Tambayoyi Daga Masu Karatu
Menene ke sa “muradin dukan dangogi” ke shiga ‘gidan’ bauta ta gaskiya?—Haggai 2:7.
Ta bakin annabi Haggai, Jehobah ya annabta: “Zan raurawarda dukan dangogi; kuma muradin dukan dangogi za ya zo; zan cika wannan gida da ɗaukaka.” (Haggai 2:7) Raurawar da “dukan dangogi” ne ya sa “muradin dukan dangogi” na al’ummai, wato mutane masu zuciyar kirki su rungumi bauta ta gaskiya? A’a.
Ka yi la’akari da sakamakon raurawar da, ko kuma girgiza al’ummai. Littafi Mai Tsarki ya ce “al’ummai su ke hauka, dangogi kuma suna tunanin al’amarin wofi.” (Zabura 2:1) “Al’amarin wofi” da suke “tunani,” ko bimbini a kansa shi ne, yadda za su ci gaba da sarautarsu. Abin da ke raurawar da su kawai shi ne idan aka yi wa sarautarsu barazana.
Aikin wa’azi na dukan duniya da Shaidun Jehobah suke yi game da Mulkin Allah da aka kafa, ya zama barazana ga al’ummai. Hakika, Mulkin Almasihun Allah da ke hannun Yesu Kristi “za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na mutane] ya cinye su.” (Daniel 2:44) Saƙon hukunci da aikin wa’azinmu ya ƙunsa yana raurawar da al’ummai. (Ishaya 61:2) Raurawar na ƙara yawa yayin da aikin wa’azi ke yaɗuwa sosai. Menene raurawar da aka annabta a Haggai 2:7 ke alamta?
A Haggai 2:6, mun karanta: “Hakanan Ubangiji mai-runduna ya ce: Sauran so ɗaya, bayan an jima kaɗan, sai in raurawadda sammai, da duniya, da teku, da sandararriyar ƙasa.” Sa’ad da ya yi ƙaulin wannan ayar, manzo Bulus ya rubuta: “Ya yi alkawari, cewa, sauran sau ɗaya tukuna zan sa ba duniya kaɗai ba amma har da sama ta raurawa. Wannan fa, Sauran so ɗaya tukuna, ya bayana alamar kawaswar waɗannan abubuwan da an raurawadda su, watau abubuwan da aka halitta ke nan, domin waɗancan da ba a raurawadda su [Mulkin], su wanzu.” (Ibraniyawa 12:26, 27) Hakika, za a halaka dukan wannan tsarin abubuwa saboda sabuwar duniyar da Allah zai halitta.
Ana jawo mutane masu zuciyar kirki ga bauta ta gaskiya ba domin ana raurawar da al’ummai ba. Abin da ke jawo su ga Jehobah da kuma bautarsa shi ne ke raurawar da al’ummai, wato wa’azi na dukan duniya na Mulkin Allah da aka kafa. Sanar da “bishara ta har abada” yana jawo mutane masu zuciyar kirki ga bautar Allah na gaskiya.—Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.
Saƙon Mulkin na hukunci ne kuma na ceto. (Ishaya 61:1, 2) Sakamakon yin wa’azinsu a dukan duniya guda biyu ne: raurawar da al’ummai da kuma shigowar muradin dangogi zuwa ga ɗaukakar Jehobah.