Ka Bauta wa Jehobah Kafin Miyagun Kwanaki Su Zo
“Ka tuna da Mahaliccinka.”—M. WA. 12:1.
1, 2. (a) Wane gargaɗi ne aka hure Sulemanu ya rubuta wa matasa? (b) Me ya sa gargaɗin Sulemanu zai iya shafan Kiristoci masu shekaru hamsin ko fiye da hakan?
JEHOBAH ya hure Sarki Sulemanu ya gaya wa matasa cewa: “Ka tuna da Mahaliccinka . . . a cikin kwanakin ƙuruciyarka, kafin miyagun kwanaki su zo.” Mene ne waɗannan “miyagun kwanaki”? Wannan furucin yana nufin lokacin da mutum ya tsufa. Sulemanu ya yi amfani da wannan furucin don ya nuna irin wahalar da waɗanda suka tsufa suke sha, wato hannaye da ƙafafu masu rawa da zuban haƙora da rashin gani ko ji da kyau da yin furfura da kuma yin tafiya a tanƙware. Babu shakka, shi ya sa Sulemanu ya gaya mana mu tuna da Mahaliccinmu tun muna ƙuruciya.—Karanta Mai-Wa’azi 12:1-5.
2 Kiristoci da yawa da suka kai shekara hamsin ko fiye da haka suna da sauran ƙarfi. Za su iya yin furfura, amma wataƙila ba su da irin matsalolin da Sulemanu ya kwatanta. Shin waɗannan ’yan’uwa za su iya amfana daga gargaɗin da aka hure Sulemanu ya rubuta wa matasa cewa: “Ka tuna da Mahaliccinka”? Mene ne wannan gargaɗin yake nufi?
3. Mene ne tunawa da Mahaliccinmu ya ƙunsa?
3 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, yana da muhimmanci mu riƙa yin tunani a kai a kai a kan darajar Mahaliccinmu. Rai babban kyauta ne. Yadda Jehobah ya halicci abubuwa yana da wuyan fahimta sosai. Abubuwa da yawa da Jehobah ya yi suna sa mu jin daɗin rayuwa a hanyoyi masu yawa. Idan muka yi tunani a kan halittun Jehobah, muna tuna ma kanmu ƙaunarsa da hikimarsa da kuma ikonsa. (Zab. 143:5) Tuna da Mahaliccinmu yana kuma nufin tuna abin da yake bukata a gare mu. Yin bimbini a kan waɗannan abubuwan za su motsa mu mu nuna godiya ta wajen yin iya ƙoƙarinmu mu bauta masa muddar ranmu.—M. Wa. 12:13.
ZARAFI MAI KYAU A NAN GABA
4. Wace tambaya ce Kiristocin da suka daɗe suna bauta wa Jehobah za su iya yi wa kansu, kuma me ya sa?
4 Idan ka yi shekaru da yawa kana rayuwa, za ka iya tambayar kanka, ‘Mene ne zan yi da rayuwata yanzu da nake da ɗan ƙarfi?’ A matsayinka na Kirista da ya manyanta, kana da zarafin da wasu ba su da shi. Alal misali, za ka iya koya wa matasa abubuwan da ka koya daga Jehobah. Za ka iya ba wasu labarai masu daɗi da ka samu yayin da kake bauta wa Allah. Sarki Dauda ya yi addu’a don ya sami zarafin yin hakan. Ya ce: “Ya Allah, tun ina yaro kā koya mani; . . . I, har lokacin da na tsufa na yi furfura, kada ka yashe ni, ya Allah; sai dai na bayyana ikonka ga tsara mai-zuwa, ƙarfinka kuma ga dukan wanda ya ke zuwa.”—Zab. 71:17, 18.
5. Ta yaya Kiristoci da suka manyanta za su iya koya wa wasu abubuwan da suka koya?
5 Ta yaya za ka iya koya wa wasu hikimar da ka samu a rayuwarka? Shin, za ka iya gayyatar matasa a gidanka don ka ƙarfafa su? Za ka iya fita wa’azi da su don su shaida irin farin cikin da kake samu a bauta wa Jehobah? Elihu ya ce: “Ya kamata yawan kwanaki su yi magana, Yawan shekaru kuma za su koyar da hikima.” (Ayu. 32:7) Manzo Bulus ya gaya wa mata Kiristoci da suka manyanta cewa su ƙarfafa wasu ta wajen magana da kuma kafa musu misali mai kyau. Ya ce: “Haka nan tsofaffin mata kuma su . . . koyar da nagarta.”—Tit. 2:3.
YADDA ZA KA IYA TAIMAKA WA WASU
6. Me ya sa ake bukatar Kiristoci da suka daɗe suna bauta wa Jehobah?
6 Idan ka manyanta a matsayin Kirista, kana da aiki sosai a taimaka wa wasu. Ka yi tunanin abubuwan da ka iya yi yanzu da ba ka sani ba shekaru 30 ko 40 da suka shige. Za ka iya yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a fannoni da yawa na rayuwa. Babu shakka, za ka iya ratsa zukatan mutane ta yin amfani da Littafi Mai Tsarki. Idan kai dattijo ne, ka san yadda za ka taimaka wa ’yan’uwa da suka bijire. (Gal. 6:1) Wataƙila ka koyi yadda za ka kula da wasu ayyuka na ikilisiya da na manyan taro ko kuma na gine-ginen Majami’un Mulki. Za ka iya taimaka wa likitoci don su iya amfani da wasu hanyoyin jinya ba tare da yin amfani da jini ba. Ko da ba ka daɗe da yin baftisma ba, ka koyi wasu abubuwa da yawa. Alal misali, idan kana da yara, babu shakka, ka koyi wasu abubuwa da za su taimaka maka. Kiristoci tsofaffi za su iya amfanar bayin Jehobah maza da mata ta wajen koyar da su da ja-gorantar da su da kuma ƙarfafa su.—Karanta Ayuba 12:12.
7. Ta yaya waɗanda suka manyanta za su iya koyar da matasa?
7 A waɗanne hanyoyi ne za ka yi amfani da abubuwan da ka koya don ka taimaka wa wasu? Wataƙila za ka iya koya wa matasa yadda za su soma da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau. Idan ke ’yar’uwa ce, shin za ki iya shawarci mata matasa da suke da yara a kan yadda za su kyautata bautarsu ga Jehobah yayin da suke renon yaransu? Idan kai ɗan’uwa ne, shin za ka iya koya wa ’yan’uwa matasa yadda za su iya ba da jawabi da kuma yin wa’azi da kyau? Za ka iya nuna musu yadda ka ziyarci ’yan’uwa maza da mata da suka tsufa don ka ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah? Ko da ba ka da ƙarfi kamar dā, za ka iya yin amfani da wannan zarafin wajen koyar da matasa. Kalmar Allah ta ce: “Fahariyar samari ƙarfinsu ne: jamalin tsofaffi kuma furfura ne.”—Mis. 20:29.
YIN HIDIMA A INDA AKE DA BUKATA SOSAI
8. Mene ne manzo Bulus ya yi sa’ad da ya tsufa?
8 Manzo Bulus ya yi amfani da abubuwan da ya koya don ya bauta Jehobah sa’ad da ya tsufa. A lokacin da aka fito da shi daga fursuna a ƙasar Roma a misalin shekara ta 61 a zamaninmu, ya riga ya yi hidima sosai kuma ya jimre da gwaje-gwaje masu yawa a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje. Saboda haka, zai iya zama a wurin don ya yi hidima hankali kwance. (2 Kor. 11:23-27) Babu shakka, ’yan’uwa da suke ƙasar Roma sun so Bulus ya zauna a wurin don ya tallafa musu. Amma ya lura cewa ana da bukata sosai a wasu ƙasashe. Saboda haka, ya tsai da shawarar zuwa Afisa tare da Timotawus da kuma Titus, bayan haka sai suka tafi ƙasar Karita da kuma wataƙila ƙasar Makidoniya. (1 Tim. 1:3; Tit. 1:5) Ya so ya je ƙasar Sifen, amma ba mu sani ko ya je ba.—Rom. 15:24, 28.
9. A wane lokaci ne wataƙila Bitrus ya je yin hidima a inda ake da bukata sosai? (Ka duba hoto na farko.)
9 Wataƙila manzo Bitrus ya fi shekaru hamsin sa’ad da ya tafi inda ake da bukata sosai. Ta yaya muka san da hakan? Idan shi da Yesu tsara ne ko kuma ya ɗan girme shi, to, wannan zai nuna cewa ya kusan shekara hamsin sa’ad da suka yi taro da wasu manzanni a Urushalima a shekara ta 49 a zamaninmu. (A. M. 15:7) Bayan taron, Bitrus ya ƙaura zuwa Babila, babu shakka ya je wurin don ya yi wa Yahudawa da yawa da suke wurin wa’azi ne. (Gal. 2:9) A wurin ne ya rubuta wasiƙarsa ta farko a misalin shekara ta 62 a zamaninmu. (1 Bit. 5:13) Ko da yake ƙaura zuwa inda ake da bukata bai da sauƙi, amma Bitrus bai bari shekarunsa su hana shi jin daɗin bauta wa Jehobah ba.
10, 11. Mene ne Robert da matarsa suka yi?
10 A yau, Kiristoci da yawa da shekarunsu suka kai 50 ko fiye da hakan sun lura cewa yanayinsu ya canja kuma sun gano wasu sababbin hanyoyin da za su iya bauta wa Jehobah. Wasu sun ƙaura zuwa inda ake da bukata. Alal misali, Robert ya ce: “Ni da matata mun kai shekaru hamsin da biyar sa’ad da muka fahimci cewa muna da wasu hanyoyin faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah. Ɗanmu ya bar gida, iyayenmu sun riga sun rasu kuma sun bar mana wani ɗan gādo. Na yi tunani cewa idan na sayar da gidana, zan iya biyan bashi kuma za mu samu kuɗin kula da kanmu kafin a biya ni kuɗin fensho. Sai muka ji labari cewa mutane da yawa a ƙasar Bolivia suna yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma abubuwa ba su da tsada sosai a wurin. Don haka, muka tsai da shawarar ƙaura. Sabawa da sabon gidanmu bai kasance mana da sauƙi ba. Kome dai ya zama dabam da irin rayuwar da muka saba da shi a Amirka. Amma an albarkaci ƙoƙarin da muka yi.”
11 Robert ya ƙara da cewa: “Yanzu mun duƙufa wajen yin ayyukan ikilisiya. Wasu cikin mutane da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su sun yi baftisma. Wata iyali da muka yi nazari da su ba su da kuɗi sosai kuma ba sa zama kusa da inda ake taro. Amma kowane sati, ’yan iyalin nan suna yin tafiya mai nisa zuwa birni don su halarci taro. Mun yi farin ciki sosai saboda ci gabar da iyalin ta yi da kuma lokacin da ɗan farinsu ya soma hidimar majagaba.”
BUKATA A YANKUNAN DA AKE WASU HARSUNA
12, 13. Ka ba da labarin wani Kirista da ya faɗaɗa hidimarsa bayan da ya yi murabus da aiki.
12 Ikilisiyoyi da kuma rukunonin da suke wasu yaruka dabam za su iya amfana sosai daga misalin tsofaffi maza da mata. Har ila, za a iya jin daɗin wa’azi a irin waɗannan yankunan. Alal misali, wani mai suna Brian daga ƙasar Ingila ya ce: “Ni da matata ba mu ji daɗin rayuwa ba sam sa’ad da na yi murabus da aiki ina ɗan shekara 65. Yaranmu sun bar gida kuma ba ma cika samun waɗanda za mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Sai na haɗu da wani ɗan Caina da yake wani bincike a wata jami’a. Na gayyace shi zuwa taro kuma ya amince da hakan, sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Bayan ’yan makonni, sai ya soma zuwa taro da wani abokinsa shi ma ɗan Caina. Makonni biyu bayan haka, sai ya kawo mutane uku zuwa taron.
13 “A lokacin da wannan ɗan Caina na biyar ya gaya mini in yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, na yi tunani, ‘Ba wai don na kai shekara 65 sai in daina bauta wa Jehobah ba.’ Sai na tambayi matata da na girme ta da shekara biyu ko za ta iya koyon yaren Caina. Mun yi amfani da kaset da aka ɗauka don koyar da wannan yaren. Hakan ya faru shekaru goma da suka shige. Yin wa’azi a yanki da ake wani yare dabam ya sa mun zama kamar matasa. Mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ’yan Caina guda 112. Yawancinsu sun halarci taronmu. Ɗaya daga cikinsu yanzu yana hidimar majagaba a inda muke.”
KA JI DAƊIN YIN IYA GWARGWADONKA
14. Me ya kamata Kiristoci tsofaffi su riƙa tunawa, kuma yaya misalin Bulus zai ƙarfafa su?
14 Ba dukan Kiristoci da suka kai shekara hamsin ko fiye da haka ba ne za su iya faɗaɗa hidimarsu ga Jehobah ba. Wasu ba su da koshin lafiya, wasu kuma suna kula da yaransu ko kuma iyayensu da suka tsufa. Bai kamata ka manta cewa Jehobah yana ɗaukan ƙoƙarin da kake yi da muhimmanci ba. Saboda haka, idan a wasu lokatai kana yin baƙin ciki don ba za ka iya yin wasu abubuwa ba, ka mai da hankali ga waɗanda za ka iya yi kuma ka yi farin ciki. Ka yi la’akari da misalin manzo Bulus. Ya yi shekaru da yawa a gidan yari kuma hakan ya hana shi zuwa ƙasashen waje don yin wa’azi. Amma a duk lokacin da mutane suka ziyarce shi, yana bayyana musu Littafi Mai Tsarki kuma yana ƙarfafa bangaskiyarsu.—A. M. 28:16, 30, 31.
15. Me ya sa tsofaffi Kiristoci suke da daraja?
15 Ƙari ga haka, Jehobah yana jin daɗin hidimar waɗanda suka tsufa sosai. Ko da yake Sulemanu ya ce lokacin tsufa yana da wuya, amma Jehobah yana ɗaukan hidimar da tsofaffi suke yi masa da muhimmanci. (Luk 21:2-4) ’Yan’uwa a ikilisiyoyi suna jin daɗin misalin da tsofaffi suke kafawa a bautar Jehobah.
16. Wane zarafi ne wataƙila Hannatu ba ta samu ba, amma me ta yi a hidimar Jehobah?
16 Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wata tsohuwa mai suna Hannatu da ta ci gaba da bauta wa Jehobah har ta tsufa. A lokacin da aka haifi Yesu, ita gwauruwa ce ’yar shekara 84. Saboda shekarunta, wataƙila ba ta sami zarafin zama almajirar Yesu da kasance cikin waɗanda aka shafe da ruhu mai tsarki da kuma yin wa’azin Mulkin ba. Duk da haka, Hannatu ta ji daɗin yi wa Jehobah hidima a wasu hanyoyi. Alal misali, kowace safiya takan je farfajiyar haikalin don ta yi addu’a a zuciyarta na wataƙila kusan minti talatin sa’ad da firist yake miƙa hadaya ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce “ba ta rabuwa da haikali, tana sujada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” (Luk 2:36, 37) Sa’ad da ta ga Yesu da yake jariri, sai ta soma “zancensa kuma ga dukan waɗanda su ke sauraron fansar Urushalima.”—Luk 2:38.
17. Ta yaya za mu iya taimaka wa Kiristoci tsofaffi da kuma naƙasassu su bauta wa Jehobah?
17 A yau, za mu iya yin amfani da hanyoyi dabam-dabam don mu iya taimaka wa Kiristoci maza da mata. Akwai wasu tsofaffi da za su so su kasance tare da mu a taron ikilisiya da kuma manyan taro amma ba za su iya yin hakan ba. Ta yaya ikilisiya za ta taimaka musu? A wasu wurare, zai iya yiwu su saurari taron ta tarho. Amma a wasu wurare, hakan ba zai yiwu ba. Duk da haka, Kiristocin da ba sa iya halartan taro za su iya tallafa wa bauta ta gaskiya. Alal misali, za su iya yin addu’a a madadin ikilisiya don ta samu ci gaba.—Karanta Zabura 92:13, 14.
18, 19. (a) Ta yaya tsofaffi Kiristoci za su iya ƙarfafa ’yan’uwa? (b) Su waye ne za su iya bin wannan gargaɗi: “Ka tuna da Mahaliccinka”?
18 Kiristoci tsofaffi ba za su iya san cewa suna ƙarfafa ’yan’uwa ba. Ka yi la’akari da Hannatu, wadda ta kwashi shekaru tana zuwa bauta wa Jehobah a haikali. Wataƙila ba ta san cewa za a rubuta misalin da ta kafa a Littafi Mai Tsarki ba kuma daga baya hakan ya ƙarfafa mu ba. Haka ma a yau, ’yan’uwa maza da mata ba za su manta da ƙaunar da kake yi wa Jehobah ba. Babu shakka, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.”—Mis. 16:31.
19 Abin da dukanmu za mu iya yi a bautarmu ga Jehobah yana da iyaka. Amma bari dukan waɗanda suke da ɗan ƙarfi su ƙuduri aniyar ‘tuna da Mahaliccinsu . . . kafin miyagun kwanaki su zo.’—M. Wa. 12:1.