Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 8/15 pp. 8-12
  • Ka Kasance Da Aminci Da Zuciya Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Aminci Da Zuciya Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ni Ma In Ba Ka Lada”
  • Ka yi “Wadar Zuci”
  • Tsohon Annabi Ya ‘Yi Masa Ƙarya’
  • Ya “Koma Tare da” Tsohon
  • Ka Zama Mai Filako
  • Ka Kuduri Aniyar Kasancewa da Aminci
  • Jehobah Ba Zai Yashe Amintattunsa Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Kai Kaɗai Ne Mai Aminci’
    Ka Kusaci Jehobah
  • An Raba Mulkin
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 8/15 pp. 8-12

Ka Kasance Da Aminci Da Zuciya Ɗaya

Zan “yi tafiya cikin gaskiyarka: ka daidaita zuciyata ta ji tsoron sunanka.”—ZAB. 86:11.

1, 2. Menene Zabura 86:2, 11, ta ce zai taimake mu mu riƙe amincinmu ga Jehobah a lokacin da muke fuskantar gwaji? (b) Yaushe ne ya kamata mu kafa aminci?

M E YA sa wasu Kiristoci da suka kasance da aminci shekaru da yawa duk da cewa an tsare su a kurkuku ko kuma sun fuskanci matsi daga baya suke faɗa wa son abin duniya? Amsar ta dangana da yanayin zuciyarmu. Zabura sura 86 ta ce, aminci yana da alaƙa da zuciyar da ba a rabe take ba. Dauda ya yi addu’a: “Ka kiyaye raina; gama ni mai-ibada ne: ka ceci bawanka wanda ya ke dogara gareka.” Ya daɗa addu’a cewa: “Ya Ubangiji, ka koya mini tafarkinka; ni kuwa in yi tafiya cikin gaskiyarka: ka daidaita zuciyata ta ji tsoron sunanka.”—Zab. 86:2, 11.

2 Idan ba mu dogara ga Jehobah da duka zuciyarmu ba, wasu abubuwa za su raunana amincinmu ga Allah na gaskiya. Sha’awoyi na son kai suna kama da nakiya da aka binne a hanyar da muke bi. Ko da yake mun riƙe amincinmu ga Jehobah a lokacin gwaji, muna iya faɗa wa tarkunan Shaiɗan. Yana da muhimmanci mu kasance da aminci ga Jehobah yanzu da zuciya ɗaya, kafin mu fuskanci gwaji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa.” (Mis. 4:23) Za mu koyi darussa masu kyau game da wannan daga abin da ya faru da wani annabi daga Yahuda wanda Jehobah ya aika zuwa wajen Sarki Jeroboam na Isra’ila.

“Ni Ma In Ba Ka Lada”

3. Menene Jeroboam ya yi sa’ad da annabin Allah ya sanar masa da saƙon hukunci?

3 Ka yi tunanin abin da ya faru. Mutumin Allah ya sanar da saƙon hukunci ga Sarki Jeroboam, wanda ya kafa bautar maraƙi a masarauta kabilu goma ta arewa a Isra’ila. Sarkin ya yi haushi sosai. Ya sa mutanensa su kama manzon. Amma Jehobah yana tare da bawansa. Nan da nan, hannun da sarkin ya miƙa wa manzon don haushi ya shanye, haikalin da ake amfanin da shi don bautar ƙarya kuma ya tsage. Nan da nan sai halin Jeroboam ya canja. Ya roƙi mutumin Allah: “Ka roƙi alherin Ubangiji Allahnka yanzu a kaina, a yi mani addu’a kuma, domin a mayas mani da lafiyar hannuna.” Annabin ya yi addu’a, kuma hannun sarkin ya warke.—1 Sar. 13:1-6.

4. (a) Me ya sa kyautar sarkin gwaji ne na aminci ga annabin? (b) Menene annabin ya ce?

4 Sai Jeroboam ya ce wa mutumin Allah na gaskiya: “Ka zo gida tare da ni, ƙa wartsake, ni ma in ba ka lada.” (1 Sar. 13:7) Menene annabin zai yi yanzu? Zai ƙi kyautar sarkin ne tun da bai daɗe ba ya sanar masa da saƙon hukunci? (Zab. 119:113) Ko kuma zai je ne tun da yake sarkin ya nuna kamar ya tuba? Jeroboam yana da kuɗin da zai kashe wa abokansa. Idan da annabin Allah yana sha’awar abin duniya a zuciyarsa, da kyautar sarkin za ta zama masa gwaji mai tsanani. Amma, Jehobah ya umurce annabin: “Ba za ka ci gurasa, ko sha ruwa, ba kuwa za ka komo ta hanyar da ka zo ba.” Sai annabin ya ba da wannan amsa: “Ko ka ba ni rabin gidanka, ba ni shiga tare da kai, ba ni kuwa cin gurasa ko shan ruwa a wurin nan ba.” Kuma annabin ya bar Bethel ta wata hanya. (1 Sar. 13:8-10) Wane darassi ne matakin da annabin ya ɗauka ya koya mana game da kasancewa da aminci?—Rom. 15:4.

Ka yi “Wadar Zuci”

5. Ta yaya ne abin duniya ya zama batun aminci?

5 Son abin duniya batun aminci ne. Za mu iya dogara ga alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai yi mana tanadin abubuwan da muke bukata kuwa? (Mat. 6:33; Ibran. 13:5) Za mu iya yin rayuwa ba tare da sa ƙwazo a samun abubuwan rayuwa ko ta yaya da ba za mu iya samu ba yanzu kuwa? (Ka karanta Filibbiyawa 4:11-13.) Za mu iya ƙyale abubuwa na ruhaniya don mu sami abin da muke bukata yanzu? Kasancewa da aminci ga Jehobah ta zama abu na farko a rayuwarmu kuwa? Amsarmu ta dangana ko muna hidimar Allah da zuciya ɗaya ko a’a. Manzo Bulus ya rubuta: “Amma ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma: gama ba mu shigo da kome cikin duniya ba, ba kuwa za mu iya fita cikinta da kome ba; amma da shi ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.”—1 Tim. 6:6-8.

6. Wace “kyauta” ce za a iya ba mu, kuma menene zai taimake mu mu yanke shawara ko za mu karɓa?

6 Alal misali, shugabanmu na wajen aiki zai iya ƙara mana girma da albashi mai kyau da kuma wasu albarkatai. Ko kuma mun fahimci cewa za mu fi samun kuɗi idan muka ƙaura zuwa wata ƙasa mu yi aiki. Da farko, irin wannan zarafin zai iya kasance albarka ne daga Jehobah. Amma kafin mu yanke shawara, ya kamata mu bincika dalilin yin haka. Abin da ya kamata mu tambayi kanmu shi ne, “Ta yaya ne shawarata zai shafi dangantakata da Jehobah?”

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu kawar da sha’awoyi na son abin duniya?

7 Duniyar Shaiɗan tana gabatar da abin duniya. (Ka karanta 1 Yohanna 2:15, 16.) Nufin Iblis shi ne ya lalata zuciyarmu. Saboda haka, ya kamata mu kasance a faɗake mu fahimci kuma mu cire sha’awar abin duniya a zuciyarmu. (R. Yoh. 3:15-17) Bai yi wa Yesu wuyan ƙin kyautar da Shaiɗan ya yi masa na dukan mulkoki na duniya ba. (Mat. 4:8-10) Ya yi gargaɗi: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luk 12:15) Aminci zai taimake mu mu dogara ga Jehobah maimakon kanmu.

Tsohon Annabi Ya ‘Yi Masa Ƙarya’

8. Ta yaya aka gwada amincin annabin Allah?

8 Da annabin Allah ya ci gaba da tafiyarsa zuwa gida da bai samu matsala ba. Amma, nan da nan ya fuskanci wani gwaji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wani tsofon annabi yana zaune a cikin Beth-el; sai ɗaya daga cikin ’ya’yansa ya zo ya faɗa masa dukan” abubuwan da suka faru ranan. Da ya ji abin da ya faru, sai tsohon ya ce musu su yi wa jakinsa sirdi don ya je ya tare annabin Allah. Ba da daɗewa ba, ya sadu da annabin yana hutawa a gindin babban itace kuma ya ce masa: “Ka komo gida tare da ni, ka ci gurasa.” Sa’ad da mutumin Allah ya ƙi, sai tsohon annabi ya ce masa: “Ni kuma annabi ne kamarka; wani mala’ika kuwa ya yi magana da ni ta wurin maganar Ubangiji, cewa, Ka dawo da shi cikin gidanka, domin ya ci gurasa, ya sha ruwa.” Amma Nassosi ya ce: “Ƙarya ya ke yi masa.”—1 Sar. 13:11-18.

9. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da masu cutar mutane, kuma su wanene suke cuta?

9 Ba mu san dalilin da ya sa tsohon annabin ya yi haka ba, amma ya yi ƙarya. Wataƙila tsohon a dā annabi ne mai aminci ga Jehobah. Amma, a wannan lokacin ƙarya yake yi. Nassosi ya haramta irin wannan hali. (Ka karanta Misalai 6:16, 17.) Masu cutar mutane suna ɓata dangantakarsu da Jehobah da kuma na wasu.

Ya “Koma Tare da” Tsohon

10. Yaya annabin Allah ya amsa gayyatar tsohon, kuma menene sakamakon hakan?

10 Ya kamata annabin daga Yahuda ya fahimci cewa wayo ne tsoho annabin yake yi. Da ya tambayi kansa, ‘Me ya sa Jehobah zai aika mala’ika wurin wani ya ba shi sabon umurni?’ Da annabin ya gaya wa Jehobah ya yi masa bayyani dalla-dalla, amma Nassosi bai faɗa ba cewa ya yi hakan ba. Maimakon haka, “ya fa koma tare da [tsohon], ya ci gurasa cikin gidansa, ya sha ruwa.” Jehobah bai yi farin ciki ba. Sa’ad da annabi da aka ruɗi ya kama hanyarsa zuwa Yahuda, zaki ya haɗu da shi kuma ya kashe shi. Hakan ya kawo ƙarshen aikin annabcinsa!—1 Sar. 13:19-25.a

11. Wane misali mai kyau ne Ahijah ya kafa?

11 A wani ɓangare kuma, annabi Ahijah da aka aika ya je ya naɗa Jereboam sarki, ya kasance da aminci har sa’ad da ya tsufa. Sa’ad da Ahijah ya tsufa kuma ya makance, Jeroboam ya aiki matarsa ya je ya tambayi Ahijah abin da zai faru da ɗansu da yake ciwo. Da gaba gaɗi Ahijah ya annabta cewa ɗan Jeroboam zai mutu. (1 Sar. 14:1-18) Ahijah ya samu albarka masu yawa har da gatar kasancewa a cikin hurarriyar Kalmar Allah. Ta yaya? Ezra ya yi amfani da rubuce-rubucensa wajen goyon bayan bayaninsa.—2 Laba. 9:29.

12-14. (a) Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da annabin? (b) Ka ba da bayanin abin da ya sa za a mai da hankali da kuma addu’a game da shawara da ke bisa Littafi Mai Tsarki da dattawa suka bayar.

12 Littafi Mai Tsarki bai faɗi abin da ya sa annabin bai tambayi Jehobah ba kafin ya koma ya je ya ci kuma ya sha tare da tsohon ba. Tsohon ya gaya masa abin da yake son ya ji ne? Wane darassi ne muka koya? Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa farillan Jehobah sun yi daidai. Kuma muna bukatar mu kuduri aniya mu bi su ko da menene zai faru.

13 Wasu suna saurarar abin da suke so idan ya zo ga shawara. Alal misali, ana iya ba wa mai shela aiki da zai rage lokacin da yake zama da iyalinsa kuma ya rage ayyuka na ruhaniya. Yana iya ya nemi shawara wajen dattijo. Dattijon yana iya cewa ba zai gaya wa ɗan’uwan yadda zai tallafa wa iyalinsa ba. Dattijon yana iya tuna wa ɗan’uwan haɗari na ruhaniya da yake tattare da karɓan aikin da aka ba shi. Ɗan’uwan zai tuna abin da dattijo ya gaya masa da farko ne, ko kuwa zai yi la’akari sosai da abin da ya sake gaya masa? Babu shakka, ɗan’uwan yana bukatar ya fahimci abin da ya fi masa kyau a ruhaniya.

14 Ka yi la’akari da wani yanayi. Wata ’yar’uwa tana iya tambayar dattijo ko ta rabu da mijinta marar bi. Dattijon babu shakka zai bayyana mata cewa ita za ta tsai da shawarar rabu da shi ko a’a. Yana iya sake tuna mata shawarar Littafi Mai Tsarki a kan batun. (1 Kor. 7:10-16) ’Yar’uwar za ta yi tunani ne a kan abin da dattijon ya faɗa? Ko kuwa ta riga ta tsai da shawara a zuciyarta ta rabu da mijinta? Yana da kyau ta yi la’akari da gargaɗin Littafi Mai Tsarki ta wajen yin addu’a game da batun kafin ta tsai da shawara.

Ka Zama Mai Filako

15. Menene muka koya daga kuskuren annabin Allah?

15 Menene kuma za mu iya koya daga kuskuren da annabi daga Yahuda ya yi? Misalai 3:5 ta ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi.” Maimakon ya ci gaba da dogara ga Jehobah yadda ya yi a dā, a wannan lokacin annabi daga Yahuda ya dogara ga nasa ra’ayin. Kuskurensa ya sa ya yi hasarar ransa da kuma dangantakarsa da Allah. Abin da ya faru da shi ya nanata muhimmancin zama mai filako da kuma bauta wa Jehobah cikin aminci!

16, 17. Menene zai taimake mu mu kasance da aminci ga Jehobah?

16 Ra’ayin son kai yana iya yaudarar mu. “Zuciya ta fi komi rikici, ciwuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya: wa za ya san ta?” (Irm. 17:9) Don mu kasance da aminci ga Jehobah, dole ne mu ci gaba da aiki tuƙuru mu tuɓe halinmu na dā na zama masu girman kai da kuma dogara da kanmu. Kuma dole ne mu yafa sabon hali, “wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.”—Ka karanta Afisawa 4:22-24.

17 Misalai 11:2 ta ce: “Wurin masu-tawali’u akwai hikima.” Dogara da Jehobah yana taimaka mana mu guji yin kuskure mai tsanani. Alal misali, sanyin gwiwa zai iya sa kada mu yi tunanin kirki. (Mis. 24:10) Muna iya gajiya game da yin wani fanni na hidima kuma mu soma jin kamar abin da muka yi shekaru da yawa ya isa haka, lokaci ya kai da wasu za su ɗauki hakkin. Ko kuma mu ji cewa muna son mu yi rayuwa ta yau da kullum. Amma, yin “ƙoƙari” da kuma “yawaita cikin aikin Ubangiji” zai kāre zuciyarmu.—Luka 13:24; 1 Kor. 15:58.

18. Menene za mu yi idan ba mu san shawara da za mu tsai da ba?

18 Wani lokaci, muna bukatar mu tsai da shawarwari masu muhimmanci, kuma ba mu san tafarkin da za mu bi da ya dace ba. Ya kamata ne mu yi abin da muka ga ya fi kyau wajen magance wata matsala? Yana da kyau mu nemi taimakon Jehobah duk lokacin da muke fuskantar irin wannan yanayin. Yaƙub 1:5 ta ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari shi yi roƙo ga Allah, wanda ya ke bayar ga kowa a yalwace.” Ubanmu na samaniya zai ba mu ruhu mai tsarki da muke bukata don mu tsai da shawarwari masu kyau.—Ka karanta Luka 11:9, 13.

Ka Kuduri Aniyar Kasancewa da Aminci

19, 20. Menene ya kamata mu ƙuduri aniyar yi?

19 Shekaru da yawa da bayin Allah suka sha wahala bayan da Sulemanu ya bijire daga bauta ta gaskiya ya gwada amincinsu sosai. Hakika mutane da yawa sun bar gaskiya. Duk da haka, wasu sun kasance da aminci ga Jehobah.

20 Kowace rana, muna fuskantar zaɓe da shawarwari da suke gwada amincinmu. Mu ma muna iya nuna mu masu aminci ne. Bari koyaushe mu kasance da aminci ga Jehobah da zuciya ɗaya, da tabbacin cewa zai ci gaba da yi wa amintattunsa albarka.—2 Sam. 22:26; NW.

[Hasiya]

a Littafi Mai Tsarki bai faɗa ko Jehobah ya kashe annabin tsoho ba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu yi ƙoƙari mu kawar da sha’awoyi na son abin duniya daga zuciyarmu?

• Menene zai taimake mu mu kasance da aminci ga Jehobah?

• Ta yaya filako zai taimake mu mu kasance da aminci ga Allah?

[Hotuna a shafi na 9]

Yana maka wuya ka jimre wa gwaji?

[Hotuna a shafi na 10]

Za ka yi tunani sosai a kan shawarwari da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba