Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 p. 12
  • “Ba Shi da Nisa da Kowane Ɗayanmu”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ba Shi da Nisa da Kowane Ɗayanmu”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Zai Kusace Ka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • ‘Ka Kusaci Allah’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Ci Gaba da ‘Mai da Hankali ga Koyarwa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 p. 12

Ka Kusaci Allah

“Ba Shi da Nisa da Kowane Ɗayanmu”

Ayukan Manzanni 17:24-27

IDAN aka kwatanta su da wannan duniyar mai girma, ’yan adam ba su taka kara sun karya ba. Wataƙila ka taɓa tambayar kanka, ‘Zai yiwu mutum ya kasance da dangantaka na kud da kud da Allah Maɗaukaki?’ Hakan zai yiwu ne kawai idan Allah, wanda sunansa Jehobah, yana son mu kusance shi. Yayi hakan kuwa? Za a iya samun amsar mai ƙarfafawa a cikin kalamai masu daɗi da manzo Bulus ya rubuta wa maza masu ilimi da ke Atina, kamar yadda aka rubuta a Ayukan Manzanni 17:24-27. Yi la’akari da abubuwa guda huɗu da Bulus ya ce game da Jehobah.

Na ɗaya, Bulus ya ce Allah “ya yi duniya da abin da ke ciki duka.” (Aya ta 24) Abubuwa masu kyau dabam dabam da suke sa rayuwa ta yi daɗi sun nuna tunani da kuma ƙaunar Mahaliccinmu. (Romawa 1:20) Zai zama wawanci a yi tunanin cewa wannan Allahn zai nisanta kansa daga abubuwan da yake ƙauna.

Na biyu, Jehobah ya “ba kowa rai, da numfashi, da abu duka.” (Aya ta 25) Jehobah ne Mai Kiyaye rai. (Zabura 36:9) Iska, ruwa, da kuma abinci waɗanda abubuwa ne masu muhimmanci ga rayuwa duk kyauta ce daga Mahaliccinmu. (Yaƙubu 1:17) Ya dace mu gaskata cewa Allahnmu mai karimci zai nisanta kansa daga wurinmu, kuma ya ƙi ba mu damar sanin ko shi wanene kuma mu kusance shi?

Na uku, Allah ‘ya yi dukan al’umman mutane daga tushe ɗaya.’ (Aya ta 26) Jehobah ba ya nuna wariya ko son kai. (Ayukan Manzanni 10:34) Ya halicci mutum “ɗaya,” Adamu, wanda dukan al’ummai, launi dabam dabam suka fito daga wurinsa. Nufin Allah ne “dukan mutane su tsira.” (1 Timothawus 2:4) Saboda haka, zarafin kusantarsa yana buɗe ga kowannenmu ko da menene kalar fatarmu, ƙasarmu, ko yarenmu.

Na ƙarshe, Bulus ya faɗi gaskiya mai ƙarfafawa: Jehobah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (Aya ta 27) Ko da yake yana da girma sosai, Jehobah bai da nisa ga mutanen da suke son su kusance shi da gaske. Kalmarsa ta ba mu tabbaci cewa, ba shi da nisa, amma “yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi.”—Zabura 145:18.

Daga abin da Bulus ya faɗa, a bayyane yake cewa Allah yana son mu kusance shi. Amma yana ba da irin wannan damar ne kawai ga waɗanda suka ‘neme’ shi kuma suka “lallaba” su same shi, in ji Bulus. (Aya ta 27) Wani bincike don masu fassara Littafi Mai Tsarki ya ce “waɗannan aikatau wataƙila suna nufin abubuwan da za su yiwu ne . . . ko kuwa fatan da za a iya cikawa.” Alal misali: A ce kana cikin duhu a cikin ɗakinka, kana iya lallaɓawa ka nemi inda ake kunna wuta ko kuwa inda kofa take, amma ka san cewa za ka gane wurin. Hakazalika, idan muka nemi Allah da gaske kuma muka lallaɓa don mu same shi, muna da tabbaci cewa za mu dace. Bulus ya ba mu tabbacin cewa za mu “same shi.”—Aya ta 27.

Kana ɗokin kusantar Allah? Idan ka “nemi Allah” cikin bangaskiya kuma ka ‘lallaba ka same shi,’ ba za ka yi aikin banza ba. Samun Jehobah bai da wuya, domin “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba