Ka Yi Shirin Yadda Za Ka Tsira?
“Ka zo kai da dukan gidanka cikin jirgi: gama kai ne na gan ka mai-adilci a gabana a cikin wannan tsara.”—FARAWA 7:1.
1. Wane tanadin tsira ne Jehobah ya yi a zamanin Nuhu?
AZAMANIN Nuhu, Jehobah “ya kawo rigyawa bisa duniya ta masu-fajirci” amma kuma ya yi tanadin tsira. (2 Bitrus 2:5) Allah ya ba wa Nuhu umurni dalla-dalla game da yadda zai gina jirgin da zai ceci mutane daga rigyawar da za ta shafi dukan duniya. (Farawa 6:14-16) Kamar yadda mai bin Jehobah ya kamata ya aikata, “Nuhu ya yi bisa ga abin da Allah ya umurce shi.” Hakika, “haka ya yi.” Shi ya sa muke da rai yau domin biyayyar da Nuhu ya yi.—Farawa 6:22.
2, 3. (a) Ta yaya ne mutanen zamanin Nuhu suka ɗauki aikin da Nuhu yake yi? (b) Da wane irin gaba gaɗi ne Nuhu ya shiga cikin jirgin?
2 Gina jirgin ba zai zama da sauƙi ba. Da gaske, mutane da yawa suna mamakin abin da Nuhu da iyalinsa suka cim ma. Duk da haka, wannan bai isa ya tabbatar musu cewa za su tsira idan suka shiga jirgin ba. A ƙarshe, haƙurin da Jehobah ya yi wa wannan muguwar duniyar ta kai ƙarshe.—Farawa 6:3; 1 Bitrus 3:20.
3 Bayan shekaru da Nuhu da iyalinsa suka yi suna aiki mai tsanani, Jehobah ya ce wa Nuhu: “Ka zo kai da dukan gidanka cikin jirgi gama kai ne na gan ka mai-adalci a gabana a cikin wannan tsara.” Da bangaskiya tare da gaba gaɗi ga kalmar Jehobah, “Nuhu kuma ya shiga, duk da ’ya’yansa, da matatasa, da matayen ’ya’yansa tare da shi, cikin jirgi.” Jehobah ya rufe ƙofa domin ya kāre masu bauta masa. Sa’ad da ruwan tufana ya zo bisa duniya, jirgin ya zama tanadin da Jehobah ya yi domin tsira.—Farawa 7:1, 7, 10, 16.
Kamani da ke Tsakanin Zamaninmu da na Nuhu
4, 5. (a) Da menene Yesu ya kwatanta lokacin bayanuwarsa? (b) Wane kamani ne ke tsakanin zamanin Nuhu da na mu?
4 “Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.” (Matta 24:37) Da waɗannan kalmomin ne Yesu ya nuna cewa lokacin bayyanuwarsa marar ganuwa za ta zama kamar na zamanin Nuhu, haka kuma ya zama. Musamman a shekara ta 1919, an sanar da saƙo da ya yi daidai da na zamanin Nuhu ga mutanen dukan al’ummai. Galibi, sun ɗauki saƙon kamar yadda mutanen zamanin Nuhu suka ɗauka.
5 Ta wurin rigyawa, Jehobah ya ɗauki mataki bisa duniya da ke “cike da zalunci.” (Farawa 6:13) Maimakon yin zalunci, Nuhu da iyalinsa cikin salama suka gina jirgi da kowa ya gani. A nan kuma, mun ga kamani a zamaninmu. Sahihun mutane a yanzu za su iya “rarrabe tsakanin adali da mugu, tsakanin wanda ya ke bauta ma Allah da wanda ba ya bauta masa ba.” (Malachi 3:18) Mutane marasa sonkai suna yaba wa Shaidun Jehobah saboda sahihanci, alheri, zaman lafiya, da ƙwazo da suke nunawa kuma waɗannan halayen sun bambanta mutanen Allah daga duniya baki ɗaya. Shaidun Jehobah sun ƙi zalunci a kowane hanya amma sun ƙyale ruhun Jehobah ya bi da su. Shi ya sa suke zaune cikin salama kuma suke biɗan adalci.— Ishaya 60:17.
6, 7. (a) Menene mutane na zamanin Nuhu suka ƙi yarda da shi, kuma yana kama da menene a yau? (b) Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Shaidun Jehobah sun bambanta?
6 Mutanen zamanin Nuhu sun ƙi yarda cewa Allah yana goyon bayan Nuhu kuma yana bin ja-gorar Allah. Shi ya sa ba su ɗauki wa’azin da yake yi da muhimmanci ba, ko kuma su yi amfani da gargaɗin da ya yi musu. Yau kuma fa? Ko da yake mutane da yawa suna sha’awar aikin da Shaidun Jehobah suke yi da kuma halayensu, wasu da dama kuwa ba su ɗauki bisharar da kuma gargaɗin da Littafi Mai Tsarki yake yi da muhimmanci ba. Maƙwabta da masu ɗaukan mutane aiki ko kuma dangi za su iya yaba wa halayen Kiristoci na gaskiya amma kuma sai su ce, “Da ma a ce ku ba Shaidun Jehobah ba ne!” Abin da waɗannan masu lura suka manta shi ne ƙauna, salama, nasiha, nagarta, tawali’u da kuma kamewa da Shaidu suke nuna wa, saboda ruhun Allah yana tare da su ne. (Galatiyawa 5:22-25) Wannan ya kamata ya sa su ba da gaskiya ga saƙonsu.
7 Alal misali, a ƙasar Rasha sa’ad da Shaidun Jehobah suke gina Majami’ar Mulki. Wani mutum da ya tsaya don ya yi magana da ɗaya daga cikin masu aikin ya ce: “Wannan wane irin wajen gini ne, ba a shan taba, ba a zagi, kowa na cikin natsuwa! Ku Shaidun Jehobah ne?” Ma’aikacin ya ce masa, “Idan na ce a’a, za ka yarda?” Sai mutumin ya amsa da sauri, “Ko kaɗan.” A wani birni a ƙasar Rasha, galadiman ya yi farin ciki da ya ga yadda Shaidun Jehobah suka gina sabuwar Majami’ar Mulkinsu. Ya ce, ko da yake a dā ya ɗauki dukan addinai ɗaya ne, amma bayan da ya ga Shaidun Jehobah sahihai marasa son kai suna aiki, sai ya daina tunanin cewa dukan addinai babu bambanci. Waɗannan misalai biyu ne kawai da suka nuna cewa mutanen Jehobah sun bambanta da mutanen da ba sa bin mizanan Littafi Mai Tsarki.
8. Menene ya kamata mu dogara da shi idan muna son mu tsira daga wannan muguwar duniya?
8 A ƙarshen “duniya ta dā” da ta halaka a rigyawa, Nuhu ya zama “mai-shelan adalci.” (2 Bitrus 2:5) A kwanaki na ƙarshe na wannan zamanin, mutanen Jehobah suna sanar da mizanansa na adalci kuma suna shelar bishara game da yadda za a tsira zuwa sabuwar duniya. (2 Bitrus 3:9-13) Kamar yadda Nuhu da iyalinsa masu tsoron Allah suka tsira a cikin jirgi, a yau mutane na bukatar su ba da gaskiya kuma su yi tarayya da ɓangaren duniya na ƙungiyar Jehobah ta sararin samaniya.
Ana Bukatar Bangaskiya don Tsira
9, 10. Me ya sa muna bukatar bangaskiya idan muna son mu tsira a ƙarshen zamanin Shaiɗan?
9 Menene ya kamata mutum ya yi idan yana so ya tsira daga wannan duniya da za a halaka wadda ke kwance a hannun Shaiɗan? (1 Yohanna 5:19) Dole ne ya fahimci cewa akwai kāriya. Sai ya ba da kansa ga wannan kāriya. Mutanen zamanin Nuhu sun ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum ba tare da nuna cewa suna bukatar kāriya daga bala’in da ke zuwa a nan gaba ba. Sun rasa wani abu, wato bangaskiya ga Allah.
10 A wani ɓangare kuma, Nuhu da iyalinsa sun fahimci cewa suna bukatar kāriya da ceto. Sun kuma ba da gaskiya ga Jehobah Allah, Mamallakin Dukan Halitta. “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe [Jehobah] sai tare da bangaskiya,” in ji manzo Bulus, “gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” Bulus ya daɗa: “Ta bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al’amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magajin adalcin Allah, wanda ke samuwa ta bangaskiya.”—Ibraniyawa 11:6, 7.
11. Me za mu koya daga yadda Jehobah ya yi tanadin kāriya a dā?
11 Idan muna son mu tsira a ƙarshen wannan muguwar zamanin, dole ne mu yi fiye da gaskatawa kawai cewa za a halakata. Dole ne mu ba da gaskiya, mu yi amfani da tanadodin da Allah ya bayar domin mu tsira. Hakika, ya kamata mu ba da gaskiya ga fansar hadaya na ɗan Allah Yesu Kristi. (Yohanna 3:16, 36) Amma ya kamata mu tuna cewa waɗanda suke cikin jirgin Nuhu ne kawai suka tsira daga Rigyawan. Hakazalika, biranen mafaka a ƙasar Isra’ila ta dā ta ba da kāriya ga duk wanda ya kashe wani ba da sane ba, amma sai ya gudu zuwa wannan birni ya kuma yi zamansa har sai ranar da babban firist ya mutu. (Litafin Lissafi 35:11-32) A zamanin Musa annoba ta goma ce ta kashe ’ya’yan fari a ƙasar Masar, amma ’ya’yan Isra’ilawa sun tsira. Me ya sa? Jehobah ya umurci Musa: “Su [Isra’ilawa za su] ɗiba daga jinin, [ɗan Ragon Faska ta alama] su shafa a dogaran ƙofa, da dokin ƙofa na bisa, a gidajen da za su ci shi . . . Kada kowane a cikinku shi fita ƙofar gidansa sai safiya ta yi.” (Fitowa 12:7, 22) Wane ɗan fari na Isra’ilawa ne zai ƙi bin dokar Allah, kuma ya fita daga gidan da aka shafa jini a dogaran ƙofa da dokin ƙofa na bisa?
12. Wace tambaya ce ya kamata kowa ya tambayi kansa, kuma me ya sa?
12 Saboda haka ya kamata mu yi tunani sosai game da yanayin mu. Muna cikin shirin da Jehobah yake yi domin kāriya ta ruhaniya kuwa? Sa’ad da matsananciyar wahala za ta soma, hawayen farin ciki da kuma godiya za ta zuba a fuskokin waɗanda suke neman kāriya. Ga waɗansu kuwa zai zama hawayen baƙin ciki ne kawai da nadama.
Gyara da Ake Samu a Kai a Kai na Shirya Mu
13. (a) Menene manufar gyaran da aka yi a ƙungiyar? (b) Ka bayyana wasu gyare-gyare da aka yi.
13 Jehobah ya ci gaba da yin gyara ga ɓangaren ƙungiyarsa da ke duniya. Wannan ya kyautata, kuma ƙarfafa tsarinsa domin kāriyarmu ta ruhaniya. Daga shekara ta 1870 zuwa 1932, mutanen ikilisiya ne suke zaɓan dattawa da dikonawa. A shekara ta 1932 an canza dattawa da ikilisiyar ta zaɓa da kwamitin hidima domin taimakon mai gudanar da hidima da aka naɗa. A shekara ta 1938, an yi wani gyara domin naɗa kowane bawa a cikin ikilisiya ta tsarin Allah. Tun daga shekara ta 1972 a ƙarƙashin ja-gorar Hukumar Mulki ta Shaidun Jehobah, ana gabatar da wasu kuma idan an yarda ikilisiyoyi suna samun wasiƙu na naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima. A shekarun da suka wuce, matsayin da Hukumar Mulki take riƙewa sun yi yawa sai aka yi wasu gyara don a rage mata nauyi.
14. Wane tsarin ayuka na koyarwa ne aka soma a shekara ta 1959?
14 A shekara ta 1950, an tattauna Zabura 45:16 wadda ta kai ga wani tsarin ayuka. Nassin ya ce: “ ’Ya’yanka za su maye matsayin ubaninka, Su ne kuwa za ka maishe su sarakuna cikin dukan duniya.” Dattawa da suke ja-gorar ikilisiya suna samun koyarwar ayyuka na tsarin Allah game da abin da zai faru yanzu da kuma bayan Armageddon. (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) An kafa Makarantar Hidima ta Mulki a shekara ta 1959. A wannan lokaci, an yi tanadin koyarwa na tsawon wata ɗaya musamman saboda bawan ikilisiya kamar yadda ake kiran shugaban dattawa a dā. An buɗe wannan makaranta domin koyar da dukan dattawa da kuma bayi masu hidima. Waɗannan ’yan’uwa kuwa, sun ɗauki nauyin koyar da Shaidun Jehobah a ikilisiyoyinsu. Ta haka, an taimaka wa kowa a ruhaniya kuma an taimake su su ƙara ƙwazo a hidimarsu na masu shelar Mulki.—Markus 13:10.
15. A waɗanne hanyoyi biyu ne ake tsarkaka ikilisiyar Kirista?
15 Mutanen da suke so su shiga cikin ikilisiya ta Kiristoci dole ne su cika wasu farillai. Daidai kuwa, an keɓe masu ba’a na wannan zamanin, kamar waɗanda ba su samu shiga jirgin Nuhu ba. (2 Bitrus 3:3-7) Musamman tun shekara ta 1952, Shaidun Jehobah sun ba da ƙarin goyon baya ga tsarin da zai kāre ikilisiyar ta wajen yin yankan zumunci ga waɗanda suka ƙi tuba. Hakika, waɗanda suka tuba da gaske ana taimaka masu su ‘miƙa karabsu domin sawayensu.’—Ibraniyawa 12:12, 13; Misalai 28:13; Galatiyawa 6:1.
16. Wane yanayi ne na ruhaniya mutanen Jehobah suke ciki?
16 Yadda mutanen Jehobah suke ci gaba a cikin ruhaniya ba a bin mamaki ba ne ko kuwa abin da bai kasance ba. Ta wurin annabi Ishaya, Jehobah ya ce: “Ga shi, bayina za su ci, amma ku za ku ji yunwa: ga shi, bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; ga shi, bayina za su yi farinciki, amma ku za ku ji kunya: ga shi kuma, bayina za su yi rairawa domin murna a zuci, amma ku za ku yi kuka domin ɓacin zuciya, za ku yi ihu domin karyewar ruhu.” (Ishaya 65:13, 14) Jehobah ya ci gaba da yi mana tanadin abinci na ruhaniya mai yawa da ke ƙarfafa mu a daidai lokaci.—Matta 24:45.
Ka Yi Shiri Domin Ka Tsira
17. Menene zai taimake mu mu yin shirin samun ceto?
17 Fiye da dā, yanzu ne ya kamata “mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗad da juna.” (Ibraniyawa 10:23-25) Idan muka kasance da ƙwazo a cikin ɗaya daga cikin ikilisiyoyi 98,000 na Shaidun Jehobah, zai taimake mu mu shirya kanmu don mu tsira. Za mu samu goyon baya daga wurin ’yan’uwanmu masu bi idan muka ci gaba da nuna “sabon mutum” muka sa ƙwazo wajen koyar da wasu su amfana daga tanadin da Jehobah ya yi domin tsira.—Afisawa 4:22-24 Kolossiyawa 3:9, 10 1 Timothawus 4:16.
18. Me ya sa ka ke ƙoƙari don ka tsaya kusa da ikilisiyar Kirista?
18 Shaiɗan da kuma muguwar duniyarsa suna son su rinjaye mu mu fita daga cikin ikilisiyar Kirista. Hakika, idan muka ci gaba da kasancewa ciki muna iya tsira a ƙarshen wannan mugun zamani. Bari ƙaunar Jehobah da godiya domin tanadin da yake yi su motsa mu mu ƙudurta fiye da dā don mu ɓata ƙoƙarin Shaiɗan. Yin bimbini a kan albarkar da muke samu yanzu zai karfafa ƙudurinmu. Talifi na gaba zai tattauna wasu albarkatai.
Menene Amsoshinka?
• Ta yaya ne zamanin mu ya yi daidai da na Nuhu?
• Wane hali ne ya kamata mu nuna don mu tsira?
• Wane gyara ne ya ƙarfafa tsarin Jehobah domin kāriyarmu?
• Ta yaya za ka iya yin shiri don ka tsira?
[Hoto a shafi na 10]
Mutanen zamanin Nuhu ba su ɗauki Nuhu da muhimmanci ba
[Hoto a shafi na 11]
Yana da amfani a ɗauki saƙon Allah da muhimmanci
[Hoto a shafi na 12]
Menene amfanin Makarantar Hidima ta Mulki?
[Hoto a shafi na 13]
Yanzu ne ya kamata mu kusanci ikilisiyar Kirista