Bincika Al’amura “Zurfafa Na Allah”
“Ruhu yana binciken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.”—1 KORINTHIYAWA 2:10.
1. Menene wasu gaskiya na Littafi Mai Tsarki da za su sa sababbin ɗaliban Littafi Mai Tsarki su yi farin ciki?
YAWANCINMU a ikilisiyar Kirista za mu iya tuna farin cikin da muka yi sa’ad da muka fara sanin gaskiya. Mun fahimci muhimmancin sunan Jehobah, abin da ya sa ya ƙyale mutane su sha wahala, abin da ya sa waɗansu mutane za su tafi sama, da kuma abin da nan gaba ke ɗauke da shi ga dukan mutane masu aminci. Wataƙila mun taɓa bincika Littafi Mai Tsarki a dā, amma ba mu fahimci waɗannan abubuwan ba, kamar yadda mutane da yawa ba su fahimta ba. Muna kama da mutumin da yake kallon wani halitta a ƙarƙashin teku. Bai iya ganin abubuwa masu kyau a ƙarƙashin tekun sosai ba. Amma da taimakon gilashin ido da ake amfani da shi don gani sosai a ƙarƙashin teku, ya yi farin cikin ganin ƙananan halittu da suke cikin teku da kuma wasu halittu masu kama da furanni. Hakazalika, sa’ad da wani ya fara taimakonmu mu fahimci Nassosi, mun fara fahimtar al’amura “zurfafa na Allah.”—1 Korinthiyawa 2:8-10.
2. Me ya sa farin cikin koyon Kalmar Allah ba shi da iyaka?
2 Ya kamata mu gamsu da gaskiya na Littafi Mai Tsarki da muka sani da farko ne kawai? Furcin nan “zurfafa na Allah” ya ƙunshi fahimtar hikimar Allah da aka bayyana wa Kiristoci da taimakon ruhu mai tsarki amma an ɓoye wa waɗansu. (1 Korinthiyawa 2:7) Hikimar Allah ba ta da iyaka kuma za mu iya samun farin ciki idan muka bincika ta sosai. Ba za mu taɓa fahimtar dukan hikimar Allah ba. Farin cikin da muka samu sa’ad da muka fara fahimtar koyarwa masu sauƙi na Littafi Mai Tsarki zai kasance tare da mu har abada idan muka ci gaba da bincika al’amura “zurfafa na Allah.”
3. Me ya sa muke bukatar mu fahimci ainihin dalilin da ya sa muka gaskata da bangaskiyarmu?
3 Me ya sa ya kamata mu fahimci waɗannan al’amura “zurfafa na Allah?” Fahimtar bangaskiyarmu da kuma dalilin da ya sa muka gaskata da ita, wato, ainihin tushen imaninmu, zai ƙarfafa bangaskiyarmu da kuma tabbacinmu. Nassosi ya gaya mana mu yi amfani da ‘hankalinmu’ (NW) don mu ‘gwada ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.’ (Romawa 12:1, 2) Fahimtar abin da ya sa Jehobah ya ce mu yi rayuwa a wata hanya zai ƙarfafa mu mu yi masa biyayya. Saboda haka, sanin al’amura “zurfafa” za su iya ƙarfafa mu mu kauce wa gwaji da zai sa mu yi ayyuka marar kyau kuma zai iya sa mu yi “himman nagargarun ayyuka.”—Titus 2:14.
4. Menene nazarin Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa?
4 Dole ne mu yi nazari don mu fahimci zurfafan al’amura. Duk da haka, yin nazari ya bambanta da karatun sama-sama. Ya ƙunshi bincika bayanin sosai don ka ga yadda ya jitu da abin da ka sani a dā. (2 Timothawus 1:13) Ya ƙunshi fahimtar dalilan da aka ba da. Ya kamata nazarin Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi yin bimbini game da yadda za mu iya yin amfani da abin da muka koya wajen yanke shawarwari masu kyau da kuma taimaka wa waɗansu. Tun da “kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani” ne, ya kamata nazarin da muke yi ya ƙunshi “kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.” (2 Timothawus 3:16, 17; Matta 4:4) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana bukatar ƙwazo sosai! Amma za mu iya jin daɗinsa, kuma fahimtar al’amura “zurfafa na Allah” ba shi da wuya.
Jehobah Yana Fahimtar da Masu Tawali’u
5. Wanene zai iya fahimtar al’amura “zurfafa na Allah”?
5 Ko da ba ka da ilimi sosai ko kuma ba ka saba yin nazari ba, kada ka yi tunanin cewa ba za ka iya fahimtar al’amura “zurfafa na Allah” ba. A lokacin da Yesu ya yi hidimarsa a duniya, Jehobah bai bayyana wa mutane masu hikima da fahimi nufinsa ba, amma ya bayyana wa mutane marasa ilimi masu tawali’u waɗanda bayin Allah za su iya koyar da su. Suna kama da jarirai idan aka kwatanta su da masu ilimi. (Matta 11:25; Ayukan Manzanni 4:13) Manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwansa masu bi game da “dukan iyakar abin da Allah ya shirya ma waɗanda ke ƙamnassa,” ya ce: “Mu ne Allah ya bayana mamu ta wurin Ruhu: gama Ruhu yana binciken abu duka, i, har da [al’amura] zurfafa na Allah.”—1 Korinthiyawa 2:9, 10.
6. Menene 1 Korinthiyawa 2:10 take nufi?
6 Ta yaya ne ruhun Jehobah yake bincika “duka [al’amura] har da zurfafa na Allah”? Maimakon ya yi wa kowane Kirista bayani game da gaskiya, Jehobah yana amfani da ruhunsa don ya ja-goranci ƙungiyarsa, wadda take fahimtar da mutanen Allah daga cikin Littafi Mai Tsarki. (Ayukan Manzanni 20:28; Afisawa 4:3-6) A dukan duniya, dukan ikilisiyoyi suna more irin wannan tsarin ayyuka na nazarin Littafi Mai Tsarki. Sau da yawa, sun kammala tsarin ayyuka na koyarwa na Littafi Mai Tsarki. Da taimakon ruhu mai tsarki, ikilisiyoyi suna taimaka wa mutane su kasance da irin halin da zai sa su fahimci al’amura “zurfafa na Allah.”—Ayukan Manzanni 5:32.
Abin da Al’amura “Zurfafa na Allah” Suka Ƙunsa
7. Me ya sa mutane da yawa ba su fahimci al’amura “zurfafa na Allah” ba?
7 Kada mu yi tunanin cewa al’amura “zurfafa na Allah” suna da wuyan fahimta. Mutane da yawa ba su fahimci al’amura “zurfafa na Allah” ba, ba wai saboda hikimar Allah tana da wuya ba ne, amma saboda Shaiɗan yana ruɗar mutane su ƙi taimakon da Jehobah yake yin tanadinsa ta wurin ƙungiyarsa.—2 Korinthiyawa 4:3, 4.
8. Menene zurfafan al’amura da Bulus ya bayyana a cikin sura ta uku ta wasiƙarsa ga Afisawa?
8 Sura ta uku ta wasiƙar Bulus ga Afisawa ta nuna cewa al’amura “zurfafa na Allah” sun ƙunshi gaskiya da yawa da mutanen Jehobah suka fahimta sosai, kamar su sanin Zuriyar da aka yi alkawarinta, waɗanda aka zaɓa daga cikin mutane da suke da begen zuwa sama, da kuma Mulkin Almasihu. Bulus ya rubuta: “Wanda ba a sanas ma ’ya’yan mutane da ke cikin waɗansu tsararaki ba, kamar yadda yanzu am bayana shi ga manzanninsa masu-tsarki da annabawa cikin Ruhu. Cewa, cikin Kristi Yesu al’ummai abokan tarayya ne cikin gādo, gaɓaɓuwa kuma na jikin, abokan tarayya kuma cikin alkawali.” Bulus ya ce wai an aike shi ya “gwada ma mutane duka ko menene wakilcin asirin da ke a ɓoye tun dukan zamanu cikin Allah.”—Afisawa 3:5-9.
9. Me ya sa gata ne mu fahimci al’amura “zurfafa na Allah?”
9 Bulus ya ci gaba da bayyana nufin Allah cewa “ta wurin ikilisiya hikima iri iri ta Allah ta sanu ga sarautai da ikoki cikin sammai.” (Afisawa 3:10) Mala’iku sun amfana ta wurin kula da kuma fahimtar hikimar Jehobah ta yadda yake bi da ikilisiyar Kirista. Gata ne mu fahimci abubuwan da mala’iku ma suke sha’awa! (1 Bitrus 1:10-12) Bayan haka, Bulus ya ce mu yi ƙoƙari mu “ruska, tare da dukan tsarkaka, ko menene fāɗin da ratar da tsawon da zurfin” bangaskiyar Kirista. (Afisawa 3:11, 18) Bari yanzu mu tattauna waɗansu misalan zurfafan al’amura da ba mu taɓa tunaninsu ba.
Misalan Zurfafan Al’amura
10, 11. Kamar yadda Nassosi suka faɗa, yaushe ne Yesu ya zama ainihin ‘zuriyar’ “macen” Allah na samaniya?
10 Mun san cewa Yesu shi ne ainihin ‘zuriyar’ “macen” Allah na samaniya wadda aka ambata a Farawa 3:15. Don mu ƙara fahiminmu, za mu iya tambaya: ‘Yaushe ne Yesu ya zama Zuriyar da aka yi alkawarinta? A lokacin da yake sama ne, ko kuma a lokacin da ya zo duniya, ko kuwa a lokacin da aka yi masa baftisma ne, ko kuma a lokacin da aka ta da shi daga matattu ne?’
11 Allah ya yi alkawarin cewa sashen ƙungiyarsa na samaniya, wadda aka kira ‘macensa’ a cikin annabci, za ta haifi zuriya da za ta ƙuje macijin a kai. Shekaru da yawa sun wuce, kuma macen ta Allah ba ta haifi zuriya da za ta iya halaka Shaiɗan da ayyukansa ba. Shi ya sa annabcin Ishaya ya kira ta “bakarariya” da kuma mai “ciwo a ranta.” (Ishaya 54:1, 5, 6) Daga baya, an haifi Yesu a Bai’talami. Amma bayan da ya yi baftisma, sa’ad da aka shafe shi da ruhu mai tsarki kuma ya zama ɗan Allah na ruhaniya ne Jehobah ya sanar cewa: “Wannan Ɗana ne.” (Matta 3:17; Yohanna 3:3) A ƙarshe ainihin ‘zuriyar’ macen ya bayyana. Daga baya, an shafa mabiyan Yesu da ruhu mai tsarki. “Macen” Jehobah, wadda tun daɗewa take ji kamar macen da ‘ba ta haihu ba,’ a ƙarshe za ta ‘tada murya.’—Ishaya 54:1; Galatiyawa 3:29.
12, 13. Waɗanne nassosi ne suka nuna cewa dukan shafaffun Kirista a duniya sun ƙunshi “bawa mai-aminci, mai hikima?”
12 Misali na biyu na zurfafan al’amura da aka bayyana mana shi ne manufar Allah na zaɓan mutane 144,000 daga cikin duniya. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4) Mun yarda da wannan koyarwar cewa dukan shafaffu da suke rayuwa a duniya a kowane lokaci sun ƙunshi “bawan nan mai-amincin, mai hikima” da Yesu ya ce za su yi tanadin ‘abinci’ ga iyalinsa a kan kari. (Matta 24:45) Waɗanne Nassosi ne suka nuna cewa wannan koyarwar gaskiya ce? Yesu yana nuni ga kowane Kirista da yake ƙarfafa ’yan’uwansa da abinci na ruhaniya ne?
13 Allah ya gaya wa al’umman Isra’ila: “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji . . . barana kuma wanda na zaɓa.” (Ishaya 43:10) Amma a ranar 11 ga Nisan ta shekara ta 33 K.Z., Yesu ya gaya wa shugabannin Isra’ila cewa Allah ya yashe al’ummansu daga zama bayinsa. Ya ce: ‘Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.’ Yesu ya gaya wa jama’ar: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Matta 21:43; 23:38) A matsayinsu na bayin Jehobah, al’umman Isra’ila ba su da aminci ko kuma hikima. (Ishaya 29:13, 14) A wannan ranar sa’ad da Yesu ya yi tambaya cewa: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima?” Wato yana tambaya ne cewa, ‘Wace al’umma ce mai hikima da za ta zama bawan Allah mai aminci maimakon Isra’ila?’ Manzo Bitrus ya ba da amsar sa’ad da ya gaya wa ikilisiyar shafaffun Kiristoci: ‘Ku . . . al’umma mai-tsarki, jama’a abin mulki’ ne. (1 Bitrus 1:4; 2:9) Wannan al’umma ta ruhaniya, wato, “Isra’ila na Allah” ce ta zama sabuwar baiwar Jehobah. (Galatiyawa 6:16) Kamar yadda dukan Isra’ilawa na dā suka zama “bawa” ɗaya, haka nan ma dukan shafaffun Kiristoci a duniya a kowane lokaci suka zama “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Gata ne mai girma mu sami “abinci” ta wurin bawan Allah!
Za Ka Iya Jin Daɗin Nazari na Kai
14. Me ya sa nazarin Littafi Mai Tsarki yakan kawo farin ciki fiye da karantawa kawai?
14 Sa’ad da aka bayyana mana sabuwar ma’anar waɗansu Nassosi, muna yin farin ciki saboda yadda suke ƙarfafa bangaskiyarmu. Shi ya sa nazarin Littafi Mai Tsarki zai sa mu farin ciki fiye da karantawa kawai. Saboda haka, sa’ad da kake karanta littatafai na Kirista, ya kamata ka yi tunani sosai. Ka tambayi kanka: ‘Ta yaya ne wannan bayanin ya bambanta da wanda na sani game da wannan batu a dā? Wane ƙarin Nassi ko kuma bayani ne zan iya yin tunaninsa da zai ƙara taimaka mini game da bayanin da aka gabatar a wannan talifin?’ Idan yana bukatar ƙarin bincike, ka rubuta tambayoyin da kake son ka nemi amsoshinsu, sa’an nan ka sa ya zama batun da za ka yi nazarinsa a nan gaba.
15. Waɗanne irin nazari ne za su iya sa ka farin ciki kuma ta yaya za su iya kawo maka albarka ta har abada?
15 Wane irin nazari ne zai sa ka yi farin cikin fahimtar wasu sababbin abubuwa? Kamar su bincika alkawura dabam dabam da Allah ya yi don mutane su amfana. Za ka iya ƙarfafa bangaskiyarka idan ka yi nazarin annabce-annabcen da suka yi magana game da Yesu Kristi ko kuma yin nazarin littattafan annabci na Littafi Mai Tsarki aya aya. Bincika tarihin Shaidun Jehobah na zamanin nan, ta wurin yin amfani da littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, zai ƙarfafa bangaskiyarka, idan kana da littafin a yarenka.a Bincika “Tambayoyi Daga Masu Karatu” da ke cikin Hasumiyar Tsaro, zai ba ka sabuwar fahimin waɗansu nassosi. Ka lura da Nassosin da aka yi amfani da su don a bayyana batun. Hakan zai taimake ka ka yi amfani da ‘hankalinka’ don ka kasance da fahimi. (Ibraniyawa 5:14) Sa’ad da kake yin nazari, ka rubuta abubuwan da ka fahimta a cikin Littafi Mai Tsarkinka ko kuma a cikin wani littafi dabam don nazarin da kake yi ya amfane ka har abada da kuma waɗanda za ka taimaka wa.
Ku Taimaki Matasa su ji Daɗin Nazarin Littafi Mai Tsarki
16. Ta yaya za ka iya taimaka wa matasa su ji daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki?
16 Iyaye za su iya taimaka wa yaransu su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Kada ku yi tunanin cewa yara ba za su iya fahimtar zurfafan al’amura ba. Idan kuka ba yaranku abin da za su bincika don shirin nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali, kuna iya tambayarsu abin da suka koya. Kuna iya haɗa lokacin gwaji a nazarin iyali don ya taimaki matasa su koyi yadda za su bayyana bangaskiyarsu kuma su nuna cewa abin da suka koya gaskiya ne. Bugu da ƙari, za ka iya yin amfani da mujallar nan “See the Good Land”b don ka koyar da labarin ƙasashen da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ka bayyana abin da kake karantawa a cikin Littafi Mai Tsarki na kowane mako.
17. Me ya sa muke bukatar mu kasance da daidaita a nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi?
17 Nazarin Littafi Mai Tsarki yana da daɗi sosai kuma yana ƙarfafa bangaskiya, amma ka kula kada ka yarda su sha kan lokacin da ya kamata ka yi amfani da shi ka shirya taro na ikilisiya. Taro wata hanya ce da Jehobah yake koyar da mu ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Amma, yin ƙarin bincike zai sa ka yi kalamai masu ma’ana a taro, alal misali, a Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya ko kuma a lokacin darussa daga Littafi Mai Tsarki na mako-mako a Makarantar Hidima ta Allah.
18. Me ya sa ƙwazon da aka sa a bincika al’amura “zurfafa na Allah” yake da muhimmanci?
18 Yin nazarin Kalmar Allah sosai zai taimaka mana mu kusanci Jehobah. Don ya nuna muhimmancin irin wannan nazarin, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hikima, kamar dukiya, kāriya ce; amma fikon sani ke nan, hikima ta kan kiyaye ran mai-ita.” (Mai-Wa’azi 7:12) Saboda haka, ƙwazo da ka sa a wurin fahimtar abubuwa na ruhaniya yana da muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya yi wa waɗanda suka ci gaba da bincike alkawari cewa za su “ruski sanin Allah.”—Misalai 2:4, 5.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene al’amura “zurfafa na Allah?”
• Me ya sa bai dace mu daina nazarin zurfafan al’amura ba?
• Me ya sa aka bayyana wa dukan Kiristoci al’amura “zurfafa na Allah?”
• Ta yaya za ka amfana sosai a nazarin al’amura “zurfafa na Allah?”
[Hoto a shafi na 24]
Yaushe ne Yesu ya zama Almasihu?
[Hoto a shafi na 27]
Iyaye za su iya ba yaransu abin da za su yi bincike a kai don shirin nazari na iyali