“Kun Ji Labarin Jimrewar Ayuba”
“Kun ji labarin jimrewar Ayuba, kun ga ƙarkon Ubangiji kuma, Ubangiji da shi ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.”—YAƘUB 5:11.
1, 2. Wane irin gwaji ne wasu ma’aurata suka fuskanta a ƙasar Poland?
KUSAN shekara biyu bayan Harald Abt ya zama Mashaidin Jehobah sojojin Hitler suka kame garin Danzig (Gdańsk na zamani) a arewacin ƙasar Poland. Yanayin ya yi wa Kiristocin da ke wurin wuya da kuma haɗari. ’Yan Sandan Ciki sun yi ƙoƙarin su tilasta wa Harald ya cika littafi na yin ridda, amma ya ƙi. Bayan ya yi makonni a kurkuku, an tura Herald zuwa sansanin fursuna da ke Sachsenhausen, inda aka buge shi kuma aka yi masa barazana a kai a kai. Wani shugaban ’yan sandan ya nuna wa Harald mafitar hayaƙin inda ake ƙone gawawwaki kuma ya ce masa, “Za ka koma ga Jehobahnka ta can wurin, nan da kwana 14 idan ka manne wa imaninka.”
2 A lokacin da aka kama Harald, matarsa Elsa tana shayar da ɗiyarsu ’yar wata goma. Amma ’Yan Sandan Cikin ba su ƙyale Elsa ba. Ba da daɗewa ba, aka kwace jaririyarta, kuma an jefa Elsa cikin sansanin fursuna da ke Auschwitz. Duk da haka, ita da mijinta Harald sun jimre har na tsawon shekaru masu yawa. Kana iya samun ƙarin bayani game da wahalar da suka sha a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1980. Harald ya ce: “Na yi shekara 14 a sansanin fursuna da fursunoni dabam dabam domin bangaskiya ta ga Allah. An tambaye ni: ‘Matarka ta taimaka maka wajen jimre wa duka waɗannan abubuwa?’ Ƙwarai kuwa! Tun da farko na sani cewa ba za ta taɓa karya imaninta ba, kuma hakan ya taimaka mini sosai. Na san cewa za ta gwammace in mutu da aminci da ta ji cewa an sake ni domin na karya imanina. . . . Elsa ta jimre wa wahaloli masu yawa sa’ad da take sansanin fursuna da ke ƙasar Jamus.”
3, 4. (a) Misalan wanene zai taimaka wa Kiristoci su jimre? (b) Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu bincika labarin Ayuba?
3 Shan wahala ba abu ba ne mai sauƙi, kamar yadda Shaidu da yawa za su iya shaidawa. Saboda wannan dalilin, Littafi Mai Tsarki ya shawarci dukan Kiristoci: “Ku lura da annabawa waɗanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, su zama gurbi gareku na shan wahala da na haƙuri.” (Yaƙub 5:10) A cikin tarihi, an tsananta wa yawancin bayin Allah ba gaira ba dalili. Misalin da waɗannan “taron shaidu” mai girma suka kafa, zai iya ƙarfafa mu mu ci gaba da jimrewa a tserenmu na Kirista.—Ibraniyawa 11:32-38; 12:1.
4 Ayuba fitaccen misali ne na jimiri a cikin labarin Littafi Mai Tsarki. “Duba, waɗanda suka jimre muna ce da su masu-albarka,” in ji Yaƙub. “Kun ji labarin jimrewar Ayuba, kun ga ƙarkon Ubangiji kuma, Ubangiji da shi ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.” (Yaƙub 5:11) Labarin Ayuba ya nuna mana sakamakon da ke jiran masu aminci, waɗanda Jehobah ya yi wa albarka. Mafi muhimmanci, ya bayyana mana gaskiyar da za ta amfane mu a lokacin wahala. Littafin Ayuba ya taimaka mana wajen amsa waɗannan tambayoyin: Sa’ad da muke fuskantar gwaji, me ya sa muke bukatar mu fahimci muhimman batutuwa da hakan ya ƙunsa? Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu jimre? Ta yaya za mu iya ƙarfafa Kiristocin da suke shan wahala?
Fahimtar Duka Batun
5. Wane batu mai muhimmanci ne ya kamata mu sa a zuciya sa’ad da muke fuskantar jaraba?
5 Don mu kasance da daidaituwa a ruhaniya sa’ad da muke fuskantar wahala, muna bukatar mu fahimci dukan batun. Idan ba haka ba, matsaloli suna iya sha kan ruhaniyarmu. Batun kasancewa da aminci ga Allah shi ne mafi muhimmanci. Ubanmu na sama ya yi wani roƙo da ya kamata mu sa a zuciya: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” (Misalai 27:11) Wannan babban gata ne! Duk da kumamanci da ajizancinmu, za mu iya sa Mahaliccinmu farin ciki. Za mu yi haka idan ƙaunar da muke yi wa Jehobah ta sa mu tsayayya wa jaraba. Ƙaunar Kirista tana jimre wa komi. Ba ta ƙarewa.—1 Korinthiyawa 13:7, 8.
6. Ta yaya ne Shaiɗan yake zargin Jehobah, kuma yaya yawan zargin yake?
6 Littafin Ayuba ya bayyana dalla-dalla cewa Shaiɗan ne ke zargin Jehobah. Ya bayyana mugun halin wannan maƙiyi da ba a gani da kuma muradinsa na lalata dangantakarmu da Allah. Kamar yadda aka nuna a batun Ayuba, Shaiɗan yana zargin dukan bayin Jehobah cewa suna da sonkai kuma yana son ya nuna cewa ƙaunar da suke yi wa Allah za ta iya yin sanyi. Ya zargi Allah tun shekaru dubbai da suka shige. Sa’ad da aka kori Shaiɗan daga sama, wata murya daga sama ta kira shi “mai-saran ’yan’uwanmu,” kuma yana wannan saran “dare da rana a gaban Allahnmu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Idan muka jimre cikin aminci, za mu iya ƙaryata zarginsa.
7. Ta yaya za mu iya kawar da raunana?
7 Dole ne mu tuna cewa Iblis zai iya yin amfani da matsalar da muke fuskanta don ya nisanta mu daga Jehobah. A wane lokaci ne ya gwada Yesu? Sa’ad da Yesu yake jin yunwa ne, bayan ya yi azumi na kwanaki da yawa. (Luka 4:1-3) Ƙarfin da Yesu ke da shi na ruhaniya ya sa ya ƙi gwajin Iblis da gaba gaɗi. Yana da muhimmanci mu yi amfani da ƙarfi na ruhaniya mu kawar da kowane irin kumamanci na jiki, wanda wataƙila rashin lafiya ko tsufa ne sanadin! Ko da “mutumi namu na fai yana lalacewa,” ba za mu karaya ba domin “mutumi namu na ciki yana sabontuwa yau da gobe.”—2 Korinthiyawa 4:16.
8. (a) Ta yaya ne fushi zai iya shafarmu? (b) Wane irin hali ne Yesu ke da shi?
8 Ƙari ga haka, rashin jin daɗi yana iya lalata ruhaniyarmu. Muna iya tunani, ‘Me ya sa Jehobah ya ƙyale wannan yanayin?’ Wani kuma yana iya tambaya idan aka yi masa abin da bai dace ba, ‘Me ya sa ɗan’uwa zai yi mini haka?’ Irin wannan yanayin yana iya sa mu yi watsi da batutuwa mafi muhimmanci kuma mu mai da hankali ga yanayinmu. Takaicin Ayuba domin abokansa mayaudara guda uku ya shafi motsin zuciyarsa sosai kamar yadda ciwon da ke damunsa ya shafe shi. (Ayuba 16:20; 19:2) Hakazalika, manzo Bulus ya nuna cewa ci gaba da yin fushi zai iya ba “Shaiɗan dama.” (Afisawa 4:26, 27) Maimakon nuna takaici a kan wasu ko kuwa yin fushi da wasu, ko kuma mai da hankali a kan rashin gaskiya na wani yanayi, zai dace Kiristoci su yi koyi da Yesu wajen “damƙa [kansu] ga wanda ke yin shari’a mai-adalci,” Jehobah Allah. (1 Bitrus 2:21-23) Kasancewa da “niya” irin ta Yesu za i iya zama kāriya daga hare-haren Shaiɗan.—1 Bitrus 4:1.
9. Wane tabbaci ne Allah ya ba mu game da wahalolin da za mu jimre ko gwajin da za mu fuskanta?
9 Fiye da komi, idan muna fuskantar wahala kada mu yi tunanin cewa Allah yana fushi da mu. Irin wannan rashin fahimtar ya ba Ayuba haushi sa’ad da abokansa da ya kamata su ƙarfafa shi suka gaya masa maganganun da ba su da daɗi. (Ayuba 19:21, 22) Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci da waɗannan kalaman: “Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” (Yaƙub 1:13) Akasin haka, Jehobah ya yi mana alkawarin cewa zai taimaka mana mu jimre kowane irin matsalar da muke fuskanta, zai kuma kāre mu daga kowane irin gwaji. (Zabura 55:22; 1 Korinthiyawa 10:13) Idan muka kusanci Allah a lokacin wahala, za mu tsara abubuwa yadda suka dace, kuma za mu yi nasara wajen tsayayya wa Iblis.—Yaƙub 4:7, 8.
Abubuwan da Za Su Taimaka Mana Mu Jimre
10, 11. (a) Menene ya taimaka wa Ayuba ya jimre? (b) Ta yaya ne lamiri mai kyau ya taimaka wa Ayuba?
10 Duk da bala’in da ya faɗa wa Ayuba, tare da zagin da masu yi masa ‘ta’aziyya’ suka yi masa, da kuma rashin sanin ainihin tushen bala’insa, Ayuba ya kasance da aminci. Menene za mu iya koya daga jimirinsa? Babu shakka, dalili mafi muhimmanci da ya sa ya yi nasara shi ne amincinsa ga Jehobah. ‘Yana tsoron Allah, yana kuma guje wa mugunta.’ (Ayuba 1:1) Rayuwarsa ke nan. Ayuba ya ƙi ya juya wa Jehobah baya, duk da cewa bai fahimci dalilin da ya sa abubuwa suka same shi ba. Ayuba ya yarda cewa ya kamata ya bauta wa Allah a lokaci mai daɗi da marar daɗi.—Ayuba 1:21; 2:10.
11 Kasancewa da lamiri mai kyau ya ta’azantar da Ayuba. A wani lokaci da ya ji kamar zai mutu, yana da farin cikin sanin cewa ya yi iya ƙoƙarinsa wajen taimaka wa wasu, ya manne wa mizanan Jehobah na adalci, kuma ya guje wa duka ire-iren bautar ƙarya.—Ayuba 31:4-11.
12. Ta yaya ne Ayuba ya yi na’am da taimakon da ya samu daga Elihu?
12 Gaskiya ne cewa Ayuba yana bukatar taimako don ya daidaita ra’ayinsa game da wasu abubuwa. Ya karɓi wannan taimakon da tawali’u, wanda hakan ya taimake shi ya jimre. Ayuba ya saurari shawara mai kyau na Elihu, kuma ya karɓi gyaran da Jehobah ya yi masa. “Na fa furta abin da ban gane ba,” in ji shi. “Domin wannan ina jin ƙyamar kaina, na tuba cikin ƙura da toka.” (Ayuba 42:3, 6) Duk da cutar da ke damunsa, Ayuba ya yi farin ciki cewa wannan gyaran da aka yi wa tunaninsa ya jawo shi kusa ga Allah. Ayuba ya ce: “Na sani [Jehobah] ka iya komi.” (Ayuba 42:2) Ta bayanin da Jehobah ya yi game da ɗaukakarsa, Ayuba ya fahimci matsayinsa a wajen Mahalicci.
13. Ta yaya ne Ayuba ya amfana daga nuna tagomashi?
13 A ƙarshe, Ayuba ya kafa misali mai kyau na nuna tagomashi. Waɗanda suka zo ƙarfafa shi sun ɓata masa rai sosai, duk da haka, sa’ad da Jehobah ya ce ya yi musu addu’a, Ayuba ya yi hakan. Bayan haka, Jehobah ya warkar da Ayuba. (Ayuba 42:8, 10) Babu shakka, fushi ba zai taimaka mana mu jimre ba, amma ƙauna da tagomashi za su taimaka mana mu jimre. Idan muka mance da laifin da wani ya yi mana, hakan zai wartsakar da mu a ruhaniya, kuma wannan tafarki ne da Jehobah zai yi wa albarka.—Markus 11:25.
Mashawarta Masu Hikima da Suke Taimaka Mana mu Jimre
14, 15. (a) Waɗanne halaye ne za su sa mashawarci ya ƙarfafa wasu? (b) Ka bayyana abin da ya sa Elihu ya yi nasara wajen taimaka wa Ayuba.
14 Wani darasin da za mu iya koya daga labarin Ayuba shi ne tamanin mashawarta masu hikima. Waɗannan sune ’yan’uwan da suke taimaka wa a “kwanakin shan wuya.” (Misalai 17:17) Amma, kamar yadda labarin Ayuba ya nuna, wasu mashawarta suna iya raunana mutum maimakon su ƙarfafa shi. Mashawarci mai kyau yana bukatar ya nuna tausayi, daraja, da kuma alheri, kamar yadda Elihu ya yi. Wataƙila dattawa da ƙwararrun Kiristoci suna bukatar su daidaita tunanin ɗan’uwan da ke fuskantar matsaloli, irin waɗannan mashawarta suna iya koyo daga littafin Ayuba.—Galatiyawa 6:1; Ibraniyawa 12:12, 13.
15 Akwai darussa masu yawa game da yadda Elihu ya bi da batun. Ya saurara sosai kafin ya mai da martani ga kalaman da ba su dace ba na abokan Ayuba su uku. (Ayuba 32:11; Misalai 18:13) Elihu ya kira sunan Ayuba kuma ya roƙe shi a matsayin aboki. (Ayuba 33:1) Ba kamar masu ta’aziyyar ƙarya uku ba, Elihu bai fifita kansa fiye da Ayuba ba. “Daga cikin ƙasa aka ɗauke ni, aka sifanta,” in ji shi. Ba ya son ya daɗa wa Ayuba wahalar da yake sha ta wajen gaya masa maganganun da ba su dace ba. (Ayuba 33:6, 7; Misalai 12:18) Maimakon ya zargi halin Ayuba na dā, Elihu ya yaba masa domin amincinsa. (Ayuba 33:32) Mafi muhimmanci, Elihu ya ɗauki abubuwa yadda Allah ke ɗaukansu, kuma ya taimaki Ayuba ya fahimci cewa Jehobah ba zai taɓa rashin adalci ba. (Ayuba 34:10-12) Ya ƙarfafa Ayuba ya jira Jehobah, maimakon ya nuna nasa adalcin. (Ayuba 35:2; 37:14, 23) Dattawa Kiristoci da wasu za su iya amfana daga waɗannan darussan.
16. Ta yaya ne abokan Ayuba su uku masu ta’aziyyar ƙarya suka zama kayan aikin Shaiɗan?
16 Shawarar hikima ta Elihu ta bambanta da kalamai masu ban haushi na Eliphaz, Bildad, da Zophar. Jehobah ya ce musu, “ba ku ambace ni da gaskiya ba.” (Ayuba 42:7) Ko da sun yi da’awar cewa suna da muradi mai kyau, sun zama kayan aikin Shaiɗan maimakon abokai masu aminci. Su ukun sun yi tsammanin cewa Ayuba ne ya jawo wa kansa bala’in da ya faɗa masa. (Ayuba 4:7, 8; 8:6; 20:22, 29) Eliphaz ya ce, Allah bai amince da bayinsa ba, kuma bai damu ba ko muna da aminci ko ba mu da shi. (Ayuba 15:15; 22:2, 3) Eliphaz ya kuma zargi Ayuba bisa zunubin da bai yi ba. (Ayuba 22:5, 9) A wani ɓangare kuma, Elihu ya taimaka wa Ayuba ya daidaita dangantakarsa da Allah, wanda shi ne burin mashawarci mai ƙauna.
17. Menene ya kamata mu tuna sa’ad da muke fuskantar jaraba?
17 Akwai wani darassi game da jimiri da za mu iya koya daga littafin Ayuba. Allahnmu mai ƙauna yana ganin yanayinmu, yana so kuma zai iya taimaka mana a hanyoyi masu yawa. Ɗazu mun karanta labarin Elsa Abt. Ka yi tunani a kan abin da ta ce: “Kafin a kama ni, na sami wata wasiƙa daga wata ’yar’uwa da ta ce sa’ad da mutum yake fuskantar jaraba mai tsanani, ruhun Jehobah na sa mutum ya natsu. Na ɗauka cewa daɗin baki kawai take yi. Amma sa’ad da na fuskanci jaraba, na fahimci cewa abin da ta ce gaskiya ne. Hakan ya faru. Zai yi wuya ka fahimci abin da ake nufi idan ba ka shaida shi ba. Amma hakan ya faru gare ni. Jehobah ya taimaka mini.” Ba wai Elsa tana magana ba ne game da abin da Jehobah zai iya yi ko abin da ya yi shekara dubu da suka shige a zamanin Ayuba ba. Tana magana ne game da zamaninmu. Hakika, “Jehobah yana taimakawa!”
Mai Albarka ne Mutumin da Ya Jimre
18. Waɗanne amfani ne Ayuba ya samu daga yin jimiri?
18 Ba dukanmu ba ne za mu fuskanci irin jarabar da Ayuba ya fuskanta. Amma ko da wace irin jaraba ce muka fuskanta a wannan zamanin, muna da cikakkun dalilai na kasancewa da aminci kamar Ayuba. Hakika, jimiri ya kyautata rayuwar Ayuba. Ya kamilta shi, kuma ya mai da shi cikakke. (Yaƙub 1:2-4) Ya ƙarfafa dangantakarsa da Allah. Ayuba ya ce: “Na ji labarinka ta wurin ji na kunne; amma yanzu idona ya gan ka.” (Ayuba 42:5) An ƙaryata Shaiɗan domin ya kasa karya amincin Ayuba. Shekaru darurruwa bayan haka, Jehobah yana ci gaba da nuna bawansa Ayuba a matsayin misali na adalci. (Ezekiel 14:14) Labarinsa na aminci da jimiri yana motsa mutanen Allah a yau.
19. Me ya sa kake jin cewa jimiri na da amfani?
19 Sa’ad da Yaƙub ya rubuta wa Kiristoci na ƙarni na farko game da jimiri, ya yi nuni ga gamsarwa da jimiri ke kawowa. Kuma ya yi amfani da misalin Ayuba don ya tuna musu cewa Jehobah yana saka wa bayinsa masu aminci. (Yaƙub 5:11) Ayuba 42:12 ta ce: “Da hakanan Ubangiji ya albarci ƙarshen Ayuba, har ya fi farkonsa.” Jehobah ya ba Ayuba ninki biyu na abubuwan da ya yi hasara, kuma ya rayu na dogon lokaci cike da farin ciki. (Ayuba 42:16, 17) Hakazalika, kowane irin azaba, wahala, ko baƙin ciki da muke jimrewa a wannan zamanin, za a kawar da shi za a kuma mance shi a sabuwar duniya ta Allah. (Ishaya 65:17; Ru’ya ta Yohanna 21:4) Mun ji game da jimirin Ayuba, mun ƙudurta cewa da taimakon Jehobah za mu yi koyi da Ayuba. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Mai-albarka ne mutum wanda ya daure da jaraba: gama sa’anda ya amintu, za shi karɓi rawanin rai, wanda Ubangiji ya alkawarta ma waɗanda su ke ƙamnassa.”—Yaƙub 1:12.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya za mu iya sa Jehobah ya yi farin ciki?
• Me ya sa bai kamata mu kammala ba cewa matsalolinmu alamu ne da ke nuna cewa Allah na fushi da mu?
• Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wa Ayuba ya jimre?
• Ta yaya za mu iya yin koyi da Elihu wajen ƙarfafa ’yan’uwa masu bi?
[Hoto a shafi na 16]
Mashawarci mai kyau yana nuna tausayi, daraja, da alheri
[Hotuna a shafi na 17]
Elsa da Harald Abt