa mabiyansa su koyar da mutane. (Mat. 28:20) Ɗaya daga cikin darussa da suka fi muhimmanci da za mu iya koya wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki ita ce yadda za su tsai da shawarwari masu kyau. Don mu yi hakan da kyau, dole ne mu guji gaya musu abin da za su yi. Ya fi kyau mu koya musu yadda za su yi tunani a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su iya tsai da shawara a kan abin da za su yi da kansu. Ballantana ma, “kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Rom. 14:12) Saboda haka, dukanmu muna da ƙwaƙƙwarar dalilin tsai da shawarwari da ke ɗaukaka Allah.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani a kan wannan batun, ka duba kan maganan nan “Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fiɗa” a rataye, shafuffuka na 215 zuwa 218 na littafi nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa muke bukatar mu koya yadda ake tsai da shawarwari?

• Yaya tsoro zai iya shafanmu, kuma yaya za mu iya sha kan tsoron da muke ji?

• Waɗanne matakai shida ne za mu iya ɗauka don mu tabbata cewa shawarwarinmu suna ɗaukaka Allah?

[Akwati/Hoton da ke shafi na 16]

Matakai da Za Mu Ɗauka Don Tsai da Shawarwari Masu Kyau

1 Ka Guji Girman Kai

2 Ka Yi Bincike

3 Ka Yi Addu’a don Samun Hikima

4 Ka Tsai da Shawarar

5 Ka Aikata Shawarar da Ka Tsai Da

6 Ka Sake Duba Shawarar kuma Ka Yi Gyara da Ake Bukata

[Hoton da ke shafi na 15]

Mutum da ba ya iya tsai da shawara yana kama da kwalekwale da ba shi da kwangwala da ke cikin teku mai hadari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba