Cin Gaba A Ruhaniya A Lokacin Tsufa
“Su waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji . . . Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai.”—ZABURA 92:13, 14.
1, 2. (a) Sau da yawa, yaya ake kwatanta tsufa? (b) Wane alkawari Nassosi ya yi game da sakamakon zunubi na Adamu?
MENENE kalmar nan tsufa take tuna maka? Tamojin jiki? Rashin ji da kyau? Gaɓoɓi marar ƙwari? Ko kuwa wani fanni na “miyagun kwanaki” da aka kwatanta dalla-dalla a littafin Mai-Wa’azi 12:1-7? Idan haka ne, yana da muhimmanci mu tuna cewa kwatancin da ke littafin Mai-Wa’azi sura ta 12 ya bayyana tsufa ba yadda Mahalicci, Jehobah Allah ya yi niyya tun da farko ba, amma don sakamakon zunubi na Adamu ne a kan jiki na ’yan adam.—Romawa 5:12.
2 Tsufa kanta ba la’ana ba ce, don ci gaba da rayuwa zai bukaci shigewar shekaru. Hakika, yana da kyau abubuwa masu rai su yi girma kuma su manyanta. Ɓarnar da zunubi ta yi da kuma ajizanci na shekara dubu shida da muke gani kewaye da mu ba da daɗewa ba za su zama abin dā, kuma dukan mutane masu biyayya za su more rayuwa yadda aka nufa dā, ba tare da ciwo na tsufa da mutuwa ba. (Farawa 1:28; Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5) A lokacin “wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Tsofaffi za su koma kwanakin ‘ƙuruciyarsu,’ kuma jikinsu zai “komo ya fi na yaro sabontaka.” (Ayuba 33:25) Amma a yanzu, dukanmu za mu yi kokawa da abin da muka gada daga Adamu. Duk da haka an albarkaci bayin Jehobah a hanyoyi ta musamman yayin da suke tsufa.
3. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci “za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai”?
3 Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa “waɗanda an dasa cikin gidan Ubangiji . . . Za su yi ta ’ya’ya da tsufa a kai.” (Zabura 92:13, 14) A yare ta alama, mai zabura ya faɗi muhimmiyar gaskiya cewa bayin Allah masu aminci za su ci gaba, su yi girma, kuma su yi nasara a ruhaniya ko da ƙarfinsu na raguwa a zahiri. Misalai da yawa na Littafi Mai Tsarki da na zamani sun nuna hakan.
“Ba ta Rabuwa”
4. Ta yaya annabiya Hannatu da ta tsufa ta nuna ibadarta ga Allah, kuma ta yaya aka saka mata?
4 Ka yi la’akari da Hannatu, annabiya a ƙarni na farko. A shekararta ta 84 ba ta “rabuwa da haikali tana sujjada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” Da yake babanta ɗan “kabilar Ashira” ba Balawi ba ne, Hannatu ba za ta iya zama a haikali ba. Ka yi tunanin ƙoƙarin da take yi don ta kasance a haikali tun daga hidimar safe har zuwa yamma! An albarkaci Hannatu sosai domin ibadarta. Ta sami gatar ganin Yesu yana jariri sa’ad da Yusufu da Maryamu suka kawo shi zuwa haikali don a gabatar da shi ga Jehobah yadda Doka ta ce a yi. Da ganin Yesu, Hannatu ta soma “bada godiya ga Allah, ta yi zancensa kuma ga dukan waɗanda su ke sauraron pansar Urushalima.”—Luka 2:22-24, 36-38; Litafin Lissafi 18:6, 7.
5, 6. A waɗanne hanyoyi ne a yau tsofaffi da yawa suke nuna hali kamar na Hannatu?
5 Tsofaffi da yawa a yau da suke tsakaninmu suna kama da Hannatu wajen halartan taro a kai a kai, suna addu’a don ci gaban bauta ta gaskiya, kuma suna son su yi wa’azin bishara. Wani ɗan’uwa mai shekara tamanin wanda shi da matarsa suna halartar taro a kai a kai ya ce: “Zuwa taro ya zama jikinmu. Ba ma son mu kasance a wani waje. Muna son mu kasance inda mutanen Allah suke. A wajen ne muke samun gamsuwa.” Wannan misali ne mai ban ƙarfafa ga dukanmu!—Ibraniyawa 10:24, 25.
6 “Idan ana wani abu game da bauta ta gaskiya kuma zan iya yi, ina son in yi.” Wannan shi ne abin da Jean, wata gwauruwa a shekarunta na 80 take cewa a kowane lokaci. Ta ci gaba: “Babu shakka akwai lokacin da nake baƙin ciki, amma me ya sa kowa da ke kusa da ni zai yi baƙin ciki sa’ad da nake yi?” Ta yi farin cikin ziyarar wasu ƙasashe don ƙarfafawa na ruhaniya. A tafiya da ta yi kwanan nan, ta gaya wa abokan tafiyarta, “Na gaji da fita yawon shaƙatawa, ina son in fita hidimar fage!” Ko da yake ba ta iya yaren wurin da ta je ba, Jean ta sa mutane su soma son saƙon Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ta yi shekaru da yawa tana hidima a wata ikilisiya da take bukatar taimako, duk da cewa tana bukatar ta koyi sabon yare da kuma yin tafiya na sa’a guda don halartar taro.
Cin Gaba da Koyo
7. Ta yaya Musa ya furta muradin ci gaba da dangantakarsa da Allah sa’ad da ya tsufa?
7 Mutum na fahimtar rayuwa da shigewar lokaci. (Ayuba 12:12) Cin gaba a ruhaniya ba ya zuwa haka kawai don yawan shekaru. Saboda haka, maimakon su dogara da ilimin da suke da shi a dā, bayin Allah masu aminci suna ƙoƙarin su “ƙaru da ilimi” da shigewar shekaru. (Misalai 9:9) Musa na ɗan shekara 80 sa’ad da Jehobah ya ba shi aiki. (Fitowa 7:7) A zamaninsa, da ƙyar ne mutum ya kai wannan shekarar, domin ya rubuta: “Kwanukan shekarunmu shekara hauya uku ce da goma, . . . domin ƙarfi sun kai hauya huɗu.” (Zabura 90:10) Duk da haka, Musa bai ji ba cewa, ya tsufa ainun ya yi koyo. Bayan ya bauta wa Allah shekaru da yawa, ya mori gata da yawa, kuma ya ɗauki hakkoki masu wuya, Musa ya roƙi Jehobah: “Ka gwada mini tafarkunka, da zan san ka.” (Fitowa 33:13) Musa yana son dangantakarsa da Jehobah ta ci gaba da ƙaruwa.
8. Ta yaya Daniel ya ci gaba da koyo a shekarunsa na 90, da waɗanne sakamako?
8 Annabi Daniel mai yiwuwa a shekarunsa na 90, ya ci gaba da bincika littattafai masu tsarki. Abin da ya fahimta ta wurin nazarin “littattafai” waɗanda wataƙila sun haɗa da Leviticus, Ishaya, Irmiya, Hosea, da Amos, ya motsa shi ya biɗi Jehobah cikin addu’a. (Daniel 9:1, 2) An amsa masa wannan addu’ar ta wajen ba shi hurarren bayani game da zuwan Almasihu da kuma bauta mai tsarki ta nan gaba.—Daniel 9:20-27.
9, 10. Menene wasu suka yi don su ci gaba a ruhaniya?
9 Kamar Musa da Daniel, za mu yi ƙoƙari mu ci gaba da mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya iya ƙoƙarinmu. Mutane da yawa suna hakan. Worth wanda dattijo ne a shekarunsa na 80 yana ƙoƙari ya ci duka abinci na ruhaniya da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake bayarwa. (Matta 24:45) Ya ce, “Ina son bin gaskiya, ina farin ciki sosai na ga yadda hasken gaskiya ke ci gaba da haskakawa.” (Misalai 4:18) Hakanan ma, Fred, wanda ya yi fiye da shekaru 60 a hidima ta cikakken lokaci, ya ga cewa yana da ban ƙarfafa a ruhaniya a soma taɗi na Littafi Mai Tsarki da ’yan’uwa masu bi. “Ya kamata in riƙa bimbini game da Littafi Mai Tsarki,” in ji shi. “Idan za ka iya sa Littafi Mai Tsarki ya zama da gaske, ya kasance da ma’ana kuma idan za ka iya daidaita abin da kake koya da ‘kwatancin sahihiyan kalmomi,’ ka san cewa ba za ka riƙa samun ɗan bayani kawai ba. Za ka ga yadda kowane bayani zai haskaka a inda ya dace.”—2 Timothawus 1:13.
10 Tsufa ba ta hana koyon sababbin abubuwa masu wuya. Mutanen da suke shekarunsu na sattin, saba’in har tamanin sun sha kan jahilci ko kuma sun koyi sababbin harsuna. Wasu cikin Shaidun Jehobah sun yi hakan da nufin yi wa mutane daga ƙasashe dabam dabam wa’azin bishara. (Markus 13:10) Harry da matarsa suna shekarunsu na sattin sa’ad da suka tsai da shawara su taimaka wa mutanen Portugal. Harry ya ce: “Da gaske kowane aiki a rayuwa ya fi wuya idan mutum ya tsufa.” Duk da haka, da ƙoƙari da nacewa, suna gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a yaren Portugal. Shekaru da yawa yanzu, Harry yana ba da jawabi a taron gunduma a sabon yaren.
11. Me ya sa ya kamata ka yi la’akari da abin da tsofaffi masu aminci suka cim ma?
11 Hakika, ba kowa ba ne yake da cikakkiyar lafiya ko kuma yanayinsa ya dace da zai ɗauki irin wannan ƙalubalen. Ka yi la’akari da abin da wasu tsofaffi suka cim ma. Wannan ba shawara ake ba mutane cewa kowa ya yi ƙoƙari ya cim ma irin waɗannan abubuwa ba. Maimakon haka, ya yi daidai da abin da manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa game da dattawan ikilisiya masu aminci: “Ku yi koyi da bangaskiyarsu, kuna tuna da matuƙar tasarrufinsu.” (Ibraniyawa 13:7) Idan muka yi la’akari da irin wannan misalai na himma, za mu ƙarfafa mu yi koyi da bangaskiya mai ƙarfi da ta motsa waɗannan tsofaffi a hidimarsu ga Allah. Da yake ba da bayanin abin da ya motsa shi, Harry da yanzu shekararsa 87 ne ya ce, “Ina son in yi amfani da sauran shekaru na da kyau kuma na kasance da amfani a hidimar Jehobah.” Fred, da aka ambata ɗazu yana samun gamsuwa wajen kula da aikinsa a Bethel. Ya ce, “dole ka nemi yadda za ka fi bauta wa Jehobah da kyau kuma ka ci gaba da yin haka.”
Ba da Kai Duk da Canjin Yanayi
12, 13. Ta yaya ne Barzillai ya nuna ibada duk da canjin yanayinsa?
12 Bi da canjin yanayi na zahiri yana da wuya. Duk da haka, yana yiwuwa a kasance da ibada duk da irin wannan canji. Barzillai Bagileyade Ya kafa misali mai kyau a wannan batun. Da yake shekara 80, ya nuna halin karimci sosai ga Dauda da rundunarsa, ya ba su abinci da wurin kwanciya a lokacin da Absalom ya yi tawaye. Sa’ad da Dauda yake komawa Urushalima, Barzillai ya raka rundunan zuwa Kogin Urdun. Dauda ya ce wa Barzillai zai sa shi cikin fadawansa. Menene Barzillai ya ce? “Yau shekarata shekara tamanin ce; na iya in raba tsakanin alheri da sharri? Bawanka ya iya ɗanɗana abin da ni ke ci ko abin da ni ke sha? Yanzu na iya jin muryar maza da mata masu-waƙa . . . ka dubi bawanka Chimham; bari shi ya haye tare da ubangijina sarki; ka yi masa kuma abin da ka ga dama.”—2 Samuila 17:27-29; 19:31-40.
13 Duk da canjin yanayinsa, Barzillai ya yi iyakar ƙoƙarinsa don ya tallafa wa sarkin da Jehobah ya naɗa. Ko da yake ya fahimci cewa ba ya jin daɗin ɗanɗano kuma ba ya ji sosai kamar dā, bai yi baƙin ciki ba. Maimakon haka, Barzillai ya nuna irin mutumin da yake, da ya ce a zaɓi Chimham don ya samu amfanin abubuwa da aka ba shi. Kamar Barzillai, tsofaffi da yawa a yau suna nuna halin karimci da rashin son kai. Suna iyakar ƙoƙarinsu su tallafa wa bauta ta gaskiya da sanin cewa “da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.” Albarka ne mu samu irin waɗannan masu aminci a tsakaninmu!—Ibraniyawa 13:16.
14. Ta yaya shekarar Dauda ta sa kalmomin da ke rubuce a Zabura 37:23-25 suka kasance da ma’ana?
14 Ko da yanayin Dauda ya canja sau da yawa, ya tabbata cewa yadda Jehobah yake kula da bayinsa masu aminci ba ya canjawa. A kusan ƙarshen rayuwarsa, Dauda ya rera waƙa da a yau aka sani da Zabura ta 37. Ka yi tunanin yadda Dauda yake bimbini, yana kaɗa molo kuma yana rera waɗannan kalmomin: “Ubangiji yana kafa tasarrufin mutum; Yana murna da tafarkinsa kuma. Ko ya fāɗi, ba za ya yi warwas ba: gama Ubangiji yana riƙe da shi a hannunsa. Dā yaro ni ke, yanzu kuwa na tsufa: amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu.” (Zabura 37:23-25) Jehobah ya ga ya dace a haɗa shekarar Dauda a wannan hurarriyar zabura. Wannan ya daɗa zurfin juyayi ga waɗannan kalmomi da suke motsa zuciya!
15. Ta yaya manzo Yohanna ya kafa misali mai kyau na aminci duk da canjin yanayi da tsufa?
15 Manzo Yohanna wani misali ne mai kyau na wanda ya kasance da aminci duk da cewa yanayinsa ya canja kuma ya tsufa. Bayan ya bauta wa Allah na kusan shekara 70, aka kai Yohanna bauta a tsibirin Batmusa “sabili da maganar Allah da shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 1:9) Duk da haka, aikinsa bai ƙare ba. Hakika, Yohanna ya yi dukan rubuce-rubucensa da ke cikin Littafi Mai Tsarki a kusan ƙarshen rayuwarsa. Sa’ad da yake Batmusa ya mai da hankali sosai ya rubuta wahayi mai ban mamaki da aka nuna masa. (Ru’ya ta Yohanna 1:1, 2) Ana ganin an sake shi daga bauta a lokacin sarautar Nerva na Daular Roma. Bayan haka, a misalin shekara ta 98 K.Z., sa’ad da wataƙila yake ɗan shekara 90 ko 100, Yohanna ya rubuta Lingila da wasiƙu uku masu ɗauke da sunansa.
Labarin Jimiri da ba ya Shigewa
16. Ta yaya ne kurame za su iya nuna ibadarsu ga Jehobah?
16 Kasawa yana iya zuwa a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, wasu mutane sun zama kurame da hakan ba sa iya magana da mutane. Duk da haka, suna tunawa da ƙaunar Allah da alherinsa. Ko da ba sa iya magana, a zuciyarsu suna gaya wa Jehobah: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” (Zabura 119:97) Jehobah ya san “masu-tunawa da sunansa,” kuma yana farin ciki cewa waɗannan sun bambanta da mutane da yawa da ba su damu da hanyoyinsa ba. (Malachi 3:16; Zabura 10:4) Yana da ban ƙarfafa mu san cewa Jehobah yana farin ciki idan muka yi bimbini!—1 Labarbaru 28:9; Zabura 19:14.
17. Menene bayin Jehobah tsofaffi suka cim ma da yake da tamani?
17 Ya kamata mu tuna cewa waɗanda suke bauta wa Jehobah cikin aminci shekaru da yawa sun cim ma abu na musamman da ba za su taɓa samu ba a wata hanya, wato, tarihin jimiri da ba ya shuɗewa. Yesu ya ce: “Ta cikin haƙurinku za ku sami rayukanku.” (Luka 21:19) Jimiri yana da muhimmanci don samun rai madawwami. Waɗanda suka “aika nufin Allah” kuma suka nuna amincinsu ta tafarkin rayuwarsu za su samu cikar “alkawari.”—Ibraniyawa 10:36.
18. (a) Menene Jehobah yake farin cikin gani game da tsofaffi? (b) Menene za mu tattauna a talifi na gaba?
18 Jehobah na ɗaukar hidimar da kuka yi da dukan zuciyarku da tamani komi ƙanƙantansa. Ko da menene yake faruwa da ‘mutumi namu na waje’ sa’ad da muka tsufa, ‘mutumi namu na ciki’ yana sabontawa yau da gobe. (2 Korinthiyawa 4:16) Babu shakka cewa Jehobah yana daraja abin da kuka cim ma dā, amma a bayyane yake cewa yana daraja abin da kuke yi yanzu domin sunansa. (Ibraniyawa 6:10) A talifi na gaba, za mu tattauna sakamakon irin wannan aminci.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Wane misali mai kyau ne Hannatu ta kafa wa Kiristoci tsofaffi a yau?
• Me ya sa shekaru ba za su hana mutum ya cim ma abin da yake so ba?
• Ta yaya tsofaffi za su ci gaba da nuna ibada?
• Yaya Jehobah yake ɗaukan hidima da tsofaffi suke masa?
[Hoto a shafi na 23]
Daniel tsoho ya fahimci tsawon lokaci da Yahudawa za su kasance a bauta ta wajen karanta “littattafai”
[Hotuna a shafi na 25]
Tsofaffi da yawa sun kafa misali mai kyau wajen halartar taro a kai a kai, suna wa’azi da himma, kuma suna ɗokin su yi koyo