Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 pp. 22-26
  • Ka Riƙa Tsai da Shawarwari Masu Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Riƙa Tsai da Shawarwari Masu Kyau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI TUNANI SOSAI KAFIN KA TSAI DA SHAWARA
  • KA KOYI YIN AMFANI DA FAHIMINKA YADDA YA DACE
  • KA RIƘA YIN ABIN DA YA DACE
  • ZA KA SAMI ALBARKA IDAN KA YANKE SHAWARWARI MASU KYAU
  • Ka Kasance da Bangaskiya Kuma Ka Tsai da Shawara Mai Kyau!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yaya Kake Tsai da Shawarwari?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • “Kowane Mutum Za Ya Ɗauki Kayan Kansa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 pp. 22-26

Ka Riƙa Tsai Da Shawarwari Masu Kyau

“Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.”—MIS. 3:5.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne yin tunani sosai kafin mu tsai da shawara yake nufi?

  • Mene ne zai riƙa taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau?

  • Mene ne zai taimaka mana mu zartar da shawarar da muka yanke?

1, 2. Shin kana farin cikin yanke wa kanka shawara kuwa, kuma yaya kake ɗaukan wasu shawarwari da ka riga ka yanke?

MUNA tsai da shawarwari kowace rana. Yaya kake ɗaukan tsai da shawarwari? Wasu mutane suna ɗokin tsai da wa kansu shawarwari dabam-dabam. Suna ganin ba wanda ya isa ya tsai da musu shawara sai su kaɗai. Wasu kuma suna tsoron tsai da shawarwari masu muhimmanci. Har ila, wasu kuma suna neman shawara daga littattafai ko mutane masu ba da shawara har ma su biya kuɗaɗe da dama don su tabbata cewa sun sami shawarar da suke bukata.

2 Mutane da yawa sun san cewa ko da yake akwai wasu shawarwarin da za su iya yankewa da kansu, amma wasu sun fi ƙarfinsu. (Gal. 6:5) Duk da haka, mun san cewa ba dukan shawarwarin da muke tsai da wa ne suke da kyau ko muhimmanci ba.

3. Mene ne zai iya taimaka mana sa’ad da muke tsai da shawarwari, kuma wane ƙalubale ne muke fuskanta?

3 Da yake mu bayin Jehobah ne, muna farin ciki cewa Allah yana mana ja-gora a kan tsai shawarwari masu muhimmanci a rayuwa. Mun san cewa idan muka bi ja-gorar Jehobah, za mu iya yanke shawarwarin da za su faranta masa rai kuma su amfane mu. Amma Littafi Mai Tsarki bai ba mu ja-gora a kan dukan matsaloli da kuma yanayin da za mu fuskanta a rayuwa ba. To mene ne zai taimake mu idan muka fuskanci irin wannan yanayin? Alal misali, mun san sata ba kyau. (Afis. 4:28) Amma wasu sun ce tsintuwa ba sata ba, musamman idan suna bukatar abin sosai ko kuma abin bai da wani muhimmanci. To wace shawara ce za mu iya yanke a irin waɗannan yanayi da wasu suke gani ba laifi ba ne? Mene ne zai iya taimaka mana?

KA YI TUNANI SOSAI KAFIN KA TSAI DA SHAWARA

4. Mene ne mutane suke ce mu yi sa’ad da muke son mu yanke wata shawara?

4 Idan muka gaya wa wani ɗan’uwa cewa muna son mu tsai da wata shawara mai muhimmanci, zai iya gaya mana mu yi tunani sosai kafin mu tsai da shawarar. Wannan shawara ce mai kyau, ko ba haka? Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu a kan yanke shawara da garaje. Ya ce: “Kowane mai-garaje wajen tsiya ya ke nufa.” (Mis. 21:5) Mene ne ake nufi da yin tunani sosai kafin mu yanke shawara? Shin hakan yana nufin cewa ya kamata mu yi tunani sosai game da batun kuma mu fahimci yanayin da kyau kafin mu tsai da shawarwari? Dukan abubuwan da muka ambata a nan suna da muhimmanci, amma ba shi ke nan ba.—1 Bit. 4:7.

5. Me ya sa ba ma yawan tsai da shawarwarin da suka dace?

5 Babu mutumin da ya cika goma. Me ya sa? Dalilin shi ne dukanmu ajizai ne da kuma masu zunubi, don haka, ba mu da ƙoshin lafiya kuma ba a kowane lokaci muke tsai da shawara mai kyau ba. (Zab. 51:5; Rom. 3:23) Shaiɗan ya “makantar” da mutane da yawa a cikinmu a dā, amma yanzu mun koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da kuma ƙa’idodinsa. (2 Kor. 4:4; Tit. 3:3) Saboda haka, ko da mutum ya yi tunani sosai kafin ya tsai da wata shawarar da yake gani ta dace, zai iya yin kuskure.—Mis. 14:12.

6. Me zai taimaka mana mu riƙa tunani kafin mu yanke shawara?

6 Ko da yake mu ajizai ne, amma Jehobah, Ubanmu na sama bai da zunubi ko kaɗan. (K. Sha 32:4) Ya ba mu abin da muke bukata don mu daidaita yadda muke tunani kuma mu riƙa yin tunani sosai kafin mu tsai da shawara. (Karanta 2 Timotawus 1:7.) Da yake mu Kiristoci ne, ya kamata mu riƙa yin tunani da la’akari a hanyar da ta dace. Saboda haka, zai dace mu koya yadda za mu riƙa kame kanmu da jiye-jiyenmu don tunaninmu da yadda muke ji da aikatawa su jitu da na Jehobah.

7, 8. Wane labari ne ya nuna cewa ko da muna fuskantar matsi, za mu iya yanke shawara mai kyau?

7 Ka yi la’akari da wannan misalin. Mutanen da suka ƙaura zuwa wata ƙasa sun saba tura jariransu zuwa wurin danginsu a ƙasarsu don su ci gaba da aiki da kuma tara kuɗaɗe gida.a Wata mata da ke zama a wata ƙasa ta haifi kyakkyawan ɗa. Jim kaɗan bayan haka, sai ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma tana bin abin da take koya. Abokanta da kuma danginta suka soma gaya mata da maigidanta cewa su tura jaririnsu wurin iyayensu don su kula da shi. Amma matan ta koya a nazarin da take yi cewa Jehobah ya ba ta da maigidanta nawayar kula da kuma horar da wannan yaron. (Zab. 127:3; Afis. 6:4) Shin za ta tura jaririnta wurin danginta don kowa yana ɗauka hakan ba laifi ba ne? Ko kuma za ta bi abin da take koya daga Littafi Mai Tsarki duk da cewa kuɗin da take samu a wurin aiki zai ragu kuma mutane za su yi mata ba’a? Da a ce kai ne me za ka yi?

8 Wannan matar ta damu sosai don mutane suna ta matsa mata. Sai ta yi addu’a ga Jehobah kuma ta nemi ja-gorarsa. Sa’ad da ta tattauna batun da ’yar’uwa da ke nazari da ita da kuma wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya, sai ta soma fahimtar ra’ayin Jehobah game da batun. Kuma ta sake fahimta cewa idan ta tura yaronta gida, ba zai sami horon da ya kamata daga iyayensa ba kuma hakan zai shafe shi. Bayan ta yi tunani sosai a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batun, sai ta yanke shawara cewa ba za ta tura ɗanta gida ba. Sa’ad da maigidanta ya ga yadda ’yan’uwa a ikilisiya suka taimaka musu da yadda yaron yake jin daɗi da samun koshin lafiya, sai ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma ya soma halartan taro tare da matarsa.

9, 10. Mene ne yin tunani sosai kafin a yanke shawara yake nufi, kuma ta yaya za mu yi hakan?

9 Wannan misali ɗaya ne kawai, amma mun koya cewa yin tunani sosai kafin mu yanke shawara ba ya nufin cewa za mu yi abin da muka ga dama ko kuma mu yi abin da mutane suke gani ya dace. Za a iya kwatanta tunanin mutane ajizai da agogo mai gudu ko kuma latti. Idan muka dogara ga agogon da ba ya tafiya daidai, za mu faɗa cikin babban matsala. (Irm. 17:9) Idan ba ma son mu faɗa cikin matsala, ya kamata mu tabbata cewa tunaninmu ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.—Karanta Ishaya 55:8, 9.

10 Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Mis. 3:5, 6) Ka lura cewa ayar ta ce “kada ka jingina ga naka fahimi.” Sai kuma ya daɗa cewa “ka shaida” Jehobah. Shi kaɗai ne tunaninsa bai da aibi. Saboda haka, idan muna so mu yanke shawara mai kyau, ya kamata mu bincika Littafi Mai Tsarki sosai kuma mu bi ra’ayin Jehobah.

KA KOYI YIN AMFANI DA FAHIMINKA YADDA YA DACE

11. Mene ne sirrin tsai da shawarwarin da suka dace?

11 Yanke shawara mai kyau yana da wuya. Hakan bai da sauƙi ga waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ko kuma koyan Littafi Mai Tsarki ba. Za su iya ƙara samun ilimi domin Littafi Mai Tsarki ya kira su ‘jarirai.’ Kamar yadda yara suke koyan tafiya a hankali a hankali, haka ma waɗanda suke koyan yadda za su yanke shawara mai kyau suke. Manzo Bulus ya kwatanta mutanen da suka manyanta da “waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” Furucin nan “aikaceya” da kuma “wasassu” suna nufin cewa ’yan’uwa da ba su daɗe da koyan Littafi Mai Tsarki ba suna bukata su ci gaba da koyo.—Karanta Ibraniyawa 5:13, 14.

12. Ka kwatanta yaya za mu koyi yanke da shawarwari masu kyau?

12 Muna tsai da shawarwari ƙanana da manya kowace rana. Wasu mutane da suka yi bincike a kan yadda muke tsai da shawara sun ce muna yawan tsai da shawara da garaje ba tare da yin tunani sosai ba. Alal misali, muna zaɓan irin tufar da za mu saka kowace safiya. Za ka iya ɗauka cewa wannan ƙaramin abu ne don haka, ba ka bukata ka yi tunani sosai. Amma yana da muhimmanci ka yi tunani ko irin tufar da ka saka ta dace da bawan Jehobah. (2 Kor. 6:3, 4) Wataƙila sa’ad da kake son ka sayi tufafi, za ka so ka zaɓi wadda ake yayin su. Shin wannan tufafin da kake so ka saya ya dace da bawan Jehobah kuma kana da kuɗin sayen su kuwa? Yin zaɓi mai kyau a waɗannan ƙananan hanyoyin zai taimaka maka ka horar da kanka, don ka iya tsai da shawara masu muhimmanci sosai.—Luk 16:10; 1 Kor. 10:31.

KA RIƘA YIN ABIN DA YA DACE

13. Mene ne zai taimaka mana mu zartar da shawarar da muka yanke?

13 Ko da mun tsai da shawara mai kyau, amma ba shi da sauƙi mu zartar da shi. Alal misali, wasu suna son su daina shan taba amma ba su da ƙarfin yin hakan. Abin da suke bukata shi ne su ƙudura cewa suna son su yi abin da ya dace, kuma su ƙoƙarta su yi hakan. Mene ne zai taimaka musu su yi hakan? Idan suka dogara ga Jehobah, zai taimaka musu.—Karanta Filibiyawa 2:13.

14. Mene ne ya taimaka wa Bulus ya yi abin da ya dace?

14 Abin da Bulus ya fuskanta a rayuwa ya taimaka masa ya san cewa bai da sauƙi a yi abin da aka ƙudura. Ya ce: “Gama nufi yana gareni, amma aika nagarta ba shi gareni ba.” Ya san abin da ya kamata ya yi, amma a wani lokaci, ba ya iya yin hakan. Ya daɗa cewa: “Ina murna da shari’ar Allah bisa ga mutum na ciki: amma ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwana.” Shin yanayin da ya sami kansa a ciki ya wuce gaban taimako ne? A’a. Ya ce: “Na gode wa Allah ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu.” (Rom. 7:18, 22-25) Sai ya daɗa cewa: “Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafata.”—Filib. 4:13, Littafi Mai Tsarki.

15. Me ya sa ya kamata mu ƙudurta yin abin da ya dace?

15 Idan muna son mu faranta wa Allah rai, dole ne mu tsai da shawara mai kyau kuma mu ƙudura yin hakan. Ka yi tunani a kan abin da Iliya ya gaya wa wasu Isra’ilawa da suke bauta wa Baal da kuma ’yan ridda a Dutsen Karmel, ya ce: “Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan? idan Ubangiji shi ne Allah, ku bi shi; amma idan Baal ne, sai ku bi shi.” (1 Sar. 18:21) Isra’ilawa sun san cewa ya kamata su bauta wa Jehobah kaɗai. Amma suna ta “ɗingishi a kan wannan imani da wancan” wato, suna son su bauta Jehobah da kuma Baal. Joshua bai da irin wannan halin. Shekaru da yawa kafin wannan lokacin, ya gaya wa Isra’ilawa: “Idan a gareku mummunan abu ne ku bauta wa Ubangiji, ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa . . . amma da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.” (Josh. 24:15) Wace albarka ce shi da waɗanda suka mara masa baya suka samu? Albarkar da suka samu ita ce sun shiga Ƙasar Alkawari, wato “ƙasa mai-zuba da madara da zuma.”—Josh. 5:6.

ZA KA SAMI ALBARKA IDAN KA YANKE SHAWARWARI MASU KYAU

16, 17. Ka faɗi labarin da ya nuna cewa za mu amfana idan muka yi abin da Jehobah yake so.

16 Wani ɗan’uwa da bai daɗe da yin baftisma ba da matarsa suna da ƙananan yara uku. Ba ya samun kuɗi sosai a wurin da yake aiki, amma ya ƙudura zai yi aikin domin yana samun lokacin halartan taro da kuma yin wa’azi tare da iyalinsa. Sai wata rana, abokin aikinsa ya gaya masa cewa su canja aiki zuwa wani kamfani da ake biya sosai kuma ana ba da ƙarin alawus. Ɗan’uwan ya yi tunani da kuma addu’a sosai ga Jehobah a kan batun. Ya san cewa idan ya soma sabon aikin, zai daɗe kafin ya sami lokaci don ya riƙa kula da iyalinsa kamar dā. Da a ce kai ne, me za ka yi?

17 Bayan ya yi tunani sosai a kan yadda karɓan aikin zai shafi dangantakarsa da Jehobah, sai ya tsai da shawara cewa ba zai canja aikin ba. Kana ganin ya yi da-na-sani ne daga baya? A’a. Ya fahimta cewa dangantakarsa da kuma na iyalinsa da Jehobah ta fi samun ƙarin kuɗi muhimmanci. Wannan ɗan’uwan da matarsa sun yi farin ciki matuƙa sa’ad da ’yarsu mai shekara goma ta ce tana ƙaunar iyayenta da ’yan’uwa da ke ikilisiyarsu da kuma Jehobah sosai. Ta ce tana so ta ƙulla abota da Jehobah kuma ta yi baftisma. Mahaifinta ya saka bautar Jehobah farko a rayuwarsa kuma ta amfana daga hakan.

18. Me ya sa ya kamata mu riƙa tsai da shawarwarin da suka dace kowace rana?

18 Kamar yadda Musa ya ja-goranci Isra’ilawa a jeji, Yesu ma ya daɗe yana wa bayin Jehobah ja-gora a wannan muguwar duniyar. Nan ba da daɗewa ba, za a halaka wannan muguwar duniyar. Kuma kamar yadda Joshua ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa Ƙasar Alkawari, hakan ma Yesu zai ja-goranci mabiyansa zuwa sabuwar duniya inda za a yi adalci. (2 Bit. 3:13) Tun da ƙarshe ya yi kusa, ba zai dace mu koma gidan jiya ba, wato halaye da tunani da maƙasudai na dā. Amma, ya kamata mu fahimci abin da Allah yake so mu yi. (Rom. 12:2; 2 Kor. 13:5) Idan kana tsai da shawarwari masu kyau a kowace rana, za ka faranta wa Jehobah rai kuma zai albarkace ka har abada.—Karanta Ibraniyawa 10:38, 39.

a Wani dalili kuma da ya sa mutane suke tura jariransu gida shi ne don iyayensu su nuna wa abokansu da kuma danginsu cewa suna da jika.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba