Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/15 pp. 20-24
  • “Ruhu Yana Binciken . . . Zurfafa Na Allah”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ruhu Yana Binciken . . . Zurfafa Na Allah”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • A Ƙarni na Farko
  • A Zamani na Ƙarshe
  • Amfanin da Ake Samu Daga Matsayin Ruhun A Yau
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Bincika Al’amura “Zurfafa Na Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ruhun Allah Yana Ba Mu Tabbaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/15 pp. 20-24

“Ruhu Yana Binciken . . . Zurfafa Na Allah”

“Ruhu yana binciken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.”—1 KOR. 2:10.

1. Wane matsayi na ruhu mai tsarki ne Bulus ya nanata a 1 Korintiyawa 2:10, kuma waɗanne tambayoyi suka taso?

MUNA godiya don aikin da ruhu mai tsarki na Jehobah yake yi! Nassosi sun kira ruhun, mai taimako, kyauta, mai shaida, da mai roƙo dominmu. (Yoh. 14:16; A. M. 2:38; Rom. 8:16, 26, 27) Manzo Bulus ya nanata wani aiki na musamman da ruhu mai tsarki yake yi: “Ruhu yana binciken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.” (1 Kor. 2:10) Hakika, Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya bayyana gaskiya ta ruhaniya masu wuya. Idan babu wannan taimakon, ba za mu iya fahimtar nufe-nufen Jehobah ba. (Karanta 1 Korintiyawa 2:9-12.) Amma, tambayoyi da yawa sun taso: Ta yaya ne ‘ruhun yake bincika zurfafa na Allah’? Ta hanyar waye ne Jehobah ya bayyana waɗannan abubuwan a ƙarni na farko A.Z.? Ta yaya da kuma ta hanyar waye ne ruhun yake binciken waɗannan zurfafan abubuwa a zamaninmu?

2. A waɗanne hanyoyi biyu ne ruhun zai yi aiki?

2 Yesu ya nuna hanyoyi biyu da ruhun zai yi aiki. Gab da mutuwarsa, ya gaya wa manzanninsa: “Mai-taimako, wato Ruhu Mai-tsarki, wanda Uban zai aiko a cikin sunana, zai koya muku abubuwa duka, ya tuna muku kuma dukan abin da na faɗa muku.” (Yoh. 14:26) Ruhu mai tsarki zai zama mai koyarwa da mai tunasarwa. A matsayin mai koyarwa, zai taimaka wa Kiristoci su fahimci abubuwan da a dā ba su fahimta ba. A matsayin mai tunasarwa, zai taimaka musu su tuna kuma su yi amfani da abin da aka bayyana musu a hanyar da ya kamata.

A Ƙarni na Farko

3. Waɗanne kalaman Yesu ne suka nuna cewa za a bayyana “zurfafa na Allah” a hankali?

3 Yesu da kansa ya koya wa almajiransa gaskiya masu yawa da ba su sani ba a dā. Amma, har ila suna da abubuwa da yawa da za su koya. Yesu ya gaya wa manzannin: “Ina da sauran zance da yawa da zan yi maku tukuna, amma ba ku iya ku ɗauke su yanzu ba. Amma sa’adda shi, Ruhu na gaskiya, ya taho, zai bishe ku cikin dukan gaskiya.” (Yoh. 16:12, 13) Ta hakan Yesu ya nuna cewa ta wurin ruhu mai tsarki, za a bayyana zurfafan al’amura na ruhaniya a hankali.

4. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., ta yaya ruhu mai tsarki ya zama kamar mai koyarwa da mai tunasarwa?

4 A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., aka zubo “ruhu na gaskiya” a kan Kiristoci misalin 120 da suka taru a Urushalima. Da akwai tabbaci na zahiri da kuma kalamai da aka furta da suka nuna hakan. (A. M. 1:4, 5, 15; 2:1-4) Almajiran sun yi magana a harsuna dabam dabam game da “ayyuka masu-girma na Allah.” (A. M. 2:5-11) Lokaci ya yi yanzu da za a bayyana musu sabon abu. Annabi Joel ya annabta cewa za a zubo da wannan ruhu mai tsarki. (Joel 2:28-32) Masu kallo suna ganin cikawar a hanyar da ba su yi zato ba, kuma manzo Bitrus ya yi ja-gora wajen bayyana wannan aukuwa. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:14-18.) Ta wannan hanyar, ruhu mai tsarki ya zama kamar malami ta wajen bayyana wa Bitrus cewa abin da almajiran suka gani cikawa ce ta annabcin nan na dā. Ruhun ya kuma zama mai tunasarwa, domin Bitrus ya yi ƙaulin zabura biyu da Dauda ya rubuta da kuma littafin Joel. (Zab. 16:8-11; 110:1; A. M. 2:25-28, 34, 35) Hakika, abin da dukan waɗanda suka taru suka gani kuma suka ji zurfafan al’amura ne na Allah.

5, 6. (a) Bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., waɗanne tambayoyi masu muhimmanci game da sabon alkawari ne ake bukatan a amsa? (b) Ta wurin wanene aka ta da waɗannan batutuwa, kuma yaya aka tsai da shawarwari?

5 Har ila, da akwai batutuwa da yawa da Kiristoci na ƙarni na farko suke bukatan ƙarin bayani a kansu. Alal misali, da akwai tambayoyi game da sabon alkawari da aka kafa a wannan ranar Fentakos. Yahudawa da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci ne kawai suke cikin wannan sabon alkawarin? ’Yan Al’ummai za su iya shiga kuma a shafa su da ruhu mai tsarki kuwa? (A. M. 10:45) Maza ’yan Al’ummai suna bukatan su yi kaciya tukuna ne kuma su miƙa kai ga Dokar Musa? (A. M. 15:1, 5) Waɗannan tambayoyi suna da muhimmanci sosai. Ana bukatan ruhun Jehobah don a bincika waɗannan zurfafan al’amura. Amma, ta wurin wa zai yi aiki?

6 ’Yan’uwa maza masu hakki ne suka ta da waɗannan batutuwan da ke bukatan amsoshi. Bitrus, Bulus, da Barnaba suna wajen taron da aka yi da hukumar mulki inda aka tattauna batun kaciya kuma suka faɗi yadda Jehobah yake mai da hankali ga ’yan Al’ummai da ba su yi kaciya ba. (A. M. 15:7-12) Bayan da suka bincika wannan tabbacin tare da abin da aka faɗa a Nassosi na Ibrananci da taimakon ruhu mai tsarki, hukumar mulki ta tsai da shawara. Sai suka sanar da ikilisiyoyi ta hanyar wasiƙa game da shawararsu.—Karanta Ayyukan Manzanni 15:25-30; 16:4, 5; Afis. 3:5, 6.

7. Ta wace hanya aka bayyana koyarwa mai wuya?

7 An kuma ba da ƙarin bayani a kan batutuwa da yawa ta wurin rubuce-rubucen Yohanna, Bitrus, Yakubu, da Bulus. Amma a wani lokaci bayan an kammala Nassosin Kirista, an kawar da baiwar annabci da kuma bayyana ilimi ta hanyar mu’ujiza. (1 Kor. 13:8) Ruhun zai ci gaba da aikatawa a matsayin mai koyarwa da mai tunasarwa ne? Zai ci gaba da taimaka wa Kiristoci su bincika zurfafan al’amura na Allah? Annabci ya nuna cewa zai ci gaba da yin hakan.

A Zamani na Ƙarshe

8, 9. Su wanene za su “haskaka” da fahimi na ruhaniya a lokaci na ƙarshe?

8 Da yake magana game da lokaci na ƙarshe, wani mala’ika ya annabta: “Waɗanda ke da hikima kuma za su haskaka kamar walƙiyar sararin sama; waɗanda suka juya mutane da yawa kuma zuwa adalci za su haskaka kamar taurari har abada abadin. . . . ilimi kuma za ya ƙaru.” (Dan. 12:3, 4) Su waye ne za su samu hikima, kuma su waye ne za su haskaka? A kwatancinsa na alkama da zawan, Yesu ya faɗi abin da zai taimaka mana mu amsa tambayoyin. Da yake magana game da “matuƙar zamani,” ya ce: “Sa’annan masu-adalci za su haskaka kamar rana a cikin mulkin Ubansu.” (Mat. 13:39, 43) A bayaninsa, Yesu ya bayyana cewa “masu adalci” su ne “’ya’yan mulki,” wato, shafaffun Kiristoci.—Mat. 13:38.

9 Dukan shafaffun Kiristoci ne za su “haskaka”? E, a wani azanci, domin dukan Kiristoci ne za su yi aikin wa’azi, almajirantarwa, da kuma ƙarfafa juna a taro. Shafaffu ne za su kafa misalin. (Zech. 8:23) Amma, ƙari ga hakan, za a bayyana zurfafan al’amura a lokaci na ƙarshe. An saka ‘hatimi’ a kan annabcin da Daniel ya rubuta har sai wannan lokacin. (Dan. 12:9) Ta yaya kuma ta wurin wanene ruhun zai bincika waɗannan zurfafan al’amura?

10. (a) Ta wurin waye ne ruhun yake bayyana zurfafan gaskiya a lokaci na ƙarshe? (b) Ka bayyana yadda aka ba da ƙarin bayani game da koyarwar haikali na ruhaniya mai girma na Jehobah.

10 Sa’ad da lokaci ya zo da za a ba da ƙarin bayani a kan wani batu na ruhaniya a zamaninmu, ruhu mai tsarki yana taimaka wa wakilan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da suka ƙware a hedkwata na duniya don su fahimci zurfafan gaskiya da ba su fahimta ba a dā. (Mat. 24:45; 1 Kor. 2:13) Hukumar Mulki gabaki ɗaya suna duba binciken da aka yi a kan wani batu kuma su yanke shawarar ko ana bukatan a yi gyara. (A. M. 15:6) Sai su wallafa abin da suka koya don dukan ’yan’uwan su amfana. (Mat. 10:27) Da shigewar lokaci, wataƙila za a bukaci ba da ƙarin haske, kuma sai a bayyana shi cikin gaskiya.—Ka duba akwatin nan “Yadda Ruhun ya Bayyana Ma’anar Haikali na Ruhaniya.”

Amfanin da Ake Samu Daga Matsayin Ruhun A Yau

11. Ta yaya dukan Kiristoci a yau suke amfana daga matsayin ruhu mai tsarki wajen bayyana zurfafan al’amura na Allah?

11 Dukan Kiristoci masu aminci suna amfana daga matsayin ruhu mai tsarki wajen bayyana zurfafan al’amura na Allah. Kamar Kiristoci na ƙarni na farko, mu ma a yau muna nazari kuma daga baya mu tuna kuma mu yi amfani da bayanin da ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu fahimta. (Luk 12:11, 12) Ba ma bukatan mu yi makaranta sosai domin mu fahimci zurfafan koyarwa na ruhaniya da aka wallafa. (A. M. 4:13) Ta yaya za mu kyautata fahiminmu na zurfafan al’amura na Allah? Ga wasu shawarwari.

12. A wane lokaci ne ya kamata mu yi addu’a don samun ruhu mai tsarki?

12 Ka yi addu’a don samun ruhu mai tsarki. Kafin mu bincika wani batu na Nassi, ya kamata mu fara yin addu’a mu roƙi Allah don ruhu mai tsarki ya yi mana ja-gora. Abin da ya kamata mu yi ke nan ko da mu kaɗai ne ko kuma ba mu da isashen lokaci. Babu shakka, irin waɗannan roƙe-roƙen cikin tawali’u za su sa Ubanmu na samaniya farin ciki. Kamar yadda Yesu ya nuna, Jehobah zai ba mu ruhunsa a sake idan muka roƙe shi da dukan zuciyarmu.—Luk 11:13.

13, 14. Wane matsayi ne yin shiri don taro yake da shi wajen fahimtar zurfafan al’amura na Allah?

13 Ka shirya taro. Muna samun ‘abinci a lotonsa’ ta wurin rukunin bawan nan. “Bawan nan” yana cika hakkinsa ta wajen yin tanadin bayanai da aka ɗauko daga Nassi da kuma shirya tsarin ayyuka na nazari da taro. Akwai dalilai da aka bincika sosai da suka sa aka ce “’yan’uwanci” su tattauna wasu bayanai. (1 Bit. 2:17; Kol. 4:16; Yahu. 3) Muna ba da haɗin kai ga ruhu mai tsarki sa’ad da muka yi iyakar ƙoƙarinmu mu bi shawarwarin da aka ba da.—R. Yoh. 2:29.

14 Sa’ad da muke shirya taron Kirista, yana da kyau mu karanta Nassosi da aka nuna kuma mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda kowannensu ya shafi batun da ake bincikawa. Yin hakan zai ci gaba da zurfafa fahiminmu na Littafi Mai Tsarki a hankali. (A. M. 17:11, 12) Karanta nassosi zai taimaka mana mu tuna da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da taimakon ruhu mai tsarki. Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu tuna inda ayar take a cikin shafi na Littafi Mai Tsarki.

15. Me ya sa za mu riƙa karanta dukan littattafai da aka wallafa, kuma ta yaya kake cim ma hakan?

15 Ka riƙa karanta dukan littattafai da aka wallafa. Akwai wasu littattafan da aka wallafa da ba a tattaunawa a taronmu, amma an shirya su ne don amfaninmu. Har ma da mujallunmu da ake rarraba wa mutanen waje, an shirya su da mu a zuciya. A wannan duniya da take cike da harkoki, sau da yawa sai mun jira wani ko kuma wani abu. Idan muna ɗauke da littattafai da ba mu karanta ba ko kuma mun karanta shi sama sama, za mu iya yin amfani da wannan zarafi mu karanta wani sashe a ciki. Wasu suna sauraron faifai na littattafanmu da aka ɗauka yayin da suke tafiya ko kuma suke cikin mota. Tun da yake an bincika su sosai kuma an rubuta su ne domin kowa ya more, dukan waɗannan littattafan suna zurfafa fahiminmu na batutuwa na ruhaniya.—Hab. 2:2.

16. Wane amfani za mu samu ta wajen rubuta tambayoyi da suka faɗo mana a zuciya da kuma bincika su?

16 Bimbini. Sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma littattafan da suka bayyana shi, ka ba da lokaci ka yi tunani. Idan ka bi tsarin koyarwa da ke cikinsa, tambayoyi za su iya tasowa a zuciyarka. Kana iya rubuta tambayoyin kuma ka yi bincike a kansu sa’ad da ka samu lokaci. Sau da yawa sai mun biɗi abubuwan da muke sha’awa ne za mu yi bincike mai zurfi sosai. Fahimin da muka samu zai zama sashen dukiyarmu da za mu riƙa amfani da ita idan bukata ta kama.—Matt. 13:52.

17. Wane tsarin nazari na kanka ko na iyali kake bi?

17 Ka keɓe lokaci don bauta ta iyali. Hukumar Mulki ta ƙarfafa dukanmu mu keɓe lokaci da yamma ko wani lokaci dabam a kowanne mako don nazari na kanmu ko na iyali. Tsarin taronmu da aka daidaita ya ba mu zarafin yin amfani da wannan shawarar. Menene kake bincikawa a lokacin Bauta ta Iyali da yamma? Wasu suna karanta Littafi Mai Tsarki, su yi bincike a kan ayoyin da ba su fahimta ba kuma su rubuta taƙaitaccen bayani a kansu a cikin Littafinsu Mai Tsarki. Iyalai da yawa suna ba da lokaci su bayyana yadda darassin ya shafi iyalinsu. Wasu shugabannin iyalai suna zaɓan batutuwan da suke ganin iyalinsu tana bukatan ta tattaunata ko kuma wanda ya shafi darussa ko tambayoyin da iyalin take son ta tattauna. Babu shakka, da shigewar lokaci za ka iya yin tunanin wasu batutuwan da za ku bincika.a

18. Me ya sa bai kamata mu daina yin nazarin zurfafan gaskiyar Kalmar Allah ba?

18 Yesu ya ce ruhun zai aikata a matsayin mataimaki. Saboda haka bai kamata mu daina yin nazarin zurfafan gaskiya ta Kalmar Allah ba. Irin wannan gaskiyar sashe ne mai tamani na “sanin Allah,” kuma an gayyace mu mu bincika ta. (Karanta Misalai 2:1-5.) Sun bayyana abubuwa da yawa game da “abin da Allah ya shirya wa waɗanda ke ƙaunarsa.” Yayin da muke ƙoƙarin mu ƙara koyo game da Kalmar Jehobah, ruhu mai tsarki zai taimake mu, domin “ruhu yana binciken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.”—1 Kor. 2:9, 10.

[Hasiya]

a Ka duba Hidimarmu ta Mulki na Oktoba 2008, shafi na 8, a Turanci.

Yaya Za Ka Amsa?

• A waɗanne hanyoyi biyu ne ruhun yake taimaka mana mu bincika “zurfafa na Allah”?

• Ta wurin wa ruhu mai tsarki ya bayyana zurfafan gaskiya a ƙarni na farko?

• Ta yaya ruhu mai tsarki yake aiki don ya daidaita bayani a yau?

• Menene za ka yi don ka amfana daga hakkin ruhun?

[Akwati da ke shafi na 22]

Yadda Ruhun Ya Bayyana Ma’anar Haikali na Ruhaniya

Ɗaya daga cikin “zurfafa na Allah” da aka bayyana a ƙarni na farko shi ne cewa mazauni kuma daga baya haikalai suna wakiltar al’amura na ruhaniya masu girma da za su faru a nan gaba. Bulus ya kira su “mazauni na gaske, wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.” (Ibran. 8:2) Wannan haikali ne na ruhaniya mai girma, wato, hanyar kusantar Allah da ta yiwu ta wurin hadaya da tsarin firistanci na Yesu Kristi.

An kafa “mazauni na gaske” a shekara ta 29 A.Z., a lokacin da aka yi wa Yesu baftisma kuma Jehobah ya amince da shi ya zama cikakken hadaya. (Ibran. 10:5-10) Bayan mutuwarsa da tashinsa daga matattu, Yesu ya shiga Wuri Mafi Tsarki a haikali na ruhaniya kuma ya miƙa amfanin hadayarsa “a gaban fuskar Allah.”—Heb. 9:11, 12, 24.

A wani wuri, manzo Bulus ya rubuta cewa Kiristoci shafaffu ‘suna girma sai suka zama haikali mai-tsarki cikin Ubangiji.’ (Afis. 2:20-22) Wannan haikalin ɗaya ne da “mazauni na gaske” da ya kwatanta daga baya a wasiƙarsa zuwa ga Ibraniyawa? Shekaru da yawa yanzu, bayin Jehobah suna tsammanin cewa duk ɗaya ne. Kamar dai ana shirya shafaffu Kiristoci a duniya su zama ‘duwatsu’ a haikalin Jehobah na samaniya.—1 Bit. 2:5

Amma, a wajen shekara ta 1971, masu hakki da suke cikin rukunin bawa mai aminci suka soma ganewa cewa haikalin da Bulus ya yi maganarsa a Afisawa ba zai zama babban haikali na ruhaniya mai girma na Jehobah ba. Idan shafaffu Kiristoci da aka ta da daga matattu suna cikin “mazauni na gaske” hakan zai fara kasancewa bayan tashinsu daga matattu ya soma a lokacin “zuwan Ubangiji.” (1 Tas. 4:15-17) Amma sa’ad da yake nuni ga mazauni, Bulus ya rubuta: “Wannan mazauni misali ne domin wannan zamani da yake nan a yanzu.”—Ibran. 9:9, NW.

Ta wurin gwada waɗannan da wasu nassosi a hankali, mun fahimci cewa ba wai ana cikin gina haikali na ruhaniyar ba ne ba kuma shafaffu Kiristoci ba ‘duwatsu’ ba ne da aka shirya a duniya don gina wannan haikalin. Maimakon haka, Kiristoci shafaffu suna hidima ne a farfajiya da kuma Wuri Mai Tsarki a haikali na ruhaniya, suna yi wa Allah “hadaya ta yabo” a kullum.—Ibran. 13:15.

[Hoton da ke shafi na 23]

Ta yaya za mu kyautata fahiminmu na “zurfafa na Allah”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba